Showing 1 words to 3000 words out of 94381 words
SHIMFIDA.
A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...!
Me zai faru a lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai? A lokacin da ka shiga shiga cikin wata duniya da zaka ji baka son barinta? ka bi ahalin cikinta kuna nutsewa cikin ramin da baku sa
n dashi ba? ka shagala da kallon FARAR WUTAR da ta juye tunaninsu, ta wanke kwakwalwar su har kowa a duniyarsu ya manta cewar wuta, WUTA ce! Duk kuwa irin FARINTA.
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA ƊAYA.
~~~~~
Wajen karfe goma sh
a biyu na rana, matar dake cikin kitchen
ɗ
in da aka zagaye da langa-langa daga
ɗ
an madaidaicin tsakar gidan ta kwance wani
ɗ
aurin itace dake gefe ta ƙara a cikin murhun gabanta sannan ta shiga firfita wutar da wani karyayyen mafici dake gefe. Dattijuwa ce
mai kyawun jikin da idan ba fuskarta ka kalla ba zaka zabge shekarunta ƙiyasi.
Kayan jikinta riga da zani ne masu kyau da har karin guga zaka hango a jiki, gashin kanta mai laushi ya sirka da kananun furfura da ta fara yiwa kan nata rumfa.
Sai da ta tabb
atar wutar ta kama sannan ta mike ta fito, a tsakar gidan ta tarad da babbar ƴarta mai suna Amina zaune tana tsintar wake a wani katon farantin silver, shekaru ne kawai suka banbanta kamannin fuskokinsu amma kammaninsu daya sak! Har yanayin jikinsu da koma
i.
Ƴ
ar siririya ce mai yalwar gashi irin na mahaifiyar tata, komai a fuskarta maidaidaci ne mai sanyin kwatance, idanunta ne kadai abinda mai
ɗ
aukar hankali don duk da ba girma ne dasu ba, amma suna da wani kyalli kamar an
ɗ
iga wani abu a cikinsu.
"Yi sa
uri ki gama Amina, sha biyu tayi gwara muyi sauri a
ɗ
ora don yanzu zaki ji su sun dawo."
Amina ta bu
ɗ
a labule
ɗ
akin dake bayanta, ta kalli agogon dake kafe a cikin dakin sannan tace.
"Ashe lokaci ya tafi har haka, ban kula ba sam wallahi."
"Garin ne ba
zafi ai shi yasa kika kwanta kika yi ta baccinki."
Da murmushi tace.
"Ni ai na gaji da tashi da wurin ne wallahi, da sun tafi makaranta sai inga gwara kawai na kwanta."
Mahaifiyar tasu da suke kira da Amma ta dauki wata tukunya dake gefe, ta nufi wajen
ruwa da ita tana fadin.
"Ki cigaba da addu'a kawai, idan da rabon ki a cigaba da karatun nan zaki yi insha Allah."
Amina bata ce komai ba, don Allah ya sani ta fara karaya, shekararta guda kenan da kammala karatun sakandire dinta, kuma sakamokonta yayi k
yau duk da cewar an taimaka musu wajen yin jarabawar, amma duk da haka ta san tana da kokarinta daidai gwargwado, shi yasa ko kadan ƙulafucin son cigaba da karatun bai bar ranta ba.
Kuma ba dole sai wani babban karatu ba, don ta da
ɗ
e da soke Jami'a a liss
afinta, ta sani cewa mahaifinta bashi da halin wannan wajen, yana iya bakin kokarin sa
wajen kula dasu da
ɗ
an abinda yake dashi kuma duk da haka kullum cikin damuwa yake yana ganin kamar baya basu abinda ya kamata, don yasha fadin cewa yayi burin cewar ƴaƴ
an sa zasu huta da duk wani gata na duniya.
Don haka tunanin ta a kullum na ta samu makaranta ne ƙarama inda zata dan koyi aikin lafiya... Don mahaifiyarta tasha fa
ɗ
a mata cewa ko allura ta iya yiwa mutane, idan tayi aure hakan zai taimake ta sosai fiye d
a ace ta zauna bata yin komai.
Zancen auren ya tuno mata da saurayin ta Abdallah, ta san shirye-shiryen komawa makaranta yake yi shi yasa bata ji shi ba kwana biyu, a matakinsa na ƙarshe yake a can wata jami'ar Sakkwato. Abdallah mutum ne mai kirki da kum
a hankali, har islamiyyar dare yake da ita a bayan layinsu wanda yasa kowa ke ganin mutuncinsa kamar yadda itama take girmama shi a kodayaushe, tana ganinsa kamar yayanta shima kuma yana taimakon ta a komai kamar ƙanwarsa.
Mu'amalarsu daban take da yadda
take ganin tsakanin ƙawarta Fatima da nata saurayin, abubuwa da yawa idan Fatiman ta gaya mata ta kanyi mamakin yadda suke iya kasancewa, don ita ko
ɗ
aga ido ta kalli Abdallah bata iyawa sosai, sau da yawa ma ta kan manta cewa mu'amalarsu aure zata kai.
"
Salamu alaikum, wai a bada gullisuwa."
Sallamar wani yaro ta katse tunaninta sanda ya tsaya daga jikin hanyar soro yana miko naira hamsin.
"Ta nawa?" Ta tambaya.
"Ta naira Ashirin."
Sai ta ajiye farantin waken ta miƙe ta karbi kudin, watanni hudu kenan
da fara sana'arta ta saida alawar madara, gullisuwa da kuma albishir, kuma ciniki take yi sosai don a kwana uku kawai take sake yin kowannensu na dubu biyu. Wannan shine babban abinda ke
ɗ
ebe mata kewa da kuma faranta ranta ganin yadda take iya yin wasu b
ukatunta da kanta har ma ta taimakawa ƙannenta da
ɗ
an ku
ɗ
in kashewa, sa
ɓ
anin a watannin baya da bata komai.
Lokaci shine rayuwarka ta duniya da kuma lahira, babu amfani ka barshi yana tafiya haka sakaka... Kalaman Ammansu kenan a kullum idan tana bayanin
abubuwan da suka dace da rayuwar mutum.
Ta
ɗ
ebowa yaron gullisuwar hade da canjinsa, ta fito daga falon nasu da babu komai sai shimfidadden carpet daidai lokacin da Fatima tayi sallama ta shigo.
"Amma ina wuni."
Ta gaishe da Ammar dake wanke bayan tukun
yar data dauka.
"Lafiya kalau Fatima, Hajiyan ta fita ko tana nan?"
Hajiya mahaifiyar Fatiman ce, kuma tana zuwa jinyar kakar Fatiman ne da aka kwantar a asibiti kullum.
"A'a bata fita ba, girki take yi tukunna."
"To bari in gani nima idan na gama nawa
ko zan iya bin ta, tun jiya nake waƙar ya kamata in koma wallahi."
"Ai jikin nata ma da sauki."
Cewar Fatiman tana nufar hanyar
ɗ
akin su Amina rike da ledar hannunta, ganin hakan yasa Amina ta dauko farantin waken da ta gama gyarawa, ta nufi wajen rijiy
a ta zago ruwa ta wanke shi sannan taje ta zuba a tukunyar dake gab da tafasa.
"Kaya Ahmad ya kawo min jiya da yazo."
Tana bude labulen
ɗ
akin Fatiman ta fada, da fara'arta kuwa ta goge ruwan hannunta a jikin doguwar rigar da ta saka sannan ta ƙarasa gefe
n katifarta inda
Fatiman ke fito da kayan, atamfa ce har guda biyu da kuma farin mayafi
ɗ
aya sai kayan kwalliya.
"Gaskiya ne Fati, wallahi ki gode Allah, Ahmad na ji dake."
Fatima ta juya idanunta alamun dadi tana murmushi. Fara ce ita sosai, farin da ta
ke alfahari dashi a kodayaushe, tana ganinshine silar samuwar abubuwa da yawa a rayuwarta, don iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne sosai.
"Ni kaina wallahi na sani Amina, shi yasa nake gode masa kullum."
"Allah kuwa yana da kyauta, Allah ya saka masa da alkha
iri... Kai wannan tafi kyau wallahi." Ta fada tana daga wata.
"Kamar kin san nima nafi ganin kyanta, har cewa nayi ko in barta sai Sallah kawai muyi ankonta ni dake."
Amina ta bude kwalin wata hoda sannan tace.
"Sallah fa da nisa, ki
ɗ
inka abarki kawai
. Ma yi wani ankon idan lokacin yazo."
"To shikenan." Fatima ta gyara zama tana kallon yadda take kallon kayan, sai kawai tace.
"Wai yaushe rabon Abdallah da ya miki kyauta ne Amina?"
Amina bata bar kallon kayan kwalliyan ba tace.
"Shi da yake dan maka
ranta ta yaya zai iya wata dawainiya yanzu, in dai sallah tazo ai yana min kaya kin sani."
Fatima ta tabe baki.
"Wannan fa daban, kyauta kuma daban. Ni wallahi Amina na sha gaya miki ki ƙyale Abdallah nan, da tuni kin fara ganin wadanda suka fishi, don n
aga alama yanzu idanunki basa ganin kowa."
Sai a lokacin Amina ta kalle ta.
"Fatee, ke fa kin san ni duk wannan abin ma ba a gabana yake ba, shi yasa nake son mu'amala ta da Abdallah saboda shima yanzu karatunsa yake son gamawa, baya takura min nima kuma
bana takura masa."
"Wai har yanzu kina ganin zaki cigaba da karatun ne?"
Ta daga kanta.
"Wallahi ban fidda rai ba Fatee, duk da na san Baba ba zai iya ba, kuma babu wanda zai yi min bayan shi din.'
"Shi yasa nake gaya miki ki hakura kawai, ba komai m
utum yake samu a rayuwa ba, a yanzu auren kawai ya kamata kiyi, ki ragewa su Baba nauyi sannan kema ki sami wajen da zaki iya
ɗ
aukar
ɗ
awainiyar wasu ma."
Kallonta kawai Amina take tana murmushi don ta riga ta sani cewa ba zata taba fahimtar abinda take ji
a zuciyarta bane, sai da ta kai ƙarshe sannan ta shiga ha
ɗ
a kayan tanafa
ɗ
in.
"To shikenan, ki bari sai bayan maulidi, idan mun fara kai ki, sai in fara wannan lissafin.
Jin haka yasa ba shiri itama tayi murmushi tana kara juya idanunta, don kamar yadda
aka tsayar da rana, bayan maulidin ne bikinta ita da Ahmad din.
"Baki san wani abu ba ma, wata mata na samu mai sayar da magunguna a can layin..."
Da haka ta shiga bawa Amina labarin da yasa ta bar hada kayan ta zare idanu tana kallonta kafin ta shiga
ɗ
aka mata duka alamun bata son zancen, ita kuma tana kyalkyala dariya.
Mahaifin Amina mai suna Alhaji Sulaiman dattijon mutum ne mai sana'ar harkar aikin katako, ya samu wadata a da, don gidan da yake zaune da iyalansa na kansa ne, amma a yanzu abubuwa sun
tsaya masa ta yadda ya
ɗ
auki hakan ya sanya a ransa har ya zama shine damuwarsa a kodayaushe. Ƴaƴan sa biyar tare
da matarsa Halimatus- Sadiya bafulatanar Niger da iyayenta suka dawo Nigeria da zama.
Amina ce ta farko, sai Aminu, Maryam, Adam da kuma aut
arsu Hafsa. Maryam, Aminu, da Adam suna matakin secondary ne a karatu yayin da Hafsa kadai take Primary, amma da yake makarantar da suke zuwa wata community school ce dake waje
ɗ
aya, tare suke tafiya dukkaninsu tare suke dawowa.
Babban damuwar Alhaji Sula
iman a yanzu shine ganin ƴaƴan sa na ƙara tasawa kuma harkar samun sa na ƙara yin baya, karayar arziƙin da ya samu ta taimaka ƙwarai wajen karya zuciyarsa akan komai, kullum cikin lissafi yake da kuma damuwar da ƙarara kowa ke gane ta duk da irin nuni da k
uma nasihar da matarsa ke yi masa a kullum.
***
Ƙ
arfe Biyu da rabi.
"Yaya dan girman Allah zaki bani naira dari? Ƙunshi zanyi."
Maryam ta fada lokacin da take ƙoƙarin cire uniform
ɗ
in ta bayan sun dawo daga makaranta. Amina na zaune tana ninke kayan w
ankinta tace.
"Ƙunshin me zaki yi?"
"Bikin yayarsu Na'imah fa, kin manta jiya nazo da katin."
Jin tayi shiru yasa ta sake tambaya.
"Zan baki Maryam, Allah ya kaimu gobe."
"Me za'a bayar? Idan ana ƙaunar Allah nima a taimaka mun."
Aminu ya fada yana s
higowa cikin
ɗ
akin.
"Kaima ƙunshin zaka yi?"
"Me kyau ma kuwa, don kin san sai yafi fitowa a hannu na ma akan bakar fatarta."
Ya fadi hakan sanin cewar shi fari ne, don ƴan mazan biyu su suka yiwo mahaifinsu sak a kammani da kuma hasken fatan, matan kum
a Suka yo mahaifiyarsu, har gwara Maryam ma ana cewa idonta irin na babansu ne, amma Amina da Hafsa babu abinda suka bari a kammanin Amman.
"Wallahi ni ba baƙa bace kaima ka sani, irin wannan kalar fatar sai ka zagaye garin nan kaf baka samu irinta ba."
"To idan ma an samu me za'ayi da ita? Da dai irin ta Amina kika ce sai in yarda, amma ke duk gidan nan ma akwai mummuna kamar ki."
Maryam ta kara ha
ɗ
e ranta tana saka hijabin data
ɗ
auko. Amina ta jefo masa wata riga dake hannunta tana murmushi.
"Ha
ɗ
a mu
kayi kawai kake zagi Aminu, dani da ita
ɗ
in me ya banbanta damu, ka takurawa Maryam wallahi."
"Haba ya zaki hada kalar ki data wannan fingilar? itama ta hakura ta kar
ɓ
i kanta yadda take ne taƙi, sai faman iyayi fal ciki."
Da ƙunƙuni Maryam ta fa
ɗ
i wani a
bun kafin ta tayar da sallarta. Hakan yasa shi dariya don shi kansa ya sani girman dake tsakaninsu ne kawai yasa take raga masa a azababbiyar magana da kuma rashin kunyar dake cikinta.
"Sai yaushe zaka fita yau?"
Amina ta tambaya sanin cewar da ya dawo
baya dadewa a gidan yake tafiya can inda yake koyon gyaran mota a can hanyar gidan zoo, har ma ya fara kwarewa don kusan shekara biyu kenan da Baba ya kai shi wajen.
"Sai na ƙarbowa Baba, kayansa daga wajen guga..." Ya shafo kansa.
"... Tun dazu ma fa y
a kamata in je, sun ce sun gama."
Kafin Amina tayi magana, Hafsa ƙaramar ƙanwarsu ta shigo gidan hannunta riƙe da ƙullin farar ledar atturuhun data siyo na girkin dare da kuma takardar yashin
madina tana zubawa a
ɗ
aya hannunta tana lashewa. Amina ta
ɗ
aga
murya ta kirata ganin bata da alamun shigowa.
"Ki shigo ki cire kayan nan ki saka na islamiyya, ga uku nan har ta kusa, Adam har ya tafi kina nan."
Tana jin hakan Idanunta irin na Amina suka ka
ɗ
a a take sannan muryarta ta koma ta kuka, ta shigo
ɗ
akin da
sauri tana fa
ɗ
in.
"Dan Allah kice Ya Maryam ta raka ni, wallahi zane ni za'ayi..."
Kafin Aminan ta amsa, Aminu yace.
"Saka kayan muje in raja ki daga nan sai in wuce.
Ai kuwa da murnarta ta ruga da gudu zuwa dakin Amma inda kayanta suke, ta sani ba wan
da ya isa ya dake ta makarantar tunda Aminu ne zai raka ta.
Aminu ya ciro Naira dari biyu daga aljihunsa ya cilla kan sallayar da Maryam ke sallah yana fa
ɗ
in.
"Gashi nan kije a zana miki abinda ba ganinsa za'ayi ba."
Amina tayi murmushi tana godewa Alla
h a zuciyarta, tana son yadda suke tallafar junansu akan irin ƙananun buƙatun nan.
Hafsa bata dawo ba suka tsinci sallamar mahaifinsu, dukkaninsu suka kalli juna a lokaci guda sanin cewa lokacin ba lokacin dawowarsa bane, ƙa'ida ne sai bayan sallar magrib
a kullum yake dawowa don har Aminu yana yawan riga shi isowa ma.
"Allah yasa kar ya tambayi kayan nan..."
Aminu ya fa
ɗ
a yana dafa kansa.
Ta tsakanin raga-raga labulen Amina ta hango yadda mahaifin nasu ya dafa kan Hafsa da ta taho ta rungume shi, sannan
kai tsaye ya nufi hanyar
ɗ
akinsa.
Taga Amma ta fito daga falo sanye da hijabi alamun salla tayi ta bin bayansa tana fadin sannu da dawowa.
"Ke maza ki dauko takalminki mu fita."
Cewar Aminun, sannan ya juyo ya kalli Amina.
"Kice masa tun dazu na tafi
kar
ɓ
i kayan."
Ai kuwa yana sanya kafarsa waje suka ji Baban yace.
"Fita ce ta kama ni Halima, ina kayan da nace a karbo min?"
Basu ji amsar da Amman ta bayar ba sai muryarsa da ta sake dagawo wajen kiran Aminu.
"Aminu! Yana gidan nan?"
"Na shiga uku..
"
Cewar Aminun, kuma Amina na kallon sanda Maryam ta murmusa a sallarta don da
ɗ
i.
"Baba sannu da zuwa, wani abu ne ya faru ka dawo yanzu?"
Ta tsinci muryarsa da yayi sauri ya tsugunna yana shafa kai ganin ya fito.
"Ni da gidana don na dawo sai ka tamba
ye ni me nazo yi? Ina kayan da nace ka karbo min?"
"To, to, bari aje a karbo."
Ya fada kamar sai a lokacin yace 'je ka karbo din,' kuma bai jira ya sake cewa komai ba ya kama hannun Hafsa da ta gama shiryawa suka yi waje.
Alhaji Sulaiman ya girgiza kans
a kawai saboda takaici sannan ya kalli Amma dake tsaye a gefensa.
"Hajiya Kilishi ce yanzun nan ta kira ni tace tana son ganina."
Daga cikin
ɗ
akin Amina zata rantse daga ita har Amman a lokaci guda suka yi murmushi.
Hajiya Kilishi ƴaruwar Baba ce, mace
ce mai kirki da son kyautatawa, ta taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu ta kowanne fanni, tun kafin Mahaifinsu ya rasa arziƙinsa har bayan komai ya caku
ɗ
e musu, don hatta ku
ɗ
in rubuta jarabawarta ta fita daga secondary ita ta tallafa aka biya, babban taimakon
da tayi musu na kwanan nan shine lokacin da Maryam ta kamu da rashin lafiyar ciwon ciki, wanda daga ita har su kowa ya wahala kafin a gano cewar wani ƙari ne ke fito mata a gefen cikin kuma yayi girman da har sai an cire shi.
A wannan lokacin komai nasu y
a riga ya ƙare wajen jinya, don hatta abinci sai daga gidan wan Baban ake kawo musu kullum ko tukunya basa dorawa,
ɗ
an abinda Baba ya samu da kuma na wajen Amman daga ƴan sana'o'in da take yi duk a asibitin suke karewa.
Don haka a dole Baban ya shiga nema
n bashi ƙofa-ƙofa, ƴanuwansa suka hada masa iya abinda zasu iya amma ko kwata ba'a shafe na lissafin ba, Hajiya Kilishi ita taji labari a danginsu, ta kira Baban har gida ta bashi tallafin naira dubu
ɗ
ari uku, ku
ɗ
in aikin har da
ɗ
oriya akai, tun daga wanna
n lokacin zuciyoyinsu suka kara girman darajarta a wajensu.
Mijin ta wani babban mai ku
ɗ
i ne kuma sanannen mutum ne, itace matarsa ta biyu kuma ƴaƴan ta biyar dukkaninsu mata, amma ance saboda zaman amanar da suke yi da uwargidanta babban
ɗ
anta ma a wajen
Hajiya Kilishin ya tashi tun yana yaro ta yadda ba