Showing 36001 words to 39000 words out of 94381 words

Chapter 13 - Farar Wuta Complete

suka bada shawarar cewar a ƙaiyade iya adadin mutanen da zata iya sani a ƙwaƙwalwar tata

har sai ta fara wayo tukunna, don haka sanin cewar gidansu cike yake da mutane yasa Baffa ya bada umarnin cewa ko bayan an yaye ta baza su kar

ɓ

e ta daga hannun Ruƙayyan ba sai tayi wayon da za'a tabbatar ciwon yayi sauƙi tukunna.

Kuma bayan hakan sai Ruƙ

ayyan ta sanya shi cikin wannan lissafin shima, tace.

"Ka taimaka kayi nesa damu Ma'aruf, wannan rayuwar ba itace mafarkina ba, ko ka

ɗ

an ba haka nake hango abubuwa ba a lokacin kake gaya min, kuma Allah ya sani na yin dukkan ƙoƙarina wajen gyara maka rayu

war amma ka ƙi barina don ban kasa ba, don haka ina so mu ka barmu mu gyara tamu, Hameeda baƙuwa ce a duniyar nan bata san komai ba, dan Allah kar son zuciyarka ya hana ka bari ta gina tata rayuwar. Allah ya sani ina tsoron kasancewar ta kusa da kai, bata

da lafiya har yanzu Ma'aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai za

ɓ

i dawowarka."

Kuma bayan wannan ranar bai sake ganin Hamidan ba, abinda ya sani kawai shine a cikin shekaru biyun ya tu

ra mata isassun ku

ɗ

in da ya san sunyi yawa ma wajen kula da yarinyar, kuma a watanni shida da suka wuce sanda aka ce Ruƙayyan zata yi aure ya san cewa sun kai ta wani asibiti a makkah, ba zai iya zuwa ba a lokacin don haka Baffa ya tura Hajiya Kilishi da S

hukra da kuma wata ƙanwar Hajiya Maimuna suka je can suka duba ta suka dawo.

Yaji kansa yana

ɗ

aurewa da tsananin mamakin da ya kasa lissafawa, tsawon lokaci... tsawon shekaru an hana shi da yake mahaifinta da kuma ƴanuwansa ra

ɓ

arta akan dalilin da har iya

yensa suka tsaya akansa, don tun su Samirah na naci da ƙorafi akan suna zuwa gidansu Rukayyan ana hana su ganinta har sai da suka daina suka cire ta a ransu, sai gashi yau ya tsince ta a irin wannan gidan, tsakiyar sabon gari zagaye da tarin arnan da bai s

an adadinsu ba.

A lokacin ƙofar

ɗ

akin ta bu

ɗ

e, wata Nurse ta shigo da takardar jerin magungunan da za'a siya kafin farkawarta kamar yadda likitan ta shar'anta, da yatsa daya kawai yayi mata nuni da ta ajiye akan drawer dake gefe, kuma budewar kofarta waje

n fita yazo daidai da shigowar Hajiya Kilishi da kuma Samira dake bayanta riƙe da kwandon abinci, duk da halin da yake ciki sai da yaji zuciyarsa tayi fatan yarinyar nan tana tuna Allah kamar yadda take tuna abinci.

"Innalillahi wainna ilaihir raji'un, me

ya faru mai gaskiya? A ina ka samo ta?"

Muryar Mamin ta fa

ɗ

a, sai da ya taso ya miƙe sosai sannan ya shiga gaishe ta, ta amsa tana ƙoƙarin riƙe hannun Hamidan da ya saki.

Kuma sautin muryarsa a hankali ya shiga yi mata duk bayanin da zai iya a wannan l

okacin yayin da take kallonsa da wannan tsananin kulawa da kuma damuwar da kullum ke

ɗ

amfare a fuskarta game dashi.

"Kar damu, komai zai daidaita insha Allah Ma'aruf, da

ɗ

in abin komai bai ja da nisa ba, ka kwantar da hankalinka dan Allah mu bi komai a san

nu kar ka damu kanka da wani tunani, Baffa ya dawo na shaida masa, shima yayi mamaki sosai amma yace a bari ta fara farfa

ɗ

owa tukunna kafin komai ya biyo baya, don haka mu tsaya anan, mu tsaya a iya nan dan Allah mai gaskiya."

Roƙon da take ya san har da

wani bari na muryar Baffa a ciki, don dukkaninsu sun san irin abinda zai iya, don haka bai ce komai ba kawai yayi shiru yana sauraren ta, sauraren da a cikinsa ta fahimci cewa ko ta cigaba da maganar ba fahimtar ta zaiyi a lokacin ba don haka sai tayi shir

u kawai ta juya tana kallon fuskar Hamidan.

A lokacin Samirah ta zubo abinci a plate ta miƙo masa, kuma ganin ƙoƙarin ta ne kawai ya gaya masa cewa ya kamata yaci abincin ba wai don ya so ba, don haka ya kar

ɓ

a a lokacin da itama ta koma gefe tana kallon f

uskar yarinyar.

A cikin tunaninsa yaji Samiran na waya dasu Munaya da kuma amaren da wai dawowarsu kenan daga wajen gyaran jiki suna tambayar sunan asibitin zasu zo, amma Mami ta kar

ɓ

i wayar tace duk suyi zamansu don in suka ce zasu taho

ɗ

in a yanzu ba'a

san adadin wanda zasu biyo su ba kasancewar suna dab da fitowa yanzu ma wasu ƴanuwan Hajiya Maimuna ma suka sauka daga jigawa.

Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, wayarsa kawai yake kallo idanunsa na wasa da adadin messages

ɗ

in dake shigowa bi da bi suna nu

nawa akan screen

ɗ

in, amma a cikin zuciyarsa tunawa yake da zagayen halin da yake ciki bayan wannan, cewar wannan shirye-shiryen bikin da ake shirin farawa har dashi a lissafin.

Don tun daga lokacin da ya samu wannan takardar mai dauke da sunan Amina, kum

a ya tabbatar cewa zancen auren bai lalace ba kamar yadda yayi fata a farko, sai kawai ya mayar da hankali kan aikinsa kuma yawan aikin ke sa shi sha'afa da zancen auren sai wasu abubuwa kamar wannan sun faru da zasu tuna masa cewar shima yana jiran faruwa

r auren ne don ya fara nasa sabon binciken da har cikin zuciyarsa yake jin cewa wannan hanyar zata iya kaishi ga nasarar da ya shafe shekaru yana lalubenta a cikin duk wani abu da ya danganci kayan Jamal.

Misali irin lokutan da Mamin ke kiransa ta bashi w

asu bayanai na cewar an kai kaya gidansu yarinyar ko kuma ya turo da wani adadin kudi za'ayi abu a kaza, abubuwan da suke sa shi yana jin cewa da gaske auren zai yi don Baffa ma ya kafa shara

ɗ

in cewa gidan zai dawo

ɓ

angaren da Baba Alhaji ya ta

ɓ

a zama, yaj

e kamar yadda Aa ya marta har sau biyu yaga gyaran da ake yi, amma daga haka bai kara tunawa ba ya cigaba da harkokinsa don damuwarsa ba sai ta komai yayi daidai bane, ta ya iya kammala abinda ke gabansa ne kafin lokacin don ya sami nutsuwar da zai yi dukk

an bincikensa akan yarinyar.

Ya cije le

ɓɓ

ensa a hankali yana tuno kalaman da Faruk ya fa

ɗ

a masa kwanakin baya.

"Sake yin aurenka shawara ce mai kyau B, amma me yasa sai wannan yarinyar? Kace mahaifinta ba wani bane, kuma kaima ba saninta kayi ba balle in

ce kana sonta ne, beleive me akwai tarin ƴaƴan masu ku

ɗ

in da har layi zasu yi idan kace zaka za

ɓ

a."

Ya fa

ɗ

i hakan ne ranar da Baffa yasa aka raba katin

ɗ

aurin auren ga kowa a Office

ɗ

in kuma mamaki ya kama su ganin cewa har da sunansa, don haka Faruk

ɗ

in

yayi wannan ƙorafin ne bayan ya shaida masa yadda al'amarin ya kasance. Kuma kallonsa kawai yayi a lokacin da dukkan tunanin da bai zo kansa ba, cewar iyayen yarinyar ba masu arziƙi bane, ya sani cewar maza irinsa basa aure a irin wa

ɗ

annan gidajen, misali

aurensa da Ruƙayya shine daidai, don ko irin manyan mutanen da suka halarci

ɗ

aurin auren nasu daga bangaren mahaifinta ma wani abu ne.

Amma baya jin ko bashi da wani abu da yake nema daga yarinyar hakan zai dame shi, don ba auren ko itace a gabansa ba, ku

ma ku

ɗ

in mahaifinta ba abinda zasu tsinana masa kamar yadda na mahaifin Rukayya ma basu kare shi da komai ba sai abinda yake ganin yanzu har dasu a silar sa. Tuna cewar bai ma ta

ɓ

a ganinta ba har yanzu yasa ya jinjina kansa a hankali, bai sani ba idan ya k

amata a kira wannan al'amarin auren gaske bane wannan.

"Ina kika baro masu yin cin-cin

ɗ

in ne da kika biyo ni?"

Yaji Mami na tambayar Samirah bayan ta ajiye wayar, sai dai bai bari ita

ɗ

in ta bata amsa ba ya miƙe tsaye, muryarsa da zurfi yace.

"Zanje in

dawo."

Sai ta girgiza kanta..

"A'a, kaje ka kwanta ka huta kawai, ni zan kwana da ita anan, ka tafi da Samira ka ajiye ta a gida sai ta

ɗ

ebo min ƴan kayan kayan da zamu buƙata zuwa, zan kira Malam Sani ya kawo min."

Ya cije le

ɓɓ

ensa ka

ɗ

an yana bin maga

nganun nata kafin ya gya

ɗ

a kansa sannan yayi mata sallama ya juya tare da

ɗ

aukar hularsa da ya ajiye daga kan wata drawer a gefe.

Samiran ta biyo bayansa, kuma har ya isa waje jikin motarsa, zuciyarsa na riƙe da yadda muryar Mamin ta fito da tsantsar damu

wa da kuma kulawar da ba mai iya ƙiyasta yawanta, a lokuta da yawa yasha ƙiyasta yadda zuciyarta ke iya

ɗ

aukar damuwar tarin mutane da tarin kyautatawa ga duk wani mahuluki da zai shigo hanyarta balle kuma shi da kowa ya sani cewa matsayinsa daban ne a waj

enta.

Ya san itace ja gaba akan komai na bikin nan, amma duk da wannan hadaniyar ta tsallake ta zata zauna, bai san irin son da yake yiwa Hajiya Maimuna mahaifiyarsa ba bayan tsananin girmanta da yake gani, amma Mami zai ajiye ta ne gefe ya tara dukkan ƙa

unar waninta a wani gefen, don yana daga cikin abinda yasa yake son yayi tsawon rayuwa mai kyau don ya kyautata mata.

A sanda lokaci ke wucewa da wannan tunanin a zuciyarsa, a lokacin Hajiya Kilishi ke girgiza kanta daga cikin

ɗ

akin asibitin bayan fitarsu

, zuciyarta na ƙara gaya mata cewar ba haka tsarinta yake ba, ita ke da ikon ƙaiyade duk mutanen da zasu shigo rayuwar Ma'aruf, don haka bata zana cewar abubuwan da ya rasa a baya zasu waiwayo shi nan kusa ba. A tunaninta yadda yarinyar tayi masa nisa haka

tayi a zuciyarsa ma, a tunaninta ko zai neme ta sai shekaru sun ja tukunna a lokacin da hakan ba zai shafi tsarinta ba, amma har me tayi a yanzu da duniyarta zata fara girgizawa?

Ta ƙara girgiza nata kan a fili tana cigaba da kallon fuskar Hamidan da ku

ma yadda

ɗ

an ƙaramin ƙirjinta ke

ɗ

agawa wajen fitar da numfashi mai nauyi, a

ɗ

aya gefen ƙwaƙwalwar ta tana hango idanun Ma'aruf da suka tafi

ɗ

auke da tsananin damuwa da kuma ƙaunar yarinyar dake nunawa ƙarara.

Ta kuma girgiza kanta wannan karon a hankali,

ai alƙawari ne cewar ba zata ta

ɓ

a iya raba zuciyar Ma'aruf tare da kowa ba, sau nawa zata zana cewar shi nata ne ita ka

ɗ

ai? Ba har da tsoron wannan yasa ta ha

ɗ

a aurensa da yarinyar data san ba zata ta

ɓ

a tasiri akansa fiye da ita ba? Ko uwar data haife shi

a yanzu ta isa ta raba soyayyar sa tare da ita ne balle kuma wannan sabuwar halittar? Ta ƙara gurgiza kanta, ba lokacinta bane yanzu, ba lokacin da zata shigo rayuwarsu bane yanzu, bata tsara mata waje ba sam.

Numfashin yarinyar har yanzu take kallo tana

so ta kai karshen lissafinta... Lissafin da ta fara tun a lokacin da wayarta ta su

ɓ

uce daga hannayenta a lokacin da Ma'aruf

ɗ

in ke mata bayanin samun yarinyar. Kuma wucewar wasu sakanni kawai, tunanin nata ya kai kan ga

ɓ

ar da kwakwalwarta tayi tanadinsa t

un a gida...

Ga

ɓ

ar da take shirin faruwa da zaren wani makamancin tarihin da ta ta

ɓ

a ja a baya, fuskar Jamal ta haska a cikin kanta a ranar da ya shiga har cikin

ɗ

akinta ya gaya mata cewa bata isa ba, wani murmushin ya su

ɓ

uce a fuskarta cike da fatan ruhi

nsa ya iya ganin yadda lokaci ke bata tarin damar dake ƙaryata kalamansa, tana fatan ace kabarinsa zai bu

ɗ

e don yaga sabon saƙon da zata aika masa a daren yau wanda zai ƙara ƙaryata kalamansa fiye da cikin masaki.

Ta miƙe a hankali ta nufi wajen da ta aji

ye jakarta, kan teburin da Ma'aruf ya ajiye hularsa, zata yi komai ne hankalinta a kwance don

ɗ

akin asibitin shi zame mata mafaka mai kauri daga duk wani tunanin da zai iya ta

ɓ

a farinta.

Ta gama tsara hotunan komai a cikin kanta har tayi musu fenti ma, sa

nnan hannunta ya jawo jakar da niyyar bu

ɗ

e ta....

***

A cikin

ɗ

akin, da misalin ƙarfe goma na safe, Ruƙƙaya ta kalli mahaifiyarta da fararen idanunta dake shaida tashin hankali da kuma fargaba ƙulli-ƙulli, ta girgiza kanta tana share hawaye.

"Wallahi M

aamah Hanan ƙawata ce ta ha

ɗ

a ni da ita, tace ta ta

ɓ

a yin aiki da wata ƴaruwarta suna da ƙoƙari sosai, shi yasa banyi tunanin komai ba na

ɗ

auke ta a lokacin, kuma itama ta ta

ɓ

a fada min inda take amma na manta."

Kukanta ya ƙaru lokacin da ta sake cewa.

"

Na shiga uku Maamah, idan na rasa Hamida ya zanyi da rayuwata? Da me Ma'aruf zai sake kallona idan har babu ita?"

Hajiya Nafisa, mahaifiyar Ruƙayya na zaune a cikin ƙaton falon gidan na ƙasa, sanye take da wata doguwar riga irinta larabawan dubai, kanta d

aure da ƙaramin mayafin rigar yayi da wayarta ke riƙe a hannu.

Idanunta na kallon Ruƙayyan ne da tsananin takaici bayan tashin hankalin da suka tashi dashi na

ɓ

atan Hamida, sai jiya da daddare jirginta ya sauka daga Paris, don haka ko da ta dawo ta hawo s

amanta bata nemi kowa ba tunda maigidan ma baya ƙasar. Sai a safiyar yau da ta tashi ne sannan ta san Ruƙayya bata gidan saboda haka ta nemi Hamida da mai aikinta Mary amma sai su Jamila da Aisha masu share-share na gidan suka shaida mata cewar ai kwana bi

yu kenan Mary ta fita da Hamidan kuma bata dawo ba.

Saboda haka kai tsaye ta kira Ruƙayyan ta shaida mata cewar ba'a san inda Hamida da Mary suke ba, kuma wucewar minti talatin sai gata ta ƙaraso cikin tashin hankalin da yafi nata, kuma a zaton ta da tazo

kai tsaye zata kira Maryn ko kuma ta bita zuwa address

ɗ

in gidansu ta kar

ɓ

o yarinyar amma sai gashi tana gaya mata wai lambar Maryn bata shiga kuma ita bata san inda take ba.

Allah ya sani idan har tana da wata matsala a rayuwarta to akan Ruƙayya ne, don

babu abinda ta nema ta rasa a duniyar nan illa ha

ɗ

in kan ƴar tata, ita ka

ɗ

ai ce mace kuma babba a cikin maza hu

ɗ

u amma a abubuwa da yawa ta kan gwammace mu'amalarta da mazan akan ita.

Ta sani cewa tun daga lokacin da Ruƙayya ta fara hankali a duniya ta r

asa ta, don daga lokacin da ta

ɗ

auki zuciyarta ta danƙa a hannun Ma'aruf shikenan take zaune da ƙirjinta fanko, don bata kara marmarin saka wani a zuciyarta har ta kalle shi da daraja ba kamar shi, tun yana cikakkensa na mutum har ciwon da zata iya kira n

a hauka yazo ya same shi, haka akayi auren tana murna su suna jiye mata baƙin ciki, kuma ko kafin ta haihu takaici iri-iri sun sha shi, sai da ya juye ƙwaƙwalwar ta tsaf ya goge wannan Ruƙayyan da take a baya, ƴar gayu mai cike da izzar da ko a cikin ƴaƴan

manya ake samun masu kwaikwayon ta.

Ya canja mata yarinya zuwa bagidajiya irin matan da basu san komai ba sai zaman aure,

ɗ

aya daga cikin abubuwan da ba zata manta ba shine lokacin aurenta har Lagos tasa aka nemo mata wasu ƙwararrun chefs(masu girki) mat

a bama maza ba don sanin halin Ma'aruf

ɗ

in, amma wucewar sati guda Ruƙayyan ta bugo mata waya cewa ya sallame su yace shi girkinta yake so, kuma duk ƙin Rukayyan da girki haka ta ajiye ra'ayinta pa gefe ta shiga makarantar koyon girki tsawon watanni don ka

wai farin cikinsa, abubuwan da ta canja a rayuwarta don

Ma'aruf baza su lissafu ba, don a abubuwa ne da ko na nesa zai hango su balle na kusa.

Don haka a lokacin da ta fahimci cewa da gaske tana shirin rasa ƴar tata, a lokacin ta miƙe tsaye tayi wani yunƙ

uri da bai bawa Rukayyan za

ɓ

in komai ba illa bin umarninta, kuma sa'arta ta zarce har bayan rabuwar tasu ta cigaba da jin maganganunta zuwa yardar da tayi ta auri Alhaji Ahmad, amma zata rantse cewar zamanta baiyi nisa a gidan Alhajin ba fitinanniyar zuciy

arta ta sake karkatowa zuwa shafin da take zaton sun barshi kenan har abada wato Ma'aruf, don haka auren bai je koina ba ta fito.

Ƴ

arta Hamida bata ta

ɓ

a damunta ba don a tunaninta ita ba tasu bace, da tayi wayo ne mahaifinta zai kar

ɓ

e ta koma wajensa, don

haka bata ko waiwayarta a al'amuranta ta Ruƙayyan take yi. Ashe duk ub*n shirin da suke yi mata ita da ƙawarta akan alaƙarta da yaron nan Jawad a banza suke kashe ƴan kudadensu, ashe har yanzu zuciyarta bata dawo daga inda ta juya ba, Tunani take zata sak

e komawa wajen wannan yaron da a wajenta kudin da yake dashi ne kawai banbacinsa da wani mahaukacin.

Har ta bu

ɗ

e baki zata yi magana, Ahmad, ƙanin Ruƙayyan dake bin Ashraf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login