Showing 24001 words to 27000 words out of 94381 words
ya kai tashar ya karo volume sannan hankalinsa a
kwance ba kamar yadda ta zata ba ya juyo ya kalle ta.
"Ya gaya min, and I was surprised har dake Mami."
Tayi murmushi tana kallonsa da
ɗ
i na cika kowanne lungu da saƙo na zuciyarta na ganinsa a gabanta, zata rantse da alƙur'ani ko ya'yan da suka fito daga
cikinta basa ƙarasawa inda Ma'aruf ke kaiwa a zuciyarta, matsalar
ɗ
aya ce kawai... duk wani ado da zai ƙawata kusancinsu dole ana kaiwa gabar da za'a yaye cewar shi ba mallakinta bane, kuma tana jin cewa da zata iya samun mai gyara mata hakan babu makawa
zata bada komai na duniyarta don kawai a wayi gari duniya ta shaida cewa shi nata ne.
"Baffa ya riga ya gama yanke hukuncinsa shi da Alhaji Baba, daga ƙarshe kawai suka tuntubeni Mai gaskiya kuma ka san ba zan iya cewa Baffa A'a ba, shi yasa sai na bada t
awa gudunmawar ta hanyar za
ɓ
o maka yarinyar da na san zata dace da yanayinka. Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata."
Wani murmushi yayi ka
ɗ
an sannan yace.
"Na dade ina gaya miki kulawar
ki ka
ɗ
ai ta ishe ni in rayu Mami, tunda har Rukayya ta kasa bana tunanin akwai wadda zata iya jurewa mess
ɗ
ina a duniyar nan kuma."
Maganganun suka ta
ɓ
o wani abu a can ƙasan zuciyar Hajiya Kilishi, wani abu da sai da ta ji shi har a ƙarƙashin tafin ƙafart
a musamman yadda muryarsa ta fito da wannan amon mai zurfi da kuma sanyi. Kuma sai da ta maida wata ƙaramar ƙwalla a idanunta sannan tace.
"Yanzu dai ka san baza'a fasa ba ko? Don haka zamu fara shirye-shirye, za'a kai musu lefe dole sannan idan kana so
ma zaka iya zuwa ka ganta."
Maimakon ya bata amsa, sai kawai ya juyo ya kalle ta, lumsassun idanunsa suka tsaya a nata.
"Wai zaman me Ishaq yake yi ne ma? Me yasa Baffa baice a ha
ɗ
a dashi ba?"
"Sai gida ya koshi ake kallon na waje Ma'aruf, kaine damuwar
mu a yanzu ba shi ba."
Kamar bai ji dadin maganar ba, don juyawa yayi yana cigaba da kallonsa ba tare da yace komai ba. Hakan yasa tayi saurin gyara zancen ta.
"Kar ka damu amma, da an gama zancen nan ni da kaina zan saka shi a gaba sai ya motsa."
Murm
ushin da ya sake yi ya sata jin wani
ɗ
aci a zuciyarta, ba sau daya ba sau biyu ba tasha tunanin kawar da Ishaq daga hanyarta kamar yadda ta kawar da abubuwa da yawa a rayuwar Ma'aruf, don duk wani abu da zai jawo ya raba zuciyarsa da kowa bayan ita, bata ƙ
aunarsa sam! Amma matsalar shine Ishaq ba ƙaramin amfani yake mata ba, amfanin da shi ta lissafa har ta bada shawarar dawo dashi wajensu bayan ya rasa iyayensa ba don kyautatawar da duniya ke kallonta dashi ba.
"Akwati nawa kake so a ha
ɗ
awa yarinyar?"
Ka
mar bai damu ba, hankalinsa kwance yace.
"Duk yadda kika yi Mami daidai ne, ni yanzu abinda ke gabana daban harkar Office ce da zanje in gyara, Baffa yace anyi asara da yawa a wannan watan."
Ba shiri maganar ta doka wata tsawa a cikin kan Hajiya Kilishi
tana janyo ta daga ramin da zuciyarta ke shirin kai ta, taji kamar ta miƙe tsaye tana karka
ɗ
e raunin daya baibayeta tun bayan data
ɗ
ora idanunta akan Ma'aruf
ɗ
in.
"Shikenan, Allah ya taimaka. Ka taho min da magungunan naka?"
Wata ƴar ƙaramar jakar daya s
higo da ita a gefensa ya
ɗ
auko ya miƙa mata ba tare da ya janye idonsa daga Tvn ba, kuma da Ma'aruf ya saurara da kyau, zai ji lokacin da ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta bu
ɗ
e jakar tana nazarin kayan ciki.
A lokacin Samirah ta shigo
ɗ
auke d
a lemo mai sanyi da kuma cake a faranti, yarinya ce ita mai tsananin kula da son kyautatawa kowa, shi yasa kusan komai na gidan yanzu sai da izininta ake yi, hatta abincin Baffa ta da
ɗ
e da kar
ɓ
ar ragamarsa sai dai ko in tana makaranta sai wani a cikin yayy
enta yayi, don su Hajiya Kilishi basa girki a gidan. Kuma ko a
ɓ
angaren Hajiya Maimuna akayi baƙi Sameerah ita zata fara tarbarsu da waje da kuma kayan cima kafin kowa, ƙarya ne wani ya shiga gidan nan yace ya fito da yunwa in har tana nan.
"Dan Allah Yay
a ka bani kwangilar sati
ɗ
aya in cicciko maka da wa
ɗ
annan kasusuwan, wallahi baka ga yadda ka rame ba."
Ta fa
ɗ
a tana ajiye masa farantin a gabansa. Ma'aruf ya
ɗ
ago ya kalle ta yana murmushi lokacin da Hajiya Kilishi ta mike riƙe da jakar magungunan tayi h
anyar
ɗ
aki. Kusa dashi ya nuna mata a kujerar yace.
"Zo ki zauna muyi ciniki Please, how much do you need? ( Nawa kike so) coz ƙarfi nake nema nima yanzu."
Ta kuwa ƙyalƙyale da dariya daidai lokacin da Shukra (ƙanwarsa dake bi masa a wajen Hajiya Maimuna
) ta shigo daga hanyar wajensu, kuma ganin Ma'aruf
ɗ
in yasa tayi murmushin dake ƙarawa fuskarta kyau tana fadin 'Alhmdlilah" sannan ta juya da sauri don
ɗ
ebo takardun research
ɗ
in da ta tara zai duba mata.
Don haka Ma'aruf bai samu shiga wajen Hajiya Maim
una ba sai da yamma tayi sosai. Kuma a falo ya same ta itama, tana zaune daga kan Wheelchair
ɗ
inta tana karatun azkar
ɗ
in yamma, yayin da Zahra da kuma Sahla ke zaune suna kallon video
ɗ
in wani tutorial daga labtop
ɗ
in Munaya da suka aro.
Ya durƙusa har k
asa a gabanta ya gaishe ta cike da girmamawa, girmamawar da bayan ita baya ta
ɓ
a kallonta da wani abu.
"Yaya jikin naka?" Muryarta mai taushi ta tambaye shi bayan sun gama gaisuwa.
"Lafiya ƙalau Hajiya, naji sauki ai."
"Allah ya ƙara sauki. Kaje wajen I
nna ne?"
Ya girgiza kansa.
"Yanzu zan shiga idan na fita."
Tayi shiru yayin da idanunta ke nazarinsa, ya sunkuyar da kansa ƙasa sanye da dogwayen kaya na farin yadin da ko a ido mai laushi ne don ya kwanta a jikinsa sosai ta yadda ya fito da ƙirar jikin
sa mai tsari, wani abu dake
ɗ
aya daga cikin abinda ke ƙara masa kwarjini a idon mutane.
A lokacin ne kuna maganar ƴar uwarta a kwanakin baya ta haska a cikin kanta.
'Ban ce ki tada hankalin gidan ki ba Maimuna, amma abin yayi yawa, kin rasa Jamal kuma Ma
'aruf shine Babba a gidan yanzu, ko yaya ne ya kamata ya dinga tunawa cewa ke kika haife shi ba ita ba...'
Tayi saurin kawar da wannan tunanin tana ha
ɗ
iye wani abu da batasan sunan sa ba, a lokainda ƙwaƙwalwar ta ke tuno mata damagaar da Baffa ya yanke t
aauresa jiya da daddare, sai dai har ta bu
ɗ
e baki zata yi masa magana kawai taga ya miƙe tsaye yana yi mata sallama, sai ta mayar da maganarta a hankali sannan ta amsa, kuma murmushin da yayi wa su Zahra a matsayin amsa tasu sallamar ya sake
ɗ
ago wani abu
a zuciyarta da ta da
ɗ
e tana danne shi tsawon shekaru. Idanunta suka bishi da kallon da har ya rufo mata ƙofar falon hankalinta bai koma kan karatun da take yi ba.
A falon Inna Danejo Ma'aruf ya tarad da ita tana sallah daga kan sallayar ta da anan take kw
ana ta yini in har ba tashi ne ya kamata ba, don haka ƙafafunsa suka tako cikin falon a hankali, yana jin kamar zai nutse a sabon carpet din da aka shimfide mata falon dashi, (wall to wall). Ya karaso ya sami waje daga gefenta ya jingina da wasu ƙullin kay
anta da ya san na wanki ne sannan ya zaro wayoyinsa daga aljihu.
Tarin messages
ɗ
in da har yanzu bai duba ba suka shiga tururuwa akan screen
ɗ
insa, sai ya zura hannunsa
ɗ
aya cikin gashin kansa kawai sannan ya cillar da ita a gefe ya dauko
ɗ
ayar.
A ciki y
a lalubo nambar Faruk, aboki
ɗ
ayan da yake dashi bayan Ishaq kuma mataimakinsa a wajen aiki.
"Ka gaya min ba maganar aiki bace dan Allah B, don wallahi as we are talking now ina Coldstone ni da yara, kowa yana son hutu a rayuwarsa Ma'aruf."
Faruk din ya
fa
ɗ
i hakan tun kafin yace komai, don shi kansa ya sani ba zai iya kirga adadin wayar da suka yi akan zancen Office
ɗ
in ba tun bayan dawowarsa. Sai dai kalmar yaran da ya furta ta daki zuiyarsa da wani irin tasirin da baya ta
ɓ
a sabawa dashi don haka ba shir
i ya tafi kai tsaye ga abinda yake son tambayarsa.
"Account number Daniel zaka turo min."
"Me zaka yi da ita? Na gaya maka gayen yana can har yanzu da kumburarriyar fuska wallahi."
Ya cije le
ɓɓ
ensa a hankali yana hango fuskar Daniel
ɗ
in a idanunsa, sand
a ya cakumo wuyansa yana kai masa naushin da baya ƙarewa, kuma duk da zafin dukan nan Daniel baya kare ba ko sau
ɗ
aya, kallonsa kawai yake da idanunsa dake nuna tsantsar mamaki da kuma ru
ɗ
ani har ya fita daga hayyacinsa.
Ya sake tuno yadda ya jawo shi ya
fito dashi har waje
ɗ
imbin jama'ar Office
ɗ
in na kallonsa, da lokacin da ya saka shi a boot din motarsa ya rufe sannan yaja motar zuwa gida, yaje gidan kuma ya fito dashi dashi daga boot
ɗ
in motar ya ja shi har falon Baffa a lokacin ma ya riga ya suma...
Sai kawai ya sake mai da kansa baya, yana motsa ytsunsa cikin gashin kansa a hankali, idonsa ya cigaba da hango masa yadda a lokacin duk da baya cikin hayyacinsa amma nauyin idanun Baffa suka sa ya durƙushe akan gwiwoyinsa sanda ya kai Daniel
ɗ
in har gaban
sa, amma kuma duk da hakan bai fasa gayawa Baffan cewar wai ya kawo shi ne ne don ya kore shi daga aiki ba...
"Just send it Umar..." (Kawai ka turo min...)
Ya fa
ɗ
a yana katse tunaninsa kuma bai ƙarasa abinda zai ce ba hayaniyar yaran nan ta shiga kunnens
a daga cikin wayar, don haka ba shiri ya katse kiran yana ƙoƙarin ture abinda ke ƙoƙarin tasowa daga ƙasan zuciyarsa.
Ya cillar da ita gefen
ɗ
ayar itama sannan ya rufe idanunsa yana cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin nasa daidai lokacin da Inna Danej
o ta idar daga sallarta.
"Wai rana kika koma bautawa ko me? Wannan wace irin sallah ce bayan la'asar?"
Inna Danejo ta kalle shi zuciyarta fara ƙal! da farin cikin ganinsa lafiya ƙalau, don a cikin addu'inta na tsukin kwanakin bata jin ko kanta ta ambata
a cikin addointa banda fatan nema masa sauki, don haka da guntun murmushi a fuskarta ta kai laziminta na sallamar sallah sannan tace.
"Idan ranar na koma bautawa Muhammadu, iyayenku ai su zasu fara biyo ni kafin ku."
Murmushi yayi a hankali sannan ya bu
ɗ
e idanunsa ya juyo ya kalle ta dasu a lumshe.
"Allah yasa da kika dama furar kin rage min, tun da na shigo nake jin ƙamshinta."
Maimakon ta bashi amsa sai tace.
"Yanzu Allah baza ka ji magana ta ka aske gashin nan ba ko? Ko iska ba ka so kaji tana rats
a ka Muhammadu?"
Ba shiri murmushinsa ya karu.
"Saboda me zan so iska ta ratsa ni? Wadda ke shiga hancina ma ta ishe ni Inna... Ki tashi ki
ɗ
auko min furar dan Allah."
Ai kuwa kamar ya ziga ta ne akan irin mitar da tayi a duk lokutan da baya nan a gidan
, ta faro ta tunda daga farko daki-daki har tana fa
ɗ
in idan ma ba zaiyi askin ba wai ya tsaya ta wanke masa da sabulun salo ta tabbata ranar sai yayi bacci mai da
ɗ
i, murmushinsa kawai yake yi yana jinta tunda dama ya riga ya shiryawa hakan.
A haka har Ish
aq ya shigo ya same su, shima aka zuba masa furar sannan ta tasa su a gaba su duka biyun kuma da zancen aure. A lokacin Ishaq ke gaya mata hukuncin da Baffa ya yanke game da Ma'aruf, don haka bayan ta gama hamdala da mitar cewa Baffan bai zo ya same ta ya
gaya mata ba, sai fa
ɗ
an kuma ya koma kan Ishaq shi ka
ɗ
ai, tana yi tana zayyano masa jikokin ƴanuwanta na ƙauye, kowacce ta fa
ɗ
o Ishaq sai ya gyada kai yace "Kuma da alamun tana da hankali."
Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, tunani da yawa ke yawo a cikin
kansa game da abubuwan dake gabansa, sai dai ko ka
ɗ
an babu batun auren nan a cikinsu, don tunaninsa ya gaya masa cewa ko iyayen yarinyar nan mahaukata ne idan ta nuna musu wannan takardar dole ne auren ba zai yiwu ba.
A hankali ya sake rufe idanunsa yana
tuno dukkan irin matakan dake rubuce a jikin takardun asibitinsa, Allah ya sani a baya baya taba damuwa da ciwonsa, yana ajiye shi ne a can ƙarshen lissafinsa, amma a yanzu... yanzu bai san me yake ji ba, tsoro ko kuma taraddadin cewa abubuwa zasu iya ƙwa
ce masa kafin ya kai ga cimma manufarsa? A cikin duhun idanun nasa ya hango a inda yake manufar tasa, abinda shi ka
ɗ
ai ne abu guda a duniyar nan da baya ta
ɓ
a ha
ɗ
awa da kowa,
ɗ
akin bincikensa yake hangowa, tunda ya dawo bai bu
ɗ
e shi ba don haka a yadda ya t
afi ya barshi yake hango shi... Yadda yayi kaca-kaca da takardu cikin takaicin da shine linzamin dukan da yayi wa Daniel.
"... Kaga Rabi ma ƴar wajen Ba
ɗɗ
ejo, yarinya ce mai hankali, ga kyau..."
Muryar Inna ta shiga kansa da wani irin tasirin da ya doka
a ƙirjinsa, tasirin da yasa ba shiri ya bu
ɗ
e idanunsa yana kallon Innar da kuma Ishaq din dake cigaba
da gyada kai yana shan furarsa, sai dai ba saurarar abinda suka cigaba da cewa yake ba, muryar Inna ta shekaru goma da suka wuce ce ta shiga haskawa a cik
insa, shekaru goma cikin wannan
ɗ
akin.
Kuma bayan muryar sai hoton ma ya canja a idanunsa, yaga yadda tsufan Inna ke raguwa da shekaru goma da yadda komai na
ɗ
akin ke canjawa da abubuwan da suke a mazauninsu a shekaru goman da suka wuce, sannan a lokaci g
uda Ishaq
ɗ
in ma ya bace, siffar Jamal ta maye gurbinsa yayin da yake zaune a gaban Innar yana dariya.
"Ga Halima ma ƴar gidan Baffayo, yarinya ce mai hankali, ga kyau, ga kyau..."
Ya ga yadda Jamal ke girgiza kansa yana dariya kafin yace.
"Akwai abubu
wa da yawa a gabana yanzu Inna, ki ajiye maganar yaran nan... Akwai abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan kafin ma in fuskanci aikina..."
Kuma a lokaci guda ƙwaƙwalwar Ma'aruf ta tsinto kalamai biyu a cikin zancen...
Abubuwan da nake son daidaitawa
a cikin gidan nan... Abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan...
Tabbas! Ya akayi bai ta
ɓ
a tunawa da wannan lokacin ba? Me yasa ƙwaƙwalwarsa bata ta
ɓ
a hasaso masa wannan ranar ba? Babu shiri idanunsa suka shiga hasko masa tarin abubuwan dake
ɓ
ullewa
ga wannan maganar, yaji su suna sauka a cikin kansa kamar zubar ruwan da aka tunku
ɗ
o da ƙarfi.
"B, Yaushe zaka fita?"
Muryar Ishaq ta janyo shi daga tunaninsa, sai kawai ya lalubo wayoyinsa a gefe da mukullin motarsa ya mike tsaye.
"Yanzu." Ya bashi ams
a idanunsa na muna tsantsar nazarin abubuwan da shi ka
ɗ
ai yake hangowa.
Kuma da haka bai jira komai ba yayi waje, yana ji Inna Danejo na ƙokarin tsaida dashi amma bai tsaya
ɗ
in ba, ya fita yana jin tasirin idanun Ishaq da ya biyo da kallo.
A harabar gida
n ya gano Munaya tsaye tana waya, duk ta rikice kamar yadda take kullum sai faman gyara glasses
ɗ
inta take alamun bayani ake mata ta cikin wayar, don haka bata ma ganshi ba har ya bu
ɗ
e motarsa ya jata ya bar cikin gidan, kuma zai iya rantsewa zuciyarsa na
lissafa kowanne wucewar lokaci kafin ya isa gida.
A ƙofar gidan ya ajiye motar don ƙwaƙwalwar sa ta gaya masa cewa ba zai iya jira har maigadi ya bu
ɗ
e masa gate
ɗ
in ba.
Ya shiga har ciki zuwa
ɗ
akinsa, ya bu
ɗ
e ƙofar da ko waye ya shigo
ɗ
akin zai ce wardr
obe ce. A ciki komai yana nan kamar yadda yake hango shi kafin tafiyarsa.
Tebura ne da duruwoyi masu cike da files
ɗ
in takardu da kuma hotuna, ga tarin printers da photocopier a gefe, sannan bayan kayan rubutu akwai allo har kala uku
ɗ
aya na rubutu biyun
kuma ya manne su da takardu da kuma hotuna. Ɗaki ne da ko makaho ya shafa zai danganta shi da kalmar binceke balle kuma ga mai ganin da kallo
ɗ
aya da zai yi masa zai bashi amsar da ba sai ya tambaya ba.
A jikin allon nan bayanai ne da kuma hotunan mutanen
da Jamal yayi mu'amala dasu tun