Showing 9001 words to 12000 words out of 94381 words

Chapter 4 - Farar Wuta Complete

motar daga baya, wayarsa na riƙe a hannunsa haskenta na haska siririyar fuskarsa da a cikin ƴan kwanakin ta ƙara ramewa, message ne kawai ke tururuwar shigowa da kuma tarin emails

tunda ya kunna wayar har zuwa yanzu, ya lumshe idanunsa kawai sai ka

llonsu yake a lokaci guda kuma yana jin hirar su Ishaq

ɗ

in daga waje.

Allah ya sani gaba

ɗ

aya ya manta cewa shirye-shiryen bikin akeyi sai a jiya da Mamin ke tuna masa cewa yau ne za'a karbi lefen Shukra, kuma jin cewa gidan a cike yake yasa shima baiyi tu

nanin ya kamata su je

ɗ

in ba, amma kuma ya kamata yaga Baffa a yau, idan yana gidan kuma fa? Sai yasa yatsan sa

ɗ

aya ya share dukkan messages

ɗ

in sannan ya lulubo nambar mahaifin nasa amma sau biyu ya buga bata shiga ba, don haka ya nemo ta Mami.

Bugu

ɗ

ay

a kuwa muryarta ta shiga kunnensa.

"Mai gaskiya na, kun taho?"

Ta kira shi da sunan data laƙaba masa tun yarintarsa.

Sai ya sake lumshe idonsa ya koma da baya jikin kujerar lokacin da Ishaq da Baba Sani suka bu

ɗ

e ƙofofin motar suka shigo.

"Eh Mami, Ba

ffa yana gida kuwa?"

"A'a yana office shima har yanzu. Na bayar direban Hajiya Madina zai kawo muku abinci yanzu, wataƙila ma kuyi daidai dashi."

Wani abu ya motsa a kirjinsa, don yayi kewar irin wannan kulawar tata a ƴan kwanakin nan, sai dai kafin ya s

aurari abinda ta cigaba da cewa hankalinsa ya kai ga abinda Ishaq ke cewa cikin wayar sa da aka kira ya amsa.

"To shikenan gamu nan insha Allahu..."

"... Akwai maganar da zamu yi Ma'aruf, nima nafi son ka samu hutu sosai zuwa goben."

Sauran maganar Mami

n ta shiga kunnensa bayan Ishaq ya kashe wayar da yake yi."

"Ma'aruf, kana jina kuwa? Da kaci abinci ka sha magungunan da aka baka "

Yaji ta sake fa

ɗ

a lokacin da Ishaq ke cewa Malam Sani...

"Sakataren Baffa ne yakira, wai Baffan yana son ganinmu a offic

e

ɗ

insa kafin muje gida, ka juya ta wanna U-turn

ɗ

in sai mu koma."

Ba shiri Ma'aruf yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaronsa, don tun bayan farkawar sa sau

ɗ

aya kawai yayi waya da Baffan, a jiya daya kira ta wayar Ishaq, ya tabbatar masa da cewar lafiya

yake jin kansa shikenan bai kara nemansu ba, amma ko Baba Usman ya sake kira a safiyar yau kafin su taho.

Yana jin yadda Mamin ke cigaba jero masa tarin tambayoyi ta cikin wayar amma hankalinsa sam baya kanta har Malam Sani yasha kan U-turn din da Ishaq y

a nuna wanda zai komar dasu baya zuwa hanyar Office

ɗ

in Baffan, wani ƙaton branch na kamfanin su inda iya ma'aikata ne kawai a wajen.

"Muhammad..."

Muryar Baffan ta kira shi kuma a lokaci guda amonta ya ratsa har cikin kansa bayan sun isa Office

ɗ

in, bay

an sun shiga ciki kuma Baffan ya sallami wasu mutum biyu da yake tare dasu a lokacin, sannan bayan Ishaq ya dauki wata wayar ƙarya ya fita don dukkaninsu sun fahimci cewa dashi kadai yake son magana. Don haka ba shiri Ma'aruf yaji maƙogwaronsa ya bushe a l

okaci guda, saboda Baffa baya ta

ɓ

a kiransa da wannan sunan sai idan har wani zance mai muhimmanci zasu yi, kuma rana ta karshe da zai iya tuna ya kira shi da hakan shine ranar da aka daura auren sa.

Ya gyara zama a hankali yana jin yadda Baffan ya cika m

asa office din ta koina saboda kwarjini.

"Sun turo min da takarda wadda take bayanin ciwon naka."

Ya san takardar shima, sun tura ta email

ɗ

insa sannan sunyi printing

ɗ

inta a cikin tarin takardun da aka sallamo shi dasu.

"Sun ce a cikin shekaru biyu kaw

ai ciwon ka ya kara ha

ɓɓ

aka har ya kai matakin karshe, shi yasa abinda kayi ya faru..."

Baffan ya fa

ɗ

i haka sannan kuma yayi shiru, wannan dai al'adar ta manya. Ƙarar sautin shigowar saƙo daga wayar dake aljihun Ma'aruf ya cika shirun dakin kafin ya cigab

a.

"Ko zaka iya gaya min a shekaru biyun baya kana ina Ma'aruf?"

Sai ya gyara zamansa a hankali, yana tuno ranar da Baffan ya na

ɗ

a shi a matsayin manajan kamfanin 'Bakori Enterprises' ranar da burinsa na farko ya fara cika a duniya.

"Baffa... Shekaru bi

yu baya shine lokacin da ka bani matsayin manaja a kamfanin nan."

Bai kalle shi ba, amma yaji sanda ya girgiza kansa.

"Ba wannan ba, rayuwarka personally Ma'aruf, kana ina?"

A yanzu ya rikice, yana jin kamar ma bai warke ba gaba

ɗ

aya, kamar ya sake bin j

irgi ya koma asibitin nan ya kwanta.

"Ka manta?"

Ya tambaya amma bai bari ya amsa ba ya cigaba.

"... Bari ni na tuna maka, shekaru biyu baya kana tare da iyalinka Ma'aruf, shekaru biyu baya kana tare da matar da naje na karba maka aurenta har ma da yari

nya, a shekaru biyu baya kai cikakken mutun ne mai kamala da mutunci a idon mutane, kuma a tsawon shekarun da kayi cikin wannan mutuncin, hankalinmu da naka bai taba tashi kamar yadda yayi a yanzu ba."

Wani abu ya zarce a maƙogwaron Ma'aruf, yaji wani

ɓ

a

ngare na ƙwaƙwalwar sa na gaya masa cewa wannan ce damarsa, yau shine lokacin da zai gayawa Baffa abinda shi da ishaq suka dade suna

ɓ

oyewa, yau ya kamata ya gayawa Baffa cewa ba haka bane, abinda ya faru a zamansa da Ruƙayya har zuwa rabuwarsu ba yadda su

ke tunani bane sam.

"Na san da wannan tunin da nayi maka ka fahimci abinda ni dama duk sauran al'umma suka fahimta Muhammad, don haka kaje ka fara shirye-shirye, nan da wata guda zan kar

ɓ

a maka wani auren tare da na ƙannenka."

Sai da aka shafe sakanni ka

fin maganar ta shiga cikin ƙwaƙwalwar Ma'aruf, da wani irin ƙarfin da sai da yayi da gaske kafin ya iya jawo iska ta shiga ƙirjinsa, sannan a karo na farko tun bayan fitar Ishaq ya

ɗ

ago idanu ya kalli mahaifin nasa.

Sai dai me? Maimakon fuskar Baffan, sai

hoton wajen ya canja a idonsa da wani lokaci da ya faru a shekaru biyu da suka wuce...

Lokacin daya shaƙe wuyan Rukayya da duka hannyensu biyu, yaji ƙarar sautin karkarin da take fitarwa a lokacin da kuma yadda hawaye ke zuba daga idanunta yayin da take

kallon ƴarsu da bata fi watanni shida a sannan ba... Babyn da ya kar

ɓ

e daga hannunta ya wancakalar da ita a cikin falon, kanta ya bugu da kujerar gefe ta shiga ƙwallara kukan daya kara

ɗ

e gidan gaba

ɗ

aya, wannan sautin kukan da a kowanne daren duniya, dashi

yake kwana a kunnuwan sa!

***

Me ya faru shekaru goma da suka wuce?

Wane bincike Ma'aruf ke yi da har ya kai ga tashin ciwonsa?

Wacece Rukayya? Me ya faru da ita da kuma ƴar ta?

Sannan wacece amarya ta hu

ɗ

u a bikin iyalan gidan Alhaji Mansour Bakori?

#Aysha Shafi'ee.

#FikraWriters

#FararWuta.

BABI NA UKU.

****

A wannan daren...

NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.

.

A cikin ƙawataccen

ɗ

akin, wata yarinya ta bu

ɗ

e ƙofar ta shigo, ba zata fi shekaru uku da ka

ɗ

an ba, tana sanye da irin kayan

yara kamarta, wani

ɗ

an gajeran skirt kalar lemon greeen, (lemon tsami) sai farar rigar da itama akayi mata da ado da irin kalar, gashinta da ba wani yawa ne dashi haka zalika tsawo ba an tufke shi cikin kalba guda biyu da ribbon masu kalar kayan.

Ta karas

o cikin

ɗ

akin daya gauraye da sanyin A.cn da aka kai maƙurarta, akwai wani tebur irin na ado dake gaban hadadden gadon dakin, ta kansa ta taka ta isa kan gadon, ta hau tana bi ta kan ƙafafun wadda ke kwance har ta isa daidai fuskarta da ta rufe da bargon d

ata lulliba gaba

ɗ

aya.

"Mammy Mammy Mammy...."

Ta kira ta na bubbuga daidai kanta da ƴan hannayen nata, a lokaci guda mahaifiyar tata ta yaye bargon daga fuskarta ta bu

ɗ

e idanunta da kyar tana kallonta.

"Menene Hameeda? Me ya kawo ki?"

Ta tambaya ranta

a

ɓ

ace.

"Mammy I'm hungry. (Yunwa nake ji.)"

Taja tsaki a hankali.

"Ina Nannynki?"

Sai kawai ta miko mata takardar hannunta, kamar ba zata karba ba sai kuma ta yatsunta biyu ta sakala ta cikinsu sannan ta bu

ɗ

e ta.

'Ajiya I'm sorry Oo, dey don call m

e now say my mother dey hospital. I'll return tomorrow by God grace.'

Ta sake jan wani tsakin mai tsayi, bata san sau nawa take gayawa Mary cewar ta daina yi mata pidgin a gida ba, amma don rashin mutunci shine har rubuto mata take yi a takarda.

Ta juya

ta sake kallon yarinyar data tsura mata idanu, dogwayen gashin idanunta sun kusa ha

ɗ

ewa da juna, yadda take lumshe su ya tuna mata da fuskarsa a lokaci guda.

...idanunka kake gani ko Ma'aruf? Irin naka ne sak!

Muryar Mami ta haska a cikin kanta ranar far

ko na zuwan Hameedan duniya, ta tuno fuskarsa, yadda ya kalmashe ta cikin hannunsa, lumsassun idanunsa na haskawa da tarin ƙaunar da kamar wani abu ba zai ta

ɓ

a giftawa a cikinta ba.

Ruƙayya ta sake yin wani tsakin da ya riga ya shiga cikin dabi'arta kafin

ta ture bargon gadon ta miƙe, wata lallausar doguwar rigar bacci ce a jikinta da idan ka kalle ta zaka ga kamar tana zamewa ne tsabar santsi da kuma kyallin da take yi.

Ta kalli agogo wajen karfe bakwai na dare.

"Baki ci abinci bane da rana?"

Ta tamba

ya tana daure gashin kanta da za'a kwana a yini ana musu da wani akan cewar nata ne, don human hair ne (gashin mutum) da aka dinka mata shi cikin nata ya saje tsaf!

"Mami tun da na sha tea, Mary bata bani komai ba. Waya take ta yi."

Gwarancin yarinyar ma

i da

ɗ

i ya fito tana kallonta. Wani tsakin ta sake ja kafin ta dauki wayarta sannan tace.

"Oya, taho muje to."

Da sauri yarinyar kuwa ta sauko tabi bayanta, suka fita daga

ɗ

akin zuwa wani dogon korido daya hada fuskokin

ɗ

akuna, suka isa wani rantsatstsen

falon da komai na cikinsa kalar ruwan gwal ne da kuma makuba, a gefensa akwai matattakalar bene, suka sauka har kasa zuwani falon da yafi wannan girma, ta jikin dining area suka shiga wata kofar da take ta kitchen ce, wani katon kitchen da yake a gyare tas

.

Babu ko tukunya guda daya akan gas don haka ta san babu wanda ya dawo a cikin kannen nata uku maza, suma can yawonsu waye ma zai gansu yanzu da magaribar nan? Dama Ashraf mai bi mata ne idan ya dawo daga aiki sau da yawa zai shigo ya dafa abincinsa tun

bayan da suka rasa Josh (mai yi musu girki) yanzu kuma yayi aure sati uku da suka wuce don haka babu mai shigowa kitchen din.

Hameeda ta

ɗ

ane kan

ɗ

aya daga cikin kujerun da suka zagaye worktable din kitchen din sannan ta zuba mata idanun tana jiran taga

me zata yi, Allah ya sani ita bata son wani girki yanzu, da safen nan fa dawowarta kenan Nigeria daga ƙasar Paris inda suka tafi ita da mahaifiyarta, shi yasa ta kwanta take ta shar

ɓ

ar baccin ta kuma yanzu ta tashi ta kama girki?... sai kawai ta dago da wa

yarta ta shiga nemo nambar Mariya, babbar ma'aikaciyar gidan.

"Hajiya barkanmu da safiya. Ina kwana." Muryar dattijuwar ta cika kunnenta, bata ko amsa ba tace.

"Mariya, abinci zaki kawowa Hameeda yanzu, a dafa mata duk abinda zata iya ci kawai."

Daga ci

kin wayar Mariyan tace.

"Hajiya ai bana gidan, yau kwana na uku a madobi, mahaifina ne ya rasu wallahi, amma su Jamila da Aisha suna nan."

Ta

ɓ

ata rai a lokaci guda don ta manta lokacin da suna can taji mahaifiyarta ta na fada, sai kawai tace.

"Allah ya

jiƙansa." sannan ta kashe wayar.

Ba zata yarda ƴarta taci abincin wa

ɗ

annan kazaman yaran ba su tsaya a iya gyaran gidan da suke yi kawai, don ko Mama Mariyan ma da suka saba da ita tun yarintarsu ba kowanne girkinta suke ci ba, tunda Josh ya mutu shikena

n kowa ya ta'allaƙa akan siyan abinci a waje tunda dama gidan ƴan maza ne ita kadai ce mace.

"Hameeda me zaki ci?"

"Mammy banda indomie." Ta fadi hakan alamun da gaske ta gaji da cin indomien, haka yasa ta gane cewar Indomie kawai Maryn ke

ɗ

ura mata da b

asa nan don haka ta gya

ɗ

a kai kawai.

Ta ajiye wayar akan table din sannan ta juya ta shiga store, ta fito da kwai guda uku a hannunta, ta kunna ruwa a kettle sannan ta fasa kwan ta soya shi cikin ƴan mintuna, ta ha

ɗ

a mata tea da ruwan zafin da yayi sannan

ta

ɗ

auko biredi a fridge ta saka mata kwan a tsakiyar, ta zauna a kusa da ita tana kallon murnar dake kan fuskarta sanda ta fara cin ƙwan, har yanzu bata kai shekara hudu ba amma tsaf ta iya cin abinci da kanta, sai kawai tayi murmushi sannan ta janyo way

arta.

Ta shiga whatapp tana fara ganin yadda messages ke tururuwa har da sababbin nambobi, sai da suka gama tsaf sannan ta danna kan sako guda

ɗ

aya mai sunan Jawad da mintuna biyu kawai akayi da turo shi.

"Baby kin dawo ko? I'm badly missing u here... Za

nzo anjima kinji." (Ina mutukar kewar ki anan.)

"Mammy nayi missing dinki."

Muryar Hameeda ta katse ta daga amsar da take shirin rubutawa. Ta juyo ta kalle ta, tana ta cin biredin da sauri alamar da gaske yunwa take ji. Itama tayi kewarta da gaske shi ya

sa ma ta kasa jiran Maamah ta taho. Bayan bikin Ashraf ne suka tafi Paris

ɗ

in ita da mahaifiyarta don medical check-up kasancewar hidimar bikin ta wajiga su da yawa, kuma satinsu

ɗ

aya acan ta gaji ta taho don ranar da suka tafi ma Hameedan na bacci a hannu

n Mary ko sallama basu yi ba.

Allah ya sani ta fara gajiya da wannan rayuwar, ba haka take hango ta ba sam, ba haka ta dinga hango abubuwa ba lokacin da mahaifiyarta dama kawayenta suka bata goyon bayan kashe aurenta ba, Maamah cewa tayi...

"Idan baki f

ito daga gidan nan ba kin kusa kashe kanki ki tsufa a banza Ruƙayya, ta yaya zaki zauna babu wani isasshen hutu sannan kuma ki fara tara ƴaƴa bi da bi? Yanzu kika fara rayuwar ki fa, kina da dama mai yawa a gabanki Rukayya."

Haka take gaya mata kullum, sh

i yasa ta rufe idanunta a wancan lokacin ta danne zuciyarta tayi abinda ya fito da ita

ɗ

in, kuma har bayan aurenta da Alhaji Ahmad, tafiya take akan wadannan kalaman na mahaifiyar tata, takunsu take bi har ya kai ga mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad

ɗ

in shim

a, kuma ko a yanzu ma bata fasa gaya mata cewar komai kaddara ce ta cigaba da cin ganiyarta ba, amma ita ta sani cewar bayan wannan ƙaddarar har da ƙaddarar zuciyarta akansa shi ma.

Ta san duk irin halayen da zuciyarta ta shiga a gidan Alhaji Ahmad, ta sa

n duk irin wahalhalun data fuskanta a kowanne lokaci na zamanta a gidan yadda ta dinga kwatanta abubuwa a gidanta na farko da kuma nasa tana ganin bambanci su a baiyane har suka kai ga matakin ƙarshe na mutuwar auren, don Maamah bata ta

ɓ

a sani bane, amma M

A'ARUF shine sanadiyar mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad.

Kuma ko a yanzu da kowa ke kwa

ɗ

aita mata auren Jawad, ita ta sani cewar abinda ya faru shi zai sake faruwa, babu wanda zai ta

ɓ

a iya cike gurbin Ma'aruf a ranta, ta so shi tun bata ma san kanta a duni

ya ba balle ta san menene son, ta so shi da dukkan kowanne bangare na ruhinta, don rayuwarta ma gabadaya tare dashi ta gina ta.

Iyayensu maza abokan juna ne tun da dadewa, saboda haka ba zata taba iya cewa ga ranar data san Ma'aruf ba, tayi wayo ne kawai

a duniya tana iya lissafo shi a cikin abubuwan da ta sani na rayuwa, don haka kowa ya sani cewar tsananin kulawar da take yi masa shi ya janyo hankalinsa akanta shima har ya kai ga soyayyar su.

Sai dai a lokacin da ta aure shi, ta auri wani Ma'aruf din ne

daban sa

ɓ

anin wanda ta sani, ta san hakan don yasha gaya mata cewa Ma'aruf din data sani ya mutu babu ko da digonsa a cikin zuciyarsa, amma ta rufe idonta daga komai tace taji ta gani har aurensu ya tabbata.

Auren da tun a darenta na farko a gidan abubuw

a suka yi juyin waina daga yadda take hasko su. Ta rufe idanunta a hankali tana tuna dukkan abubuwan da suka faru a wa

ɗ

annan shekarun, irin wahala da barazanar da rayuwarta ta fuskanta, sai dai ashe bata san gwara su sau dubu akan abinda zata je ta tarar a

gaba ba, don a yanzu ta gane abinda taso ta manta a baya, cewar duk duniya Ma'aruf ne kadai namijin daya tattara duk wasu halayen da take so a wajen namiji. Shi yasa bata son sake maimaita kuskure na uku a yanzu, bayan guda biyun da tayi a baya na fitowa

daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login