Showing 75001 words to 78000 words out of 94381 words

Chapter 26 - Farar Wuta Complete

cinyarta, zuciyarta na bugawa ne kamar zata faso kirjinta ta fito yayin da kowanne kalaman Hajiya Kilishin ke shiga kunnenta da tsantsar rudani da kuma tashin hankalin

da akace ba'a saka masa rana.

Kuma shirun da Hajiya kilishin tayi baiyi tsawon da zata iya fitar da komai ba lokacin da muryarta ta cigaba da cewa.

"Bari in

ɗ

auko miki komai tun daga farko Amina, ta haka ne zaki fahimci zance na.

Lokacin da ina yarinya

a wajen kakata na girma, ita ta raine ni tun daga lokacin yaye har girma na, a wajenta na samu tarbiyya da kuma tarin wayo da dabaru irin na zaman duniya, har yasa tun a ƙananun shekaru ina iya kallon rayuwar mutum na bashi shawara mai kyau da zata

ɓ

ulle g

a matsalolin sa, hakan yasa ƙawayena dama mutanen unguwar a lokacin suka laƙaba min sunan ƴar baiwa.

Bayan wani lokaci sai wannan kakar tawa ta rasu don haka dole na koma gidanmu inda naje na tarar da tarin ƴanuwana, don mahaifinmu matansa uku ne

kuma ƙar

amar cikinsu wato mahaifiyata ce kawai mai ƴaƴa tara, sauran biyun akwai mai goma sha

ɗ

aya da kuma sha uku.

Rayuwar gidanmu ba dadi sam, saboda a wajen kakata na saba komai namu mu uku ne kawai dani da ita da kuma wani almajirinta Awwalu da take riƙewa, d

on haka sai rayuwar gidan yawan tazo min a wuya, gashi babu ruwan kowa dani hatta mahaifiyata kuwa da hankalinta yafi karkata kan yayyena da suka fi girma a lokacin, don haka da lokacin shigata babbar sakandire yayi sai na samu mahaifina nace ya maidani ma

karantar kwana don zata fi mun da

ɗ

i, al'amarin kamar ba zai yiwu ba da ƙyar da rabo dai na samu na tafi.

A can na hadu da ƙawayena biyu kuma ƴanuwan da zan iya kira da na jini wato Salamatu da Saratu, wadannan mutane biyun Amina sunyi min duk wani gata a

lokacin zama na a makaranta da ya kamata ace iyayena ne suka yi min, hatta ku

ɗ

in jarabawar karatuna tsaf su suka biya min har muka kammala, don ban da

ɗ

e da shiga makarantar ba mahaifina ya rasu abubuwa suka sake harigitsewa a gidanmu.

Kowacce mace taƙi fi

ta tare da ƴaƴanta kuma aka ƙi a raba gado kowa ya koma yana zaman kansa ne da kuma zaman gasa a tsakani don kowacce mace tana so ne ace ƴaƴanta sune suka fi samun arziƙi, musamman Innata da take ganin itace ƙarama an riga an rainata ita da ƴaƴanta don hak

a bata damu da duk wata hanyar da yayyena ke bi su samo ku

ɗ

i ba indai za'a samun, burin kowacce kawai ace ita da ƴaƴan ta su ke ƙyallin maiƙo a gidan.

Abinda nazo na tarar kenan bayan na kammala makaranta na dawo, wani abu da tun bana saka shi a raina har

ya zamo kwanci tashi nima tunanina ya karkata ga hakan, sai dai ni tawa ƙwaƙwalwar ta raina irin hanyoyin da suke bi, na kasa yarda cewa mutum ba zai iya magance matsalolin kansa a rayuwa ba sai ya tsugunna neman taimakon wani daban, don haka na shiga amf

ani da ƙwaƙwalwata wajen cimma manufata.

Almajirin da kakata ta riƙe Awwalu yana aikin masinja a wani kamfani, da taimakon sa da kuma dabara ta na samu aiki a kamfanin a matsayin mai gyara da kuma harha

ɗ

a takardu... In taƙaice miki zance Amina, wata na bi

yu a wajen nan na fara karbar ku

ɗ

i sama da albashi na ba tare da kowa ya sani ba, kafin a shekara kuwa, ni da Awwalu muna samun daidai da abinda ma'aikatan wajen nan ke samu, ban ta

ɓ

a bawa wani jikina ba sannan ban ta

ɓ

a bin wani malami ko boka ba, da wayo

da dabarata nake komai ta yadda babu mai zargina kuma dukkan wani bincike ba zai ta

ɓ

a biyowa ta kaina ba.

Ku

ɗ

in da nake samu a kowanne wata sai da ya zama hatta a cikin gidanmu babu wanda ake kallo sai ni, mahaifiyata da ƴanuwana duk suka dawo suka raja'a

a kaina, aka shiga bani wani irin girma da ban san yana wanzuwa a duniyar nan ba, ya zama zan iya taka kowa a gidanmu in zauna lafiya, nasa aka rushe

ɓ

angaren

ɗ

akunan mu aka gina mana danƙarere da ya tsone idon sauran ƴanuwana kafin daga baya suma su dawo

su kwantar da kansu."

Muryarta tayi shiru a daidai wannan lokacin alamun ta tuna wani abu da ya saka ta murmushi, wani murmushi da har sautin sa sai da ya fito kafin tace.

"A wannan lokacin ne kuma na nemowa kaina mijin aure Amina, munyi ƙoƙarin canja k

amfanin aiki ne ni da Awwalu don na yarda da karin maganar da hausawa ke cewa zama wuri

ɗ

aya tsautsayi, don haka muka je kamfanin Bakori a wata ranar laraba, inda kafin mu shiga na hango Alhaji Mansoor ya fito daga ciki ya shiga motarsa, tun da na ganshi a

wannan lokacin na sawa zuciyata cewa shine mijin aure na, don haka bamu nemi aikin ba nace da Awwalu mu juya, kuma kafin sati ya zagayo na bi hanyar da sani na ya manne a zuciyar Alhaji Mansoor.

Na kashe ku

ɗ

i sosai a wannan lokacin duk da ba sai na gaya

miki yadda na aiwatar da komai ba zan gaya miki cewa sati guda na shafe ina siyan shafi guda a jaridar da Alhaji Masoor ke karantawa, ana wallafa hotona cikin irin ayyukan da na san dole suka ja hankalinsa.

Har da masinjan ofis

ɗ

insa da ma direbansa na ha

ɗ

a baki dasu suna bashi labaraina, kuma bayan ya yarda da auren nawa, sai da na toshe bakin mutane da yawa wajen fallasa wani abu mummuna akaina.

Lokacin da na shigo gidan nan kuwa Amina da naga Maimuna, a lokaci guda na raina kaina na kuma ƙara yarda cew

a sa'ata ce kawai ta shigo dani cikin rayuwar Baffa, don wanda yake da mata irin Maimuna babu abinda zai kaishi auren irina.

Amma ban damu sosai ba, tunda na san na shigo daular arziƙi ne kuma na ciri tuta a cikin ƴanuwana da a lokacin suka maida ni kamar

mahaifinmu saboda biyayya.

Ban da

ɗ

e ba lokacin da Maimuna ta sami cikin Shukra ƴarta ta uku, don haka sai nayi amfani da hali irin nawa na ja

ɗ

anta na biyu wato Ma'aruf a jikina, na so ha

ɗ

awa har da Jamal ma amma shi da yake yafi wayo a lokacin sai ya ma

nnewa uwarsa.

Ni na yaye Ma'aruf da hannuna Amina, ni na raine shi tun daga wannan shekarun har zuwa girmansa, don ko bayan haihuwar Maimuna bai bar wajena ba itama kuma bata yi magana ba saboda nauyi na da take ji a sannan, don a lokaci guda na zage na k

ar

ɓ

i gidan, ni nake yin komai musamman da bata da lafiya, bayan tayi haihu kuma ni nayi

ɗ

awainiyar da ƴanuwanta ma basu yi ba, hakan yasa a lokaci guda na samu soyayyar kowannensu, hatta Baffa kuwa, don sanda ya aure ni ba zan tantance irin son da yake min

ba, amma a cikin shekara guda sai da na tabbata ni da Maimuna munyi kunnen doki a zuciyarsa.

Soyayyar kowa na siya tsakani da Allah don bana yarda da gaibu Amina, kamar yadda baba yarda da aikin wani boka ko malam da baya zuwa ko'ina, ni ina yin shiri na

shekara da shekaru ne ba na wani

ɗ

an lokaci ka

ɗ

an ba.

A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana har ta kai na fara haihuwa nima, a wanann lokacin tsananin kirki da kyautatawata yasa na kere Maimuna a zuciyar Baffa ta yadda ita kanta bata damu ba, don tana

ganin cewar na cancanci hakan."

Tayi shiru wucewar wasu sakanni tana kallon Aminan kafin ta cigaba.

"Bari na gaya miki wani daga cikin babban sirrina don ki ƙara tabbatarwa cewa da gaske nake al'amarina... Nice na gurguntar da Maimuna..."

Babu shiri Ami

na ta

ɗ

ago ta kalle ta, idanunta na haskawa da tsananin mamakin da yake ƙaruwa akan wanda take ciki. Sai kawai tayi murmushi mai zurfi tana kallonta itama.

"Ƙwarai Amina, ni na saka Maimuna ta rasa ƙafafunta, kin san dalili?"

Ba ta bata damar amsawa ba t

a cigaba.

"Na gaya miki Maimuna tana kyau, to labulen

ɗ

aki na kawai nake

ɗ

agawa in hango ta ranar girkinta ta nufi

ɓ

angaren Baffa, idan tayi kwalliyar nan bana iya daurewa kishina dake tasowa Amina, rana daya na yanke cewar ba zan iya jurar cigaba da gani

n zuwanta ba don haka takanas na tafi asibiti na samu wani ma'aikaci a

ɓ

angaren ƙashi, na bashi maƙuden ku

ɗ

a

ɗ

en da a lokaci guda ya bani wani magani mai kama da poison wanda ke lalata har ƙashin mutum.

Kuma sai da na jira har bayan watanni hu

ɗ

u da rashin

lafiyar zazza

ɓ

i ya kamata sannan na ha

ɗ

a baki da wani yaro daga Nijar yazo har gida yayi mata allurar maganin nan a matsayin likita, kuma babu wanda ya san ni na dauko shi don

nambarsa na sanya a wayar Baffa da sunan likitan gidan Dr. Ashiru, nace idan yaz

o yace Dr. Ashirun ne ya turo shi.

Kuma bayan yayi mata allurar ƙafafun nata sun lalace gaba

ɗ

aya na bashi ku

ɗ

i ya koma ƙasar sa Nijar, shi kuma Dr. Ashiru yazo yace bai san yaron ba, da aka duba lambar aka ga ma ba tasa bace dole aka haƙura don ko ƴan san

da basu iya samo komai ba.

Kuma bayan haka ni na zauna nayi jinyarta Amina, tun kafin a yanke ƙafafun har muka je India aka cire su gaba

ɗ

aya, shekara guda da rabi na

ɗ

auka ina jinyarta, na hana kowa wannan

ɗ

awainiyar hatta ƴaƴanta da ƴanuwanta tunda na sa

n na samu abinda nake so, na san tsawo na da nata ba zai ta

ɓ

a daidai a idanun Baffa ba, kuma hakan ya ƙara min ƙima a idanun kowa a gidan nan ta yadda nake cin kare na babu babbaka, kowa yana girmama ni da bani darajar dana siya a wajensu, hatta ƴaƴan Maim

una a idon kowa kamar nawa suke don babu adadi su Munaya zasu zo su fa

ɗ

a min abinda mahaifiyar tasu ma baza su iya fa

ɗ

a mata ba ko kuma su nemi shawarata akan abinda ita bata ma sani ba.

Don haka yanzu na san kin fahimci cewa saboda ni kika samu soyayyar

kowa gidan nan, da kuma abinda nake nufi cewa duknwanda kika furtawa wannan zancen kamar kin bude masa kofar lahirarsa ne."

Muryarta tayi shiru a wannan lokacin, wucewar wasu sakanni sai kuma ta taso a hankali ta dawo kujerar kusa da inda Aminan ke zaun

e, kuma bata damu da rashin kallonta da har yanzu bata yi ba ta cigaba.

"Mu dawo kan abinda ya kawo ni, dalilin da yasa na aura miki Ma'aruf Amina, kamar yadda na fa

ɗ

a ba don ki zo kiyi rayuwar zaman aure bane kamar yadda naga kin fara kokarin yi a yanzu,

na kawo ki gidan nan ne saboda ki taya ni mu ƙarasa babban burin da nake dashi a duniya.

A farkonsa ban tsara dake ba, amma daga ranar da Baffa ya yanke shawarar cewa dole Ma'aruf ya ƙara aure, daga ranar kika shigo cikin lissafina Amina, don Ma'aruf gin

shiƙi ne guda a cikin burin da nake son cimmawa a yanzu, ina

ɗ

ora shi ne akan matakan da zasu kaini ga yin nasara

ɗ

aya bayan

ɗ

aya, don haka idan har aka samu matar da zata ra

ɓ

e shi wadda ba zan iya juyawa ba Amina abubuwa zasu lalace min ba ka

ɗ

an ba, shi y

asa tun kafin kowa yayi wani yunƙuri musamman mahaifiyarsa dana san a tarin ƴanmatan dake danginsu zata iya ha

ɗ

a shi da wata, na duba bayana na za

ɓ

o ki."

Sai da ta sake gyara zamanta tana fuskantar Aminan dake zaune a gabanta ta sunkuyar da kanta sannan t

ace.

"Ɗago nan ki kalle ni Amina..."

Ta kuwa

ɗ

ago da kan nata amma bata kalle ta ba, gashin idanunta sun hade suna shaida jiƙewar hawaye alamun kuka take yi, wani murmushin yaso giftawa a le

ɓɓ

en Hajiya Kilishin amma ta tare shi, don da kukan Aminan da ku

ma shi

ɗ

in, duka bata ga muhallinsu a yanzu ba.

"Sati guda zan baki kiyi tunani, idan har kika yarda dani, zan ƙawata rayuwarki da dukkan ƙawar da baki taba tunani ba Amina, zan miki liƙin alheri har sai hannayenki sun kasa tarewa, zan

ɗ

aga ki ki zama tau

raruwa a idon kowa musamman cikin danginki, zan kyautata rayuwarki da ta dukkan makusantanki idan har kika miƙo min hannunki na kama kamar yadda na tsara komai..."

Ta sake yin shiru tana kallon ha

ɗ

ewar gashin idon nata, sai kawai ta ha

ɗ

iye yawun dake baki

nta sannan ta ƙarasa furta abinda ke tahowa tun daga ƙasan zuciyarta, abinda take jin ko da duniya zata taru akanta ba zai canja ra'ayinta ba.

"... Idan kuma har kika zabi yin kato

ɓ

arar fallasa ni don ki tsira, na rantse miki da ubangijin da ya halicce mu

rayuwarki zata dulmiya ne a baƙin ruwan da zaki yi ta yin ihun da babu wanda zai ta

ɓ

a jiyo muryarki!"

***

Tun da ya shigo gidan jikinsa ya bashi akwai wani abu da ya faru, don fitilar falo ma a kashe take, iya hasken ta korido ne kawai yake a kunne, a

falon ya ajiye wayoyinsa da su ka

ɗ

ai ne a hannunsa sannan kai tsaye ya nufi hanyar koridon,

ɗ

akinsa yayi niyyar wucewa ya watsa ruwa don Allah ya sani a gajiye yake, amma a lokaci guda idanunsa suka kai kasan ƙofar dakinta da nan ma fitilar a kashe take.

Har ya wuce ya dawo ya tsaya ya kwankwasa, kusan sau uku amma shiru bata amsa ba, sai yayi tunanin sallah take don a lokacin masaltai ke kiran isha'i, don haka sai kawai ya juyo ya dawo

ɗ

akinsa.

Ya kunna fitulun ciki da suka gauraye da haske a

ɗ

akin komai

yana fitowa tar cikin kammalen da yake. Ma'aruf yana da tsaftar da duk wanda ya zauna dashi zai gane, don indai abu nasa ne to ba zaka ta

ɓ

a zuwa kaga komai ba'a muhallinsa ba, sannan kuma yana da haƙurin da zai zauna da wanda bai damu da hakan ba, shi yas

a ya iya zama da Ishaq dake wular da komai inda yaga dama.

Minti goma kawai ya

ɗ

auke shi gama shiryawa cikin wasu kayan bayan yayi wanka, ya dawo falon daidai lokacin da wayarsa ke ƙara a inda ya ajiye ta, lambar mutumin da yasa ya nemo masa bayani akan M

r. Okafor ne, ya tsaya kawai yana kallon kiran ba tare da ya dauka ba har ya katse sannan ya tura masa dan guntun saƙo cewar suyi magana zuwa gobe.

A yanzu ya sani cewar tarawa kansa abubuwa yana

ɗ

aya daga cikin abinda ke saka shi damuwa har ciwonsa ya t

ashi don Allah ya sani a yanzu yana tsoron ciwonsa fiye da kowa, ya sani cewa idan abubuwa suka lalace masa a yanzu bai san me ya cimma a rayuwarsa ba. Shi yasa bai

ɗ

auki kiran mutumin ba, don a yau ka

ɗ

ai abubuwan da ya fuskanta suna da yawa.

Takardar sam

macin da ya samu

ɗ

azu a Office ta girgiza shi ba ka

ɗ

an ba, ya kasa hango inda Rukayya da iyayenta suka samu karfin gwiwar kaishi kotu akan zancen Hamida, kalaman Baffa su suka bashi damar ƙin saurararsu amma bai taba tunanin hakan daga garesu ba. Ya kira I

shaq sunyi maganar amma duk tsawon tattaunawar su ya gaya masa cewa chance din da suke dashi ka

ɗ

an ne don a matsayin Hamida na mace dole ne a wajen mahaifiyarta ya kamata ta zauna har girmanta kuma ƴan bayanan da suke dashi game da dalilin su na dawowarta

wajensa basu da karfi sosai.

Sannan bayan yayi haka ya san yayi aiki a Office din amma ya tabbata idan ya koma gobe zai samu kura-kurai da yawa, don a cikin aikin ya gama yanke dukkan abinda ya riga ya tsara game da zancen kotun da kuma Hamida.

Kuma baya

buƙatar yin zancen da kowa shi yasa ko cikin gida bai shiga ba tunda Baffa baya nan yayi tafiya Abuja, yaga kiran Mami amma shima bai bi bayansa ba kuma itama bata sake kiran ba har yanzu.

Ƙ

afafunsa suka sake komawa kitchen

ɗ

in bayan ya kunna fitila yana

nazarin komai, akan table

ɗ

in kitchen

ɗ

in, jerin kayan abincinsa ne kamar yadda take tsara su kullum, yaji wani abu ya zarce cikin makogwaronsa, a cikin ƴan kwanakin nan ya sani cewar yarinyar nan ta taimakawa ƙwaƙwalwar sa wajen samun hutu ta wani

ɓ

angar

en, don akwai nutsuwa sosai ace idan aiki ya zuƙe shi da rana akwai inda zai iya zuwa ya huta ba wannan hargitsatsen gidan nasu shi da Ishaq ba. Kamar ya zauna yaci abincin sai kuma kawai yaji ba zai iya hakan ba alhallin bai ganta ba.

Sai kawai ya zaro w

ayarsa ya kira lambar Samirah, bugu

ɗ

aya biyu kuwa ta dauko, muryarta a ciki ta fara cewa 'To Mami.' kafin tayi sallama.

"Yaya barka da dare."

"Kun yini lafiya?"

"Lafiya ƙalau."

Ta amsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login