Showing 51001 words to 54000 words out of 94381 words
ta fara fahimtar m
anufarsa akanta kafin ta yanke hukuncin da zata iya kare kanta dashi.
Ta miƙe zaune a hankali tana son daidaita ganinta, a sannan ne ƙwaƙwalwarta ta tuna mata cewar bata yi sallar asuba har gari ya waye haka, ƴar wayarta dake gefe ta jawo tana tunanin yad
da akayi alarm
ɗ
inta bai tashe ta ba amma sai ta tarar ta mutu saboda ba caji, don haka ta mike da sauri ta nufi bandakin a lokacin da idanunta suka sake kallon ƙofar dakin ta tabbatar muƙullin data kulle ta dashi yana jiki har yanzu kafin ta shiga ciki.
Bayan ta idar da sallar ta da
ɗ
e tana addu'ar neman gafara da kuma ƙwarin gwiwar tunkarar duk abinda ke gabanta kafin ta mike, a cikin akwatin kayan kwalliyar nan ta samo sabulu, ta shiga tayi wanka, kuma duk da cewar komai sabo ne a wajenta bata sha wahala
r gane kan fanfunan dake ciki ba tayi wankan ta fito.
Ta dawo cikin
ɗ
akin dake ƙara tuna mata cewar rayuwarta ta canja da gaske, don har yanzu yanayin da take ciki ba zata iya fassarashi ba, aayƙin da take ji daya ne kawai na cewar ƴan gidansu zasu zo, do
n haka da ƙyar ta ture duk wani tunani dake ranta ta shirya cikin wata doguwar rigar da hannunta ya fara kaiwa a cikin kayan dasu Ummi suka jera mata jiya, bata
ɗ
aura
ɗ
ankwalin ba sai kawai ta yafa shi akanta.
Ta kalli kanta a mudubin
ɗ
akin tana ganin yad
da idanunta suka fara washewa da kukan da tasha a jiya kafin tasa duka hannayenta tana gyara zaman
ɗ
ankwalin akanta, siraran awarwarayen da har yanzu ke hannunta suka shiga rawa suna tuna mata da zamansu, don haka tayi saurin cire su gaba
ɗ
aya ta ajiye akan
mudubin sannan ta juya ta kalli kofar dakin.
Kai tsaye ta ture komai a ranta ta nufi kofar ta bu
ɗ
e ta, korido ne mai dan tsawo dake dauke da ƙofofin
ɗ
akuna guda uku, ta sani cewa dole a daya daga cikin dakunan ya kwana tunda yace mata yana nan, don haka
bata ko yi gigin bude kowacce ba kafafunta suka taka suka fita zuwa falo, anan ne, zuciyarta ta narke da kowanne abu na cikinsa dake shaida ha
ɗ
uwarsu tun daga nesan da take, komai yana ha
ɗ
ewa cikin kalar
ɗ
anuwansa cikin wani simple ado daya dace da wurin.
Ta jinjina kai a hankali kafin ƙafarta ta tafi zuwa daya korido
ɗ
in anan, tana jin yadda fatarta ke sulalewa akan santsin wajen duk da ƙurar data lura akwai, kofar wani katon kitchen anan da komai na cikinsa ash ne da kuma fari, akwai store mai
ɗ
an girma
data bu
ɗ
a ta tarar da kayanta fal a ciki, wasu ma duk a cikin buhu suke ba'a bu
ɗ
e ba.
Ta dade tsaye tana kallon kayan da kuma tsarin drawers din kitchen din kafin ta hango wats kofa a can gefen fridge, taje ta bude ta, hanya ce mai dan fadi dake zagayawa
kowanne bangare na gidan, inda daga can jikin katangar kuma ta hango wata kofa data tabbatar ta nan ne ake shiga cikin gidansu. Ta rufe kofar ta dawo tana sake komawa store din nan don ganin kayanta, tsji wani abu kamar magana amma bata tabbatar ba ta ciga
ba da duba kayan.
A lokacin ne kuma ta jiyo muryarsa, kamar irin ruwan saman dake sauka a lokaci guda tana ƙarasowa hanyar kitchen
ɗ
in, ba shiri hannayenta suka nemi hannun kifar store
ɗ
in amma kafin ta iya rufe ta gabadaya, ya karaso don hannun nata ya
t
saya cak tare da numfashinta, idanunta suka hango mata shi ta zirin ƙofar da bai gama rufuwa ba, kuma a lokaci guda taji zuciyarta tayi kuli-kulin kubra ta fa
ɗ
o daga wata sama mai nisa.
Ashe jiya bata lura da tsawonsa sosai ba, a yanzu daya canja cikin wa
ni yadi kalar sararin samaniya da irin
ɗ
inkin rigar da bai kai gwiwa ba, bata jin a cikin abokan Aminu gabadaya data sani akwai wanda zata iya kwatanta shi tare dashi. Ta hadiye yawu tana kallon yadda idanunsa ke lumshewa da sauraren abinda ake gaya masa t
a cikin wayar kafin yayi magana.
"Me kace?" Muryarsa a hankali ta fito, da wani irin amon da yasa jikinta girgizawa, numfashinta yana katsewa ba gaira ba dalili. Me yazo yi ne ma a kitchen din?
Ta ga ya girgiza kansa sannan ya zura hannayensa cikin gashi
n kansa yana motsa su, a lokacin ne kuma iska ta buso mata da ƙamshin turarensa, wani abu kamar ƙamshin musk ko mint, ko kuma meye hancin nata ya jiyo mata, sai kawai ta juyar da kanta gefe yayin da muryarsa ta sake fitowa.
"That issue aside Faruk, ba yan
zu zamu neme shi ba, let's give him atleast two weeks to settle down, (mu bashi kamar sati biyu da zai huta) babu wuya zamu kama shi a sannan. Yanzu let's just focus akan wa
ɗ
annan mutanen, I have somewhere to be now amma zan kira Martha ta min sending duk
wani back-up da muke dashi akansu, zuwa yamma we decide where to meet sai ka kawo naka mu ga me zamu fitar."
Murza ƴan yatsunta kawai Amina ke yi tana fatan ya juya ya fita, amma ga mamakinta sai kawai taji wata muryar mace ta taho tana fa
ɗ
in.
"Yaya baka
ganta bane?"
Kuma kafin ƙwaƙwalwar ta ta gama lissafawa, wata budurwa ta shigo cikin kitchen
ɗ
in hannunta dauke da wani katon food flask, doguwar riga ce a jikinta shade din albasa (onion color) da wani dan karamin mayafi data yafa a sama maroon colour.
"Bata nan kitchen
ɗ
in?"
Ta sake tambaya tana ƙarasowa ciki fuskarta
ɗ
auke da murmushi, a lokaci guda taji wani abu ya ratsa ta har tafin kafa, don babu wata kwana-kwana ta gane ƙannensa ne suka zo, kuma shigowar sa kitchen
ɗ
in ita yake nema. Taga yadda h
annayensa ke motsawa a cikin gashin nasa alamar bai san me zai ce ba lokacin da yarinyar ta tafi tana ajiye food flask
ɗ
in can kusa da gas cooker.
Sai kawai tayi karfin halin
ɗ
auko wani jug a gefe sannan ta bu
ɗ
e ƙofar store
ɗ
in ta fito, zuciyarta na gaya
mata ai tunda a yanzu ƙirgen ya tashi daga su biyu ta tsira.
"Sannu da zuwa."
Muryarta tasa duka su biyun juyowa suna kallonta, yarinyar ta washe baki cikin fara'a sannan ta taho da sauri ta rungume ta.
"Ashe kina ciki, Barka da safiya."
Sai da zuciyar
ta ta buga a kirjinta saboda mamaki, mamakin da ta daure cikin nata murmushin itama tana rungume ta.
"Sunana Samira, tare muke da Surayya da Munaya suna falo, fatan kin tashi lafiya?"
Ta fa
ɗ
a bayan ta janye daga jikinta, sai ta
ɗ
aga kai da nata murmushin
mai fadi ta amsa da.
"Lafiya kalau, nagode sosai."
A lokacin ne kuma idonta ya kai kansa, ta san kallonta yake tun da ta fito don tana jin tasirin yadda idanun nasa ke shiga jikinta, gabanta ya fa
ɗ
i sakamakon
ha
ɗ
a idanun da suka yi, kallon da yake mata
mai cike da nazari ne, kamar yana saka scanner cikin idonsa yana son tantance ta.
Kuma a lokacin ne babban al'amarin safiyar ya faru, bakinsa ya motsa da wani guntun murmushi yana rufe idanunsa ya bu
ɗ
e su akanta, kamar ma ƙifta mata idanun yayi, abinda ka
fin ta gama tantacewa ya juya ya bar kitchen
ɗ
in.
A kusa da kafafunta taji cikinta ya fa
ɗ
i gaba
ɗ
ayansa har ƙasa tsabar tsurewa da kuma mamaki, ilahirin jikinta ya
ɗ
auki rawa kafin muryar Samirah ta cigaba da magana cikin tunaninta, sai ta hango kanta ta t
sugunna tana ƙoƙarin tattara jikinta waje
ɗ
aya kafin ta iya fahimtar me take cewa.
"Abinci muka kawo muku kafin mu fara zagayen gidan sauran amaren, gamu nan da kaya fal cikin mota kowacce tayi mantuwarta... Na san kema kinyi taki ko?"
Bata gama daidaita
tunaninta ba, don haka bata san sanda ta
ɗ
aga mata kai ba tace.
"Ina tashi nima naga na manta chager wayata."
"Ai sai a hankali ma zaki yi ta neman wasu abubuwan, Ya Shukra har da system
ɗ
inta gabadaya ta manta kuma project
ɗ
in masters take yi..."
Ta g
yada kai tana ƙoƙarin murmushi sanda wata ta ƙaraso cikin kitchen
ɗ
in itama, watakila itace zasu yi sa'anni
ɗ
aya ko kuma ace ta fita da kadan, tana da glasses wanda kana gani ka san medicated ne, ita kuma bakar abaya ce a jikinta wadda ta fito da
ɗ
an haske
n fatarta don ita ba fara ce sosai kamar Samiran ba, zata iya jera su layi
ɗ
aya da yayan nasu.
"Ashe kina nan matar Yaya..."
Ta fada da nata murmushin itama tana karasowa kuma ga mamakin Amina itama sai kawai ta rungume ta tana fadin.
"Oyoyo, we welcome
you into the Family dear, jiya mutane basu bar mu mun ganki ba."
A yanzu ƙwaƙwalwar Amina kwancewa tayi gabadaya, don ita ko a gyangyadi bata taba kawowa haka abubuwa zasu kasance ba, ko jiya sai da su Aunty Ma'u suka gaya mata cewa tayi taka-tsan tsan d
a ƴanuwansa.
"Ƴan gayu ne na karshe Amina, kija jikin ki ki tsira da mutuncinki..."
Haka Aunty Ma'un ta ra
ɗ
a mata a kunne.
To me yasa ne komai yake faruwa sa
ɓ
anin tunaninta ne? Ko dai akwai wani abu da ba daidai yake tafiya bane?
"Sunana Munaya.."
Ta
kara fa
ɗ
a tana miko mata hannu, sai tayi karfin halin mika nata tana murmushi itama.
"Yanzu zaki ganta kamar normal mutum amma idan kika tabo wajen karatu zaki fara tunanin aljana ce."
Samirah ta fa
ɗ
a tana kallonta.
Sai kawai ta girgiza kanta.
"Yarinya
r nan ta raina ni da yawa, kar ki yarda da ita."
"Wallahi da gaske nake Aunty Amina idan kina da ƴanuwa a Buk ki tambaye su kowa zai ce miki ya san GB (Genius Brain) haka suke ce mata, irin ƙwaƙwalwar su
ɗ
aya da Yaya."
Munaya ta girgiza kanta tana murmus
hi.
"Astagfirullah, Allah ka tsare ni daga sharrin yarinyar nan, zo muje ku gaisa da Surayya, tana can tana ta aikin pressing waya."
Da haka Munayan taja hannunta suka yi hanyar fita, Samurah ta biyo bayan su.
A falon wadda suka kira da Surayya na zaune
kan kujera mai zaman mutum
ɗ
aya tana ta faman danna wayar hannunta, daga ƙasa kuma wasu ƴan mata biyu ne
su ma da kallo daya zaka yi musu ka san ƴan aiki ne, gabansau dauke da wasu trays din dake dauke da food flask har hudu da kuma jug na lemo shima kala
biyu, alamu su suka shigo dashi daga motar da Samirah tace suke.
Kuma da shigowarsu Surayyan da zata ce sun yi sa'anni da Munaya ta dago da nata murmushin itama sannan ta ajiye wayar ta taho ta rungume ta, a yanzu Amina taji kamar ta saba ne ma da yanayi
n gaisuwar tasu.
"Na san ma wannan mai bakin ta gaya miki sunana koh?"
Ta tambaya tana kallon Samirah da tayi wajen ƴan aikin nan tana gaya musu akwai wata baƙar keda da badu shigo da ita ba.
"Nima tun kafin in shiga ta gabatar dani ai." Cewar Munaya ta
na neman waje kan daya daga cikin kujerun.
Amina ta daga kai tana murmushi.
"Ta fada min, naji dadin ganin ki kuma."
"Haba dai godiyar tamu ce ai, na san na samu wajen zuwa idan Mami ta matsa min da zancen waya, da fatan dai ba zaki damu ba idan kina ga
nina a compound din gidan nan."
"You dey mad? Kike fada a gaban yarinyar nan? Kema kin san kamar Mamin taji ne ai."
Cewar Munaya tana dariya, Surayya ta kalli Samiran dake tsaye tana jinsu.
"Ta gaya mata mana, itama ai tana da nata secret din a wajena."
"Ba dai zancen wannan cake pack din Ya Salma bane, wlhy sai inyi confessing in fada, tunda idan nayi cake din ai har da Mamin ake ci ace yayi dadi."
"What? Kayan Salman kika dauka? Amma bata sani ba har yanzu ko?" Cewar Munaya.
Surayya ta koma kan kuje
ra tana sake
ɗ
aukar wayarta.
"Ki bari kawai, kuma wallahi guda daya ne a cikin kayanta, ranar da ta nema ta rasa, inaga Yaya Ishaq za'a kira yayi aikinsa a gidan nan."
Suka kyalkyale da dariya gabadayansu yayin da Amina ke tsaye har yanzu da jug din nan
data dauko a hannunta tana taya su da murmushi.
A lokacin
ɗ
aya yarinyar nan ta dawo daga waje. Samirah ta karbi kedar tana miko mata tace.
"Gashi Aunty Amina, cupcakes ne na san zaki iya yin baƙi a cikin satin nan, wadannan kuma abinci ne breakfast da Di
nner, naga yayan ma ya fita, flask din da na kai Kitchen kuma miya ce a ciki, murfin suka balla yanzun nan da safe shi yasa na riƙo shi kar ta zube."
Wannan karon Amina ta tabbata mamakin da take ciki ta kai ta har wuya tana shirin nutsewa.
"Kar ki wani
damu idan yarinyar nan ce ina jin sai kin dinga korarta daga gidan nan akan abinci..."
Kafin Munayan ta karasa fada wayarta tayi kara. Sai ta miƙe tana cewa...
"Ya Shukra ce, kuzo mu tafi kafin ta fara mitar nan tata."
Surayya ta mike kuma ga mamakin Am
ina sai suka zo suka sake rungume ta daya bayan daya suna gaya mata cewa in suka dawo zasu shigo sai suje cikin tare ta gaida su Mami. Itama ta rako su har kofa tana fadin su gaishe su.
Bayan sun fita, ta tsaya daga barandar falon tana kallon compound din
gudan da yasha wasu interlocks masu ƙyalli, da kuma shukokin wasu kananan bishiyu a jikin katangar da basu fara girma sosai ba.
Ji tayi zuciyarta ta washe da wani abu da baza ta iya fassara shi ba, mamaki na yawo akanta har yanzu na yadda abubuwa ke canj
awa daga zaton ta, kirkinsu yasa taji sun burge ta sosai yadda basu
ɗ
auki kansu wani abu ba, taji zuciyarta na
dokin ta saba dasu fiye da haka, kafin ta juyo ta dawo tana rufe kofar
ɗ
akin, idonta ya kai kan tarin flasks din nan tana tunanin yadda zata yi d
a abincin, ko da yake ba ita ka
ɗ
ai suka kawowa ba har dashi ta sani.
Zuciyarta ta buga da ta tuno cewar zai sake dawowa gidan ya same ta, ta tuno kallon da yayi mata har da murmushi da yadda taji a lokacin tana kasa tantance tsoro ne ko akasin sa... Ashe
dukkan abubuwan da take hangowa da sauki sun sha banban da tunaninta...
Kwankwasa kofar da akayi ya katse tunaninta, ta tafi da sauri ta bude tana fatan su Maryam din da take jira ne, su din kuwa... Har da Hafsa dasu Mimi da Fatima da wasu daga cikin ƴaƴa
n Baban kurna, su takwas, sun riko wasu sauran tarkacenta da tsintsiyoyin nan... Ranta ya karasa yin fari ƙal ta hau rungume su daya bayan daya tana murna, rungume sun da bata san tayi ba sai da taji Fatima na cewa.
"A ina kika koyo wannan sabuwar gaisuwa
r kuma?"
Ita ka
ɗ
ai ta cije lebbenta tana murmushi.
**
A cikin
ɗ
akin Hajiya Kilishi, ta kalli kawarta Salamatu tana girgiza kai.
"Banbanci na dake kenan, bana fa
ɗ
uwa na hakura, a sannu nake bin abu ina gutsira har in kai ga ci, kuma nasha gaya miki haku
rin da kika kasa a tare da Shamsu (mijinta) kenan. Shi yasa har rayuwa ta kawo ki wannan ga
ɓ
ar."
Hajiya Salamatun ta girgiza kanta itama.
"Ga
ɓ
ar da nake cin duniya ta da tsinke ba, kar ki kawo wannan zancen kuma bayan mun gama na Saratu, mu tattauna abin
da ya kawo ni, Ya zaki yi da al'amarin ƴar tasa?"
Hajiya kilishi ta kalle ta sosai tace.
"Na gaya miki ai, saboda ban samu nasara akanta a asibitin nan ba hakan baya nufin na hakura, ai na rantse sai naga bayanta don ko wajen uw*rta ba zan bari ta koma b
a tunda har zata fara zame min ƙalubale tun daga yanzu. Babu wanda ya isa ya shiga zuciyar Ma'aruf da tasirin da yafi nawa Salamatu kema kin sani.
Saboda haka matsalolin nawa zan hade guri guda, bayan tsinannun asibitin nan da suka hana ni kwana a wajenta
sun sallame ta, wani Creche wai ya kaita a hanyar Bompai saboda kin san muna cikin sha'anin bikin nan. Saboda haka a yanzu da komai ya lafa zan saka ne ya dawo da yarinyar wajen ita Aminar, ta yadda zan aiwatar da manufata hankali a kwance.
Kin san dai d
alilin da yasa na shiga na fita ya auri yarinyar nan, saboda daga ita har iyayenta zan iya juya su sannan an tabbatar min tana da sanyi halin da al'ummar gidan nan kaf zasu karbe ta cikin ƙankanin lokaci, na gaya miki tana da irin fuskata Salamatu, fuskar
da zata da
ɗ
e tana yin abun da ba mai iya
ɗ
ora zarginsa akanta."
Hajiya Salamatu ta kalle ta tsawon wasu sakanni tana nazarin maganganunta kafin ta girgiza kanta tace.
"Kin san nice mai gano miki da matsalar dake ba kya taba hangenta Kilishi, jiya da suka
kawo yarinyar nan banga fuskarta ba, amma daga yanayin jikinta kawai na san ƙarama ce, kuma idan har halinta ne zai sa jama'ar gidan nan su sota, ba