Showing 69001 words to 72000 words out of 94381 words

Chapter 24 - Farar Wuta Complete

yanka carrots ta

ɗ

ago ta kalle ta tace.

"Ki kara fa

ɗ

ar abu guda

ɗ

aya ki gani idan ban jefe ki da grater nan ba."

Amina tana murmushi daga inda take blinding

abarba tace.

"Ki ƙyale ta haka mana Samirah, shikenan don tazo sai da dalili? Da nan da cikin gidan ai duk

ɗ

aya ne."

Samiran ta girgiza kanta.

"Ba zaki gane bane Aunty Amina, saura fa sati biyu ta fara exams, da su Zahra suna nan zasu gaya miki a irin

wannan lokacin ba'a ganinta wallahi, idan ta shiga

ɗ

aki sai ta yini akan littafi sallah ce kawai ke tada ita, ko Hajiya sai dai tayi ta fa

ɗ

an taci abinci, Allah karatun da take yi har na gama rayuwata a duniyar nan ba zanyi rabinsa ba..."

Bata karasa ba k

uwa lokacin da Munaya ta saita daidai bakinta da wani katon karas din dake gefenta ta jefe ta dashi, amma duk haka Samiran bata yi shiru ba, ta cigaba da bayanin ta tana fa

ɗ

in ita bata yarda da zuwan nan nata ba sam, wanda ke saka su dariya.

Amina ta tsiy

aye ruwan abarbar a hankali cikin wani katon bowl tana kokari kar ya ta

ɓ

a ciwon hannunta da bata da

ɗ

e da jinsa ba wajen yanka albasa, tana jinsu har yanzu Munaya na rokonta akan ta kyale ta amma Samiran taki yin shiru.

Munaya tana da saukin kai sosai, don

tazarar shekarun dake tsakaninsu da Samiran da

ɗ

an yawa, amma idan suna hira irin haka ba zaka ce ba, ta juya tana kallonsu, ita kanta dai ta

ɗ

anyi mamaki zuwan Munayan tunda tun bayan ranar da suka zo gaba

ɗ

aya suka gaisa sau

ɗ

aya ra kara shigowa ranar da

suka yi zancen littafin nan.

Samirah ce dama kusan kullym zata leko

ɗ

an bsyami ko saƙonta, a dazu ma tazo kawo mata wata darduma ne mai kyau daga Hajiya Maimuna taga tana aikin shine ta tsaya don ta taya ta, bata da

ɗ

e ba kuma sai ga Munayan itama ta shig

o, ganin suna aikin yasa itama ta tsaya taya su.

"Ki cigaba Kar ki fasa, I have my ways of torturing you kin sani wallahi."

Munayan ta fa

ɗ

a yayin da suke dariya dukkaninsu, Amina ta

ɗ

auko bowl din da ta juye ruwan abarbar ta taho don ta saka shi fridge y

a

ɗ

anyi sanyi kafin ta ƙarasa abinda zata yi tazo ha

ɗ

a lemon.

Fridge

ɗ

in yana daga gefen kofar shigowa kasancewar shine na karshe a yadda drawer kitchen

ɗ

in take a jere, don haka ta taho wajen daidai lokacin da Ƙofar kitchen din ta bu

ɗ

e Ma'aruf ya shigo c

iki, yana sanye da wata loose riga fara mai dogon hannu, gashin kansa a barbaje kota'ina kamar yadda yake tun safe kasancewar bai fita ba yau, amma babu banbanci da cewar yana nan din, don

tun safen yana

ɗ

akinsa yana faman wani aikin a computer, banbancin

jiya da yau shine a yanzu fuskarsa fayau take, babu gajiya irin ta jiya ko kadan, ya riga ya manta duk wannan tunanin meeting din nan, don bayan dawowarsa a jiyan ya bata labarin cewa komai ya tafi daidai tsakaninsu da mutanen da suka yi meeting

ɗ

in.

"Kin

yi addu'a mai kyau kuma Allah ya amsa."

Kalaman da ya gaya mata kenan a jiyan wanda ta kwana suna yawo acikin kanta. Shi yasa a yau ma da safe breakfast mai da

ɗ

i suka yi yana kara gaya mata irin nasarar da suka yi suka shawo kan mutanen nan

ɗ

aya kamfanin

suka kulla alakar kasuwancin a tsakaninsu, hirar dake ƙara sawa tana fahimtar abubuwansa da yawa, tana jin zuciyarta na canjawa game da tunaninta akansa, wasu abubuwa da yawa a cikin kanta na gaya mata cewa ba shine wannan Ma'aruf

ɗ

in da ya bata wannan sa

ƙ

on ba... Ba shine kuma wanda Iyayenta suka gaya mata yana da matsalar ƙwaƙwalwa ba.

Shi yasa ko da ya gaya mata cewa Ishaq

ɗ

in da suke waya kullum ya dawo daga tafiyar da yayi zai zo a yau, zuciyarta tayi tunanin aƙalla ta tarbe shi da irin tarbar da ya

kamata, ba don komai ba sai don ta san hakan ne ya dace kuma ko zata yiwa kanta ƙarya ta sani cewa tana son yadda zamansu ke tafiya duk kuwa da yadda koina a tunaninta ke gaya mata cewa akwai abinda ke shirin faruwa.

Ƙ

afarta ta ƙarasa wajen Fridge

ɗ

in ne

daidai lokacin da ya shigo, taga idonsa ya haska da mamaki yana kallon su Munayan da kuma aikin da suke yi.

"Me yake faruwa anan?"

Muryarsa tasa dukkaninsu juyowa a lokaci guda, kuma a taken fuskar kowannensu ta fa

ɗ

a

ɗ

a da murmushi yayin sa Munaya ta kira

shi cikin wani abu mai kama da waƙa.

"Yayaaaaa B...."

A ƴan kwanakin nan Amina ta fahimci kusan duk sanda suka ganshi haka ne, haka gaisuwarsu ke farawa kamar sun da

ɗ

e rabonsu dashi, hakan ya tabbatar mata cewar ba ganinsa suke yi sosai a baya ba, a yan

zu ne lokaci ya kawo musu shi kusa dasu wataƙila kamar yadda suka saba a ganinsa a baya.

Kuma kafin tace wani abu, dukkansu suka ajiye mata aikinta sunyi wajensa, wani abu ya fa

ɗ

a a zuciyarta ganin yadda kowannensu fuskarsa ke

ɗ

auke da fara'a sun baibaye

shi da maganganun da kallon fuskokinsu kawai yake yi, ba irin Samirah da ta shiga bashi labarin da ta gama bata a

ɗ

azu na wani competition

ɗ

in kamfanin Maggi da aka za

ɓ

e ta zasu je suyi a Abuja, Munaya kuma tana ta maimatawa wai ta gaya masa labtop

ɗ

insa t

ake so ko kuma ya siyo mata wata sabuwa irinta...

Me yasa ne wai take tunanin akwai wani rami a rayuwar wa

ɗ

annan mutanen?

Tana jiyo muryoyinsu har lokacin da ta shiga store don neman wani abu ba tare da ita taxe komai ba, kuma ba'a da

ɗ

e ba taji an ƙwank

wasa kofar store

ɗ

in dake bu

ɗ

e a hankali sau biyu kafin muryarsa tayi magana a bayanta.

"Akwai ruwa anan?"

Ta juyo ta kalle shi, yana tsaye daga ƙofar store

ɗ

in, ta manta cewa ruwan dake ajiye a kitchen ya ƙare tun dazu kuma bata fito da wani ba, don hak

a da sauri ta juya bayanta inda katan din ruwan yake a jere ta bu

ɗ

e na saman ta

ɗ

auko

ɗ

aya, yana tsaye yana kallonta har ta ƙaraso ta miƙo masa, kuma ga mamakinta tana ƙarasowa sai kawai ya hado robar ruwan da hannunta gaba

ɗ

aya ya jawo ta zuwa gabansa, ƙa

fafunta suka taho dab dashi yayin da ya dago da hannun nata yana kallo, ba shiri numfashinta ya katse a ƙirjinta lokacin da yasa

ɗ

an yatsansa

ɗ

aya ya ta

ɓ

a daidai wajen data yanke

ɗ

azu.

"Me ya faru?"

Muryarsa ta fito a yana kallon ciwon.

Sai da ta ha

ɗ

iye

yawu tana ƙoƙarin saita tunaninta kafin tace.

"Da wuƙa na yanke."

"Me kika saka a wajen toh?"

Muryarsa ta sake tambaya a hankali ta yadda har tana jin ƙarar wukar da Munaya ke amfani da ita daga can kitchen

ɗ

in, da kuma nuryar Samirah da ta fita waje t

ana waya.

Ta sake ha

ɗ

iye wani yawun a makogwaronta.

"Ba komai na wanke ne kawai."

Sai ya kawo daya hannunsa yasa su duka biyu ya rike natan, sannan ya bu

ɗ

a ciwon sosai don yaga zurfinsa, zafin ya tafi har cikin kanta ta runtse idanunta da sauri tana cij

e lebbenta, sai yayi saurin sakin wajen sannan ya rufe yatsan nata da duka hannayensa biyu kafin yace.

"I'm sorry na duba ne na ga yadda yayi and it was deep." (kuma yayi zurfi.)

Ta bu

ɗ

e idanunta a hankali sannan ta

ɗ

aga kai ba tare da tace komai ba, kum

a bai saki hannunta nata ba sai ya cigaba da rike shi yana kallonta, hakan yasa ta

ɗ

ago da idonta kalle shi da

ɗ

an ƙaramin mamaki.

"Aikin me kuke yi haka?"

Ya tambaya tun kafin tayi wani tunanin, sai ta girgiza kanta.

"Abinci ne kawai."

"Kala-kala haka

?"

Muryarsa ta sake fitowa da wani abu da ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta yana kassara ƙarfinta, taji kamar wani yana zazzaga mata wani magani mai karfi ne da aka haƙiƙance zaiyi tasiri akanta, kuma a yadda tata muryar ta fito tana rawa, kamar dama

anyi mata baki ne cewar hakan ne zai faru.

"Kace abokin ka zai zo."

"Ishaq?" Ya tambaya kai tsaye sai kuma ya sake cewa.

"Ya salam duka saboda shi kuke yin wannan aikin?"

Shi ko kadan unaninsa bai kawo masa cewa don Ishaq

ɗ

in zai zo ya kamata ayi wani

abu ba, duk da a baya ma idan zaiyi baƙi Ruƙayya kan shirya musu wani abun amma a yanzu ya riga ya manta da hakan kwata-kwata, saboda haka a lokaci guda zuciyarsa taji dadin hakan, sai kawsi ya gyada kansa yana kallonta sannan yace.

"Thank you."

Ta

ɗ

aga

kanta da sauri itama tana fatan hakan ne karshen zancen nasa, don bata san me zata zama ba idan har ya cigaba da magana rike da hannunta a hakan. Kuma kamar yaji fatanta, sai ya zare hannunsa nasa a hankali, taji

ɗ

uminsu yana barin fatarta.

"Zan nemo abu

in rufe miki ciwon anjima insha Allah."

Da haka ya juya ya fita rike da robar ruwan a hannunsa.

A lokaci guda Amina taji kamar numfashinta yayi wata tafiya mai nisa ne sai a yanzu take iya zuƙo shi, ssi kawai ta juya itama ta

ɗ

auko wata robar ruwan ta b

alle hancinta ta shiga sha yayin da bayanta ya jingina da drawers din store

ɗ

in.

Sai da ta kusa shanyewa sannan ta tsaya, tasa bayan hannunta tana goge wanda ya zuba a gefen bakinta. Bata san me yake shirin fara damunta ba amma koma meye, so take ta tunaw

a kanta cewa duk abinda ke faruwa wannan gaske ne ba labari ba da komai zai tafi daidai, abubuwa ba zasu tafi kamar a mafarki tare da mutumin da daga shi har ita basu san juna ba sai bayan aurensu kuma har yanzu bsta san manufarsa akanta ba.

Ma'aruf ba za

i ta

ɓ

a sauko da kansa haka akan ita

ɗ

in da ba kowa ba, don ta sani cewa bayan matar daya aura Allah kadai ya san matan daya sani a a rayuwarsa ko ma wanda yake tare dasu a yanzu, to don me yasa hankalinsa zai tsaya akan ita din da ba kowa ba, ita

ɗ

in da sa

baiyane yake cewar ba sa'ar rayuwarsa bace.

Ta girgiza kanta tana kokarin rufe robar ruwan, wannan lokacin kamar zubar ruwa ne kawai kafin zuwan tsawa, kamar iska ce mai da

ɗ

i kafin guguwa, sannan kamar ka

ɗ

awar ruwan teku ne a hankali kafin ambaliyar sa,

akwai wani abu dake jiran ta bayan wannan, kawai dai dan adam baya taba sanin lokacin da ƙaddara ko kuma wata masifar rayuwar ke zuwar masa ne.

Muryar Amma ta cikin mafarkin nan ta gifta a cikin kanta lokacin da take cewa

"Me yasa kika yarda ba zaki iya

ba Amina..."

A hankali tayi ajiyar zuciya tana fatan Allah yasa koma meye ke shirin faruwa ta iya tunkararsa da ƙafafunta a tsaye, daidai lokacin da a zahiri ta jiyo muryar Samirah ta shigo tana kiranta.

"A ina kika ajiye sugar?"

Sai kawai tayi sauri ta

ƙarasa goge bakinta sannan ta ajiye robar ruwan ta fita.

****

Karfe Bakwai daidai Ishaq ya iso, kuma Amina bata san me ya faru ba, don minti biyar bayan zuwansa sai ga sallamar

ɗ

aya abokin Ma'aruf da shima ta riga ta haddace shi a waya mai suna Faruk.

Su uku ka

ɗ

ai suka cika falon da surutu kamar su biyar, kuma duk yadda take ganin Ma'aruf na da magana sai a lokacin taji nasa mai sauki ne, don kafin taji muryarsa taji tasu da yawa musamman Faruk

ɗ

in, don shi yafi Ishaq yi mata magana sosai ma, har matars

a da ƴaƴansa yayi alkawarin kawo mata tunda yace yanzun a sama kawai Ma'aruf ya kira shi yace masa yazo.

Kuma har lokacin da suka zo

ɗ

in su Munaya basu tafi ba, Samirah dai taso tafiya amma sai Munayan tayi ta roƙonta akan su ƙara tsayawa tukunna, wani ab

u da ya ƙara bawa Amina mamaki don ita kanta ta san babu wani dalili Munayan ba zata yi ta cewa su tsaya ba. Ilai kuwa a lokacin da suka je kai musu abincin nan, a lokacin ta samu amsarta, saboda idon Ishaq na kan Munaya tunda suka shiga har ta juya Kitche

n don ta

ɗ

auko wani abun, kuma zata rantse ma taga sanda suka yiwa junansu murmushi lokacin da take zuba masa lemo, Allah ya sani yau ta fara ganin Ishaq

ɗ

in amma sai taji zuciyarta na jiyewa Munaya da

ɗ

i idan har hasashenta akansu gaskiya ne, don duk inda

nutsatsen namiji yake za'a saka Adam a wannan layin, kuma itama Munaya babu ruwanta da wani hargitsi sam.

Sun ji da

ɗ

in tarbar da suka samu kwarai, don ba'a kalamansu ka

ɗ

ai ta fahimci hakan ba, har a fuskar Ma'aruf da kuma yanayin kallon da yake mata tun l

okacin da taje ta sako wani dogon hijabi bayan shigowar su, wani abu da ita kanta taji ta kyauta da tayi hakan.

Bayan sallar isha'i ne sannan suka yi musu sallama suka fita, kuma sun da

ɗ

e a waje suna magana don har bayan tafiyar Faruk

ɗ

in shi da Ishaq su

na nan, har su Munaya suka tafi ta ƙarasa wanke iya kwanukan da aka

ɓ

ata kasancewar basu tara wanke-wanken ko

ɗ

aya ba dama a

ɗ

azu.

Kuma tana sallah lokacin da ta jiyo ƙarar fitar motar Ishaq

ɗ

in, sai dai har ta idar ta gama addu'o'in ta da komai bata ji l

okacin da Ma'aruf ya shigo ba ko kuma don haka ta ƙudirta a ranta cewa cikin gida ya shiga. Da wannan tunanin ta ninke sallayar tare da hijabin ta ajiye su a gefe, ta

ɗ

auko wayarta don kiran su Amma, sai dai daga layin nata har na Aminu bai shiga ba, kuma

bata son kiran Baba a wannan daren, don haka ta bari zuwa gobe, ta nufi wardrobe

ɗ

inta don ta

ɗ

auko

kayan bacci, wata sabuwar doguwar riga ta dauko sannan ta dawo gaban gadon don ta canja.

Ɗ

ankwalinta ta fara cirewa ta ajiye shi a kan gadon sannan ta shig

a kokawa da zip

ɗ

in rigarta, amma ga mamakinta saiya riƙe

ɓ

am yaki ko motsi, gashi ciwon hannunta ba zai bari ta rike shi da kyau ba, na dama kuma yaki ƙarasawa can saman, dama tunda tazo saka kayan ta kula yana da matsala amma bata yi tunanin ta kai haka

ba.

Har sai da hannunta ya ƙage ta tsaya ta tattaro dukkan ƙarfinta sannan ta cigaba da jansa, kafin a lokaci guda kamshin turaren Ma'aruf ya shiga hancinta.

***

A waje bayan Faruk ya tafi, sun dade a tsaye shi da Ishaq suna hirar tarin wasu abubuwan da

suka shafe su wanda yawanci duk akan matsalolin dake baibaye da rayuwar Ma'aruf ne, sai kuma zancen Abdurrahim, ƙanin Ma'aruf

ɗ

in dake can New York wata makaranta ta Bebaye irinsa, (Rochester Institute of Technology.) Don Baffa ya gaya musu cewa saura wat

anni biyu kawai ya kammala ya dawo gida.

Bayan wannan sun tattauna zancen Hamida ma inda Ishaq yayi-yayi da Ma'aruf akan ya

ɗ

auko yarinyar daga inda ya kaita ya dawo ta ita cikinsu, amma ya

ɓ

ata bakinsa a banza don ya riga ya rantse cewar Ruƙayya ba zata

ta

ɓ

a sanin inda Hamida take ba sai ya kammala da al'amarinta gaba

ɗ

aya, ko shekaranjiya da Mami taso yi masa zancen itama kai tsaye ya dakatar da ita ta hanyar gaya mata cewa lokacin da zai

ɗ

auko ta bai yi ba, don haka itama taja bakinta tayi shiru, don du

kkaninsu sun sani cewar idan har ya furta abu, Baffa ne kawai zai iya sauke shi daga kansa, amma ko da suka yi magana da Baffan shima cewa yayi...

"Wannan zancen naku ne kai da mahaifiyar yarinyar Muhammad, duk abinda kuka yanke idan har ba kuskure bane m

u namu addu'a ne tunda kune kuke da iko akanta fiye damu. Kuma kowannen ku yana da ikon da zai riƙe ta, duk da dai a matsayinta na mace an fi so ta zauna a gaban mahaifiyarta, amma idan har za'a samu matsala wajen tarbiyarta ko lafiyarta kamar yadda aka fa

ra yanzu, to zamanta a wajen naka zai fi."

Wannan zancen na Baffa shi ya bashi ƙwarin gwiwar cigaba da shirin da yake da niyya wanda yake jiran lokacin kawai. Daga ƙarshe kuma suka ƙare da zancen ginin su wanda Ishaq

ɗ

in ya gaya masa cewar ya samo wasu sa

babbin masu ginin da zasu fara aikin tunda Ma'aruf ya sallami wa

ɗ

ancan.

Kuma baiyi mamaki ba da Ishaq

ɗ

in baiyi masa zancen Amina ba, don ya riga ya fahimci cewa ba sai yayi

ɗ

in bane, akwai wasu abubuwa da ba lallai sai sun furta su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login