Showing 45001 words to 48000 words out of 94381 words
kuka, kukan dake kwance a ƙirjinta tun bayan
ɗ
aurin auren da su Kawu
Mallam suka kirata soro bayan dawowarsu, Kawu mallam
ɗ
in ya danƙa mata sadakinta dubu
ɗ
ari a hannunta, da kuma bayan tafiyarsu da ƴanuwansu na Niger suka ƙaraso suna fa
ɗ
in angon bai je ba... Kalaman da suka sata tambayar me yasa take yaudarar kanta ne? da
kansa yazo har nan ya garga
ɗ
e ta tun kafin komai yayi nisa don haka don ya fara nuna mata bala'in da ta kawo kanta cikinsa hakan ba komai bane.
Har bayan sallar magariba gidan nasu a cike yake, koina yayi kaca-kaca da ruwa da kuma abincin da aka zuzzubar,
sannan ga tarin wanke-wanke fal a gefe, don haka ana idar da sallar magaribar ƴanuwansu na Niger suka fara aiki kotaina, Allah ya taimaka da wutar Nepa don haka akwai haske koina.
A lokacin ne kuma motocin
ɗ
aukar amarya suka hallara!
***
A cikin motar
dake tafiya kan titin Lamido cresent,
ɗ
an karamin mayafin da Ruƙayya ta yafa akan doguwar rigarta ya zame ya sauka kan kafa
ɗ
unta, gashin kanta baƙi sidik da ya ha
ɗ
u dana ƙarin data nanna
ɗ
e cikin bun ya fito ta cikin hasken street lights da kuma na fitilar
motar ƴan sandan dake jiniya a bayansu, amma bata damu ba, hannayenta na rawa ne yayin da take kokarin sake kiran layin mahaifiyarta daya katse saboda rashin service yanzu da suke magana.
Ta samu kiran ya shiga a lokacin da muryar Ashraf dake tuƙa motar d
a kuma ta abokinsa Bilal da suke kira da B-man ta shiga kunnenta. Ashraf
ɗ
in ne ke tambayar abokin nasa idan har lambar wayar da suke jira an turo masa, amma a gajarce kawai ya bashi amsa yana girgiza kai.
"Ina jin ki Ruƙayya kuna ina?" Muryar mahaifiyar
tata ta shiga kunnenta daga cikin wayar.
Sai a lokacin ta jawo mayafin ta sake rufe kanta sannan tace.
"Maamah muna hanya, mun
ɗ
auko Bilal
ɗ
in yanzu zamu tafi can sabon garin, su Ibrahim ma sun je sun taho da police
ɗ
in suna bin mu a baya, muna jira ne
yanzu a turo masa da number wanda ya sani a gidan don a tabbatar idan tana nan."
Daga cikin wayar Hajiya Nafisa tace.
"Ko bata nan ku ƙarasa ku sami iyayenta ko kuma duk wani wanda zai iya baku bayani akanta, duk abinda ake ciki da kun isa you let me kno
w, yanzu zan kira Daddy in gaya masa."
Ta gya
ɗ
a kanta kafin kiran ya katse, idanunta na tafiya kan abokin Ashraf
ɗ
in dake danna wayarsa hankali a kwance, tsawon kwanaki kenan suna nemansa amma ba'a same shi ko a waya ba sai a yau da da wanin abokin Ashraf
ɗ
in ya kira cewar gashi nan ya dawo daga Ondo, don haka ba shiri suka taho har wajen da aka kwatanta musu yana nan, kuma cikin sa'a suka same shi. Amma don rashin mutunci irin nasa bai fito ya same su ba sai da suka yi kusan awa guda suna jiransa, har su
Ibrahim da Ahmad da suka je suka taho da police
ɗ
in da aka kai report wajensu, sannan ne ya fito da uzurin cewar wasu abubuwan yake kammalawa da baza su iya jira ba.
Kuma duk da irin tashin hankalin da yaji suna ciki da kuma ma babban labari na
ɓ
atan
ɗ
an
mutum guda, bai nuna ko a jikinsa ba bayan Allah ya sawwake guda din da ya furta. Ta sani cewa shi kansa Ashraf
ɗ
in yaji haushi amma bai nuna bane saboda abu suke nema daga wajensa dole sune a ƙasa, amma duk da haka ta fahimci cewa akwai wani abu ne da ya
faru da babu wannan kalmar ta abota a yanzu tsakaninsu.
Sai dai ba wannan ne a gabanta ba yanzu, a cikin kwanakin da suka gabata, zuciyarta ta mutu ta miƙe fiye da ƙirgan mai ƙirga, ƙarya ne ta iya kwatanta tashin hankalin da take ciki, tashi hankalin da
sai da ya shafi kowa a gidan nasu gaba
ɗ
aya, ya zamana ba abinda ake yi banda fafutukar neman Mary ko ta wacce hanya amma basu same tan ba, hatta mahaifinta dake can ƙasar Romania yana aikinsa kullum sai yayi waya tsakaninsa dasu da kuma ƴansanda akan abi
nda ake ciki.
Idanunta ka
ɗ
ai idan ka kalla sune shaidar rashin baccin da kuma na abincin da take ciki. Ta rantse a ranta fiye da sau shurin masaki cewar Mary zata gwammace bata zo duniya ba idan har suka kama ta, tunaninta baya iya lissafa abinda ya kama
ta tasa ayi mata.
Sun isa cikin unguwar ta sabon gari a lokacin da duhu ya riga yayi sosai, a lokacin kuma gabanta ya shiga fa
ɗ
uwa cike da tsananin tsoro ganin irin caku
ɗ
a
ɗɗ
un
layikan da suke wucewa da kuma mutanen cikinsu, zata yi rantsuwa ba adadi cewa
Mary ba zata ta
ɓ
a rabarsu ba inda ta san daga waje irin wannan take fitowa, amma a haka ta zauna tana kula da ƴarta tsawon watanni bakwai.
Kwatancen Bilal ya kai su har wai takurarren gidan da mutane ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, bata san l
okacin da ta dunƙule ƙarshen mayafinta akan bakinta ba yayin da kwalla ta shiga fitowa daga idanunta da suka riga suka ka
ɗ
a, zuciyarta bata iya kwatanta mata cewa Hamida tana wannan wurin ko ka
ɗ
an.
Ibrahim da Ahmad da suka fito daga motarsu bayan sun tsay
a suka bada shawarar cewa ta tsaya su suka shiga ciki, amma jikinta na rawa ta girgiza musu kai, ruhinta zai bisu ciki ne ko da ta tsaya
ɗ
in.
Ashraf da Ahmad ne suka fara shigewa gaba sai Bilal da kuma Ahmad, ita tana daga bayansu sai kuma ƴansanda biyar
dake rufa musu baya, warin iskar gidan ta fara shaƙa kafin ta fahimci girman da yake dashi daga ciki, ga tarin ƙofofi birjik daga kowanne gefe inda hayaniya ke fitowa kamar zata fasa kunne.
Kuma ganin ƴan sandan yasa hayaniyar gidan ta ƙaru har da masu i
hu suna shigewa
ɗ
akunansu, a tsakar gidan su Ashraf da kuma ƴansandan suka shiga tambayar cewa Mary suke nema, kuma wasu ƙattin inyamurai da su ka
ɗ
ai suka tsaya suka shaida musu cewar Maryn dake gidan sun fi mutum ashirin.
Koina a jikin Rukayya kawai rawa
yake yayin da take kallon ƙofofin
ɗ
akunan da dukkan fatanta na duniya, da ƙyar da kwatance aka samu wani a cikinsu ya gane wadda suke nema, kuma kai tsaye suka shaida musu cewa kwana biyu da suka wuce Maryn tare da iyayenta suka kwashe kayansu tsaf! suka
tafi garin su.
Sai da ƙyar ƴan sandan nan suka samu mutanen nan suka fito musu da wani tsoho da akace
ɗ
anuwansu ne. Kuma shima ganin ƴan sandan ya ru
ɗ
a shi, ya dinga rantsuwa bai san komai ba sai da yaga da gaske ana shirin tafiya dashi sannan yayi bayani
cewar ya san yarinyar da ake neman, kuma har da ita a dalilin barin su Mary garin bayan ciwon mahaifiyarsu.
Ruƙayya gabansa taje ta tsugunna a lokacin yayin da yake bayani da gur
ɓ
ataciyar hausarsa.
"Wani mutum ne anan yazo ya dauki yarinyar ya tafi dash
i, kuma Mary yace ya bawa yarinya maganin bacci mutumin zai kamata, kuma the madam she's serving zai ce ta
ɓ
atar da yarinya, ita bata san yadda zata yi ba, don haka sun kwashe kaya nasu sun tafi."
"Shi mutumin da yazo ya tafi da yarinyar waye shi?" Wani d
aga cikin
ɗ
ansandan ya tambaya tsaye akansa.
"Mary yace shine oga na inda babanshi Mr. Okafor yake aiki."
"Ka san wajen aikin nasa?"
Ya
ɗ
ago cike da tsoro yana kallon
ɗ
an sandan.
"Ka san wajen da baban nata yake aiki?"
Wannan karon Ruƙayya ce ta tamba
ya, muryarta na rawa da dukkan fatan na cewar amsar da zai bayar ta kasance abinda take son ji, kuma cikin abinda zata iya kira da sa'a, sai ya daga kansa yace.
"Eh ya sani, wajen inda ana..."
Bai karasa ba
ɗ
an sandan ya bashi umarnin tashi su tafi, jiki
nsa na rawa ya miƙe tsaye ya shige gaba, aka sanya shi a motar ƴan sandan bayan sun fita, suka fara yin gaba sannan su kuma suka shiga nasu motocin suka bi su.
Wannan karon Ibrahim ya shigo motarsu ya zauna a wajen Bilal da shi ya koma motar Ahmad, tana j
i kowannensu na waya, Ashraf da matarsa yana gaya mata inda suke, Ibrahim
ɗ
in kuma da Daddy yana yi masa bayanin abinda ya faru.
Fuskarta ta juya waje idanunta na bin fitulun kan titi ke haskawa akan gilashin da kuma fuskarta, hawaye take sharewa da gefen
mayafinta yayin da hannyenta ke rawa kamar zuciyarta, bata iya hango yadda zata kasance idan har bata sami Hamida a wajen nan ba.
Sun iso daidai gaban wani dogon gini mai
ɗ
auke da gilasaivda kuma fitulu kamar rana, akwai manya-manyan rubutu a sama wanda
bata iya karantawa ba saboda halin da take ciki da kuma ƙwallar da ta taru a idanunta. Ashraf da ya tsayar da motar ya juyo ya kalle ta, kuma ganin yadda take share hawaye yasa ya girgiza kansa yace.
"Stay inside, bari muje mu gani."
Da haka ya bu
ɗ
e ƙofa
r motar ya fita, Ibrahim na bin bayansa.
Sai kawai ta kifa kanta akan cinyoyinta ta shiga rera kukan da take kasancewa a cikinsa duk dare, gani take idan har ta rasa Hamida rayuwarta ta gama rushewa gaba
ɗ
aya, ba lallai ne ta samu fatan da dashi take gani
n zai sake gina rayuwarta ba.
Don samun Ma'aruf shine ƙarshen fatanta yanzu a duniya, bata hango komai a gabanta sama dashi, wani gefe na zuciyarta na jin cewa zata iya hakura da Hamidar ma idan har rayuwa zata iya dawo mata da Ma'aruf ta wata hanyar, am
ma ta san daga shi har iyayenta babu mai sake kallonta idan babu yarinyar, don haka ba zata ta
ɓ
a rasa ta ba.
Wayarta tayi ƙara a lokacin daga gefenta, ta kalli screen
ɗ
in tana karanta sunan Jawad da ya fito tar! akai, tun da ta barshi a hotel
ɗ
in nan bata
ƙara bi ta kansa ba, ya kira wayarta sau da yawa bata
ɗ
aga ba, a jiya da yamma har gidansu yazo amma ta aika masa da saƙon ba zata iya fitowa ba, tana kallonsa ta tagar
ɗ
akinta ya juya da motarsa ya fita.
"Babe I'm really sorry, ki manta maganar da na ga
ya miki dan Allah, just talk to me!"
Sakƙon message
ɗ
insa bayan katsewar kiran ya nuna akan wayar, sai kawai ta
ɗ
auke kanta tana kallon waje, bata lissafa Jawad a cikin matsalolinta na rayuwa ko ka
ɗ
an.
Ta kalli wajen daidai lokacin da idonta ya kai kan s
u Ashraf da ƴan sandan nan, magana suke da wasu mutane a ƙofar wajen basu shiga ciki ba, kuma ta cikin hasken fitulun wajen taga Ibrahim ya dafo kansa ta baya tare da riƙe ƙugunsa alamun wani abu ake gaya musu da ya sa shi mamaki don ta hango mutanen na ma
gana.
Ta hango Ashraf daga gefen tsohon da ya rako su yana sauraren mutumin kafin ya dunƙule hannunsa
ɗ
aya akan bakinsa alamun nasa mamakin shima. Ba shiri ta bu
ɗ
e handle
ɗ
in motar ta fita, hasken fitulun wajen na shigar mata ido amma bata damu ba ta rats
a ta tsakanin sauran ƴan sandan da kuma Bilal ta isa gabansu, ta isa gabansu lokacin mutumin ke cigaba da cewa.
"... Ai na gane wanda yake bayani, shine dai Ma'aruf
ɗ
in manajan kamfanin nan, sai dai idan kuna da hanyar da zaku same shi a gida, amma bana j
in ko ranar litinin zai shigo, don yau aka
ɗ
aura aurensa na gaya maka!"
Ya rufe bakinsa lokacin da ta cikin hasken fitulun wajen ƙwaƙwalwar Rukayya ta karanto mats manyan rubutun dake saman ginin... 'Bakori Enterprises'
Kuma wayar hannunta da ta fara fa
ɗ
uwa, ita ta juyo da hankalin kowa a wajen kafin su ankara da tata fa
ɗ
uwarta har ƙasa!
***
Daga Babi na gaba labarin FARAR WUTA zai fara insha Allah!
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA TARA
~~~~~
Let's go back to when we had not
learn our names, when we introduced our souls, while our heart gasped for breaths. -Aliyu Jalal.
*
A cikin sabon gidan mutane sun fara raguwa sosai, ba kamar a
ɗ
azu da koina yake a cike da mutane ba, Aunty Safiyya ta taho daga hanyar falo ta biyo wani
ɗ
a
n dogon korido mai
ɗ
auke da
ɗ
akuna ta shigo ƙofar
ɗ
akin dake gefe, a cikin
ɗ
akin duk ƴan uwa ne na kurkusa sai kuma amaryar dake tsakiya kanta a sunkuye tana faman kukan da babu sauti sai hawaye kawai da take sharewa.
Aunty Safiyan da ta shigo tace.
"Na
rasa yadda akayi aka manta da tsitsiyoyin nan wallahi, yanzu da ba sai a share gidan ba kafin mu tafi."
"Aunty ai na zata sharar dare babu kyau."
Ummi dake kokarin dora akwatuna can saman wardrobe din dakin tare dasu Momi ta fada tana juyowa.
"Wannan a
i kamawa tayi..." Cewar Aunty Ma'u.
"Baki ga falon nan ba duk kasa ce wallahi, don bana ji akwai wanda ya shigo babu takalmi."
"Ni maigidan ma nake ji, haka zai shigo yaga waje duk ƙura?"
Ɗ
aya daga cikin matan Baban Kurna tace.
"Da za'a iya tunda akwai
kofa ta baya sai a shiga gidan a tambayo su wallahi.
Mahaifiyarsu Ummi da itace zaune a gefen Amina rike da hannayenta ta girgiza kai tace.
"A hakura kawai, gobe da safe insha Allah sai su Maryam su zo su kawo mata kawai, su taya ta sharar ma."
Ta fada
tana kallon Maryam din dake tsugunne a gaban Amina ta riko
ɗ
aya hannunta.
"Ɗan kunnayen nan naki suna cikin wata ƴar ƙaramar jaka pink, ina jin a cikin wata Ghana must go aka saka."
Cewar Maryam din tana kallon idanun Aminan da duk yadda suka yi ja sabo
da kuka wannan kyallin na cikinsu na nan. Ta san ba zata amsa ba saboda haka ta cigaba da cewa.
"Hijaban sallarki ma suna cikin wannan karamin akwatin na undies, Amma ce tace in sa miki anan."
Sai ta gyada mata kai kawai tana ƙara share hawayenta lokacin
da Aunty Safiyya ke tambayar su Ummi idan sun kwashe kayan cikin akwatunan kafin su dora su.
"Duk mun zuba su a cikin wadrobe
ɗ
in, na kayan kwalliyar nan ne da kuma wannan Ghana must go
ɗ
in zamu bari a ƙasa.
"Eh, ku barsu ta gyara ta kanta, sai ku zo mu
tafi kuma don goma ta wuce."
Jin haka yasa Fatima ta taho daga wajen su Ummin tana ƙarasowa gaban Amina, lokacin da Maryam ke cewa.
"Idan zamu zo goben zamu zan taho da Hafsa insha Allah."
Fatiman ta sunkuyo tace.
"Amina litattafan nan naki ba'a
ɗ
ebo
ba, sai dai daga baya ko Aminu ya kawo miki."
Sai a lokacin ta
ɗ
ago da idanunta ta kalle su, me yasa ne suke ta yi mata zancen kaya bayan ba abinda ke gabanta kenan ba? Mantawa suka yi cewa tafiya zasu yi su barta? Su barta a wannan wajen da bata san mak
amar abinda zata fuskanta ba, ko Abdallah ta aura ai dai sun san cewa wannan lokacin mai ciwo ne a wajenta, balle kuma mutumin da bata san ya yake ba balle takamaimai halinsa. Aunty Ma'u ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta tace.
"Sai hakuri Amina, kin ji d
ai duk nasihar da akayi miki daga can gida, sannan su ma iyayen mijin naki kinga yadda suka kar
ɓ
e ki, sunce ƴa suka karba ba suruka ba tunda dama duk
ɗ
aya ne, kuma kowa ya san halinki Amina, duk wanda ya sanki yabonki yake yi... Mutanen nan sune basu sanki
ba, kuma yanzu ne mafarin zamanku, dan Allah ki
ɗ
orar da halinki a wajensu Amina... Don wannan ga
ɓ
ar itace mafi alkhairin rayuwarki, ki sa su zasu zo suna bamu labarin kyautatawarki..."
Ba shiri Amina ta sake fashewa da wani sabon kukan da ya nemi mazaun
insa a zuciyar duk wanda ke
ɗ
akin, taji zuciyarta na sake karyewa da tausayin kanta, kalaman suna tuna mata da na Gwaggo Balkisa a dazu kafin tahowarsu,
ɗ
akin Amma da suka cika aka kaita don ayi mata wannan fadan na al'ada, kuma sai da kowa ya gama nasa sa
nnan ita Gwaggon ta kamo hannayenta duka biyu tace.
"Amina kin sani cewa daga yau sabuwar rayuwa zaki fara wadda babu iyayenki bale kuma sauran ƴanuwanki a kusa, zaki zama
ɓ
arin wani mutum daban da zai bukaci tsananin kulawarki,
Kiyi amfani da hankalinki
da kowa yake yabo ki zame masa mata kuma Uwa, ki kokarin zame masa komai a rayuwa ta duk wata hanyar da zaki iya.
Ba abu ne mai wuya ba Amina, don maza banbancin su kadan ne dana yaro ƙanƙani, kulawarki kawai yake buƙata sai ki ganshi a tafin hannunki. K
ar ki dauki kulafucin barin gida ki sa a ranki fiye da ƙima, shima nasa iyayen zai bari yazo ya zauna dake, banbancin kawai shi namiji ne da zai daure ke kuma mace ce, ki saki ranki ki