Showing 18001 words to 21000 words out of 94381 words
bayan da suka ga Amman bata basu amsa ba, tayi shiru kawai tana kallonsu, wanda hakan yasa Adam yasha jinin jikinsa, ya sake kallon fuskar Amman da kuma ta Amina ya tabbatarwa kansa cewa basu yi daidai da lokacin da ya kamata ba,
don haka ya nufi kofa, sai dai har yasa ƙafarsa
ɗ
aya a waje ya tuna da saƙon da aka bashi.
"Au na manta wallahi, Yaya in kin fito ana kiranki a waje."
Da haka ya juya yayi hanyar Kitchen ayana fadin zai sake zuwa yaci abinci. Amina ta ƙara share hawayen
idanunta, Abdallah ne ta sani, don dama tun jiya take tsammanin zuwansa dama don ta sani lokacin komawarsa makaranta yayi, sai dai yazo a lokacin da take jin bata son ganin fuskar kowa, maganganun Baba da Amma sun riga sun cike duniyarta ta yadda bata tuna
nin a cikin zuciyarta ma akwai wani waje komai kankantarsa da zai sake
ɗ
aukan wani abu a daren yau.
"Ki tashi kije, ganinsa zai sa ki sake yankewa kanki hukuncin da ya dace Amina, daga daren yau zuwa gobe kawai kike dashi..."
Muryar Amman ta sake fa
ɗ
a, t
aji kamar tayi ihu lokacin data
ɗ
ago ta kalle ta, Hafsa na tsaye har yanzu sai kallonsu take alamun rashin fahimta akan fuskarta, kuma daga yanayin Amman ta san ko ihun tayi ba zata canja maganarta ba don haka ta sake goge hawayen da bayan hannunta sannan
ta miƙe a hankali tana jin yadda kowa ce kalma da iyayen nata duka furta tayi mata tsaye a zuciya bayan nauyinsu da take ji a kafa
ɗ
unta.
Akan igiyar tsakar gida ta tarar da hijabin da Maryam ta goge
ɗ
azu don gobe za'ayi musu hotunan photo album
ɗ
in sauka
a islamiyyar su, na sallar idinsu ne, dogo har ƙasa kalar ruwan ƙasa, ta jawo shi kamar zata saka amma sai ta fasa, ta nufi ƙofar soron ta tsaya, ziciyarta na ƙoƙarin ƙulla ta yadda zata yiwa Abdallahn bayanin komai, komai
ɗ
in da itama bata gama sani ba, t
aji
ɓ
angare da yawa a cikin ƙwaƙwalwar ta na gaya mata cewa fitar ta a wannan lokacin ba alkhairi bace, don haka sai kawai ta dawo ta kira Adam dake karo da kwanuka a kitchen.
"Adam zo."
Ya juyo riƙe da plate yana kallonta kafin ya ajiye shi ya biyo baya
nta, suka koma har hanyar soron.
"Adam dan Allah kaje kace masa bani da lafiya sosai, ya dawo gobe ba zan iya fitowa yanzu ba."
Kamar ya tambaye ta dama ta sanshi ne tunda bai taba ganinsa a gidan nasu ba, sai kuma kawai ya fasa ganin yadda idanunta suka
yi ja ya san ba lallai taso tambaya a lokacin ba, ya juya ya fita, ita kuma ta tsugunna a wajen tana ƙara share hawayenta ba tare da ta fahimci kuskuskuren da tayi ba.
Lokacin da Adam ya fita, Ma'aruf na tsaye har a lokacin kuma ganin tahowarsa yasa ya
ɗ
ago da hannayensa duka biyu a hankali yayi baya da hular (hood) dake kansa, fuskarsa ta fito cikin hasken ƙwan fitilar barandar gidan,
"Yaya tace wai dan Allah kayi haƙuri bata da lafiya ba zata iya fitowa ba ka dawo gobe."
Ba shiri wani murmushin ya sub
uce a fuskar Ma'aruf, For real? Shine ma zai dawo goben? Bata san me ta tsallake bane, sai kawai ya gyada kansa tare da fa
ɗ
in.
"Okay."
Har Adam zai juya yayi saurin tsayar dashi.
"Kana ji ko,
ɗ
an tsaya ka bata wannan."
Adam
ɗ
in kuwa ya tsaya, shi kuma
ya bu
ɗ
e ƙofar motar ya bu
ɗ
e aljihun dake jikin dashboard ya zaro wata jotter da biro daya san Ishaq baya taba rabo dasu motarsa a matsayinsa na lawyer, ya yago takarda guda
ɗ
aya ya
ɗ
ora daga saman yayi wani rubutu layi biyu da rabi kawai sannan ya rubuta s
unansa daga ƙasa. Ya kalli abinda ya rubuta din yayi wani guntun murmushi kafin ya juyo ya mikowa Adam
ɗ
in
"Nagode sosai kaji."
Ya fa
ɗ
a yana sake yi masa wani murmushin, da fara'a shima Adam
ɗ
in ya amsa yana masa a sauka lafiya kafin ya juya, shi kuma ya
jefa kansa baya jikin motar yana cusa hannunsa na hagu cikin gashin kansa.
Ba haka yaso ba, amma hakan ma yayi... Ya riga ya gama da yarinyar nan ya sani, don abinda su Baffa ke tunani ba zai ta
ɓ
a yiwuwa ba.
Aka
ɗ
auke wuta a daidai lokacin, unguwar tayi
wani irin duhu din
ɗ
im kamar yadda yake jin zuciyarsa! Don haka ba shiri ya kunna motarsa ya shiga ya bar wajen.
"Gashi yace in baki."
Adam ya fa
ɗ
a a cikin duhun soron bayan ya koma, Amina tayi saurin sake goge hawayenta kafin ta karbi takardar ba tare d
a tunanin komai ba don ta san ba wani abu bane Abdallahn ya iya rubuto mata fatan samun sauƙi dama, ta damƙe ta a hannunta sannan ta miƙe ta bi bayansa. A kitchen suka tadda Amma na kokarin kunna kyandir guda biyu Hafsa kuma na sake zuba abinci itama, kuma
bayan ta amsa sallamarsu sai ta miƙowa Amina guda
ɗ
ayan yayin da Adam ya shiga fadan cewar Hafsan ta dauki farantinsa.
Ta wuce
ɗ
akinsu kai tsaye, ta ajiyewa Maryam Hijabin akan katifarta sannan ta manna kyandir din akan wata kwalbar magani, a gabansa ta
tsugunna hannunta rike da takardar, daga jikinta har zuciyarta daban take jinsu, wucewar awa guda kawai ta tafi da Aminar da take a baya, a yau da safe ma... tana jin zata rubuta dukkan abinda ya faru a daren yau a wajaje da yawa ta yadda ba labarinsa ba z
ai ta
ɓ
a gogewa ba.
Ta sake goge wani hawayen sannan ta bu
ɗ
e takardar a hankali, zuciyarta cike da fatan ta karanta wani abu mai rangwame daga Abdallan ko yaya ne wataƙila ya iya zaftare wani
ɓ
angare na damuwarta, sai dai kuma rubutun da idanunta suka gan
i a jiki shine abu mafi tashin hankali fiye da duk maganganun da rayuwarta taci karo dasu a wannan daren.
Kar ki yarda da auren nan, da gaske ne abinda suka fa
ɗ
a miki, I'm a psycho, zan kashe ki idan har kika shigo rayuwata. Ma'aruf B.
*****
11:15Am.
"
Mai gaskiya kaci abincin kasha magunguna naka?"
Muryar Hajiya Kilishi ta tambaya cikin wayar dake kare a kunnenta, kuma a cikin wayar aka bata amsar data sa ta gya
ɗ
a kanta kafin ta sake cewa.
"Zan kira Ishaq, zamu yi maganar komai dashi, idan zaka shigo
kawai ka taho da magungunan duka."
Har tayi shiru sai kuma tace.
"Dan Allah Ma'aruf kafin ka shigo kaje ka aske gashin nan dan Allah, ko
ɗ
azu da na shiga wajen Inna Danejo abinda ta fara tambayata kenan."
Amsar da Ma'aruf
ɗ
in ya bayar mai tsawo ce, don
ta dade tana saurarensa kafin tace,
"Shikenan idan ka shigo kayi mata wannan bayanin da kanka, akwai faten dankali a
ɗ
aya daga cikin kwanukan abincin nan ka ganshi?"
Ya fadi abinda ya saka ta yin dariya kafin ta sake cewa.
"To aci lafiya, sannan idan ka
wuce 1 baka shigo ba, zaka ganmu gabadaya gidan mun taho."
Ya fadi wani abun da ya kara saka ta dariyar da tafi ta farko tana fadin.
"Ai da ƴanmata zamu zo sai suyi muku sharar."
Da haka suka yi sallama, tana sauke wayar daga kunnenta.
"Wallahi na dad
e ina gaya miki Hajiya, da irin mahaukatan secret agent din nan na turawa ya kamata ki samu aiki, ko banza dukkanku zaku amfana da juna, ke da kudinsu su kuma da kissa irin taki."
Cewar Hajiya Salamatu, wata hamshaƙiyar ƴar gayu dake zaune daga gefen Haji
ya kilishin.
Wajen ƙarfe goma sha
ɗ
aya ne na safe a lokacin, kuma kasancewar ranar ta asabar ce kowa yana nan, gidan cike yake da hayaniya da kuma hada-hadar masu aiki da suka gama abincin safe suke kokarin
ɗ
ora na rana.
A cikin
ɗ
akin da suke zaune an
ɗ
a
ge labulayen tagogin dakin guda biyu iska da hasken rana na shigowa yayin da a lokaci guda kuma filutulun
ɗ
akin suke a kunne ha
ɗ
e da fankar da aka ware har ƙarshenta. Hajiya Kilishi dake zaune itama cikin nata adon daidai misali ta ajiye wayarta a gefe san
nan ta kai hannu ga robar ketchup
ɗ
in dake kan katon farantin da aka zubo musu kayan breakfast akai, ta sake zubawa a farantin dankalin turawan dake hannunta ta sannan tace.
"Idan har zaki samo min me zai sa in ƙi sanya hannu Hajiya, kin san ai waje in da
i da ra
ɓ
a da kuma sirri ba na ƙinsa."
Hajiya Salamatu ta sake kai kofin shayinta baki tana girgiza kai.
"Ai kullum ina gaya miki al'amarinki abun mamaki ne Kilishi, wallahi duk yawona a doron duniya ban ta
ɓ
a ganin mace irinki ba, yadda ba boka ba malam,
kike juya komai da
ɗ
an yatsa guda kuma hankalinki a kwance."
Hajiya Kilishin tayi wata guntuwar dariya alamun ta saba da jin hakan daga bakin ƙawar tata.
"Mu bar wannan zancen yanzu Salamatu, mu tafi ga abinda yasa na kira ki."
Sai da Hajiya Salamatun g
yara zamanta a hankali tana ajiye kofin daga durowar gefen gadon, idanunta ka
ɗ
ai zaka kalla ka san cewar da gasken ta tattara dukkan hakalinta ga abinda Hajiya Kilishin ke ƙoƙarin
ɗ
orawa akan tsohon shirin da suka saba.
"Auwalu yana riƙe da ma'aikata har
yanzu, sannan wannan auren kamar ya tabbata ne mu ajiye shi a gefe, me kika cigaba da shiryawa daga ƙarshen ƙullin da muka yi wa zaren, me kika tsara?"
"Tsari na da yawa Salamatu, farko dole ne in fara sakin manufata tun yanzu akan ita yarinyar, dole ne t
a
ɓ
oyayyiyar hanya in ƙara bincike akan zuciyarta ta yadda zan fara ƙawata tunaninta da miƙakkiyar hanyar da zata ƙulle ta a gaba.
Na biyu, dole ne a yanzu inyi taku mai nisa daga mahaifin yarinyar da kuma maigidana, zan ƙara zame hannuwa daga al'amarin n
a in zama ƴar kallo ta yadda ko ƙura ba zata hau kan farina ba, balle wani
ɗ
igo na baƙi, amma zan kusanci mahaifiyar yarinyar dole, don haka ne ingantacciyar hanyar da kowa zai kalla a yanzu.
Sannan na san Ishaq zai shaida min dukkan sabon tsarin magungun
an Ma'aruf, don haka wannan ma babu matsala, komai zai cigaba ne daga inda ya tsaya. Game da auren su Salma kuma wannan komai tsaftatacce ne don kin san bana ta
ɓ
a ha
ɗ
a ƙasa da gari waje guda. Daga Auwalu kuma, mun sake bude wani sabon account zai loda kuda
den wancan watan..."
Ta fa
ɗ
i hakan sannan tayi shiru a hankali, ramin bakinta na wasa da wani murmushi mai armashi.
"A yadda lissafin komai yake Salamatu, shekara guda tayi yawa kafin komai ya
ɓ
are!"
Hajiya Salamatun tayi nata murmushin itama yayin da t
ake kallon fuskarta.
"Na fahimta Kilishi nima na lissafa wannan adadin tun a wancan karon. Sai dai kin san a kullum nice mai hasko miki ƙalubalen da ke bakya ƙirgawa dasu. Ƙalubalen da duk zare
ɗ
aya ne ya ƙulle su suke reto a jikinsa, ƙalubalen kuma da sh
ine raunin ki Kilishi, shi kadai ne raunin da na san ubangijin ya halitta a ƙirjinki, Ma'aruf!"
Murmushin da kullum ke sauka a fuskarta duk sanda Hajiya Salamatun ta furta mata magana makamanciyar wannan shi tayi a yanzun ma, tayi shi tana ajiye farantin
hannunta, ta jawo tissue a gefe ta goge maiƙon hannunta sannan ta miƙe, ta isa ga makekiyar wardrobe
ɗ
in dake
ɗ
akin ta bu
ɗ
e waje na biyu, a ciki kayan Ma'aruf ne wanda ya cire daga jikinsa ranar da aka tafi dashi tafi London ba'a hayyacinsa ba.
A gaban ka
yan akwai dukkan tarkacen dake cikin aljihunsa a wannan ranar, muƙullin mota, chewing gum, chapet, biruka da kuma wallet
ɗ
insa, wallet
ɗ
in ta dauko sannan ta rufe wardrobe
ɗ
in ta dawo gaban Hajiya Salamatu ta miƙo mata ita.
Sanin halinta sarai yasa Hajiya
Salamatun ta kar
ɓ
a ba tare da ta tambaya ba, ta ware cikinta, kuma bayan tudun ku
ɗ
in da taji a ciki da kuma jerin credit cards, wani hoto da aka maƙala a jiki shi ya
ɗ
auki hankalinta, samari biyu ne a jikin hoton wanda kallo
ɗ
aya kawai zai shaida maka cew
ar wa da ƙani ne, don bayan
girman da
ɗ
aya yafi
ɗ
aya, akwai kammani sosai a fuskarsu. Suna dariya mai cike da nisha
ɗ
i yayin da babban ke miƙo hannunsa kamar zai naushi ƙaramin.
Ƙ
aramin Ma'aruf ne Hajiya Salamatu ta sani, babban kuma...
"Jamal..." Sassany
ar muryar Hajiya Kilishi ta furta tare da tunanin Hajiya Salamatun.
"Jamal shine ƙalubale na kuma shine rauni na Salamatu, shi yasa na rufe idanuna nayi abinda ya kamata akansa, don haka kamar kullum zan gaya miki cewa ki yarda bani da wata matsala a duni
yar nan yanzu idan ba kuma ƙaddarar ubangiji ba. "
Ta fadi hakan yayin da take tsaye akanta, Hajiya Salamatun ta
ɗ
ago ta kalle ta, wannan murmushin na baya ya tafi, idanunta sun canja ta yadda ko
ɗ
igon raha babu a cikinsu.
"Kar ki ƙara lissafa Ma'aruf a
cikin ƙalubale na Salamatu, don kinfi kowa sanin matsayinsa a waje na."
Kuma a cikin idanuwan nata, Hajiya Salamatun ta shiga hango abubuwan da suka faru wasu tarin shekaru da suka wuce!
******
11:20 Am
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Wai baka da
imani ne Ishaq? Tun da na tashi kake ta masifa a gidan nan kana mita, nace maka wallahi ko ganin yarinyar banyi ba balle inyi mata wani abu, do I have to bury myself before you believe?" (haƙa kabari zanyi in shiga kafin ka yarda dani?)
Ma'aruf ya fada a
lokacin da yake zaune kan dining table din falon gidansu, inda ya samu ya ture wasu litattafai da kuma kayan wankin Ishaq ya dora plate
ɗ
in abincin da yake ci.
Ishaq na tsaye daga cikin falon shima rike da nasa kofin shayin da kuma remote
ɗ
in da yake koka
rin chanja channel daga ta labaran da Ma'aruf ya kai.
"Ka gayawa wani ba ni ba, na san halinka sarai B, hankalinka ba zai taba kwanciya haka ba idan har ba kayi abinda kake so ba. I'm just advising you (shawara nake baka) komai zai iya faruwa idan har mag
anar nan ta lalace kuma Baffa ya san da saka hannunka."
Ma'aruf yayi murmushi a hankali sanda yake jin zafin faten dankalin dake sauka cikin maƙogwaronsa wanda motsawar Adam's apple
ɗ
insa kadai zai shaida maka hakan.
"Wai ina zaka je ne ma? Yau asabar fa
?"
Ya canja akalar zancen nasu ba tare da ya kalle Ishaq
ɗ
in ba, don tun da farko kayan jikinsa sun riga sun nuna masa cewa Office zai je. Babu adadi na lokutan da zuciyar Ma'aruf ke motsawa a duk lokacin da yaga Ishaq na yin wani abu da ya danganci aikin
sa, aikin da yake so kuma abinda shine mafarkinsa ya fito dashi zahiri kuma yake yi
ɗ
in. Shi nasa burin da kuma mafarkin sun dade da ka
ɗ
ewa shekaru goma da suka wuce. Abinda yake yi a yanzu, ba rayuwarsa bace ko ka
ɗ
an, wata rayuwa ce da ta zama dole ya ƙar
asawa mai ita.
"Thanks to you, nayi missing tarin ayyukan da dole inje in san halin da ake ciki kafin Monday, Idan ciwon ka ya sake tashi Ma'aruf wallahi ka nemi mai raka ka asibiti."
Murmushi Ma'aruf keyi har a lokacin yana cigaba da cin abincinsa yayin
da ƙamshin curry da kuma naman dake cikin abincin ke gauraye
ɗ
akin, ya kai hannu yana cusa yatsunsa cikin gashin kansa, wani abu da ya riga ya zama
ɗ
abi'arsa kafin yace.
"Ka san me Mami take ce min yanzu? Wai inyi aski kafin in shiga gida, don Inna Danej
o na tashi da safen nan abinda ta tambaye ta kenan."
Ba shiri Ishaq shima yayi nasa murmushin kafin ya gya
ɗ
a kai don har ya hango irin rigimar da za'ayi da Ma'aruf din da ba zaiyi askin ba da kuma Inna Danejon da ba zata haƙura, don kafin tafiyarsu London
ta kawo dalilai sun fi ashirin na cewar rashin lafiyar Ma'aruf tana maƙale da gashin kansa ne, Baffa ne kawai bai bada goyon baya ba da tuni sai dai Ma'aruf
ɗ
in ya tashi yaga kansa
ɗ
al!
"Hular sanyi kawai zaka dauka, in zaka shiga wajenta ka saka kace an
yi askin ba'a bude kan ne."
Ya fa
ɗ
i hakan lokacin da ya gama neman abinda yake so a jikin Tvn don haka ya ajiye remote din ya juyo ya kalle shi.
"Za'a kawo maka motar ka ne?"
"Eh, na kira direban Office tun dazu nace yaje ya
ɗ
auka ya kaita Carwash, I'm
sure kafin 12 zai dawo da ita."
Ishaq ya gya
ɗ
a kansa.
"Shikenan mu ha
ɗ
u a gidan, nima can na nufa idan na tashi insha Allah."
Ya fa
ɗ
i hakan yana juyawa hanyar ƙofa, idanun Ma'aruf suka bishi da kallo yana tunanin wani abu, kuma sai da ya isa ƙofar da za
ta fitar dashi waje har ya bu
ɗ
e ta sannan yayi saurin kiran sunansa.
Ya kuwa juyo a take kamar shima dama jiran kiran yake yi. Ma'aruf ya girgiza