Showing 21001 words to 24000 words out of 94381 words
kansa yana kallonsa.
"Wallahi ban ga yarinyar ba Ishaq, kawai dai na bata wani saƙo ne da na san dole ba zat
a taba yarda ba."
****
11:30Am.
"Na yarda!"
Kalaman guda biyu suka fito daga bakin Amina lokacin da take tsugunne a gaban iyayenta guda biyu da dukkan fuskokinsu ke haskawa da tsananin mamaki.
Tata fuskar fayau take, ba abinda zaka iya tsinta a jiki.
Ta gyara zamanta sannan ta sake maimaitawa kamar wani ya sata.
"Na yarda zan aure shi Baba."
Maimaitawar ta fiyo tare da fa
ɗ
owar flask
ɗ
in ruwan zafin da Amma ta
ɗ
auko don juyewa Baba ruwan wanka, ya subuce a hannunta ya fa
ɗ
i har ƙasa, kwalbar ciki ta t
arwatse yayin da ruwan zafin ya fallatsa akan dukkaninsu.
*
Me kuke tunani yasa Amina ta yarda da auren Ma'aruf?
Wacece ainihin Hajiya Kilishi?
Me ya faru da Jamaal?
Shekarun cikin labarin sun wuce da wasu abubuwa da zamu fara kwance su daga Babi na g
aba insha Allah...
☺
️
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA BIYAR.
~~~~~
Ana gobe sallah ne ranar, ita da Maryam sun je kasuwa siyayar mayafai da takalmi, tun kusan sha biyu suka fita har mutane suka fara alwalar sallar la'asar basu gama
siyayyar ba.
Maryam dake riƙe da ledar kayan da suka siyo kalli tsinken kwakwar da suka auno tsawon kafar Hafsa dashi tace.
"Ai wallahi dama na san takalmin yarinyar nan shi zai bamu wuya, kafa kamar ba ta mutane ba ƴar firit da ita."
Amina ta share gum
i a gefen fuskarta tace.
Har tunani nake ko ba daidai na auno ba wallahi gashi mun kusa gama siyen komai..."
Bata karasa ba ta tuno da sakon garin da Amma tace su siyo zata yi teba dashi da daddare.
"Kin san na manta da garin Amma... zo muje wancan layi
n na san zamu samu."
Maryam ta girgiza kanta.
"Mu raba tafiyar kawai lokaci ƙara wucewa yake, ga wani kantin takalma can, bari naje na duba idan ma ban samu ba zan jira ki sai kizo ki same ni anan."
Da haka suka raba tafiyar, Maryam ta tsallaka ta cikin
cunkoson mutanen ta nufi kantin ita kuma tabi layin gefensu inda nan
ɗ
in ma turuwar mutanen ce wadda dama sun riga sun shirya mata, don tun ana saura sati
ɗ
aya sallar suka so zuwa kasuwar amma rashin ha
ɗ
uwar kudin yasa dole sai yau suka samu suka fito.
G
a rana, ga azumi amma yadda mutane suka hargitse baza kace kowa a gajiye yake ba. Da kyar ta samu ta
ɓ
ulla layin da masu garin suke, kuma akan ragin naira hamsin
ɗ
in da zasu yi ku
ɗ
in mota dashi, sai da ta kusan shanye layin tana tambaya da ƙyar ta samu wan
i acan ƙarshe yace zai rage mata.
Tana tsaye yana ƙoƙarin auna mata, wani yaron shagon nasa ya shigo, irin samarin nan ne masu magana, yana shigowa ya haye kan
ɗ
aya daga kantocin shagon yana fadin.
"Allah na tuba a yadda ake wannan ranar ga azumi ai wall
ahi komai talauci na ba zanyi aikin sauke gari ba, don mugunta kaga yadda suke jefo musu buhun nan daga sama, wani har sai ya kai ƙasa wallahi kafin ya
ɗ
ago."
Maganar ta
ɗ
auki hankalinta, tana hango yadda nauyin buhun gari yake ace mutum ya dauka a wannan
ranar.
"Yau ma mota ta sauka ne?"
Mai shagon ya tambaya yana miko mata ledar garin.
"Gata can yanzu ta tsaya, ka san shi Auwalu ko da goma yaga sunyi ƙasa sai yayi aike."
Ta miƙa masa ku
ɗ
in tana fa
ɗ
in ta gode, amma kafin ya karba saurayin yayi saurin
miƙo hannu ya karba sannan ya miƙo mata yana mata murmushi, irin halin ƴan kasuwa.
A kofar shagon kuwa tana fita taga motar ana ta sauke garin, tausayin masu yin dakon ya tafi har cikin ranta ganin yadda ko a ido buhun ke da nauyi, tana tafe tana ganin fu
skokinsu lokacin da idonta ya kai kan fuskar da ta sa ba shiri hannunta ya saki ledar garin nan... Mahaifinta ta gani dauke da wani katon buhu yana ƙoƙarin kaiwa inda sauran ke saukewa, mahaifinta dai Baba, Baban daya shirya tsaf a yau ya fita suna yi masa
a dawo lafiya.
A wannan lokacin yana ga
ɓ
ar farfa
ɗ
o wa daga karayar arzikinsa ne, don duk da kokarinsa wajen yi musu kayan sallah, har saida aka ha
ɗ
a da ku
ɗ
in Aminu kafin komai ya isa, bata san lokacin da hawaye ya fara biyo kuncinta ba, taga ya sauke ya
koma sake
ɗ
auko wani... Baba mutum ne mai tsananin son dogaro da kansa kowa ya sani, yayyensa duka sunyi kokarinsu wajen tallafa musu tunda al'amarin ya faru, amma babu wanda ya isa ya
ɗ
auke maka cin yau da gobe sai Allah, don haka ta san nauyin ya cigaba
da tambayarsu ne yasa har ya kawo kansa yin wannan aikin don kula dasu.
Hawayen ya cigaba da bin fuskarta yayin da zuciyarta ke rawa a kirjinta, tunanin ta
ɗ
aya ne a lokacin, idan har mahaifinta zai iya sadaukar da girmansa yayi
wannan aikin don kawai ya
fita kunyarsu meye su baza suyi don fita tasa kunyar a duniya da kuma lahira ba?
Ta share hawayenta lokacin da wani mai wulbaro ke miko mata ledar garin da Allah yaso bata fashe ba. Kuma bata fadawa Maryam abinda ta gani ba, bata fadawa Amma ba, bata fada
wa kowa ba, don ta san hakan wani abu ne da Baban ba zai ta
ɓ
a so waninsu ya sani ba.
Kuma a wannan daren sai gashi ya dawo da ledar kaza har guda biyu ta miyar sallah, su Hafsa suka yi ta tsallen murna yana binsu da nasa murmushin shima.
Wajen karfe biyu
n dare bayan kowa ya kwanta, ta hango shi ta ƙofar
ɗ
akinsu a wajen ban
ɗ
aki yana miƙe bayansa, kukan da tayi a cikin filonta a wannan daren Allah ka
ɗ
ai ya san yawansa, abu
ɗ
aya kawai ta sani shine tayi wa kanta alƙawari a wannan ranar cewa ko abinda yafi ra
yuwarta ne zata sadaukar a duniya don farantawa mahaifinta.
*
"Wallahi gani nake yi kamar zaki ƙyalƙyale da dariya ki gaya min wasa kike yi."
Fatima ta fa
ɗ
a tana kallon Amina data idar da sallah a gabanta.
"Ke ma kin san ai ban ta
ɓ
a miki irin wannan w
asan ba, da gaske nake Fatee, don yanzu haka ma Baba ya tafi gidan Kawu Mallam ya fa
ɗ
a masa."
"Ya fada masa cewa kin yarda zaki auri wanda yake da matsalar ƙwaƙwalwa Amina...? inalillahi wa'inna ilaihir raji'un Amina kin san Allah ko da nake cewa ki rabu
da Abdallah ki samu wanda yafi shi ba irin haka nake nufi ba, ya za'ayi kiyi irin auren da ake bada labarin ire-iren sa a sigogi mara sa da
ɗ
i?"
Fatiman ta ƙarashe muryarta na karyewa. Amina ta cire hijabin sallar tana kallonta,
"Ban gane me kike nufi b
a?" Ta tambaya tana kallonta. Fatima ta girgiza kai kafin ta gyara zamanta.
"Amina duk wanda yaji batun auren wallahi shaidar da zaiyi miki daban, kowa cewa zaiyi auren ku
ɗ
i zaki yi, musamman ƴan unguwar nan da kin san daman ƙiris suke jira akanki."
Amin
a ta ha
ɗ
iye wani abu a maƙogwaronta, abinda Fatiman ta fa
ɗ
a gaskiya ne ta sani, kuma maganar iri
ɗ
aya ce da maganganun Amma na jiya, duka su biyun ƴancinta suke nemar mata, amma a wajenta darajar mahaifinta itace a gaba da ita kanta don haka ta riga ta gam
a yankewa kanta hukunci, ta gayawa zuciyarta cewa zata tsaya tare da mahaifinta koda zata mutu sau biyu idan ana yi.
"Fatee na tabbata ba fa ba wai matsala ce sosai ba, kawai sun fa
ɗ
a ne saboda kinga a aure ba'a
ɓ
oye komai, kuma ma Baba yace baza'a bari m
aganar ta fita ba, kema kin san ba zan iya
ɓ
oye miki bane."
Ta fa
ɗ
i hakan yayin da idanunta ke hango takardar data cusa cikin kayanta a jiya, babu wanda ya san da ita, babu wanda ta gayawa hatta Amma kuwa duk yadda kowanne abu mai hankali a cikin kanta ya
tsorata da maganar dake rubuce, amma ta sani cewar in har iyayenta suka ji hakan dole zai iya sake zama wani ƙalubale musamman ma a wajen Amma don haka ta yanke hukuncin
ɓ
oyewa tunda ba zata taba fatan abinda zai hadassa mahaifinta yaji kunya ta dalilinta
ba.
Kuma kafin Fatiman ta sake cewa wani abu suka tsinci sallamar Ummi daga tsakar gida, ƴar Kawu mallam wadda suke kusan sa'anni da Aminan.
"Ina amaryar take?" Muryarta ta fito da fara'a bayan ta gaisa da Amma da kuma Maryam wadanda suke kitchen, ta ka
raso ya
ɗ
age labulen
ɗ
akin tana kallon Amina bakinta a washe.
"Yarinyar nan da tsinannen wayo, sai dai muji kawai wai zaki yi aure?"
Sai dai Amina tayi wani guntun murmushi kafin tayi mata sannu da zuwa.
"Ni ba zan amsa ba wallahi, tunda sai da muka ga
meeting
ɗ
in su Kawu yayi tsawo sannan da kyar muka san me ake ciki, da ake
ɓ
oye mana naga wanda zai raka ki siyayyar kayan bikin ai."
A cikin maganar ta Amina ta tsinci wani abu, cewa da gaske Baba yake a
ɗ
azu daya shaida mata cewar kowa zai ji maganar au
ren ne ta fuskar alkhairi, babu wanda zai san me ake ciki, gashi kuwa ko iyalan Kawu Mallam
ɗ
in da ake taruwa a gidansa basu san komai ba, zurfin maganar ya tsaya a iyakar Baba da yayyensa ne sai kuma Amma, Fatima, Maryam da Aminu da suka sani a yau. Ance
zancen duniya baya
ɓ
uya, amma har cikin ranta tana fatan zancen ya tsaya a iya wadannan mutanen kawai.
"Ai ni ban yi zaton har
ɗ
an bokon naki ya gama makaranta ya shirya ba, shi yasa wallahi abun ya bamu mamaki sosai, har su Umma ma cewa suka yi koda wasa
Amma bata yi musu zancen a kurkusa ba."
Amina ta girgiza kanta.
"Ai ba shi bane Ummi, wani ne daban."
Sai da Ummin tayi shewa kafin tace.
"Gaskiya ne yarinyar nan, kice da karfinki kika taso, Fatima bani labari don na san zanfi ji a wajenki, wane ne s
abon kamun?"
Fatima tana take tace.
"Wallahi kin san al'amarin Allah ai, kawai komai a lokaci guda yazo."
"Eh, amma dai da maiƙon sa ko? Yadda komai ya taso a lokaci gudan ai na san a shirye yazo ko?"
Kawu malam mutum ne malami mai sauƙin sha'ani, amma
n sai Allah ya bashi matansu duka ukun masu azabar son ku
ɗ
i, kuma suka taso da ƴaƴansu ma gaba
ɗ
aya akan hakan, gashi mata sunfi yawa a ciki don haka a zaune yake cewa basa auren kowa sai mai abin hannunsa ire-iren ƴan kasuwa, gasu da surutu da kuma kau
ɗ
i,
hakan yasa duk kusancinsu dasu Amina basu fiye shiga cikinsu sosai ba don halayensu sun banbanta duk kuwa da cewa suna da mutukar kirki.
"Ai kuwa dai yana da ku
ɗ
i gidansu ma haka."
Fatima ta bawa Ummin amsa har a lokacin tana murmushin yaƙe.
"Kice dole
ne mu raƙashe a bikin nan, wallahi azo a saka mana rana ma nan kusa Momi tazo mu fara shirye-shirye, zaki yi anko?"
Amina taji wani abu ya tokare mata a maƙoshi, don ita har ta yanke hukunci bai ta
ɓ
a zuwa kanta cewar ma biki za'ayi ba, gani take kamar jan
a'iza kawai za'ayi akaita, kuma sai Allah ya taimake ta kiran Amma yazo a daidai lokacin don bata san amsar da zata bawa Ummin ba.
Amma ta kalle ta bayan ta isa kitchen din, fuskarta fayau tace.
"Kizo ki zuba muku abinci gashi nan an sauke."
Ta ha
ɗ
iye y
awu a hankali tana ƙarasawa ciki, lokacin da flask
ɗ
in ruwan zafin nan ya fa
ɗ
i daga hannun Amma, sai ya zama kar ya fashe da dukkan irin hukuncin da take tunanin Amman zata dauka akan ƙin bin maganarta da tayi, don a lokacin bata ce komai ba, juyawa tayi k
awai ta bar wajen yayin da Baba ke saka mata albarka, kuma bayan taje ta same ta a
ɗ
aki, abu daya kawai tace.
"Rayuwarki ce dama Amina, na nuna miki kuskuren dake ciki ne kamar yadda yake alhaki na a matsayin uwa, kuma tunda har kinga zaki iya dauka, ga f
ili ga maidoki nan, zuciyata ba zata riƙe ki da komai ba, Allah ya baki sa'a."
Daga haka bata ƙara cewa komai ba, kuma bata yi fushin da Amina tayi zato ba, harkokinta ta cigaba da yi a gidan kamar dama maganar bata taso ba, kamar dai shekaranjiya da Baba
bai ko ziyarci gidan Hajiya Kilishi ba, balle su san da komai.
Ta zuba abincin ta kai musu, suna ci Ummi na da
ɗ
a bada bayanin yadda abubuwa zasu kasance wanda daga ita har Fatiman yaƙe kawai suke suna amsa mata, wajen la'asar ta tafi, lokacin ma Fatima t
a da
ɗ
e da tafiya asibiti inda tace yau za'a sallamo kakarta.
Wajen ƙarfe biyar, Aminu ya shigo gidan riƙe da wani flask lokacin da take wanke-wanke ita ka
ɗ
ai a gidan, don Amma ma ta shirya ta tafi gidan wata ƴaruwarta a Goron dutse ta shaida mata al'amari
n.
"Ina yarinyar nan take?"
Ta san Maryam yake nema don haka tace.
"Ta tafi makaranta tun
ɗ
azu."
Sai ya ajiye flask
ɗ
in a ƙofar kitchen sannan ya ƙaraso ya tsugunna a kusa da ita, muryarsa
ɗ
auke da nutsuwar da zaka shafe rabin rayuwarka kafin kaji ta a
wajen Aminu yace.
"Hukuncin da kika yanke yayi daidai Amina, ba don Amma ba daidai ta fa
ɗ
a ba, sai don kare mutuncin Baba da kika yi, kuma na tabbata Allah zai duba hakan ya kyautata rayuwarki."
Kwalla ta taru a idonta lokaci guda, don haka ta gyada kai
kawai ba tare da tace komai ba. Wucewar wasu ƴan sakanni shima yana tsugunee kamar yana sake biya abinda ya fada a zuciyarsa, sai kuma yayi gyaran murya sannan ya koma Aminun da yake.
"Kin gayawa Malam ne?"
Ta san Abdallah yake nufi don dama haka yake k
iransa, saboda haka ya girgiza kanta tace.
"Na san dai zai zo anjima."
"Kice yau Malam zai dan
ɗ
ani baƙin cikin latecomer kenan."
Bata san lokacin da ta watso masa ruwan wanke-wanken ba tana jin wani abu a zuciyarta na fadawa, ya kauce shima yana dariya
sannan yayi hanyar fita yana fa
ɗ
in.
"Idan wannan ƙwalamammiyar ta dawo kice mata ga wainar masar da take ƙalata nan na samo mata."
Bayan ta gama wake-wanken ta koma
ɗ
akinsu har a lokacin ƴan islamiyar basu dawo ba balle kuma Amma, a ƙasan kayanta ta sake
ɗ
auko wannan takardar tana karantawa, idanta suka tsaya akan sunan yayin da a yanzu bayan tsoron ma'anar rubutu wani sabon tsoro daban ke shigarta.
Ma'aruf B.
Ta karanta sunan tana jin yadda tsoron harafan kadai ke zanuwa a zuciyarta, ba wai don ta sans
hi ta gane waye ba sai don zuciyarta bata cika manta fuskokin mutane ba koda kuwa sau
ɗ
aya ta taba arba dasu, kamar dai shi rana guda ta ta
ɓ
a ganinsa a rayuwarta kuma bata ƙara ba daga sannan.
Ranar
ɗ
aurin aurensa, ranar da Baba yasa suka tafi tunda sassa
fe ita da Amma don wai suyi yinin bikin da gaske kamar yadda aka rubuta, a lokacin da ya shigo gidan shi da abokansa da ƴanuwansa bayan
ɗ
aurin auren, ita da Amman suna raku
ɓ
e daga can jikin wata kujerar a falon Hajiya Kilishin, kuma duk da tarin ƴan bikin
mata da suka yanyame shi da tsokanar 'ango kasha ƙamshi...' sai da idanunta suka iya hango mata shi yasha farar shaddar dake ƙyalli kamar murmushinsa, yana tsaye daga tsakiyar mutane yayin da masu hoto ke ta yi musu kala-kala.
A wannan lokacin gani take k
amar bambancin su ita da Amma da mutanen gidan ya zarta na mutum-mutum, don bayan Hajiya Kilishin da ta amsa gaisuwar su cike da fara'a ta kuma sa aka kawo musu abinci babu wanda ya ƙara lura dasu a
gidan, sai wata mace guda
ɗ
aya da tace Amma ta ara mata h
ijabinta lokacin sallar azahar, itama da alama irinsu ce don ta
ɗ
ebo tarin ƴaƴan da ta cika musu faranti taf da abinci suna ta ci. Daga baya ma dole suka bar cikin falon suka zagaya baya can wajen
ɗ
akunan masu aiki, inda anan ne suka
ɗ
an sake har Amma ma t
aga wata ƴar ajinsu ta sakandire a ƴaƴan dattijan da sune manya-manyan masu aikin gidan.
Don haka kwatanta tsoron cewar a wannan karon ita zata maye gurbin wannan kyakkyawar amaryar da aka shigo da ita gidan wajen yamma abu ne da ta tabbata babu wanda zai
iya kwatanta shi a duniyar nan.
Tsaya ma tukunna... Ina matar tasa take??
*****
"Baffa ya gaya maka komai ko?"
Hajiya Kilishi ta tambaya tana kallon Ma'aruf
ɗ
in dake zaune a gabanta, a cikin falon
ɓ
angarenta suke su biyu sai Surayya dake can wajen din
ing tana danne-danne a wayarta, yana zaune a kujerar dake kallon Tv yana kokarin canja channel daga ta india zuwa wata channel da ya san a lokacin ana wani Tv show na likitoci mai suna 'Code Black'.
Sai da