Showing 81001 words to 84000 words out of 94381 words
mu a jigawa ne?
😉
Wace mafita Amina zata
samu game da Hajiya Kilishi kafin zagayowar sati guda?
A yau kun fara jin tarihin Hajiya Kilishi!
😰
Ku shiryawa abinda ke faruwa daga
É“
angaren Ruƙayya.
Har da Jawad ma.
😅
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
BABI NA SHA HUDU.
~~~~~~
I fa
ll in love with your kindness, because it adds peace to my wounded but striving soul.
- Unknown.
***
Ruƙayya na tsaye daga jikin windon, hannunta rike da kofin wani shayi dake tiriri, idanunta na manne akan shukokin harabar gidan nasu dake waje, kamar n
azarinsu take tana son gano wani abu a jikinsu, amma a zahiri kalaman aminiyar mahaifiyarta da ake kira da Hajiyar Sudan wadda ke magana a baya ne suka shiga kunnenta.
" ... Da mun tura wanda za'a samu ya kwance abin nan ke kin sani Nafi, yadda na ake da
tabbacin na kabari baya dawowa haka aiki na yake ci..."
Sai kawai ta juyo a hankali tana kallon Hajiyar Sudan
É—
in kafin kai tsaye ta katse ta.
"Ban gane ba, ta yaya zamu iya kai abin har cikin gidan?"
"Yanzu duk bayanin da muke yi baki ji komai ba? Tuna
nin me kike yi bayan wannan?"
Cewar Mahaifiyarta Hajiya Nafisa, amma ga Hajiyar Sudan
É—
in wani shu'umin murmushi tayi tana kallonta sannan tace.
"Ƙyale ta Nafi, yanzu zata fahimce ni tsaf."
Ta fada ba tare da ta
É—
auke idonta daga kan Rukayyan da itama k
e kallonta ba, kuma da hannunta na hagu ta yi mata inkiya da alamun ta ƙaraso ta zauna a gefenta.
Rukayya ta kalli wajen, ta sake kallon fuskarta... Allah ya sani bata son matar sam, don ta da
É—
e tana zargin itace ta bawa mahaifiyarta shawarar data fito da
ita daga gidan Ma'aruf, sai a yanzu da suka ga da gaske babu yadda zasu yi da ita akansa sannan suka hakura, ko kuma tace mahaifiyarta ta hakura don har yanzu bata gama yarda da ita Hajiyar Sudan
É—
in ba sam, amma sanin cewar bata da wata hanyar da ta wuce
tata yasa ta cije lebbenta kawai sannan ta ƙarasa ta zauna ba tare da kallonta ba.
Kuma kai tsaye sai ta fara bayani daga inda ta san zata fahimta.
"Yanzu mun aika masa da takardar sammaci, ba nufinmu a shiga shari'a ba kamar yadda nayi miki bayani, a i
ya gaban alkali za'a sulhunta komai a tsakaninku kin san duk abinda zaki fa
É—
a da kuma shaidun da muka samu wanda zasu saka komai ya tagi daidai, don haka daga nan za'a baki Æ´arki ki taho gida da ita.
Kwana
É—
aya kawai a tsakani, zaki ha
É—
a kayanta wanda a c
iki zamu san yadda za'a dinke ƙullin nan a cikin jakar yadda babu wanda zai tiya gani, sai ki kirashi wani waje inda zaku ha
É—
u ki kalallame shi da zancen wannan yarjejeniyar taku, ki karbi kuskurenki da komai ki kuma bashi yarinyar da cewar kin yarda ta ko
ma hannunsa kamar yadda kuka shar'anta, ki gaya masa cewa bayan wani lokaci ya dinga kawo miki ita kina ganinta.
Da wannan zamu barta a wajenta tsawon sati guda inda a sannan ne za'a sami wadda zata je gidan da sunan ta kawo sauran kayanta, a wannan lokac
in za'a sami dabarar da zata kwance ƙullin nan, wanda da anyi hakan Ruƙayya, shikenan sai ki cigaba da kurbar shayinki kina kallon abinda zai biyo baya."
Ta ƙarashe zancen da wani faffa
É—
an murmushin da ya sassauta zuciyar Rukayyan a lokacin, don sosai yas
a ta jin cewar kamar da gaske sunyi nasarar sun gama, tayi niyyar magana amma sai mahaifiyarta ta riga ta.
"Idan komai ya tafi daidai, sai ke kuma ki bar hakarƙarin mu ya huta haka kije can ki ƙarata."
"Ai babu abinda zai kuskure ma, na gaya miki idan k
inga an samu sa
É“
ani a wannan abin Nafi, to gawar da aka binne zata fito ta dawo duniya, don haka ku kwantar da hankalinku kawai."
Wannan zancen yasa su yin dariya dukkaninsu kafin hankalin Ruƙayya ta juya ga wayarta da ta shiga ƙara daga can inda ta baro
ta a jikin windon data tsaya.
Ta mike a hankali riƙe da kofinta ta koma wajen, sunan Jawad daya nuna akan screen din wayar yasa ta kur
É“
ar shayin kafin ta
É—
auki wayar ta kara ta a kunnenta.
"Barbie yau kika ce, 5pm."
Me yasa zai tuna mata? Ta sani, ta sa
ni cewa shekaranjiya ta gaji da nacinsa da ba zai kare ba tace masa zasu hadu a yau, kuma da zata iya a yanzun ma zata kara masa lokaci ne, amma ta san ko ta kara ba zai barta ba don haka dole ne ta daurewa kanta a yau ta fuskance shi.
A hankali ta ajiye
kofin hannunta akan windon, sannan tace.
"Ban manta ba J."
Taji ajiyar zuciyarsa daga ciki kafin yace.
"Then where did you decide?" (Ina kika zaba?)
Ta sake cije lebbenta na ƙasa
"Where we first met." (Wajen da muka fara ha
É—
uwa.)
Kalaman suka daki zu
ciyar Jawad da tasirin da ita bata san shi ba, don a nata
É“
angaren ta zabi fadar haka ne don zuciyarta ta tsara mata cewar a wajen da suka fara ha
É—
uwar anan ya kamata ta kawo ƙarshen alaƙarsu gaba
É—
aya, ko yaƙi, ko ya so.
Kuma ƙarfe biyar da ƴan mintunan t
ayi mata a kofar Joint
É—
in 'Harish', ta fito daga motar ta bayan ta jera ta a layin sauran dake wajen sannan ta gyara zaman dan mitsitsin mayafin data dora akan doguwar rigar jikinta ta atamfa, wadda akayi mata wani
É—
inkin mai kyau daga kasa kuma tayi bu
É—
e
war umbrella, takalmin kafarta ba mai tsini bane wannan karon don ta sani rashin nutsuwar zuciyarta ba zai barta ta iya tafiya a cikin mai tsinin ba, ta shiga ciki babu mutane sosai, Æ´an ka
É—
an ne kawai ke zaune akan kujerun wajen yayin da iskar yamma da ku
ma ƙamshin shuke-shuken wajen ke shiga hancinta.
Daga can karshe ta hango Jawad, zaune akan table din da a wajensa suka fara ha
É—
uwa, ba zata tantance idan tebur din ne ko an canja shi ba amma dai wajen ne, yana sanye da wasu dogwayen kaya Kaftan, yasa hul
a dark brown wadda ta fito da hasken fatarsa tar a cikin yammar, Jawad mai kyau ne ba sai kowa ya tuna mata hakan ba. Kuma da alamu ya jima a wajen don tuni an sauke shi da shishar da yake bula hayakinta a iska.
Kafafunta suka ƙarasa wajen a hankali sanda
shima ya hango ta, kuma a lokaci daya murmushi ya sauka akan lebbensa yana ƙara tuna mata da kammaninsa.
"Kina da cika alƙawari Babe, yana daya daga cikin abubuwan da suke kara haukatani akanki."
Bata yi murmushin da ta saba kamar kodayaushe ba sai kawa
i ta jawo kujerar dake fuskantarsa ta zauna.
"Wane flavour za'a kawo miki?" Ya tambaya yana tasowa daga kishingi
É—
en da yake.
Ta ajiye wayarta akan table din tare da earpiece
É—
in hannunta sannan ta kalle shi sosai.
"Ka san ba abinda ya kawo kenan ba Jawa
d, idan zaka kyauta ma just put yours aside muyi magana."
Ya gyada kansa yana kallonta.
"Zanyi duk abinda kika ce Barbie."
Da haka ya ajiye tasan gefe yana cigaba da kallonta, idanunsa na lumshewa akan fuskarta. Bata damu da yadda yake kallon nata ba ka
i tsaye ta fara magana.
"Jawad abubuwa sun caku
É—
e a rayuwata yanzu, I've got alot going on table da ba sai nayi maka bayaninsu ba amma hakan ne yasa na yanke alaƙa ta da kai, don bani da wannan lokacin Jawad, abinda nasa a gabana ya karato don haka dole n
e na ajiye ka a gefe.
Kuma nayi ƙoƙarin nuna maka hakan ta duk hanyar da zan iya amma ka kasa ganewa, shi yasa na yarda muyi wannan haduwar don in shaida maka komai baki da baki."
Tunda ta fara maganar bai ko kifta idanunsa ba, kallonta kawai yake da duk
kan irin emotion din da zata iya tsinta a cikin idanunsa, wanda basu dame ta ba ta cigaba.
"Idan baka manta ba Jawad, tun farkon alakarmu na gaya maka cewa babu aure a tsakaninmu na san baka dauki maganar da muhimmanci ba a lokacin amma ni da gaske nake t
un a sannan. Bari na fito fili na gaya maka gaskiya Jawad, a lokacin da na ha
É—
u da kai ina cikin damuwar da ni kaina ban san mecece ita ba that is bayan mutuwar aurena na biyu, so na kula ka ne kawai don ka taimaka min in manta damuwa ta, and you really di
d help 'cox we wasted away ta hanyar ta hanyar da har sai da kasa na kusa manta cewa ina da abinda nake so bayan kai.
Yadda kayi treating
É—
ina Jawad da tsananin kulawa da komai shi yasa zuciyata ta yi laushi akanka har kayi tunanin duk abinda nake yi maka
zai iya sawa na canja ra'ayina akanka, but honestly ban
É—
auke ka komai ba more than a toy (abin wasa), baka ta
É“
a zama wani abu mai daraja har da zan kalla da sunan aure ba Jawad.
Zuciyata ta mutum
É—
aya ce a duniyar nan kuma ina jin cewa ko za'a tsaida ta
shin duniya akaina ba zan taba iya canja hakan ba. So ka taimaka min mu karkare komai a yanzu, Let's just end everything here don ni tuni na fara gudanar da da sabuwar rayuwar da a cikinta zan cimma burina, ka taimaki kanka ka manta dani kaima Jawad.
Eras
e all those memories kayi pretending babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu wanda na san a cikin kankanin lokaci zaka ji ka manta dani gaba
É—
aya. Ka kalli kanka, kana da komai the looks, status, ku
É—
i, age, time... You have it all J. (Kana da komai) zaka samu
Æ´anmata guda dubu da kallo
É—
aya zaka yi musu and in no time they will be throwing themselves over you. Ka fahimta dan Allah Jawad cewa ni ba komai bace a rayuwarka."
Ta ƙarashe da dukkan fatan ya fahimce ta a cikin idanunta, kuma har a lokacin kallonta y
ake shima, sai da ta kai ƙarshe
É—
in sannan ya ƙifta idanunsa a hankali, yana komawa da baya, ya jingina sosai da kujerar da yake kamar kwanciya zai yi sannan muryarsa ta fito.
"Anything more Barbie?" (Akwai wani abu kuma Barbie?)
Ta ha
É—
iye yawu a makogwa
ronta sannan ta girgiza kanta.
"Nothing more Jawad, shikenan idan har ka fahimce ni."
Sai ya gyada kansa ha
É—
e da rufe idanunsa ya bu
É—
e kafin yace.
"Thank you." ( Nagode.)
Ta kalle shi tsawon wasu sakanni zuciyarta na son nazarin yanayin dake kan fuskar
sa wanda bata gane ba kuma ta kasa gano komai
É—
in, hakan yasa kawai ta dauki wayarta data ajiye sannan ta mike tsaye.
"Nagode nima, sai wani lokacin."
Ya sake gyada mata kansa ba tare da yace komai ba, kuma da haka ta juya ta tafi, idanunsa suka bi bayan
ta da kallo, zuciyarsa na tsagewa da yadda jikinta ke ka
É—
awa da tafiyar da take yi yayin da ƙwaƙwalwar sa ke dawo masa da kalaman abokinsa Haro.
"Ka sake gwada ta for the last time Man, idan har tana nan akan bakan ta cewar ba zata saurare ka ba, nayi mak
a alƙawari ni zan taya ka yarinyar nan tayi biyu babu a rayuwar ta, dama na tsane ta J, kaima ka san na tsane ta!"
Ya cije bakinsa da ya bushe yayin da wani guntun murmushi ya sauka akan le
ɓɓ
en nasa lokacin da Ruƙayya tayi kwana ta fita daga wajen tana
É“
a
cewa ganinsa. Wayarsa ya zaro a cikin aljihunsa ya shiga neman nambar Haron, bugu ka
É—
an kuwa ya
É—
aga lokacin da ya jawo kan shisharsa, kuma sai da ya zuƙo hayaƙinta ya busa a iska sannan yace.
"Tayi biyu babu Haro, let the plan start!"
***
Jigawa,
11:0
5 Am.
"Gwara ki fito fili kawai ku fadi gaskiya, yanzu ke baza ki so in fara tafiya in gano me akeyi ba? Idan yaso ko ta email sai na rubuto muku abubuwan da zaku tanada?"
Aminu ya fada yana kallon Amina da ta gama gaya masa irin tashin hakalin da ta shi
ga jiya, tana zaune a gabansa tana ƙoƙarin zuba sukari a kofin tea
É—
in data take hada masa.
Abinda ya fa
É—
a yasa ta yin murmushin da bata shirya masa ba tana kallonsa, kafin tace.
"Allah ya shirye ka Aminu, ai wallahi ina jin mutuwar ce ka
É—
ai ma zata iya
kashe bakin ka."
"Daga fadar gaskiya, yanzu ke tsakani da Allah baza ku so ku sami wata Æ´ar expo ba? Wannan harkar fa harka ce ta dindin idan an tafi an tafi kenan."
Tissue din dake gefenta Amina ta dauko ta jefe shi dashi a fuska.
"Aminu wannan fa ba z
ancen wasa bane."
Ya
É—
aga duka hannayensa sama.
"To shikenan, ai ke yanzu naga alama dama baki shirya mata ba, gashi nan har kin canja sai washewa kike yi wai ke amarya, dan Allah Amma bata yi haske ba?"
Ya tambaya yana kallon Amman da ta idar da sallar
walha a lokacin, bata amsa ba sai jawai ta juyar da kanta gefe kawai ta cigaba da laziminta.
Kuma sai akayi sa'a kafin shima ya kara cew komai wayarsa a gefe tayi kara, ya
É—
auka ya shiga sake amsa gaisuwar tarin mutanen da duk bayan Æ´an mintuna ake kiran
sa. Amina ta sake kallon Amma data juyar da kanta tana lazimi, kafin itama ta sunkuyar da nata ƙasa a hankali ta shiga wasa da wani zobe a yatsanta, wani abu take ji yana tokarewa a cikin zuciyarta duk sanda ta kalli Amman.
Kusan awar su guda kenan da sau
ka, awa guda da zuciyarta ta narke lokacin da Ma'aruf ya tsugunna a gaban su Baba harma dasu Baban Kurna da suka yi sa'ar ganinsu don a safiyar ranar suma suka zo, yadda ya tsugunna a gabansu kansa a ƙasa suna amsa gaisuwarsa wani abu ne da girmansa yasa h
ar yanzu ta rasa inda zata ajiye shi a cikin ranta, don har ciki ya shigo ya gaishe da Amma da kuma
Aminun, sannan har yanzu idanunta suna hango mata damin kudin daya ajiye a gefen shimfi
É—
ar Aminun lokacin da zai fita.
"Guess what?" (Kin san me?)
Ta tuna
yadda muryarsa ta furta hakan daga bayanta lokacin da ta sake binsa wajen mota tare da wasu yara don su
É—
auko kayan nan ita kuma ta dauko jakarta da lokacin da suka tsabar zumu
É—
i tsaya bata ko tuna da ita ba ta bu
É—
e kofar motar ta fita.
Yadda ya tsaya a
kusa da ita bayan ta juyo yasa ta kallon gefe ta hango yaran suna tafiya cikin gidan kafin girgiza kanta a hankali idanunta a kasa tana kallon jakar data dauko.
"Naga yadda zaki koma idan kin ƙara girma."
Hakan yasa tayi saurin
É—
agowa ta kalle shi, ya ha
rde hannayensa duka biyi a kirji riƙe da wayoyinsa, kuma a take sai ya bata amsar tambayar da idanun nata ne suka yi masa.
"Kamar ki
É—
aya da Mamanki, na da
É—
e ban ga masu kama haka irinku ba."
Ru
É—
ani idon nata ne ya tafi lokacin da ta sake sunkuyar da kan
ta kafin ta iya lalubo muryarta.
"Haka kowa yake cewa." Ta fa
É—
a a hankali.
"Haka kowa yake gani that's why."
Bata ce komai ya sake cewa.
"Naji dadin ganinsu sosai Amina, yanzu naga inda kika samo wannan kirkin naki."
Bata san lokacin da wani guntun mu
rmushi ya su
É“
uce a lebbenta ba duk da halin da take ciki. Ta sake
É—
agowa ta kalle shi, har a lokacin kallonta yake da yanayin da bata iya fassara shi, yanayin da yake ƙara tuna mata cewa har yanzu bata san inda zata ajiye shi a zuciyarta ba.
"Nagode sosai
."
Sai a lokacin tayi masa godiyar da tunda suka taho a hanya take fama da ita a bakinta tana tunanin yadda zata fade ta, kuma murmushin da yayi a wannan lokacin sai da ya kusan tsinka zuciyarta ba don kalaman Hajiya kilishi dake daure da zuciyar tata tam
au ba.
A wannan lokacin Ma'aruf na kallonta ne tunanin mai yawa a zuciyarsa, Allah ya sani wani abu ya motsa a zuciyarsa game da ita tun daga ranar da ya fara ganinta.
Ya cewa zuciyarsa tausayinta ne da kuma mamakin ganin ƙankantar ta, don a lokacin da M
ami tayi masa zancenta da kuma lokacin da ya tsinci sunanta a kayan Jamal, zuciyarsa bata kawo masa ko kadan cewar zai ganta karama irin haka ba. Kuma duk sanda ya sanda yake tare da ita a yanzu yana mantawa da dalilin da yasa ya yarda da aurenta ko kuma y
adda na auren nasu ya kasance, yana ji ne kawai kamar zamansu wani abu ne da ya da
É—
e daga cikin tsarinsa, don abubuwa da yawa ya banbanta da irin zaman da yayi da Rukayya.
Tare da Ruƙayya gani yake kamar duk abinda yake yi dole ne, don ita tana da tarin e
xpectation
É—
inta akansa, ta da
É—
e tsara wata irin rayuwa tare dashi a cikin kanta da a wancan lokacin shi ba abinda ke gabansa kenan ba, shi yasa abubuwa da yawa kai tsaye zata gaya masa tace yayi kaza ko ya kamata yayi kaza wanda duk da ba saurarata yake y
i ba, hakan baya masa