Showing 54001 words to 57000 words out of 94381 words

Chapter 19 - Farar Wuta Complete

kya tunanin zuciyar yaron ma zata iya ta karkata kanta?"

Hajiya Kilishi ta gya

ɗ

a kai tana murmushi.

"Da

ɗ

ina dake ragon azanci Salamatu, ai dama haka nake so, in ba haka ba don me nake ta ko

ɗ

a ta da ƴanuwanta a wajensa, so nake ta siye min zuciyar kowa har shi

ɗ

in kamar yadda nima nayi, ta yadda a nutse zan sa ta dinga kai min saƙona kowacce kusurwa babu mai

zarginta."

Hajiya Salamatu ta sake girgiza kanta.

"Baki gane ba Kilishi, abinda nake nufi shine idan har ta siye zuciyar Ma'aruf da darajar da zata fi taki nauyi fa? Idan har yayi nisa a duniyarta ta yadda ba zai iya jiyo ko da muryarki ba fa?"

Wannan k

aron dariyar da Kilishi tayi sai da ta ratsa kowanne bango a dakin ta kuma fita ta windon

ɗ

akin da yake a rufe, tabi iska zuwa nisan da ƙarfin amonta zai iya kaiwa, hatta jikinta sai da ya girgiza saboda nauyin dariyar, kafin ta kalle ta sosai tace.

"Ita

kanta yarinyar ai na shirya mata Salamatu, sau nawa zan gaya miki ne Ma'aruf nawa ne ni kadai?!"

***

Tafiyar ta fara! Insha Allah.

#Aysha shafi'ee.

#fikrawriters

#FararWuta.

BABI NA GOMA.

Ina mai baku hakuri, an samu jinkirin wannan babin ne saboda

rasuwa da aka yi min ba a gari ba don haka har tafiya sai da ta kama ni zuwa can... Ina rokon ku taya ni addu'ar Allah ya jikanta ya gafarta mata.

Sannan duk a cikin kwanakin nan mun rasa Abdallah ma,

ɗ

an gidan Sanah S. Matazu editar Fikra, ina rokon Alla

h ubangiji ya bata hakurin rashinbsa yasa mataryin can ne, sannan ina yiwa duk wanda ya rasa wani nasa ma addu'a, mutuwa na ta

ɓ

a mu a bangarorin da bamu san muna dasu ba, Allah yaji ƙan wadanda muka rasa mu kuma ya kyautata namu zuwan.

Ameen ya Allah.

~~

~~~~~

We should talk.

- Unknown

**

"Maamah don me yasa zai kira shi? Nace ya kira shi ne? Me yasa zai yi deciding abinda bai shafe shi ba kai tsaye?"

Muryar Ruƙayya ta fito da ƙarfi a lokacin da take kallon ƙaninta Ahmad da

ke tsaye a gaban gadon da take kwance. A cikin asibitin da aka kwantar da ita ne, tun bayan lokacin data fa

ɗ

i take asibitin ba'a sallame ta ba sakamakon hawan da jininta ke tayi babu sauka, don hatta fuskarta da kafafunta dukkansu a kumbure suke suntum.

"

To hell with you and him! Shi waye da baza'a kira shi a gaya masa yayi ba daidai ba? Me yasa akan Ma'aruf ƙwaƙwalwar ki ba zata taba hankali bane Rukayya? Meye a duniyar nan ki gani a jikinsa da sauran maza badu dashi? I swear to God idan kika kara daga mi

n murya a yanzu zan sake kiranshi na zage shi a gaban idanunki."

"Maamah kina jinsa ko? Kina jin abinda yake fa

ɗ

a?!"

Ta fa

ɗ

a tana juyawa wajen mahaifiyarsu Hajiya Nafisa dake zaune daga gefe tana ha

ɗ

a mata tea, idan da sabo ta saba da wannan fada a tsaka

ninsu, don ko Ashraf da yake sakon Rukayyan basa fa

ɗ

a tare kamar yadda suke yi da Ahmad

ɗ

in, shi mutum ne kaifi

ɗ

aya mai tsatsatsauran ra'ayi, Rukayya kuma ba'a taka ta tayi shiru, don haka inuwarsu bata ta

ɓ

a zama

ɗ

aya.

A yanzu ma dalilin

ɗ

aga jijiyoyin w

uyan nasu, Ahmad

ɗ

in ne ya zo ne yana shaida musu cewa shi ya sake kiran Ma'aruf akan zancen Hamida, tunda sunyi magana da Ashraf yace zai tuntube su kuma bai sake cewa dasu komai ba, don haka shi

ya kira shi da

ɓ

acin ran hakan wanda a ƙarshe wayar tasu ba

ta ƙare da da

ɗ

i ba, don Ma'aruf

ɗ

in har gargadi ya masa da cewar labarin zai canja idan har ya sake kiransa.

Ita kanta bata ga aibu a abinda Ahmad

ɗ

in yayi ba, don Allah ya sani idan da Ruƙayya zata bata dama a lokaci guda ne zasu juya dukkan tanadin da s

uke mata akan Ma'aruf ita da kawarta zuwa sharri, zata fi jin karfin gwiwar cutar dashi akan abinda suke yi a yanzu, don haka ta cigaba da ha

ɗ

a mata shayin kawai tana jinsu, tana ji kamar Ahmad na furta rabin kalaman dake cikin ranta ne da ba zata iya fa

ɗ

a

wa Rukayyan ita da kanta ba.

Kuma sai da taji kalaman nasa na shirin yin tsauri da yawa sannan ta kalle shi tace.

"Ahmad, fita daga wajen nan."

System

ɗ

insa da ya ajiye akan Fridge din

ɗ

akin bayan shigowarsa ya

ɗ

auka cike da fushi sannan ya nuna Rukayya

n da

ɗ

an yatsa tace,

"Daga yau kar ki sake kirana a matsayin danuwanki duk sanda wani abu ya ha

ɗ

a da mutumin nan, idan ba haka ba daga ke har shi I'm gonna rip your as* off! (Zaku gane kuranku!)"

Da haka ya fice tana bugo ƙafar

ɗ

akin asibitin, Rukkaya ta

koma da baya ta rufe fuskarta da duka tafukan hannayenta biyu lokacin da Hajiya Nafisan ke miƙo mata kofin shayin.

"Kin san halinsa ai sarai, amma kika biye masa kuke

ɗ

aga murya a cikin asibiti, na sha gaya miki da kin ga ransa ya

ɓ

aci kawai ki rabu dash

i, wannan shine girman."

Ta girgiza kanta a hankali sannan ta bu

ɗ

e fuskar tana karbar kofin.

"Maamah ba zan iya shiru akan abinda yake fada ba, kina ji fa yace har gargadi Ma'aruf yayi masa, to waye ya san iyakar abinda ya gaya masa ma? me yasa zai sake

ɓ

ata min al'amura ya sake

ɓ

allo wani abu kuma?"

Ta ƙarasa tana kar

ɓ

ar shayin, kuma gar

ɗ

in abubuwan da aka cika masa da kuma

ɗ

uminsa ya sauka har cikin ƙirjinta, ya sanya ta lumshe idanuwanta a hankali kafin ta bu

ɗ

e su sosai akan kofin, da

ɗ

aya hannun nata

shiga murza bakinsa a hankali ba tare da ta kalli Mahaifiyar tata ba tace.

"Maamah kince kawai aura masa yarinyar akayi ko?"

Taji sanda Hajiya Nafisan tayi ajiyar zuciya kafin tace.

"Tabbatar min akayi cewa a cikin sati uku akayi komai, ance bai taba g

aninta ba ma har aka daura auren, sannan yarinyar bata da wani daraja, mahaifinta ance irin sana'ar ƙananun aikin katakon nan yake yi, don haka na tabbatar miki akwai wata manufa ta daban dangane da auren nan da bamu sani ba, amma ba wai aure yayi irin wan

da kika sani ba."

Wannan karon Ruƙayya rufe idanuwanta tayi duka, tana jin yadda wani tiririn zafi na daban da yafi karfin shayin dake hannunta yana cigaba da zurara a cikin ƙirjinta yana kona duk inda ya bi.

"Nima na sani ba auren gaske bane Mami, don w

allahi na san babu ta yadda za'ayi yarinyar nan ta shigo cikin tsarinsa, a yanayin arzikinsa dana gidansu ko haukacewa yayi akwai ƴanmatan sa suka fita daraja da yawa da zasu so shi a haka."

Shi yasa bana son inyi wasa da kowacce irin dama Mami, a yanzu b

an damu da duk hanyar da zamu bi mu lalata komai ba, don ban damu da manufar kowa ba, burina kawai kada yarinyar nan ta da

ɗ

e a rayuwar Ma'aruf, don ta haka ne kawai zan iya cimma burina Maamah, idan akwai ta, na sani ba zan ta

ɓ

a iya samun abinda nake so ba

."

Kafin Hajiya Nafisan dake kallonta tace wani abu, ƙarar ringtone

ɗ

in wayarta ya cika

ɗ

akin, don haka ta dauko wayar tata dake gefen bedside drawer ta miko mata, Ruƙayya ta karba tana kallon sunan da ya fito akan screen

ɗ

in, Jawad... Taji ranta ya ƙara

dugunzuma ya

ɓ

aci a take, bata san wane irin mutum ne shi marar zuciya haka ba? Me yasa zai cigaba da damunta alhali da kowanne yare da zai iya fahimta ta gaya masa cewa ya rabu da ita? Sai kawai ta danne buttton

ɗ

in wayar gaba

ɗ

aya ta kashe ta sannan ta aj

iye ta a gefe.

Takaicin dake cike fal da tausayin ƴar tata ya nuna akan fuskar Hajiya Nafisa kafin ta girgiza kanta a hankali.

"Na gaya miki ki kwantar da hankalinki ki samu sauƙi mu koma ki gida, don Hajiya Saude ta gaya min sai da ha

ɗ

in kanki tukunna s

annan komai zai daidaita, nayi miki alƙawarin Ma'aruf da ƙafarsa zai tako har inda kike ya neme ki."

Wani abu kamar murnushi ya fito kan lebben Ruƙayyan yayin da ta sake jingina kanta baya da jikin gadon kafin a hankali kuma ta

ɗ

ago da kofin shayin nan ta

kai bakinta.

Daga can jihar Abuja, a cikin gidan rawar da Jawad yake a can sama, inda yaken wani lungu yana zaune akan luntsememiyar kujerar wajen shi kadai, a gabansa wani haddadden kwandon shisha ne da yake zuƙa yana hurawa lokaci zuwa lokaci, a

ɗ

aya h

annun nasa kuma wayarsa ce da hasken screen

ɗ

inta ke haska fuskarsa yayin da yake danna number guda cikin contact list

ɗ

insa ana kuma maimaita masa abu guda daga daya bangaren wayar.

"The number you're trying to call is currently switched off, Please try

again later." (Lambar da ake kira a kashe take, a sake gwadawa bayan wani lokaci.)

Hannunsa ya sake danna number yayin da aka sake maimaita masa maganar.

"Jawad?? For real? Kai kadai anan sama? Na zata wasa su Sa'id suke da suka ce kana nan ai."

Wani ab

okinsa da suke kira da Haro ya ƙaraso daidai wajen yana zama daga gefen kujerar, bai ce dashi komai ba don haka ya sake kallonsa yace.

"Naji rumours din, it was bad man, amma bai kamata hakan ya dame ka ba, kar ka jawowa kanka depression."

Sai a yanzu Ja

wad ya juyo ya kalle shi, ya san abinda yake magana, jita-jitar dake yawo cewa za'a cire mahaifinsa daga kujerar Minister, har a tunaninsa abinda zai dame shi kenan? To me zai same su idan an cire shin tunda ko a yanzu sun tara dukiyar da ya san har su mut

u ba zata kare ba, ya zuki hayakin ya fesar sannan yace.

"Kar Allah yasa a fasa cire shin, al'amarin wannan tsohon ya isa ya dame ni ne Haro? abinda yake gabana daban."

Kan shishar Haro ya kar

ɓ

a yana dariya sannan yace.

"Pray tell."

Sai kawai ya jefo m

asa wayar hannunsa shima sannan ya jingina da kujerar. Haro ya cafe wayar sannan ya kalli screen

ɗ

inta, kuma sunan da ya karanta na farko akan call log din ya sashi jan tsakin da bai shirya ba.

"Ban san ranar da asirin da yarinyar nan ta naka zai karye ba

Jawad, har sau nawa zan gaya maka ka rabu da wannan tsilar abar, ub*n me zata tsinana maka da baka samu ba a duniyar nan? You're young, kana da kudi, kana da status mai kyau, kana kan lokacinka Man, sannan babu yarinyar da zaka kalla duk kasar nan ka kasa

samunta. Me yasa ba zaka yi hankali ka fahimci cewa wannan yarinyar sharri ce ma a rayuwarka ba?"

Jawad ya lumshe idanunsa ya bude yana saurarensa ta cikin sautin kidan dake tashi daga can kasa kuma sai da ya kai har karshe sannan ya girgiza kansa, idanu

nsa na kallon fitilar dake samansu mai kala-kala a cikin duhun wajen yace.

"Ba zaka gane ba Haro, ba zaka gane abinda nake ji bane, na rantse da Allah idan Ruƙayya bata aure ni ba, ba zata sake auren kowa ba a duniyar nan!"

***

"What do you find? Me ka

samo?"

Faruk ya tambaya riƙe da Tab

ɗ

in hannunsa yana kallon Ma'aruf dake kokarin fitar da lissafin da suka kwashe fiye da awa guda suna yi akan kamfanin wasu abokan kasuwancinsu da suka gano cewar suna da nasu kamashon cikin wannan mummunar asarar da har

yanzu suke bincike akanta.

Suna zaune ne daga cikin office din Ma'aruf

ɗ

in, bayan kusan jiran awa uku da Faruk din yayi yana jiran dawowar Ma'aruf da ya bar office din tun kusan sha

ɗ

aya na safe.

Kuma sai da ya dawo sannan ya bu

ɗ

e email dinsa ya karanta

bayanan da Martha sakatariyar tasa ta turo masa sannan suka fara ha

ɗ

a komai suna tarawa da ƙaiyadewa.

"So shi wannan Mr. Ishmael Grahm

ɗ

in shine ya karbi aikin accountant

ɗ

insu a farkon shekarar nan kenan kuma sunansu

ɗ

aya da wanda ya tafi har surnane

ɗ

i

n."

Ma'aruf

ɗ

in ya fa

ɗ

a, idanunsa manne da tab

ɗ

in gabansa yayin da muryar tasa ta fito kamar ta ƙwace ne daga cikin tunaninsa.

"What a ina ka ga hakan? Dama sun canja accountant ne? When?"

Faruk yayi tambayoyin yana komawa cikin kan tasa wayar.

"A cik

in wanda ka min sending zaka duba, anyi naming dinsa 13th March na wannan shekarar."

Kuma sai da Faruk din ya kusan zuwa can ƙasa wajen nemowa kafin ya isa inda yake gaya masan, idanunsa suka ƙanƙance yayin da yake karanta bayanin dake wurin.

"Bala'i! B

ya akayi hankalinka yaje wajen nan, I was goung through it fa tun safe amma wallahi ban gani ba."

"Shi yasa na gaya maka na kusa korarka daga aikin nan, ban san me yake

ɓ

ata maka tunaninka ba kwana biyu."

Dariya Faruk

ɗ

in yayi yana cigaba da karantawa ka

fin yace.

"Aikin Shahida ne wallahi, tunda ta yaye Aarif nake ji kamar watannin farkon auren mu muka koma."

A lokaci guda Ma'aruf ya tsaya da karanta abinda yake yi ya juyo ya kalle shi, sai kuma ya girgiza kansa sannan yace.

"Baka da hankali Faruk, na

da

ɗ

e ina gaya maka."

Faruk

ɗ

in ya sake yin dariya yana daukar tambulan

ɗ

in lemon da Martha ta kawo musu kafin yace.

"Inji wanda yake amsa sunan sabon ango, you didn't even tell me ya yarinyar take."

Yaya yarinyar take. Maganar ta sake tuno masa da fuska

rta a yau da safe kafin ya fito, sati guda kenan da yin auren, kuma a cikin sati gudan nan baya jin magana ta ha

ɗ

a su wadda tafi kirgen cikin yatsu, wani lokacin dai su kan ha

ɗ

u da asuba idan jamlock

ɗ

in kofar falo ya rufe bayan ya fita masallaci, zata zo

ta bu

ɗ

e masa idan yayi knocking sanye da dogoon hijabinta har kasa, ranar farko bata ce dashi komai ba, amma a rana ta biyu ne ta fara gaishe shi. Sannan kuma sau da

yawa idan ya koma da daddare zai ganta, har ya fahimci wani lokaci ma tana fitowar ne kawa

i don ta gaishe shi.

Bayan hakan maganganun da suka ha

ɗ

a su baya jin sun wuce biyar, ya san ranar juma'a da zai fita masallaci ya tambaye ta dardumar sallah ta dauko wata sabuwa kuwa fil mai laushi ta kawo masa, sai kuma ita da ta tambaye shi Panadol ya f

ita da kansa ya siyo mata, amma bayan hakan baya tunanin wata maganar ta kara hada su don baya son ya takura ta ko kadan, so yake hankalinta ya kwanta ta fahimci cewa da gaske ba abinda zai mata, don a o farkon nan ya lura cewa da gaske a tsorace take dash

i.

Ya rasa irin tasiri kalamansa suka yi a zuciyarta, ya kasa gane ma me yasa ta yarda da auren idan har tana tsoronsa haka, wataƙila laifin tun na wannan ranar ne, da ta fito ya ganta, da tun a lokacin zai san tayi ƙanƙanta yayi mata wannan barazanar, do

n haka yake son da kanta ta karkade duk wani tunani da take yi game dashi da kuma damuwar kalaman nan.

A shekaranjiya da yaji tana waya da wata tana yi mata bayanin cewa har yanzu bata fara girki ba, a cikin muryar tata yaji da wani abu kamar damuwa, wani

abu da ya tsaya masa a rai yasa yasa ba shiri a lokacin da ya shiga cikin gida yaji Mami na yiwa Malam Sani lissafin cefenan wata, ya bishi a baya ya ƙara masa wasu ku

ɗ

in yace duk abinda ya siya na cikin gidan ya sake siyan rabin sa ya kai mata.

Komai

na wannan auren daban yake da lokacinsa da Rukayya ya sani, babu abu ko guda daya da zai danganta shi da farkon wancan

ɗ

in, kamar komai

ɗ

in yana zuwa ne a kishiyar

ɗ

ayan, sai dai abu daya kawai zai iya dorarawa shine a yanzu yana jinsa mutum mai ƴanci tund

a babu ruwanta dashi sabanin a wancan da kwanakin farko suka sa shi yaji kamar an tsare shi a wani waje ne da lissafin abubuwan da ya kamata yayi.

"Kaji ai matsalata da kai kenan, da an ta

ɓ

o wani zancen ba na aiki ba you lack interest, na tabbata da nayi

ta jiranka ma anan wani aikin ka tafi yi."

Faruk ya fa

ɗ

a yana jawo shi daga cikin tunaninsa, kuma ba tare da ya juyo ya kalle shi ba yace.

"Saboda ni ba mutum bane kenan bani da wasu personal problems, to ka leƙa motata ka gani wanki naje na kar

ɓ

o sannan

na karbo

ɗ

inki, har B&L naje samo maigadi, sannan na tsaya a zoo road nayi aski."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login