Showing 66001 words to 69000 words out of 94381 words
gaskiya ba.
Komai zuwa yake sa
ɓ
anin tunaninta, ita har yanzu bata ga wata alama ta ciwon nan nasa da ta riga ta gama tsorota dashi ba, shi yasa zuciyarta ke ta tantama ma aka
n idan shi ya rubuto mata wannan saƙon, har Fatima ta gayawa cewa in dai ba warkewa yayi ba, to ba koyaushe ciwon ke tashi ba. Shi yasa tare suka yarda da tsarinta na kyautata zamansu, da tunanin idan ya san bata da niyyar cutar dashi, ba lallai yayi mata
wani abun ba duk lokacin da ciwon nasa ya tashi.
Sai dai ita bata tsara da yadda zuciyarta ke jin dadi tun lokacin da ya fara cin abincin nata ba, jiya duk da rikicewar mafarkin nan da take ciki sai da zuciyarta ta fa
ɗ
a ganin kwanukan abincinta a gefensa.
.. Tunanin hakan ya tuna mata da yadda ya riƙe hannunta a lokacin, har yanzu tana jin kamar shatin yatsun sa akan fatar ta, tana jin kamar akwai wani abu dake ƙonewa a jikinta saboda tasirin yadda yatsun nasa suka zagaye duka hannun nata gaba
ɗ
aya.
Da wann
an tunanin ta kammala ha
ɗ
a abincin breakfast
ɗ
in lokacin da ta tsinci bugun ƙofar nan. Kayan jikinta riga da skirt ne na wata atamfa ash da tun ganinta da ita da farko tayi mata kyau wa ido, kuma sai akayi sa'a mai dinkin ya zabi wani
ɗ
inki mai kyau da ya
dace da ita don haka suka karbeta sosai, kuma yau bata saka mayafin data saba ba sai ta yiwa
ɗ
ankwalin V kawai ta yafa shi a haka.
Ta bu
ɗ
e ƙofar lokacin da hoton wata budurwa ya shiga idonta, doguwa ce, fara, kamaninta na yare ne amma kuma kyakkyawa ce, t
a bazo gashin data
ɗ
ora a saman kanta mai kyau sannan matsatstsiyar rigar data saka ma mai kyau ce, don ta fito da kowanne lungu da saƙo na jikinta yayin da hannunta ke rike da wata ƙatuwar jaka irin ta aiki.
"Good Morning my name is Martha, I'm..." ( Bar
ka da safiya, sunana Martha, nice...)
"She's my sectary." (Sakatariyata ce.)
A lokaci guda muryar Ma'aruf ta fa
ɗ
a daga bayanta, kuma ba tare da jiran komai ba taji hanayensa masu dumi dun sauka a bayanta, daidai wajen da zip din rigarta ya fara, sannan ƙ
amshin turarensa ya cika hancinta. Bata san lokacin da ta juyo da kanta ta kalle shi ba, idanunta na nuna mamakin da dukkan wani abu
mai hankali a jikinta ke yi na yadda ya tsaya kusa da ita amma shi ba ita yake kallo ba, wadda ta kira kanta da Martha din
yake kallo da wani dan guntun murmushi a le
ɓɓ
ensa.
Kuma bata sake shiryawa ba sanda taji ya jawo ta baya ka
ɗ
an yana ha
ɗ
a ta da jikinsa, kanta ya tsaya daidai kafa
ɗ
unsa.
"You're welcome Martha, meet my wife Amina Sulaiman."
Sai da numfashin Amina ya kats
e a ƙirjinta jin yadda ya ambaci cikakken sunanta amma hakan baiyi nisa ba saboda Martha da ta miƙo mata hannu tana jiran su gaisa, sai tayi saurin mika mata nata itama tana murmushin da bata san a yaya ya fito ba.
"You came with everything right?" (Kinzo
da komai ko?)
Taji muryarsa daga saman kanta tana sake tambayar Martha
ɗ
in wadda ta
ɗ
aga kai.
"Yes sir, everything is intact, I just need to explain some things to you about Document A." (Eh yalla
ɓ
ai, komai ya cika bayanin wasu abubuwan kawai zan yi mak
a.)
Har yanzu da murmushi a fuskarta ta amsa, kuma sai kawai yasa hannunsa ya sake matso da Amina gefensa, suka bawa Marthan hanyar shiga ciki, ta wuce su kuwa tana ƙoƙarin fito da takardu da kuma labtop daga jakar hannunta.
"Kin tashi lafiya?"
Muryarsa
ta tambaye ta tun kafin ta dawo da hankalinta kansa, sai tayi baya da ƙafafunta da sauri wanda hakan yasa ya saki hannun nata, kuma maimakon ta amsa sai tace.
"Barka da safiya."
Ya shafo gashinsa ta baya.
"Barkanmu dai, hope kin dawo daidai?"
Ta san
me yake nufi don haka ta
ɗ
aga kanta sau biyu idanunta akan yatsunta, ya cigaba da cewa.
"Wannan sakatariyata ce sunanta Martha zamu yi meeting anjima ne and I left my things a office shine tazo ta kawo min."
Bata san me yasa yake mata bayanin mutanen da
ke rayuwarsa ba, Farko da Faruk ya fara, sannan wani Ishaq da har yanzu bata gabshi ba bands yawan wayar da take jin suna yi, sai kawai ta
ɗ
aga kanta a hankali alamun ta fahimta.
"Zamu
ɗ
an yi briefing a ciki, ba zaki damu ba?"
Da sauri ta sake girgiza ka
nta, a wane dalilin zata damu, gidanta ne? ya gyada kansa shima sannan ya juya ya shiga ciki, hannayensa duka biyu sanye a cikin aljihunsa duka biyu, don rigar shaddar dake jikinsa bata kai gwiwa ba, kayan kamar ma sababbi ne, light brown, suna ta kyalli a
cikin hasken safiyar.
Wajen da ya dora hannunsa a bayanta ya sake
ɗ
auka da irin abinda take ji a hannunta, sai kawai ta shaƙi wani numfashi mai nauyi a ƙirjinta sannan ta rufe ƙofar falon a hankali.
***
"Me? Me kika ce Amina? Ya kawo wata arniya cikin
gidan da sassafen nan?"
Muryar Fatima ta fa
ɗ
a cikin wayar dake kare a kunnen Amina, a hankali ta rufe idanunta sannan ta kai kofin shayin dake hannunta baki ta kur
ɓ
a.
"Ba yadda kike tunanin bane Fatee, yace min sakatariyarsa ce, kuma zancen aiki ma suke
tayi wai meeting suke dashi anjima."
"Duk da haka ni dai banga wannan ya dace ba, ko ba komai gidan aurenki ne ya kamata a mutunta ki a cikinsa ko ba komai."
Saura ka
ɗ
an murmushin da take yi ya su
ɓ
uce a cikin wayar saboda yadda Fatiman ke yawan fadar 'Gi
dan aurenta' ita kanta da take ciki bata ganin hakan kamar gaske tunda har yanzu babu wanda ya san abinda gobe zata haifar.
"Ni sai naji muryarki ma kamar akwai wata damuwar daban bayan wannan, me ya same ki?"
Fatiman ta sake tambaya, sai tayi ajiyar zuc
iya kawai, Fatima ta santa ciki da bai kwatankwacin yadda Amma ta santa, don sau da yawa ma abubuwan da zata iya
ɓ
oyewa Amma da Fatiman zata yi shawara su haƙa su binne, ko Maryam da take ƴaruwarta ba komai nata ta sani kamar yadda Fatin ta sani ba, Don ha
ka a yanzu ma dalilin kiran da tayi mata kenan, sai gashi ta gane tun kafin ta kai ga gaya mata.
"Wani mafarki nayi da ya tashi hankalina jiya, ban taba irinsa ba Fatee, wallahi na tsorata sosai don har na farka ina jin kamar gaske ne."
"Ya salam! Allah
ya kyauta, kinyi addu'a dai ko?"
Tambayar ta dawo mata da muryarsa sanda ya tambaya jiya 'Kinyi addu'a?'
"Nayi, har asuba ma ina ta nafila, amma da na sake tunowa hankalina yake kara tashi, gashi na kasa fahimtar komai a cikinsa."
"Babu abinda yake nufi
insha Allah, ki cigaba da addu'a kawai kina kokarin yin taka-tsan tsan da komai insha Allah ba abinda zai faru Amina. Zanje wajen Malam mai almajirai anjima insha Allah in saka ayi miki rubutu, wataƙila wani satin zamu zo da Maryam sai in taho miki dashi.
"
"Ba watakila ba, ku zo dan Allah Fatee..."
"Kin san Amma ce tace sai an kwana biyu tukunna." Ta katse ta, sai ta girgiza kanta kamar tana kallonta.
"Wallahi ko kullum zaku zo na gaya miki mutanen nan basu da matsala Fatee, yanzu kwana biyu ma kusan ku
llum ni kadai nake yini saboda duk sun koma makaranta, babu mai shigo min."
Fatima ta girgiza kanta itama.
"A abinda muka sani yanzun kenan Amina, gwara mu jira mu ga abinda lokaci zai haifar kafin komai ya daidaita, kar a sake
ɓ
allo wani abu daban."
Ta
ha
ɗ
iye wani abu a makogwaronta kafin ta amsa.
"Toh shikenan. Ki gaishe min dasu Mamah da Ahmad idan yazo."
Sai Fatiman tayi dariya tace.
"Na gaya masa waccar gaisuwar taki ma sai cewa yayi wai kina matar auren yanzu kike cewa a gaishe shi? Wai in gaya
miki kiyi azumi guda uku."
Suka yi dariya a tare kuma da haka suka yi sallama fuskar Amina
ɗ
auke da murmushin dake cike fal da kewar gida kamar kodayaushe. Ta ajiye wayar a gefenta tana kallon lokacin daya nuna akan
ɗ
an screen
ɗ
inta kafin hasken ya
ɗ
auke.
***
"Eh, yanzu zan fito... I will be there in 10 minutes insha Allah. "
Ma'aruf ya fa
ɗ
a cikin wayar da yake yi a lokacin da ya fito daga
ɗ
akinsa.
"Idan kana yiwa Allah Faruq kar ka tsaya a wani wajen, Let's not make them wait." (Kar mu barsu su jira.)
Abinda aka fa
ɗ
a a cikin wayar yasa shi kallon lokacin a agogon hannunsa kafin ya kashe wayar, a yanzu ya shirya cikin wasu kayan daban ba na safe ba, ƙarfe uku daidai, Martha ta da
ɗ
e da tafiya kuma shima bai da
ɗ
e da tashi daga kan system
ɗ
insa ba.
Don b
ayan tafiyar Marthan anan Amina ta same shi da kayan breakfast
ɗ
inta, ta durƙusa har ƙasa ta ajiye a gabansa, ya tuna yadda skirt din kayanta ya baje a
kan carpet
ɗ
in lokacin da ta durƙusa, a lokacin yaji yana don ganin yadda ƴan siraran ƙafafun nan nata s
uka lanƙwashe da durkusawar, kuma bata ce komai ba ta shiga zuba masa kawai, idonta a kasa, dogwayen gashin idon na sama ya ha
ɗ
e dana kasa kamar ta rufe su ne gaba
ɗ
aya amma kuma tana cigaba da abinda take yi.
Bai san me yasa duk abinda tayi yake jin kamar
wannan ne karon farko da yake fuskantar rayuwar aure ba, shekarar sa uku tare da Ruƙayya a matsayin matarsa, amma har yanzu ba'a zo wajen da yaga wani abu nata yayi kamanceceniya da irin rayuwar da yayi da Ruƙayya ba, gani yake kamar komai sabo yake faruw
a.
Yaso sunyi magana a lokacin nan, amma yawan aikin dake gabansa bai barshi ba, ya raina meeting din daga farko sai a yanzu da yaga yawan abinda za'a tattauna ya san cewa da gaske mutanen suke kuma idan har suka yi nasara ba karamin alkhairi zasu samu ta
re dasu ba, saboda haka dole ya ture komai gefe ya maida hankalinsa kan nazarin bayanan nasu, kuma watakila itama ta lura da hakan don tunda ta shiga
ɗ
aki bayan yaci abincin tazo ta kwashe kayan bata sake fitowa ba.
Jamilu yazo tun dazu yayi tabe-tabensa
a motar komai ya dawo dai, dama ya sani gyaran ba lallai ya zama mai yawa ba tunda motar bata cika bashi matsala ba tunda ya siye ta, don haka bayan ya gama saka links din ya nufi hanyar kofa rike da wayoyinsa kawai, ya riga ya kai duk abinda yake bukatar
tafiya dashi motar tun
ɗ
azu, din ya kusan haddace komai, zuciyarsa dama idanunsa kawai biyo dukkan abinda ya san zaiyi magana akai suke.
Ya
ɗ
ora hannunsa akan ƙofar falon har ya bu
ɗ
e lokacin da yaji muryarta.
"A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a."
Idanuns
a suka juyo da sauri zuwa inda take tsaye, daga hanyar koridon nan ne alamun daga daki ta fito, hannunta na hagu na riƙe da wani baƙin bokiti data ciko jikakkun kaya dasu, yabi hannun nata da kallo da kuma gaban rigarta daya jiƙe yana tabbatar masa wanki t
ayi,
ɗ
ankwalin da take yafe dashi tun safe ta
ɗ
aura shi a yanzu, yayi baya ma kamar zai zame gashinta na fitowa ta gaba, mai laushi ne da alama don duk ya tashi sama.
Bai san lokacin da wani guntun murmushi ya su
ɓ
uce a fuskarsa ba kafin ya
ɗ
aga mata kai.
"Ameen ya Allah, nagode sosai."
Kuma ga mamakinsa sai itama tayi nata guntun murmushin sannan muryarta ta ƙara fitowa.
"Insha Allah meeting
ɗ
in zai tafi daidai."
Tana fa
ɗ
in haka ta shige hanyar Kitchen
ɗ
in dake gefenta bokitin na bin bayanta.
***
Dab
da magariba ne lokacin, Aminu ya kammala komai na aikinsa na ranar a garejinsu, kuma har yayi sallama da kowa ya fito bakin titi lokacin da wayarsa tayi kara, yana tsaye da gefen titin ya dauko ta ya duba, Baba ne, don haka ya dauka da sauri ya kara a kun
nensa yana gaishe shi.
"Lafiya kalau Aminu, kun tashi ne?"
"Eh Baba, yanzu ma na fito zan taho gida."
"To ka biyo ta nan, akwai kayan da zaka dauka sai mu tafi tare."
"Insha Allah Baba gani nan."
Da haka ya kashe wayar, ya sauke ta
ɗ
aga kunnensa daida
i lokacin da mai mashin
ɗ
in ya taho da wani irin saurin da ba Aminun ka
ɗ
ai ba hatta mutanen dake baya dashi basu ga wucewarsa ba sai dai ƙarar injin mashin
ɗ
in da kuma sanda yabi ta kan Aminun dake tsaye a bakin titin ya take shi tun daga kan ƙafafuwan sa.
Salatin mutane har da ihun wasu ya gauraye iska a lokacin da mai mashin
ɗ
in ya murde kan mashin
ɗ
in ya miƙe titi ba tare da ta tsaya ba, kansa na dauke da hular kwano baka don haka babu wanda ya iya ganin fuskar sa.
Wasu daga cikin mutanen suka bishi da
jifa amma babu wanda ya same shi, gudu kawai yake yi har lokacin da ya fita daga unguwar baki
ɗ
aya, ta lunguna ya dinga gujewa danja ba tare da ya tsaya a koina ba har ya zuwa unguwar Sardauna Cresent ƙofar gate
ɗ
in gidan da ya fito, inda tun kafin ya kar
asa mai gadin dake zaune a waje yana jira yayi saurin bu
ɗ
e masa gate
ɗ
in ya shige.
A gaban wata ƙatuwar bishiya dake harabar gidan ya tsayar da mashin
ɗ
in sannan ta cire hular kwanon dake kansa, daidai lokacin da wayarsa ta shiga fitar da karar vibration
daga aljihunsa. Ya
ɗ
ago ta ya danna wajen amsawar ba tare da ya damu ya duba sunan mai kiran ba.
"Awa ta biyu a waje kafin yaron ya fito." Ya fa
ɗ
a yana ƙoƙarin balle ma
ɓ
allin rigarsa na gaba.
Daga
ɗ
aya
ɓ
angaren wayar, Hajiya Kilishi tayi murmushinta mai
armashi kafin tace.
"Kace min an gama kawai Awwalu."
"An gama Hajiya, kema kin san komai daidai yake tafiya."
Ta gya
ɗ
a kanta a hankali, tabbas haka ne, komai daidai yake tafiya, me yasa ma zata damu da tambaya? Awwalu ya ta
ɓ
a kasawa umarninta ne?ko kuw
a ta manta sanda yayi babban aikin da yafi wannan a wajen hatsari ne ma? Aikin da shine ginshiƙi samun ƴancin da take kirgawa dashi a kowacce nasarar da take samu.
Bakinta ya sake tafiya da wani murmushin, abinda ya faru yanzu tsaraba ce ga Amina, don ba'
a banza zata bu
ɗ
e mata fuskarta ba, ba'a banza zata san wace ce ainihin Kilishi ba, dole ne ta tunkare ta da kakkarfar hujjar da kokwanton ikonta ba zai ta
ɓ
a samun waje a zuciyarta ba.... Aminu shine farko a yanzu, kuma idan komai ya tafi daidai zai zama n
a karshe, amma da an samu wani akasi ƙofar ta bu
ɗ
e kenan, duk wanda ya ji
ɓ
anci Amina ya shigo cikin lissafinta.
Zata
ɗ
aure Amina ne da jijiyoyin jikinta, bata isa ta tsallakewa dukkan sharrinta ba a yanzu, ta riga ta shigo cikin jerin mutanen da take juya
wa da yatsan hannunta.
"Ya batun Ma'aruf
ɗ
in Hajiya? Na gaya miki yayi nisa a binciken da yake yi, idan har ya riga mu nemo inda Mr. Okafor yake wallahi abubuwa zasu canja daga kalar da muka san su, ya kamata ki tsayar dashi har sai mun riga shi nemo mutu
min nan mun tura shi lahira tukunna."
Muryar Awwalun ta katse ta daga tunaninta, kuma a lokaci guda sai murmushin dake kan fuskarta ya
ɗ
auke, yanayin fuskarta ya koma wani iri da babu abinda zaka tsinta a ciki, ta ha
ɗ
iye wani abu a cikin maƙogwaronta tana
kallon tarin magungunan Ma'aruf
ɗ
in da ta baje daga kan gadonta, a hankali ta girgiza kanta sannan tace.
"Kar ka damu Awwalu, ina sane dashi so nake ya kammala da mutanen RTL
ɗ
in nan tukunna, idan sun gama daidaitawa kuma ku
ɗ
a
ɗ
en sun shigo zamu jefi tsun
tsu biyu da dutse
ɗ
aya ne, kafin ya dawo hayyacinsa munyi gaba da ku
ɗ
in kuma munyi gaba da shi Mr. Okafor
ɗ
in... Kamar koyaushe sai bayan ya tashi zai fara lalube cikin duhu!"
***
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
BABI NA SHA BIYU.
Life
is what happen to us when we are busy making other plans.
-Unknown.
**
Ranar lahadi ne da misalin ƙarfe hu
ɗ
u na yamma, Amina na tare da Samirah da kuma Munaya a kitchen suna aiki tare da hirarsu wanda mafi yawanci Samiran ce ke tsokanar Munaya akan zuwa
n da tayi, tunda tun farko Samiran ce ta fara zuwa kafin ita kuma ta shigo m daga baya.
"Wallahi sai ayi baƙi kashi-kashi su zo gidan nan su tafi baki ganta ta fito ba, amma kiga wai itace yanzu tazo taya aiki babu gaira ba dalili."
Cewar Samiran a lokac
in da take daka tafarnuwa ƴar kadan da zata saka a miyar dake kan wuta daga bayanta.
Munaya tana