Showing 63001 words to 66000 words out of 94381 words

Chapter 22 - Farar Wuta Complete

ba, sun koma baƙiƙ-ƙirin dauke da kyallin kwalla yayin da fuskarsa ke nuna dukkan wasu kalolin tashin hankalin da bata ta

ɓ

a gani a fuskar Aminun

ba, Aminun mai raha da fara'a, Aminun data sani mai

ɓ

oye damuwarsa a kodayaushe.

"Me yasa kika kasa Amina?"

Muryarsa ta sake tambaya da amon da ya kara hargitsa ta, kuma bata san lokacin da ya matso gabanta ba sai kawai taji ya riƙo hannunta na dama.

Ta kalli inda hannun nata ya kamata ya kasance, babu komai sai yadda yatsunsa suka riƙe ta, lokacin da ta

ɗ

ago da idonta sai taga ashe ya jawo ta ne har sun iso wajen duhuwar bishiyun nan, tashin hankalin ta ya ƙaru don tana jin yadda ƙafafunta da basa nan

suke tafiya, da kuma yadda hannayenta ke rawa a cikin nasa.

Hankalinta ya kasu wajen nazarin bishiyun sanda suka tsaya a wani waje, ta juyo tana kallon yadda yanayinsa ke haskawa da dukkan raunin da bata ta

ɓ

a hange ba, taji ta ƙara rikicewa, taji abubuwa

da yawa suna tasowa cikin kanta, tambayoyi fal suna ihu da kokawar fitowa daga bakinta da ta san babu shi balle har ta iya furta su, kowanne lungu da saƙo na tunaninta ya cika da hanƙoro, kamar tana jiran wani abun da bata san meye ba.

Kuma kwatsam sai t

a nemi bishiyun nan dake kewaye dasu duka ta rasa, warin ƙonewarsu ya cika hancinta amma babu su

ɗ

in balle kuma alamun wutar, kuma babu wani

ɓ

ata lokaci kunnenta ya fara jiyo mata muryoyinsu, Maryam ta fara ji, tana ihu mai ha

ɗ

e da salati, sai ta jiyo ta H

afsa da Adam ma, kowanne yana kuka mai nuna tsananin azaba, bata san ya akayi ta iya tsinto muryoyin su Fatima, Ummi har ma da ta wasu daga cikin ƴaƴan kawu Malam ba.

Kuma kafin wani abu ya sake giftawa a cikin kanta ta jiyo muryar Baba yana faman kiran s

unayen su Maryam

ɗ

in har ma da sauran mutanen da bata iya tantance muryoyinsu ba, hankalinta ya kara tashi duniyarta ta rikice, ihu da hargowar suka cika kanta kota'ina, kuma a lokacin da ta juya zata kalli Aminun sai taga babu shi, a yanzu Amma ce tsaye t

ana kallonta, fuskarta

ɗ

auke da wani irin murmushi mai ciwo yayin da take kallonta da dukkan wani fata na duniya.

"Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina?"

Tayi tambayar a lokaci guda da itama ta neme ta ta rasa, wajen ya koma babu komai sai tashin ihun

ƴanuwanta da kuma hargowarsu yayin da warin ƙonewar nan ya cigaba da cika wajen. Ta kasa gane komai ko kuma abinda yake shirin faruwa, abinda kawai zata ita tunawa kafin ta farka shine daga cikin muryoyin dake ihu, ta jiyo wata murya da ta kasa gane wacec

e ko kuma inda ta santa, muryar tana ƙyalƙyala wata irin dariyar da bata ta

ɓ

a jin irinta ba!

Dariyar ta shiga amsa kuwwa a kowanne

ɓ

angsre na wajen yayin da ihun mutanen dake amsa sunan rayuwarta ke cigaba da tashi.... A lokacin ne kuma ta farka a firgice

, kafafunta suka mike tsaye akan gadon bakinta na biyo kalaman Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, a cikin

ɗ

akinta take har yanzu, akan gadon da bacci ya

ɗ

auke ta, amma tun yaushe? Don rediyon wayarta da ta bari a kunne yanzu ƙarar shuuuu kawai take fitar

wa.

Tasa hannu ta jawo ta da sauri, ta kashe rediyon tana neman lokaci, karfe

ɗ

aya da rabi na dare, wani salatin ya sake su

ɓ

ucewa a bakinta cike da mamakin yadda akayi tayi bacci mai nisan haka, sai kawai ta wullar da ita gefe ta janyo dankwalinta daya za

me akan filon data kwanta tayi saurin

ɗ

aure kanta, koina a jikinta rawa yake har yanzu yayin da mafarkin ke ƙara dawowa cikin kanta, bata fahimci komai a cikinsa ba amma Allah ya sani ta tsorata sosai da yadda abubuwa suka faru don bata iya tunawa idan ta

ta

ɓ

a irin wannan mafarkin a rayuwarta.

Taji maƙogwaronta ya bushe yayin da amon muryar nan dake dariya a cikin mafarkinta ke dawo mata, bata san me hakan

ke nufi ba, bata san waye zaiyi dariya alhali tashin hankali irin wannan yana faruwa ba, kuma har a

yanzu tana jin cewa kamar ta san muryar amma ta kasa tabbatar da inda ta santa.

Makogwaronta ya ƙara bushewa yayin da take kokarin saita zuciyarta da har yanzu ke bugawa, ta sauko daga kan gadon, wata doguwar riga ce a jikinta ta bacci da bata kai ƙasa ba

ta gaba, don haka kusan tun daga saman gwiwoyinta a waje suke, kuma ba tare da tunanin komai ba tayi hanyar fita daga

ɗ

akin.

Kitchen zata je ta

ɗ

auko ruwa, wataƙila zai iya wanke bugawar da zuciyarta ke yi bayan ƙishirwar, idan ta dawo tayi sallah raka'a

biyu kuma, watakila tunaninta zai iya komawa daidai.

Jikinta na rawa har a lokacin da ta isa kitchen

ɗ

in, ta bu

ɗ

e ƙofar a lokaci guda da hasken fitilar da aka kunna ya shiga idonta kafin shi, yana zaune daga kan worktable

ɗ

in tsakiya na kitchen din, fiti

lar dake saman wajen ita ce a kunne da labtop a gabansa yana danne-danne, a gefe kuma foodflask

ɗ

in abincin data dafa ne.

Kuma duk da rikicewar da take ciki, ta gane cewar babu riga a jikinsa, wata bakar singlet ce kawai da ta fito da fa

ɗ

in kafa

ɗ

unsa ta k

owanne gefe, shima ya dago daga kan labtop din yana kallonta daidai lokacin da ta bude ƙofar.

"Me ya faru? Me ya same ki?"

Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, kuma ba shiri wani abu ya zarce maƙogwaronta jin yadda muryarsa ta fito a cikin shirun daren ta

na gaya mata kamar har yanzu a cikin mafarkin take, sai ta

ɗ

aga girgiza kanta kawai da sauri sannan ta sake ha

ɗ

iye abinda ke bakinta kafin tace.

"Ba komai, ruwa zan

ɗ

auka."

Da haka ta saki hannun kofar ta nufi wajen fridge, Ma'aruf ya bita da kallo zuwa

wajen fridge

ɗ

in, yanayin fuskarta a firgice yake sosai duk da kokarin da tayi wajen

ɓ

oye hakan, kuma ko daga yadda muryarta ta fito ya san akwai wani abun, da wuri tayi bacci ya sani don bayan ya dawo yaga alamun hakan duk da yau cikin gida kawai ya wuce

wajen Mami, acan yaci abincin darensa ma bayan sun tattauna maganganun da yasa ta kira shi, zancen Hamida.

Kuma bayan ya shigo ya tarad da nata abincin jere a falo, haka kurum sai yaji wani iri, sai yaji kamar bai kyauta ba, ya sani ba zata ji dadi ba ida

n har ta farka ta ganshi a yadda ta ajiye tunda jiya ta bashi kuma yaci.

Bai tsara komai tare da ita ba, abinda ya sani kawai shine aurensu zai zame masa garkuwa ne har lokacin da zai gama da case

ɗ

in dake gabansa na kamfanin nan kafin ya fara binciken da

zai shafe ta. Amma tun jiya da yaci abincin nata, sai yaji wani gefe a zuciyarsa ya kara nutsuwa da ita, har yana gaya masa gwara nata ma akan na Mami, tunda aƙalla ya san ita tayi da kanta, na Mamin kuma idan Samirah bata nan masu aikinta ne kawai.

Don

haka dole a yanzu da ya

ɗ

ebo aikin daya shirya zai kwana akansa, ya

ɗ

auko abincin daga falo ya taho kitchen tunda babu Dining area a gidan, kuma ba yunwar yake ji ba amma da ya zuba ya fara ci sai yaji kamar dama bai ci komai ba, yaji hankalinsa ya sake nu

tsuwa sannan aikin da yake yi na tafiya akai-akai yayin da dukkan maganganun da suka yi da Mamin akan Hamida ke dawowa kansa kafin ta shigo a yanzu da yanayinta a hargitse.

Sai kawai ya tura kujerar da yake kai baya ya mike tsaye.

"Wani abu ne ya same ki

?"

Ya sake tambaya yana tahowa inda take shirin bu

ɗ

e fridge

ɗ

in, kayan jikinta yake kallo a yanzu, kamar na bacci ne... wata riga mai tsawo daga baya amma daga gaba kamar an guntule ta har wajen gwiwarta, don haka kafafunta na tsaye a waje, kuma bai san m

e yasa ba sai yaji wani abu a zuciyarsa na yabawa da yadda

ɗ

ankwalin kanta yayi kala

ɗ

aya da rigar, Pink. Kallonsa take yi itama, idanunta farare na nuna dukkan wani alamun tsoron da ba sai ta furta ba, don haka kai tsaye cikin hasashensa ya sake tambaya.

"Mafarki kika yi?"

Amina bata san lokacin da ta

ɗ

aga kanta ba don kayan jikinsa a yanzu sun karawa rikicewarta tasiri, bayan baƙar singlet din nan, three-quarter din wando

ne kuma a jikinsa wanda da kadan ya wuce gwiwa, sannan ga muryarsa mai zurfi da ta

ji tana tayar da wasu abubuwa akan fatar ta bayan rawar da jikinta ke yi.

Kuma bata yi aune ba sai jin hannunsa kawai tayi ya riƙo nata

ɗ

aya, ya jawo ta zuwa wajen kujerar daya taso ya zaunar da ita a ta gefen inda yake zaune kafin shima ya zauna.

"Kinyi

addu'a?"

Tambayar ta tuna mata da abu na farko da ta kamata a e tayi, amma tsabar rikicewar da tayi, zuciyarta bata kawo mata wannsn lissafin ba, sai ta girgiza ksnta a hankali don ko tayi ƙokarin yin ƙaryar ma bata san me zata ce ba, ba zata iya wani tu

nani mai kyau ba slhali har yanzu yana riƙe da hannunta sannan ga kafafuwanta tun daga kan gwiwarta a waje daga ƙasan rigar nan, bama za'a lissafa da kayan jikinsa ba...

"Suratul Ikhlas sau uku, Suratul Falak sau uku, Suratul Nas sau uku..."

Muryarsa mai

zurfi ta sake fa

ɗ

a yana kallonta, bata da wani zabi sai ta rufe idanunta, ta ha

ɗ

iye yawu a maƙogwaronta kafin a hankali bakinta ya shiga karanto su, bata jin sautin muryarta yana fitowa amma tana kaiwa karshe, ya sake cewa.

"Ayatul Kursiyu..."

Ta kai ƙa

rshe lokacin da taji kamar almara, ƴar rikicewar tata na bin iska, kuma shirun da yayi riƙe da hannunta bai saki ba wani abu ne daya saita numfashinta daga hawa da saukar da yake faman yi, taji kamar hannayen nasa sunyi wa nata wata rumfa ne ko kuma sun za

ma wani bango da ba abinda ya isa ya ratsa ta cikinsu ya cutar da ita, don haka a hankali nutsuwarta ta fara dawowa jikinta.

"Mafarki ba gaskiya bane, daga shaidan yake zuwa ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru insha Allah."

Sai kawai ta gyada k

anta a hankali yayin da take ture dukkan wani tunani daga cikin kanta tana yarda da kalaman nasa don ta samu zuciyarta ta dawo daidai, Mafarki ba gaskiya bane, ta shiga biyawa zuciyar tata layi bayan layi.

Abinda bata sani ba a wannan lokacin shine, wani

lokacin mafarki na juyewa tamkar mudubi, ya nuna abinda zahirin ke iya haifarwa!

***

Ƙ

arfe bakwai na safe.

Idan akwai wani abu daya rage a rayuwar Ma'ruf ta baya, shine ƙaunarsa da football (ƙwallon kafa) shi ka

ɗ

ai ne abu guda

ɗ

aya bayan sunansa da kuma

kamanninsa da zai ce basu canja daga Ma'aruf

ɗ

in da yake a baya ba, Ma'aruf

ɗ

in da yake kafin rasuwar Jamal, amma duk wani abu bayan hakan komai da yake yi ba rayuwarsa bace.

Son football

ɗ

in ne kawai yayi yawa a zuciyarsa da ba zai iya barinsa ba, shi y

asa yawanci duk weekend da safe yana stadium

ɗ

in Sani Abacha, team ne dasu guda da suke da ranakun yin wasa da kuma ranakun training, sannan yana

ɗ

aya daga cikin members

ɗ

in dake kula da wajen ma, duk wani taimakon harkar kudi da ake yi a wajen su suke bad

awa, idan ya gama ya fito haka zaka ga samarin nan ma'aikatan wajen sun biyo bayansa har wajen mota don ya sallame su, don haka babu wanda bai sanshi ba a wajen.

Yau asabar can yayi niyyar zuwa don tun da ya dawo daga sallar asuba ya shirya, amma yayi-yay

i da motarsa taƙi tashi, jiya lafiya lau ya ajiye ta kuma a saninsa bata da wata matsala amma sharrin karfe ance ba abinda ba zai iya ba, haka ya hakura ya rabu da ita, sai kawai ya fito da ball

ɗ

in sa daga booth

ɗ

in motar ya shiga training

ɗ

in da ya saba

a compound

ɗ

in gidan.

Kusan ƙarfe bakwai da rabi lokacin da wayarsa tayi ƙara daga can saman motar inda ya ajiye ta, kuma sai da ya kai ball din sama sau biyu sannan yazo ya

ɗ

auka, Martha ce.

"Barka da safiya sir, RTL sun bugo waya cewa yau zasu sauka a

Kano, don haka meeting din zai zama karfe hu

ɗ

u na yamma."

Ta zayyano dukkan bayanin da harshen turanci, hannunsa ya zura cikin kansa don kwata-kwata ya manta da zancen cewa zasu iya yin meeting din a yau, yayi niyyar babu inda zai fita zai zauna ya huta n

e don Allah ya sani ya aikatau a cikin satin nan gashi jiya ma bai wani samu bacci mai yawa ba. A hankali ya cije le

ɓɓ

ensa yayin da ta cigaba da yi masa bayanin cewar sunyi waya da Faruq da sauran board members

ɗ

in nasu ta shaida musu komai, shi gabadaya y

a manta ma da nasa takardun da ya kamata ya karanta kafin a shiga meeting din jiya a Office.

"Sannan kuma Sir ka manta papers na background Information din a Office, dole zaka buƙace su kafin a shiga meeting

ɗ

in."

Ya sake motsa hannunsa a cikin gashin ka

nsa.

"Na sani Martha, yanzu kuma ban san ya za'ayi ba gashi motata taƙi tashi, amma bari na kira Ishaq sai a

ɗ

auko min tasa."

"Okay sir." Ta amsa muryarta a ƙasa.

Da haka suka gama wayar sannan ya shiga laluben nambar Ishaq

ɗ

in da har yanzu bai dawo ba,

bugu

ɗ

aya biyu kuwa ya

ɗ

aga.

"A ina ka ajiye muƙullin motarka?"

"Me za'ayi?" Ishaq

ɗ

in ya amsa daga cikin wayar.

"Motata ta samu matsala ne kuma ina da meeting anjima."

"Ka kira Jamilun?" (Makanikensu.)

"Ban kira shi ba, tunani nake sai anjima tukunn

a saboda gaba

ɗ

aya na manta da meeting

ɗ

in ne."

Dariya Ishaq

ɗ

in yayi daga ciki yace.

"Wallahi tayar motar nan a sace na tafi na barta, I don't know ma ya take take yanzu."

Ya girgiza kansa kafin yace.

"Baka da amfani."

Da haka ya kashe wayarsa, ya kir

a Malam Sani.

"Yalla

ɓ

ai Barka da safiya."

"Barka dai Malam Sani, nace dan Allah akwai mota a cikin gida ne?"

"Ai kuwa Babu ranka ya da

ɗ

e, don su Baffa sun tafi gona a tasa shi da Baba Usman, ta Hajiya kuma a tsaye take tun wancan watan don haka na baro

za'a kaita asibiti da ta Mami, school bus din kuma ka ganni da ita a ƴankaba."

Sai kawai ya gya

ɗ

a kansa alamun ya fahimta kafin suyi sallama ya kashe wayar, Martha ya sake kira yace ta kira direban kamfanin nasu kawai ya kawo ta kawo masa takardun.

Da ha

ka ya mayar da ball

ɗ

in cikin booth

ɗ

in motar sannan yayi hanyar cikin gidan, ya shiga cikin falon ya shiga cikin a lokaci guda da ƙamshin wani air freshener mai sanyi ya shiga hancinsa, yana tabbatar masa da cewar matar gidan ta tashi kenan, ya nufi hanya

r dakinsa don yayi wanka ya shirya yayin da yanayin fuskarta a jiya da daddare ke haskawa a idonsa da kuma wa

ɗ

annan siraran ƙafafun nata.

***

Ƙ

arar kwankwasa kofar gidan ta shiga kunnen Amina a lokacin da take kammala aikinta na karshe a kitchen, ta san

ba Ma'aruf bane, don a yanzu ƙwaƙwalwarta

ta haddace yanayin nasa bugun kofar duk da ba kullum yake manta mukullinsa ba.

Ta kashe gas

ɗ

in da sauri sannan ta goge hannunta kafin ta fito, har yanzu wani iri take jin jikinta, mafarkin jiyan nan dana abinda y

a faru bai gama barin tunaninta ba sam, don bayan ta koma

ɗ

aki a jiyan bata iya komawa bacci ba, sallah tayi sannan ta zauna tunane-tunane har lokacin asuba, kuma sai bayan asubar sannan bacci ya

ɗ

auke ta, baccin da baiyi nisa ba ƙarar wani abu ta tashe ta

.

Kuma ba'a dade ba wata yunwa ta dame ta, don haka a gurguje ta karasa karatun Azkar

ɗ

inta sannan tayi wanka kafin ta fito zuwa kitchen, inda anan ta hango Ma'aruf ta cikin sliding windows

ɗ

in dake wajen sink yana ball, ta fahimci ƙarar data tashe ta ken

an. Yana sanye da wata loose-fitted riga fara kal, da bakin wando irin na sports, (track pants) da kuma takalmin ball, rigar ta fito da ƙirar jikinsa sosai, sannan yadda yake juya ball din a kafafunsa cikin kwarewa ya tabbatar mata cewar da a cikin filin b

all yake tabbas zai iya yin kokarin ture kowa ya ci.

Ta da

ɗ

e tsaye tana kallonsa cike da mamaki, don bata ta

ɓ

a tunanin mutum so committed kamar shi zai samu irin wannan lokacin ba, ta fahimci a kullum ƙara sanin wasu halayensa dake bata mamaki take kuma h

ar yanzu ba'a zo kan wani abu guda da tayi hasashensa game dashi a baya ya zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login