Showing 12001 words to 15000 words out of 94381 words

Chapter 5 - Farar Wuta Complete

gidansa har kuma da auren Alhaji Ahmad.

Ta riga yankewa kanta shawarar cewa ba zata sake biyewa kowa ba, ra'ayin zuciyarta kawai zata bi, zata samo yadda zata koma cikin rayuwar Ma'aruf

kotawacce hanya kuwa, kuma bata ma tunanin cewa hakan zaiyi mata

wuya tunda tana da abinda daga shi har iyayensa zai kassara su. Hameeda...

Tayi murmushi tana sake kallon yarinyar, lokaci yayi da a yanzu zata san waye mahaifinta!

***

A wannan daren....

Na baki amanar rai na, daiman

Yau zaki ceton raina, abadan

Ki

n ƙulle mini kwa

ɗ

on raina, da'iman

Ki taho, raina yana sururi numfashina kece abadan dai'man!

"Maryam dan Allah ki kashe waƙar nan, dan Allah."

Amina ta fa

ɗ

a tana hararar rediyon da Maryam din ta kunna, ta jingina ta da langa-langar langar kitchen

ɗ

insu

yayin da ita take ciki tana girki.

"Haba mana Yaya, kin san yadda nake son irin waƙoƙin nan fa, kuma yanzu zasu cire ma don wani shirin zasu fara."

Maryam

ɗ

in ta fa

ɗ

a daga cikin kitchen

ɗ

in, kuma jin tayi shiru yasa ta kara da...

"Idan ana yi wallahi j

i nake kamar in tashi sama don dadi, da wayarki android ce ai da har sai kin gaji da jin su ma."

Amina ta girgiza kanta daga kan tabarmar da take zaune Hafsa a kwance akan cinyar ta tana tsefe mata kalbar da ta ba

ɗ

e ta tsaf da wani sabon yashi da aka zube

a layin nasu inda yara kamarta ke tururuwar wasa.

"Ni basu dame ni ba sam, kawai a yanzu ne ban ga amfanin jin waƙar ba tunda kin san abinda yake faruwa."

Jin haka yasa Maryam

ɗ

in tayi shiru tana cigaba da yanka cabbage

ɗ

in dake hannunta, kuma a daidai

lokacin ma suka cire waƙar, muryar wani ma'aikaci daga gidan rediyon ta fara gabatar da shiri na gaba a jerin shirye-shiryen su, amma tuno abinda ke faruwar kamar yadda Amina tace, yasa Maryam ta ajiye wuƙar hannunta ta taso ta kashe rediyon gaba

ɗ

aya.

A j

iya da Baba ya fita zuwa kiran Hajiya Kilishin da yace, bai dawo ba sai wajen sha

ɗ

aya saura na dare har su Hafsa da Adam sunyi bacci a sannan, wanda hakan wani abu ne sabo a wajensu, wani abu daban, saboda ba don sun kira shi a waya har ya

ɗ

auka ba ma, Am

ina ta san tsaf Amma zata iya saka hijabinta a daren ita da Aminu su fara tafiya nemansa.

Shi ba mutum ne mai dadewa a waje ba musamman idan dare yayi, abubuwa da yawa komai muhimmancin su in har dare ya raba to zai ajiye su ne sai zuwa gobe, ko hirar ma

za irin ta daren nan Baba baya ta

ɓ

a zaman yinta, tun suna yara sun taso da sanin cewa lokacinsa da daddare nasu ne, a cikin iyalansa zai zauna ayi wasa da dariyar da a cikinta zai fahimci dukkan matsalolinsu.

Don haka a jiyan da ya kai goma sha

ɗ

ayan dare

dole zuciyoyinsu suka kasa nutsuwa sai lokacin da suka ji ƙarar shigowarsa da kuma rufe kofar gidan da yayi, babu wuta a lokacin, sannan Aminu ya fara tararwa jingine da bango yana danna wayarsa.

Kuma ta cikin

ɗ

an hasken fitilar tsakar gidan da batiranta

suka gama yin sanyi, Amina ta hangi fuskarsa tattare da dukkan wani nau'i na damuwar dake fitowa har a cikin sautin muryarsa sanda yake amsa gaisuwarsu, gaisuwar da daga ita bai sake cewa komai ba, ya nufi hanyar

ɗ

akin sa kawai ya shige.

Amma ta

ɗ

ebi kwa

nukan abincinsa ta bishi dasu yayin da suma kowa ya kama hanyar makwancinsa, Aminu yayi hanyar soro inda ƙofar

ɗ

akinsu shi da Adam take, su kuma suka dauki Hafsa suka shige nasu dakin, kuma ba sai ta tambaya ba, Amina ta sani daga ita har Maryam da Aminun

babu wanda yayi baccin kirki

a ranar. Kuma babban abinda ya ƙara tsurar dasu shine na yadda har a yau basu ji komai ba, ko daga bakin Amman kuwa.

Baban bai ko je aiki ba a yau, tun safe ya fita zuwa gidan wansa da suke kira da Kawu mallam kuma bai dawo ba

har yanzu, Amman ma kusan a daki ta yini tun bayan fitarsa, ita kadai tayi ta kai kawo a gidan bayan sun tafi makaranta, tace mata wai gyaran durowarta take yi, amma tsaf Amina ta sani cewa kayan nata data barbaza akan katifar

ɗ

akinta ba don ninki ta fito

da su ba saboda yanayin dake fuskarta kusan iri daya ne da wanda ke kan fuskar Baba tun a jiya da daddare, kuma wajen la'asar sai ga kiran Baba a wayar Aminan cewa Amman taje ta same shi a gidan Kawu mallam

ɗ

in, wanda hakan shine abinda ya ƙara

ɗ

aga hanka

linta, da ƙyar Aminu ya shawo kanta bayan sun dawo daga makaranta kafin ya tafi wajen aikinsa shima.

Sai dai kafin ta bawa Maryam amsa, Adam yayi sallama yana shigowa.

"Salamu alaikum, wallahi Yaya yarinyar nan ƙarya take, babu wanda ya ture ta, wasan ba

nzan su kawai suke yi, ga sauran ƙawayen nata can ma har yanzu a kusa da yashin."

Ya zayyano dukkan wannan bayanin daga tsaye kasancewar shi yaje ya zaƙulo ta tsakiyar masu wasan yashin. Da jin haka kuwa Hafsa tayi narai-narai da muryarta ta shiga rantsu

wa tana fa

ɗ

in da gaske ture ta akayi ta fa

ɗ

a kan yashin, wanda kowa ya san ƙarya ne wasanta tayi daga yadda baƙin gashin kan nata ya bur

ɗ

ine tsaf da ƙasa.

"Ko baki

ɓ

ata kanki ba meye amfanin zuwa wajen yashi da magriba Hafsa?"

Amina ta fa

ɗ

a a hankali tan

a kama wata jelar, don ita ko ka

ɗ

an ba ta fadan nasu take yi ba, jikinta ne kawai zaune a gidan amma hankalinta ruhinta zarya kawai suke a hanyar gidan Kawu mallam kamar tururuwa, shi yasa ko girkin daren ma tace Maryam tayi.

Allah ya sani abu na ƙarshe d

a zata so a yanzu shine wata matsala ta sake gifta musu, rayuwarsu ta haska da kaloli mabanbanta a shekarun baya, sun fuskanci abubuwan da ko a labari basa son tunawa, kuma har yanzu ƙoƙarin tashi suke, ƙoƙari Baba yake don ganin rayuwarsu ta daidaita ko d

a ba kamar a baya ba, don haka ta yaya zasu ta

ɓ

a son ace sai sun sako daga farko idan wani abu ya sake gifta musu ya a yanzu...

Har sai da ta gama wankewa Hafsa gashin nata da karkashi sannan Amma ta dawo, Baba kuma bai shigo ba sai bayan sallar isha, wan

da kafin ayi hakan har Aminu ya riga su dawowa, a tsakar gidan ya tarar dasu tana sake yiwa Hafsa wata kalbar bayan ta wanke matta kan, yayi wanka yazo ya zauna a cikinsu shima yana ta mita da tsokana akan girkin da Maryam

ɗ

in tayi, jollof din shinkafa da

taliya ce da ko a ido tayi kyau, amma tunda ya zauna yake sukar abincin yana kuma kai loma.

"Wallahi akayi miki aure kika je kina irin wannan abincin sati daya zaki yi ya koro ki, ace jollof amma ba mai sa faman kora ruwa nake kamar dambu nake ci."

An ka

wo wuta a lokacin don haka tsakar gidan yayi tar da wasu sababbin ƙwan fitilar da ya ha

ɗ

a da kansa ya saka musu. Maryam da a lokacin take wanke uniform dinta daga can bakin famfo tace.

"A haka babu man kake ƙoƙarin tayar da plate din ai."

"To idan ina ji

n yunwa ya zanyi? rufa miki asiri kawai nake ma wallahi, don yanzu ina tafiya wajen Isah (mai shayin layinsu) kowa sai ya gane cewar a gidanmu ba'a iya girki ba kenan, kinga masu kokarin zuwa nan gaba ma sai su fasa. Kuma Amina ita ta riga ta samu kece a r

uwa."

Maryam ta juya bayanta amma yana ganin adadin yadda gefen fuskarta ke juyawa wajen murgu

ɗ

a baki tana fa

ɗ

ar wasu abubuwa da ba jin su yake ba. Yayi murmushi yana sake fa

ɗ

in.

"Hotonki zan nemo a wayata in maida shi fari da baki in rubuta ga matar da

akan girkinta aka ƙirƙiri sunan abincin 'Ci kar ka mutu, 1987.'"

Bai saurari abinda take cewa ba ya juya ya kalli Amina da bata sanya baki a hirarsu har yanzu ba, ganin damuwar dake kan fuskarta har a lokacin ya dawo da hankalinsa kanta sosai.

"Wai har y

anzu damuwa kike? Nace miki fa ki kwantar da hankalinki tun dazu. Ni alamar ma da na gani kamar wasu maƙudan ku

ɗ

i Baba ya samo shine aka tafi gidan Kawu mallam

ɗ

in ake ta faman lissafi."

Ba shiri dole Amina tayi murmushi tana kallonsa.

"Aminu Allah ya sh

irye ka, komai sai ka maida shi wasa wallahi."

"To me yasa zaki yi ta damun kanki akan abinda bai ƙaraso ba tukunna."

Ya fa

ɗ

i hakan sanda ya juyo, idonsa ya kai kan hannun Maryam dake ta cu

ɗ

a kayan wankinta.

"Ke, idan kinyi ƙunshin nan ma haka zaki ciga

ba da irin wannan wankin? Kwana biyu ya goge? Ku

ɗ

ina zaki taso ki dauko min Allah indai haka ne."

"Kudin ka ai sun riga sun shigo kenan wallahi baza su dawo ba, sai dai idan nayi ƙunshin ka kankare shi."

Amina ta kalli yadda yake murmushi yana kallon Mar

yam din, ta san shima ya damu, watakila damuwar ma har tafi tata, amma haka Aminu yake a kodayaushe, shi mutum ne da zai sa kaji kamar baka da wata matsala koda kuwa kana nutsewa a cikinta ne tsamo-tsamo. Lokacin da Baba ya shiga tashin hankalin karayar ar

ziƙinsa, Amma tace Aminu shi ya

ɗ

auki kaso mai yawa bayan addu'a wajen dawo dashi daidai.

A daidai lokacin Amman tayi sallama ta shigo, kuma kallonta kawai Amina tayi taji gabanta ya fa

ɗ

i duk duk da cewar yanayin damuwar fuskar tata ya ragu akan da safe.

"Haba Amma kun barmu sai kace marayu a gidan nan, ko shirin yaƙin duniya kuka tafi yi yaci ace kun gama."

Duk da yanayin Amman sai da tayi wani guntun murmushi tana girgiza kai sanda suka shiga yi mata sannu da zuwa, don ta saba a irin lokutan wasansa, A

minu ya riga ya mayar da ita kamar kakarsa.

A lokaci guda sai komai ya dawo daidai a gidan, da duk yawansu ji suke kamar a cikin wani fanko suke, Adam ya dawo daga siyan wainar fulawar da Maryam ta aika shi, Aminu ya kafa ya tsare cewar sai yaci rabi don

wai ya san da kudinsa ta siyo, duk dauriyar Maryam sai da ta rufe idaninta ta fito da duk masifar dake cikinta wanda dama abinda yake jira kenan don haka shi da Adam suka dinga kyalkyala mata dariya.

Sannan a ƙarshe bayan sun shiga falo, wani film din in

diyan da ake yi a tashar Bollywood ya

ɗ

an daukewa Amina hankali daga wannan damuwar ganin cewar Amman ma har ta sake tana kokarin sakawa Hafsa maballi a wuyan rigar makarantar ta, tana yi tana mitar yadda Hafsan ke yawan yar da ma

ɓ

allan rigar.

Falon ya

ɗ

a

uka da sautin wakar film

ɗ

in da ake yi lokacin da take ke kallon fuskar kowa tana murmushi, yadda Hafsa ta zuba manyan idanunta tana saurarar kashedin da Ammar keyi mata akan maballin, da yadda Aminu da Adam ke cigaba da dariya tsokanar Maryam da bata gane

wa ta daina biye musu, har ma da idanun Maryam

ɗ

in da suka cika da haushi fal! Haka take so... Haka take so rayuwa ta kasance musu a kodayaushe.

Sai dai rayuwar bata ta

ɓ

a biyewa muradan zuciya, ita da zuciyar ma sunyi hannun riga, ƙaddara take kallo a kod

ayaushe tana bin takunta, don a lokacin da Baba ya dawo bayan sallar isha a lokacin komai ya ruguje, zuciyar Amina ta sake ruftawa cikin ramin da yafi wanda ta fito daga cikinsa zurfi. Su Hafsa suna makarantar dare a lokacin, Aminu kuma ya fita wajen aboka

nsa sannan Maryam da wata ƙawarta sun tafi bakin titi wajen mai yin zayyanar allo kasancewar suna dab da yin sauka a islamiyya, gidan ya rage sai ita ka

ɗ

ai, kamar dama ƙaddarar ta za

ɓ

i wannan lokacin ne don ita kadai

ɗ

in.

Amma ta kira ta zuwa

ɗ

akin Baba l

okacin da take kokarin ha

ɗ

a kan kitchen

ɗ

insu, kiran daya tabbatar mata da cewar abinda take jira ne zai kasance kuma a hanyar zuwan tunanin ta ya

ɗ

an

ɗ

aure don a zaton ta ita da Aminu ya kamata su zayyane wa komai.

Ta shiga ciki lokacin da Baba ya rufe f

lask din nasa abincin da ya gama ci, ta zauna a daidai saitin Amma da har a lokacin ta kasa tantance yanayin fuskarta.

"Amina jiya da naje gidan Hajiya Kilishi aurenki na bayar ga

ɗ

ansu."

Maganar ta fito daga bakin Baban kai tsaye ba wane shamaki balle k

ewaye kewaye, kuma ta tafi kai tsayen har zuwa cikin ƙwaƙwalwar ta, sai dai bata nutse ba, zagaye kawai ta dinga yi a zaman kan nata kamar mai jiran a bu

ɗ

e mata ƙofar shiga.

Shiru ya ratsa

ɗ

aukacin dakin, shirun da a cikinsa Amina ta kasa ko zuƙar numfash

i, kuma bata damu da tsayinsa ba don har a lokacin bata gane maganar da Baban ya fa

ɗ

a ba, shiru kawai tayi kamar bata ji shi da farko ba a yanzu take jira yace wani abu, sai da shi da kansa yaga bata da alamar magana sannan ya sake kiran sunanta.

"Amina..

"

Ta kuwa

ɗ

ago ta kalle shi, da idanunta dake haskawa a cikin hasken fitilar

ɗ

akin, sai ya cigaba shima kamar bai fadi maganar farko ba.

"Jiya da naje gidan Hajiya Kilishi da mijinta nayi magana ba da ita ba, kiran nasa ne ba nata ba, don da na isa gidan

mota kawai tasa aka

ɗ

auke ni aka kaini har ofishin mijin nata.

Acan na tarar dashi tare da ƙaninsa, mutane ne manya-manya Amina masu mutunci da kuma kwarjini, kuma kai tsaye suka shaida min cewar aurenki suke nemawa

ɗ

ansu, yace min Hajiya Kilishin ita da

kanta ta roƙe shi alfarmar hakan saboda yarda da hankali da kuma tarbiyar da muka baki. Al'amarin ya girgiza ni kamar yadda kika ji shi a yanzu kema, amma wallahi a wannan lokacin ba zan iya kallon idanun wadannan mutanen ince musu 'A'a' ba don bani da wa

ta hujja ko dalilin da zai sa in fa

ɗ

i hakan..."

Ba fahimtar abinda yake fa

ɗ

a Amina take ba har a lokacin, kallonsa kawai take tana jin yadda muryarsa ke karyewa da kowacce kalma daya fada, mahaifinta mutum ne da ta sani jajirtacce, ko a lokacin da yake ci

kin tashin hankalin karayar arziƙinsa, baya taba fasa binsu da alkawuran cewa zai inganta rayuwarsu don kar su karaya da komai. Amma a yau kiri-ƙiri take jin duk wata amon karaya a muryar tasa, amon da take ji yana bin jijiyoyin ta yana tayar da tsigar jik

inta bi da bi ta kowanne

ɓ

angare.

"Na san karatu ne a ranki Amina, kuma na san ba sau daya ba sau biyu ba na sha yi miki alƙawarin cika miki wannan burin amma a kullum abinda muke tsarawa daban, wadda ƙaddara ta tanadar mana daban, kuma na san ba sai nayi

miki bayanin wannan ba don a ƙananun shekarunki kin gan kalolin ƙaddarar mabanbanta, shi yasa nake son ki kalli wannan

ɓ

angaren ƙaddarar ma, ki kalle ta idanun rahma Amina, Allah ya sani a zuciyata na yarda cewa ban miƙa ki inda

zaki wahala ba, don komai

halin da zan shiga a duniya ba zan yarda da duk abinda zai cutar daku ya matso kusa ba balle har in kai ku da hannu na.

Kin san Hajiya Kilishi kin san kirkinta, kin san yanayin gidanta, ina ga kinje kusan sau biyu ke da mahaifiyarki, saboda haka Amina wal

lahi zuciyata bata bani cewa zaki wahala a wannan wajen, damuwata kawai shine yunƙurin rushe miki burin ki da nayi da kuma cewar na yanke hukunci a lokaci guda."

Yayi shiru a lokacin, Amina ta ha

ɗ

iye wani abu a makogwaron ta da bata san sunansa ba, magang

anun Baba a gefe suke daga cikin kanta, har a yanzu damuwar dake cikin muryarsa itace a gabanta, ita take lissafawa tana son kirga adadinta. A hankali ta juyar da idanunta kan Amman dake zaune a saitinta, kuma a hankalin idanunta suka fahimci abinda ta kas

a ganewa a fuskar tata

ɗ

azu, damuwa ce fal ke yawo a cikin nata idanun!

Wani abu da ya ƙara rikita tunaninta a lokaci guda... Don bata taba tunanin cewa irin wannan maganar ce zata saka Amma cikin damuwa itama ba, idan har zata iya tunawa tun farko dama

ita tafi son zancen aurenta akan karatun da take naci, kawai ganin cewar daga ita har Baban akan son karatun suka tsaya yasa ta sallama itama, amma duk da haka tasha gaya mata cewar ba ba lallai sai ta gama karatun zata yi aure ba, to me yasa wannan magana

r zata dame ta?

Sai ta sunkuyar da kanta ƙasa sannan ta gyara zamanta a hankali, tana jin nauyin idanun iyayen nata biyu dake kallonta, so take tace musu in har wannan ne abinda ya tashi hankulansu a gidan tun jiya to su kwantar dashi, don a cikin aure da

zancen rashin karatun tana jin ba wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login