Showing 39001 words to 42000 words out of 94381 words

Chapter 14 - Farar Wuta Complete

(wanda yayi aure) ya hawo saman daga shi sai gajeren wando da riga.

"Wai Maamah ki

dawo ƙasar nan baki gaya mana ba. Sai da na shigo wajen 12 maigadi yake ce min ai kin dawo."

Ya fa

ɗ

a yana ƙarasowa kusa da ita ya zauna, kuma sai a lokacin idonsa ya kai kan Rukayya dake kuka.

"Me ya faru?" Yayi tambayar ga dukkansu biyu.

Hajiya Nafisa

ta nisa sannan ta bashi amsa.

"Hamida ce ba'a gani ba, ita da mai kula da ita."

"What? Ta yaya? Tun yaushe?"

"Itama bata gidan ai, sai da na dawo tukunna."

Ransa a

ɓ

ace yace.

"Me nake gaya mata a gidan nan Maamah, don me zata dauko wata ƙedara wai it

a zata dinga kula da ƴarta, wai don ta iya turanci? Turancin banza su Hausawan ba su iya turancin bane?"

Hajiya Nafisa ta girgiza kanta.

"Ajiye wannan zancen Ahmad tunda komai ya faru, yanzu nemanta ne a gabanmu. Ya za'ayi?"

Kafin ya bada amsa, Ibrahim

ya shigo riƙe da wayarsa a hannu yana fa

ɗ

in.

"Is it true yarinyar nan ta

ɓ

ata? Umar just called me now wai ya ganki a waje

ɗ

azu kuna tambayar Hamida."

Hajiya Nafisa ta gya

ɗ

a kanta don ita yake kallo sanda ya shigo yana tambayar.

"Ƴansanda

ɗ

in dake gadi

a bakin titi muka tambaya suka ce mana tun shekaranjiya Maryn ta fita da Hamidan kuma basu dawo ba."

"Ya salam! This is bad, yanzu me ake ciki?"

Tambayar tasa Ruƙayya sake fashewa da kuka.

Ahmad yace.

"Akwai wani abokin Ashraf da ya ta

ɓ

a zuwa nan yace

min ya san ita mai aikin, ban

ɗ

auko wayata daga

ɗ

aki ba, Ibrahim kira shi."

Ya kalle shi.

"Wa zan kira?"

"Ashraf

ɗ

in zaka kira kace ya baka number B-man."

Wayar Hajiya Nafisa tayi kara a lokacin, ta kalli number dake kiran nata, mahaifinsu ne don loka

cin da Rukayyan ta dawo tace bata san inda Maryn take

ba shi ta kira ta gaya masa halin da ake ciki. Ta

ɗ

auki kiran ta kara a kunnenta, gaya mata yake yi cewa yasa an turo da ƴan sanda gidan zasu zo su nemi bayanai don su kamo Maryn.

Kuma bayan ta sauke w

ayar kallon Rukayyan ta cigaba da yi a lokacin Amir

ɗ

an autansu ya shigo rike da kofin shayinsa ya zauna a gefenta yana bata hakuri.

Gayawa zuciyarta take yi cewa ba zata sake kuskuren rasa ƴarta ba a karo na biyu, bata son Ma'ruf amma idan har yanzu shi

ne za

ɓ

in Ruƙayya, shi abinda zai daidaita rayuwarta, to zata hakura kawai ta kar

ɓ

i wannan ƙaddarar, zata dawo mata da Ma'aruf cikin rayuwarta ko ta wace hanya.

***

"Allah yayi miki albarka, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah yasa ki zama haske a cikin gid

an aurenki, Allah yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin duk wani hakkinki, Allah yasa ku zamewa junaku inuwar salama har a

ranar alƙiyama, Allah ya sanya albarka a zuri'ar da zaku samu, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi..."

Duk wannan addu'ar tana fitowa ne yayin da ruwa ke sauka akan Amina daga bakin wata dattijuwa ƴaruwar Amma

mai suna Gwaggo Balkisa da suka zo daga Nijar a lokacin da gidansu Amina ya cika da

ɗ

imbin jama'ar dake shaida Kamu ko kuma wankan amarya da a ƙa'idar zuri'arsu Amma ake yinshi kwanaki kafin

ɗ

aurin aure, al'amarin da yazo musu babu shiri don kwatsam suka s

amu baƙoncin ƴanuwan Amman tun daga Nijar mutane har motoci biyu.

"Bikin ƴarki ta fari guda kice ba sai mun zo ba Halima? Idan kince ku komai yazo muku cikin gaggawa an gaya miki mu yanzu muka fara tanadi ne? Har a aika da katinan

ɗ

aurin aure amma ace wai

iya maza ne kawai zasu taho? Yau ko Amina ba ƴarki ta sunna bace kina tunanin zamu ƙi halartar bikinta ko da kuwa tsakaninmu daku nisan bangon duniya ne?

Amina tana tuna yadda Amman ta sunkuyar da kanta tana saurare kafin tayi musu bayanin yadda al'amari

n auren yazo, kuma fahimtar al'amarin ya kawo cece-kuce a tsakaninsu, wa

ɗ

anda suke tsofaffi a ciki basu ga aibin komai ba don sun yarda cewa dama uba ke da ikon bada ƴarsa budurwa zamani ne kawai ya canja komai, amma sauran suma sai tunaninsu ya zama irin

na Amma cewar tasirin taimakon da Hajiya Kilishi ke yiwa Baba shi ya rufe idanunsa saboda auren bai kamata ba.

Sai da aka kira Aminan ta tabbatar musu cewa ita ta amsa auren da bakinta sannan kowannensu yayi shiru. Ta fa

ɗ

i hakan a lokacin da take kallon i

danun Amma dake

ɗ

auke da sauran labarin da bata ƙarasa musu ba, sauran labarin da ko ƴanuwan Baban basu sanshi ba, tana jin yadda zuciyarta ke bugu akai-akai cike da fatan kar nauyin kalaman su rinjayi zuciyar Amma a wannan lokacin, amma bata yi maganar b

a, bata ce komai ba.

Kuma hakan yana tuna mata da matsayinta na Ammar su, matar da tunda suka taso a rayuwarsu babu wata rana da zasu iya

ɗ

orar da sa

ɓ

anin cewa fa

ɗ

a ya shiga tsakaninta da mahaifinsu, kuma ba wai ba'ayi ba, ta tabbata ana yi ma fiye da tar

in wasu gidajen auren, kawai babu ƙofar da zasu gane ne. Ta tuna watarana da taji ta tana yiwa Aunty Safiyya nasiha bayan wani sa

ɓ

ani da ya shiga tsakaninta da mijinta.

"Sirrin mijinki sirrinki ne Safiya, idan kika bu

ɗ

e kamar kin tonawa kanki asiri ne, ko

wa kika budewa littafin da wannan karatun zaiyi ta kallonki koda kuwa kin

cigaba da zama ko kuma kin rabu dashi, mafitar matsaloli da yawa a hannunki suke, da wuya ake kaiwa ga

ɓ

ar da wani ne zai iya magance miki damuwarki..."

Zata lissafa Ammanta cikin m

anya-manyan jajirtattun mata a gidajensu, zata lissafa ta cikin irin mutanen da mata da yawa ya kamata su kalla suyi koyi dasu, don ita kanta babban makamin da take taƙama dashi na shirin tunakarar sabuwar rayuwar da zata yi, halayen Amman ne.

Sai dai duk

yadda ta kai ga dake zuciyarta, a wannan lokacin da Gwaggo Balkisa ke mata wannan addu'ar tana zuba ruwan

ɗ

umi daga saman kanta, kuka take sosai, kuka mai nauyi, kuka mara sauti, kuka da zata iya cewa ya zarce na amare da yawa, don nata kalolin taraddain

dake cikinsa basu da adadi, ba na barin gida ne kawai ba, bana shirin fuskantar wata sabuwar rayuwa bane, wataƙila idan tace na shirin mutuwa alhali tana numfashi ne, hakan zai iya fassara rabin abinda take ji.

Tana sanye da wani farin saƙi dasu Gwaggon s

uka taho dashi, anyi mata

ɗ

aurin ƙirji dashi kawai, yayin da gashinta mai laushi da yawa ke mannewa a fatar kanta da kuma wuyanta saboda ruwan dake bi ta cikinsa, tana zaune akan wani sabon turmi dasu Aunty Safiya suka siyo a cikin kayanta, yayin da sauran

jama'ar bikin ke tsaitsaye zagaye da, gidan ya cika danƙam don har ƴan unguwa sun shishigo.

Taga lokacin da Tanti ta shigo cikin masu zuba ruwan ta

ɗ

ebo nata itama tana kwara mata tare da nata addu'oin dake ƙara karya zuciyarta suna saka kukanta ƙaruwa.

A lokacin ne kuma fuskar Ma'aruf ta haska Idanunta, ranar da ta fara ganinsa, ranar da ta ta

ɓ

a ganinsa, yana dariya a tsakanin mutanen dake taya shi murnar aurensa, babu shiri wani kukan mai ƙarfi ya sake su

ɓ

ucewa a bakinta.

A haka sai da duk wani babba n

a danginsu da kuma dangin Baba suka zo suka yi sannan aka rufa mata wani farin saƙin, aka lullu

ɓ

eta dashi har ƙasa sannan kuma sauran ƴanuwan Amman da basu kai irinsu Gwaggo Balkisa ba suka shiga fesa mata turare ana gu

ɗ

a. Al'ada ce sabuwa ga duk wanda ya

halarci wajen, irin dangin Baba da kuma sauran ƴan unguwa don haka abin ya birge kuma ya ƙayatar ga duk wanda ya gani, kuma duk da cewar ba wani abinci aka raba ba, amma kowa ya tafi yana yaba abinda akayi.

"Na gaya miki su Nusaiba duk cewa suka yi baza s

u zo ba wai tunda ba ke kika fada musu ba, ba'a gaiyace su ba kenan."

Fatima ta fa

ɗ

a da daddare bayan an gama komai mutanen duk sun tafi, wadanda suka rage iya na cikin gidan ne kawai.

"To ba shikenan ba, su sha zamansu. Dasu da masu karyatawa suna cewa

karyane duk su ƙarata can, ranar da suka zo nemanki akace musu kina gidanki sai su san cewar da gaske ne."

Ummi ta fa

ɗ

a tana kallon Aminar wadda a yanzu ta canja zuwa wata doguwar riga daga cikin

ɗ

inkin kayan sallarta, har yanzu bata fara amfani da kayan

lefen nan ba duk kuwa da an karbo daga dinki, gani take kawai kamar basu gama tabbata nata ba har yanzu.

Dukkaninsu suna zaune ne a cikin dakinsu tare da ƙawayen su Ummin da kuma ƙawayen Amina da basu fi biyar ba, don kamar yadda Ummin ta fa

ɗ

a ne da yawan

su da Fatima ta gaya musu cewa suka yi ƙarya ne basu yarda ba.

Amina bata ce komai ba saurarensu kawai take yayin da take riƙe da ƙaramar ƴar Aunty Safiyya da tayi bacci a cinyarta, daga tsakar gida hayaniya ce kawai ke tashi cikin hausa da kuma zabarmanc

i daga ƴanuwan Amma, ƴaƴan Baban kurn dana Kawu Malam da kuma yayyensu Ummi duk suna nan, tabarmarsu daban ana ta hirar yaushe gamo, don ma ƴaƴan su Kawu Ibrahim dana Kawu Hamza basu ƙaraso daga Abuja bane, wanda su dama ba sa'anninsu bane, su hudu ne

duk

sunyi aure a can Abujan

ɗ

aya ce kawai a Kaduna, don haka ko zasu zo tabbas sai ana i gobe

ɗ

aurin auren ne tare da iyayensu, Kawu Hamza ne kawai yake da ƴa sa'ar su Aminar amma tana Ghana ta samu scholarship tana karatu.

Amina ta sani cewar ƴanuwan mahaifi

nta suna da arziƙin da tun lokacin da ta gama karatu zasu iya daukar nauyin cigabanta, amma basu yi

ɗ

in ba, don duk yadda zumuncinsu yake da karfi akwai raunin taimako a tsakaninsu, kowa yafi maida hankali kan iyalansa kawai, kuma Baba mutum ne mai son dog

aro da kansa a komai shi yasa shima bai cika tambayarsu abu ba idan har ba wanda hannunsu ya miƙo masa ba.

Ta lumshe idanunta tana sauraren hirar dasu Fatima ke yi a gefenta, Baba bai ƙara yi mata maganar auren ba har yau tun daga ranar da ta shaida masa

amincewarta, amma a kodayaushe ta kalli fuskarsa sai taji ƙarfin gwiwarta na ƙaruwa, taji zata iya yin abinda yafi wannan ma idan har zai umarce ta. A hankali maganganun da ta gayawa Fatima ranar da tazo mata da labarin Ma'aruf suka shiga dawowa kunnenta.

"Fatima, Baba yasha wahala akanmu a rayuwarsa, yaga tashin hankalin da ba zan iya lissafa miki ba duk saboda mu. Lokacin da nake shekara hudu, Amma tayi fama da wata irin rashin lafiya bayan haihuwar Aminu, Baba shi yayi

ɗ

awainiyar konai damu har tsawon

shekara guda kafin ta warware. Lokacin da ina aji

ɗ

aya a sakandire nayi wata rashin lafiyar ciwon ƙafafu har bana iya tafiya, wani abokinsa ya kwantanta masa wajen wani mai magani a garin Benue, ni dashi kawai muka tafi, daren farko a hanya mota ta lalace

mana gashi motocin dake wucewa basa tsayawa saboda gudun ƴan fashi, a bayansa ya goya ni Fatima, muka dinga bi ta daji tare da sauran mutanen motar har washegari kafin Allah ya taimaka mu isa wani ƙauye.

Lokacin da zanyi jarabawar shiga sakandire, Baba ya

sadaukar da lokacinsa da komai wajen koya min karatu ba dare ba rana, idan ya dawo daga kasuwa yana gyangyadi yana hamma zamu yi karatun nan, ranar da sakamakon jarabawar ya fito kuma naci, ranar na fara ganin hawaye a idanun Baffa, hawayen farin ciki.

S

anda Maryam bata da lafiya kuma karayar arziƙi ta same shi, kin sani Fatima, kin san yadda Baba ya koma kamar mai roƙo yana bi kusufa-kusafa don tara adadin kudin da ake buƙata. Kullum so yake mu girma, mu zama wasu mutane da al'umma zasu amfana suyi alfah

ari dasu, don haka ba lallai ne mu hango fa'idar wannan hukuncin nasa a yanzu ba, amma na tabbatar miki Baba ba zai yarda da zancen auren ne haka kawai ba, yace ya amsa musu ne saboda nauyin idanunsu da yaji, amma ni na sani cewar akwai wani abu daban da y

asa ya amsa wanda ba lallai ne dukkanmu mu fahimce shi yanzu ba.

Kema na yarda da maganarki kamar yadda na yarda da ta Amma, sai dai bana jin zuciyata zata dauki taku sama da tasa, don ban san wane irin butulci zanyi ba idan har na kunyata mahaifina a ido

n duniya, gwara ko meye ya same ni da inyi sanadin hakan."

Kuma tun daga lokacin, shikenan ta kashe bakin Fatiman, bata kara cewa komai ba, bata ƙara ƙalubalantar ta da komai ba, ta fauwalawa ubangiji al'amarin kamar yadda itama tayi, har ta saki jikinta

cikin su Ummi itama ta siya atamfar nan ta kai

ɗ

inki.

"Gobe zanje in karbo

ɗ

inkina, kuma zamu je ni da Maryam wajen masu sarƙar nan mu ƙara yi musu tuni."

Fatiman ta fa

ɗ

a tana katse tunaninta. Sai ta gyada kai kawai sannan tace.

"Ɗazu Maryam take gaya m

in, wai ta samo me zuwa ta mana ƙunshi ma."

"Ƙunshi a ina? Me zuwa gidan ce zata miki? Ai kar ma ku fara wannan zancen, ku

ɗ

i zaki kar

ɓ

o zoo road zamu tafi jibi-jibin nan, idan aka gyara miki gashin nan naki da hannayenki, ba wanda za'a sake yiwa bayanin c

ewa ke amarya ce."

Ummi ta fa

ɗ

a, kuma tana ƙarashewa wata ƙawarsu ma ta

ɗ

auka da fa

ɗ

in.

"Ni wallahi naga ta kara haske ma akan ranar da muka zo daga kasuwa."

"To kina raba amare da gyare-gyaren jiki ne? Kawai ki tambaye ta sirrin tunda kema kin kusa fa

ra naki."

Momi ta fa

ɗ

a suna ƙyalƙyalewa da dariya, Amina kuwa ta ha

ɗ

iye yawu, don ita bata san wani abu gyaran jiki ba, vasiline

ɗ

in da take shafawa kullum shine dai, robar ko ƙarewa bata yi ba balle ta canja ko kuma ta waiwayi mayukan cikin lefen nan, ab

inda ta sani kawai shine idan har da gaske tayi fari to kuwa tabbas na tsora ne.

Don Allah ya sani idanunsa ka

ɗ

ai idan ta tuno zuciyarta na bugawa da sautin dake barazanar saka ta kuka duk da ƙwarin gwiwar da take ji, tsoron daban ne don bata san me shi d

a kuma zuciyarsa suka tanadar mata ba... Ta rufe nata idanun a hankali tana jiyo hayaniyar su Aunty da Aminu daga waje akan motar da zata fara

ɗ

aukan kaya, don gobe Tanti tace ya kamata a fara jere.

Tsoro take ji da gaske,

Tana ji kamar tana fa

ɗ

owa ne da

ga wata sama mai nisa, kamar tana tafiya cikin idanun nasa inda ruwan cikinsu zai nutsar da ita da kuma numfashinta.

Abinda bata sani ba shine har yanzu a ga

ɓ

a take, bata shiga koina ba ma balle ta fara nutsewar!

***

Wasa farin girki!

#Aysha Shafi'ee.

#FikraWriters

#FararWuta.

Bari nayi sauri na wuce, a yafe min.

🙏🙏🙏

BABI NA TAKWAS.

~~~~~

Ɗ

imbin jama'ar dake yin tururuwa suna ƙara cika kowanne

ɓ

angare na cikin masallacin su suka shaida auren mutum takwas

ɗ

in da aka

ɗ

aura kowanne kan sadaki m

abanbanci, motoci kawai kake gani daga koina an ajiye su yayin da wasu ke ƙara shigowa suna da

ɗ

a adadinsu. Jama'a kuwa babu wanda ya san adadinsu sai ubangijin daya tara su gurin, dattijai da samari har ma da yara masu tasowa, gasu nan kala-kala kowanne an

go da ƙungiyarsa da sai faman gaisawa ake ana

ɗ

aukar hoto.

Daga can gefe, Kawu Ibrahim ya ƙaraso inda tasu tawagar ƴanuwan take, ya tsaya a kusa da Kawu Hamza yana girgiza kansa.

"Ka san yaron nan har yanzu bai iso ba."

"Ai ba zuwa zaiyi ba, gwara mu ma

mu hanzarta mu bar wajen nan don ni jirgi na na ƙarfe uku ne ma, kuma akwai abubuwan da zanyi kafin nan."

Kawu Ibrahim ya juya ya hango su Kawu Mallam dake tsakiyar mutanen yana gaisawa da sauran ƴanuwansu fuskarsa cike da irin kalar tasa murnan, sai kaw

ai ya juyo da kansa yace.

"Har yanzu na kasa gano dabararsu akan auren nan, babu wani abu dake nuna min cewa ba don saboda kudin mutanen nan komai ya faru ba."

"Koma meye dalilin nasu, a yanzu komai ya riga ya faru, kuma duk matsalar data faru daga yanzu

kuma na tabbata shi

ɗ

in yana da hannun

ɗ

aukarta."

Kawu Ibrahim ya girgiza kansa.

"Muyi fatan alkhairi kawai, don har cikin zuciyata ina tausayin yarinyar nan, Amina tana da hankali wallahi."

"Hankalin da bai kamata ace an ƙuntata rayuwarta tun daga yan

zu ba. Ai wallahi da nine da ikon Kawu mallam, auren nan ba zai ta

ɓ

a faruwa ba."

Kafin Hamzan ya sake magana wayarsa tayi kara don haka ya dauka yayi gefe yana ƙoƙarin amsawa. Kuma sai a lokacin idanun Ibrahim suka iya hango masa Baba (mahaifin Amina) yan

a daga tsakiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login