Showing 93001 words to 94381 words out of 94381 words
nuna mata ajiyar da tayi na wata bakar jaka, ta dauko ta sannan ta sake bu
ɗ
e wani wajen inda jakun
kunan ta suke a jere, kuma a cikin aljihun guda
ɗ
aya ta
ɗ
auko Sachet mai yawa na wani magani sannan ta rufe komai ta juyo, da takunta a hankali ta sake dawowa wajen da Aminan ke zaune akan carpet, inda daga gabanta akwai wani stool da aka bari a wajen, ta
ajiye wannan jakar da kuma magungunan a gaban Amina sannan ta nemi kan stool din ta zauna kafin muryarta ta sake ratsa dakin.
"Komai mai sauƙi ne Amina, umarni na kawai zaki dinga bi shikenan sai duniyarki ta koma kamar aljanna, don zan cika miki dukkan w
adannan alkawuran dana dsukar miki har ma da karin wasu da bamu lissafa ba, Kin fahimce ni ko?"
Kuma kamar yadda ta zata, sai ta
ɗ
ago ta kalle ta idanunta na shaida sauran tsoron da a lokacin dama ya kamata ace yana barin fuskar tata, ta gya
ɗ
a kanta sau b
iyu sannan ta sake maida shi kasa, kuma abinda Hajiya Kilishi ta gani a idanun nata ya shiga barazanar goge kokwanton da take yi akanta, amna tayi wulli dashi a lokaci guda.
"Yayi kyau, yanzu ki saurareni sosai kiji abinda nake so dake."
Amina ta sake gy
a
ɗ
a kanta tana ƙara gyara zamanta lokacin da Muryar Hajiya Kilishin ta cigaba da shiga kunnenta.
"Akwai abinda zanyi a kamfanin su Ma'aruf cikin satin nan, kuma zan yi shi ne ba tare da yana nan ba, don haka yanzu za ki taya ni abinda ya kamata ace ni zan
yi don dama lokaci yayi da hakan zai koma hannunki.
Abinda ke cikin jakar nan magunguna ne, na san an gaya miki cewa Ma'aruf yana da wata rashin lafiya ta ƙwaƙwalwa, sunanta 'Bipolar Disorder' ya same ta ne a shekarun baya lokacin da rayuwarsa ta canja ba
yan rasuwar
ɗ
anuwansa, cuta ce dake canja tunaninsa a duk lokacin da ta tashi, abubuwa suna caku
ɗ
ewa a cikin kansa har baya sanin abinda yake yi.
A London ake yi masa magani tun daga wancan lokacin kuma suna
ɗ
ora shi akan ingantattun magunguna tun daga sa
nnan, amma da farko Ma'aruf bai karbi ciwonsa hannu biyu ba balle har ya dinga kula da kansa, baya taba shan magungunan sa akan kari wanda hakan ke ƙara bawa ciwonsa bigiren ya
ɗ
uwa, tun kafin yayi aure nake yi miki wannan zancen Amina kuma tun a sannan na
kar
ɓ
i magungunansa na ajiye a wajena.
Ma'aruf kamar
ɗ
an dana haifa na dauke shi, kin sani tun a wancan labarin dana baki, don haka a baya na tsaya da ƙafata sosai wajen takura masa a duk lokacin da ya kamata yasha maganin, kafin daga bisani na fahimci cew
a hanyar nasarata tana tattare da ikon da nake dashi ne akan magungunan sa. Ina son Ma'aruf Amina, amma son da nake yiwa cikar burina yafi karfin nasa, shi yasa nake rufe idona a duk lokacin da buƙatar in kwantar dashi ta taso min ina yin hakan."
Tayi shi
ru na tsawon wasu sakanni tana kallon yadda tasirin maganganun ke aiki a fuskar Amina kamar yadda ta zata kafin ta cigaba.
"Magungunan dake cikin jakar nan har America naje na nemo su Amina, magunguna ne dake birkita ƙwaƙwalwar mutum a lokaci guda ya fita
daga hayyacinsa, kuma dama ciwon Ma'aruf abinda yake bukata kenan ya tashi, don haka duk sanda nake shirin yin wani abu da na san zai iya zame min ƙalubale, sai in kwantar dashi in gama duk abinda zan yi kafin ya dawo hayyacinsa."
Ta kai karshen maganar
kamar bata karasa ba, don dukkansu shiru suka yi yayin da nauyin kalaman ke zagaye iskar dakin, ba irin ga Amina da taji hannayenta har rawa suke yi
ɗ
auke da sabuwar rikicewar da maganganun suka sata, don yau ne
karo na farko da ta ji ciwon Ma'aruf daga ma
kusantansa, ko shi bai gaya mata ba, cewa kawai yayi 'I'm a mess Amina...'
Zuciyarta ta ajiye komai a gefe ta shiga gaya mata cewa har ta gama rayuwarta a duniya ba zata taba iya ha
ɗ
uwa da wata muguwar halittar irin Hajiya Kilishi ba.
"Na san idan Ma'aru
f yayi aure dole ne zargi zai shiga zuciyar wasu idan har na cigaba da rike magungunan sa, don haka wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sa na kawo ki gidan nan, daga yau magungunan nan sun koma hannunki.
Ki
ɗ
auka ki tafi dasu, guda uku ne a ciki,
ki
ɓ
alli kowanne guda
ɗ
aya ki bashi a gobe, don jibi zan fara aiwatar da abinda ke gabana kuma a sannan bana buƙatar ganinsa a kamfanin.
Wannan shine aikin ki na farko Amina, kuma idan komai ya tafi daidai, zaki fara ganin daidai bari nayi miki alkawarin
farko tun a yanzu, idan na samu abinda nake so Amina zan sa a fitar da
ɗ
anuwanki Aminu ƙasar waje a gyara masa kafafunsa su kamar yadda duke a da."
Shirun da ya sake ratsa
ɗ
akin mai tsawo ne da babu abinda zaka tsinta a ciki kafin Hajiya Kilishi ta kai ƙ
arshen zancenta da magana ta karshe kuma mafi girman da daki zuciyar Amina babu zato, maganar da daga ita har Amma basu taba hango ta ba balle tasa ta a jerin tunanin Hajiya Kilishin, kuma duk da dauriyar da take da ita a lokacin sai da kalaman suka tasa a
llon kirjinta girgizawa da karfin da ta san har Mamin ta lura.
"Maganin dake gefe kuma naki ne Amina, ki dauka ki dinga shansa kullum, na san ba zan iya hana Ma'aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma kuma ba zan lazimci wani abu ciki ba don babu shi ko
kadan a cikin lissafina!"
***
Yaya kuka ga shara
ɗ
an farko na Kilishi??
Ta yaya kuke ganin Amina zata bullo musu??
😅😅
Ta yaya zata sa komai ya faru ba tare da Hajiya Kilishi ta
ɗ
orar da zargin da take mata ba??
Mu dai jira hukuncin Amma ko??
And the
Uban gaiyar is over there going crazy akan ƙafafun Amina ba tare da ya san me ke shirin tunkaro shi ba!
😅
Wani ya gaya masa cewa su Rukayya ma na can nayi masa nasu shirin suma...
Jawad ma kuma yana nasa!
A tsakiyar komai kuma dai, zamu samawa Ma'aruf
wannan nutsuwar da yake nema insha Allah.
😍😍
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
SANARWA.
~~~~~~
Assalamu alaikum.
Fatan alkhairi ga tarin Masoyan FARAR WUTA da ma duk wani littafi da ya kasance nawa. A lokaci irin wannan nakan nemi kalamai
in rasa, nagode da dukkan support
ɗ
in ku tun daga shafin farko na farar wuta zuwa in da na tsaya.
Ina kuma ganin tarin saƙonni da ƙorafin ku akan rashin samun update akan lokaci, ina jin kalmar HAKURI kamar tayi ka
ɗ
an, amman ita ka
ɗ
ai nake da ita. Na far
a littafin nan ne ba tare da na hango tarin uzururrukan da suka dinga taso mun ba, suka kuma zama dalilin rashin samun update
ɗ
in da ba kwayi.
Na sani...
Na kuma fahimta tun kafin ku furta.
Kuyi HAƘURI, don saboda dalilai da yawa littafi na biyu (Farar
Wuta 2) zai koma Paid Story cikin tsarin da nake fatan dukan mu zamu ji da
ɗ
in shi. Wanda na
ɓ
atawa a farkon tafiyar nan zuwa yanzun, banda kalamai masu yawa sai neman afuwa da kuma bada hakuri.
Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma bamu aron lokaci
n sake haduwa dan karasa tafiyar FARAR WUTA.
Kar ku manta yanzu tafiyar ta fara...
Zan baku labarin yadda nasara ke samuwa babu boka ba Malam!
Zan baku labarin soyayyar Ma'aruf da wataƙila zata narkar da zuciyarku kamar ruwa.
Zan kuma baku labarin yadd
a mata ke samawa kansu mafita ta hanyar wayo da dabarar da Allah ubangiji ya halitta a ƙwaƙwalwar kowacce mace.
Ku tuntube ni ta wannan lambar. 08067794315.
Nagode muku fiye da yadda baki zai iya furtawa.
#AyshaShafi'ee
#fikrawriters
#FararWuta.