Showing 72001 words to 75000 words out of 94381 words

Chapter 25 - Farar Wuta Complete

a tsakaninsu ba, wasu

abubuwa ne da ƙarara kowannensu ke ganewa idan

ɗ

ayan yana ciki, don haka a yanzu ma Ishaq ya riga ya sani cewar ya riga ya yanke koma wane irin hukunci ne game da zamansu ba sai sun

ɓ

ata lokaci wajen biya shi ba.

Da haka suka yi sallama, sabon maigadin da

ya samo ya sake budewa Ishaq gate

ɗ

in gidan, shi kuma ya koma ciki.

***

Yayi sakanni biyu tsaye daga bakin kofar yana kallon yadda take kokawa da zip

ɗ

in rigarta kafin ta ankara dashi, watakila jikinta ne kawai ya bata cewar yana daga bakin kofar, don a

lokaci guda ta juyo da sauri tana kallonsa, fararen idanunta suka zare akansa yayin da a lokaci guda ta saki hannayenta duka biyun suka sauka a gefenta.

"I'm sorry banyi sallama ba ko?"

Sai ta girgiza kanta.

"Babu komai ban ji lokacin da ka shigo bane.

"

Ya cije lebbensa tsaye a jingine kofar kafin yace.

"I'm sorry bana so in

ɗ

auki lokaci ne kiyi bacci."

Idanunsa na kallon fuskarta da yaga kamar tana ƙoƙarin kore wani abu wani abu mai kama da mamaki kafin ta tambaya.

"Wani abu kake so?"

Lokaci ne ya

tsaya cak a cikin kansa da wannan tambayar yayin da fatar bakinsa ta bude kamar zai ce wani abu yana kallonta, tsakaninta da Allah ta fadi hakan ba tare da ta san tarin ma'anonin da za'a iya fitarwa daga kalaman nata ba, ganin tana cigaba da kallonsa yasa

ya sake cije le

ɓɓ

ensa na ƙasa sannan ya girgiza mata kai.

"I want to treat your hand." (Hannunki zan duba.)

Ya fa

ɗ

a yana kallon yadda fuskarta ke nuna tarin yanayi kala-kala, ƙafafunsa suka tako cikin

ɗ

akin a hankali zuwa inda take tsaye, kuma kamar a w

ani shiri sai iska ta buso daga windon da yake fuskantar su daidai lokacin da ya tsaya a gabanta, kuma bai

ɓ

ata lokaci ba yasa hannunsa

ɗ

aya ya

ɗ

auko nata mai ciwon nan.

Gaba

ɗ

aya tsawonta iya kafadarsa ne, gashin kanta da babu dankwali ya taso sama yana s

haida laushinsa, da zai iya a wannan lokacin zai zare ribbon din data

ɗ

aure shi ne don ya sauko kafadunta yaga iya tsawonsa, amma sai ya daurewa wannan tunanin ta hanyar kallon yatsun hannunta da yake riƙe dasu.

Ya san cewa shi mutum ne da yake ƙarbar res

pect daga

ɗ

imbin mutane, kuma a iya kokarinsa yana kokarin ganin ya kyautatawa duk wanda ya shigo hanyarsa, da kuma kaffa-kaffa musamman a yanzu don ganin bai yi wani abu da zai iya cutar dasu ba, amma Allah ya sani bai ta

ɓ

a ha

ɗ

uwa da wanda a lokaci guda y

aji zuciyarsa na tsoron ciwonsa akanta ba irin yarinyar nan, yarinyar da a baya bai damu da yadda zaiyi kokarin samun bayanin da yake so daga gare ta ba,

Wani bandeji ne mai ha

ɗ

e da audugarsa a jiki, don haka magani kawai ya

ɗ

iga a jiki daga cikin wata ƴa

r kwalba sannan ya rufe ciwon nata dashi, ai kuwa ta runtse idanunta a lokaci guda tana jin zafin na tafiya har tafin ƙafarta.

"Zuwa safe zaki iya cirewa sai a saka wani, insha Allah a kwana biyu zai warke."

Ya fa

ɗ

a yana sakin hannun nata, kuma duk da za

fin da take ji haka ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta.

Ya rufe maganin sannan ya wuce ta zuwa wajen da mudubin

ɗ

akin yake, ya ajiye roll

ɗ

in plaster da kuma kwalbar maganin akai sannan ya juyo ya dawo inda take tsaye tana cigaba da danne ciwo

n.

Kuma bata yi wani tunani ba lokacin da ya tsaya a bayanta, dab da ita sosai, don haka da sauri ta juyo gabadaya ta kalle shi amma sai ya saka hannayensa duka biyu akan kafa

ɗ

unta ya juyar da ita.

"Zan taimaka miki da zip

ɗ

in ne..."

Ya fa

ɗ

a muryarsa na

fitowa dab da kunnenta sosai, kuma kafin tayi ƙokarin kamo tunaninta muryar tasa ta cigaba da cewa.

"Akwai abubuwa da yawa game dani a zuciyarki na sani, amma ina so a saman komai kisa a ranki cewar ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insh

a Allah."

Ya furta hakan yayin da hannunsa ya kai kan zip

ɗ

in, sauran yatsunsa na

ɗ

aya hannun suna taba fatar bayanta, sai kawai ta rufe idanun gabadaya tana ƙoƙarin saita numfashinta, kuma da ja

ɗ

aya kawai hannunsa yayi ya sauke zip

ɗ

in sai dai bai kai s

hi har ƙasa ba, daga daidai tsakiya ya barshi, taji sanda yatsunsa suka dauke daga saman fatar ta, da kuma sanda yake matsawa, sai ta bu

ɗ

e idonta lokacin da ya zagayo daidai saitin ta.

"Nagode." Ba zata ba ta

ɓ

a iya tantance yanayin yadda muryar tata ta fi

to ba, ya gya

ɗ

a kansa.

"You are welcome, sai da safe."

Da haka ya juya ya nufi kofar

ɗ

akin yana rufo mata ita.

Sakan

ɗ

aya, biyu, uku, suka wuce Amina tana ƙoƙarin saita numfashinta kafin a hankali ta

ɗ

auko rigar baccin nan ta karasa abinda zata yi, wand

a har ta gama komai ta kashe fitilar

ɗ

akin kalamansa na yawo a cikin kanta.

...ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah.

Sai kawai ta rufe idanunta sannan ta dunkule jikinta akan gadon, kuma bata bawa zuciyarta wani damar tunani ba

don bata san buhu nawa zata kwance na tambayoyin da bata da amsar su a zahiri dama cikin kanta ba.

Ya rabbi lakaal hamdu kam yanbaghi li jalaali wajhika wa adheemu sul

ɗ

aanik.

Bakinta ya furta addu'ar hankali yayin da take jin ma'anar ta na tafiya har ƙa

san zuciyarta.

***

Washegari...

Ƙ

arfe goma na safiyar Litinin, a irin wannan lokacin Amina ta saba da wani irin shiru don ko'ina tsit yake, duk wani mai fitar safe ya da

ɗ

e da yin gaba, ƴan makaranta da masu aiki da mafi yawanci sun fi yawa a kowanne gid

a.

Tana daga kitchen a lokacin tana ƙoƙarin fara aikinta ta tsinkayi ƙarar ƙwanƙwasa kofar, mamaki ya

ɗ

an kamata don ta san babu wanda zata yi tunanin zuwansa a wannan lokacin, ta gyara zaman

ɗ

ankwalinta yadda ta yafa shi sannan ta fito daga kitchen

ɗ

in t

a iso ƙofar falon kuma ba tare da tunanin komai ba ta bu

ɗ

e ta,a lokaci guda siffar Hajiya Kilishi dake tsaye ta shiga idonta tun kafin sakon saninta ya ƙarasa ƙwaƙwalwar ta.

Tana sanye da wata ha

ɗ

addiyar lafaya ruwan makuba (maroon) da ta nanna

ɗ

e ta tsaf

a jikinta, fuskarta kamar kullum

ɗ

auke da wannan murmushin nata, murmushin dake haska annurin fuskarta a kodayaushe yana ƙawata kammaninta.

Babu dalili Amina taji gabanta ya fa

ɗ

i amma tayi saurin kore hakan wajen yin nata murmushin itama.

"Sannu da zuwa

Mami, barka da zuwa."

"Barkanmu dai Amarya. Yau dai na ajiye kyuiyata a gefe nazo ganin

ɗ

akin amarya."

Wani murmushin mai ha

ɗ

e da kunya Amina ta sake yi kafin tayi baya don bata hanya tana kara fadin 'Barka da zuwa', kuma kai tsaye kuwa ta shigo ha

ɗ

e da

sallama yayin da ƙamshin dadda

ɗ

an turarenta ke rufo mata baya.

"Wa'alaikum salam."

Ta amsa sallamar tana rufe ƙofar har a lokacin da murmushi a fuskarta, murmushin da a lokaci guda ya

ɗ

auke sakamakon juyowar da Hajiya Kilishi tayi tun kafin ta kai tsakiy

ar falon tace.

"Idan akwai muƙulli rufe ƙofar dashi Amina, akwai maganar da zamu yi ne."

Zuciyarta ce ta fara bugawa a kirjinta kafin ta juyo ta kalle ta, amma ganin murmushin dake kan fuskarta har yanzu, yasa itama ta dawo da wani dan guntu kan le

ɓɓ

enta

sannan tace.

"Toh Mami."

Da haka ta rufe kofar tana ƙoƙarin gayawa zuciyarta cewa gabanta ba fa

ɗ

uwa yake ba sannan ta juyo ta ƙaraso ciki.

A lokacin ta zauna daga tsakiyar kujera mai cin mutum uku a falon don haka ita tameni waje daga

ɗ

aya karshen ƙato

n carpet

ɗ

in ta zauna tana fuskantar ta.

"Barka da Asuba Mami, fatan kun tashi lafiya?"

Ba kallonta take ba amma daga yanayin yadda muryarta ta fito wajen amsawa ta fahimci har yanzu murmushin take yi.

"Mun tashi lafiya, Ya bakunta kuma? Ko da yake ai n

aga su Samirah sun saka kin saba tuni."

Bata ce komai ba illa wasa da karshen skirt dinta da take yi tana cigaba da murmushin da zata kira na dole, don bata san me yasa zuciyarta ta kasa zama waje

ɗ

aya ba.

Hajiya Kilishi ta kalli ƙaton screen din Tvn dak

e tsakiyar falon dama sauran kayan kallon da aka jera akan hadadden stand

ɗ

in Tvn da dubu tamanin da biyar ta bayar aka siyo shi sannan tace.

"Gidan shiru ke ka

ɗ

ai baki ko kunna Tv ba?"

Da wani murmushin a fuskarta tace.

"Ai ba'a hada Tvn ba har yanzu M

ami."

Muryarta ta fito ƴar ƙarama a cikin shirun dakin, kamar tana son ta shaidawa Hajiya Kilishin ƙanƙanta da kuma rauninta.

"Baku gaya min ba ai, gashi jiya kuwa yaro mai gyaran satelite ya shigo har cikin gida, da ya karaso ya hada muku, amma a bar ki

a gida haka shiru, shi ya fice ya tafi hadaniyar gabansa ba zai tuna da wani sha'anin Tv ba.

Sai ta sake girgiza kanta tana cigaba da murmushin.

"Ba komai Mami, duk sanda aka sa baza'a makara ba ai."

Ta fadin hakan lokacin da take kokarin mikewa, amma

a lokaci guda Hajiya Kilishin ta tsayar da ita.

"Ina ziki je kuma?"

"Mami, kayan breakfast zan kawo miki."

Ta fa

ɗ

a taka kallonta, sai ta girgiza kanta.

"Barsu nagode, dawo ki zauna."

Umarnin dake cikin muryar ya ka

ɗ

a hantar ta, taji wani abu yana ƙoƙa

rin

ɓ

allewa daga cikin zuciyarta, amma sai tayi saurin ture hakan ta dawo ta zauna

ɗ

in, hannunta na ta

ɓ

a hannun kujerar gefenta kamar tana neman taimakon ta.

Kuma zaman nata sai ya zama kamar shine farawar wani shafi na farko a rayuwata, don watakila idan

zata bada labari, zata fara ne ta kansa, daga lokacin da kafafunta suka sake komawa kan carpet

ɗ

in nan da kuma lokacin da muryar Hajiya Kilishi ta sake ratsa shirun

ɗ

akin da cewar.

"Amina kunyi waya da mutanen gida kuwa jiya?"

Sai da ta ha

ɗ

iye wani dunƙ

ulen abu da bata san sunansa ba a kirjinta sannan ta girgiza kai.

"A'a Mami, na kira su dai jiyan amma bai shiga ba."

"Ina wayarki?" Kai tsaye ta sake wata tambayar da ta fito kamar tsawa.

Kan Tv's stand

ɗ

in nan ta nuna inda bayan fitowarta da safen ta

saka ta a caji.

"To matso ki kira su."

Wannan karon sai da ta kalle ta tsawon wasu sakanni fuskarta na haskawa da mamaki sannan ta matso a hankali zuwa wajen wayar, lokacin da ta cire ta daga caji taji kamar hannunta na rawa amma tayi saurin fara dannawa

ta lalubo nambar Amma.

Sai da ta sake kallon Hajiya Kilishin da murmushin fuskarta ya rage tasiri kafin ta kara wayar a kunnenta, kuma cikin wata iriyar sa'a, bugu

ɗ

aya biyu sai Amman ta dauka, sautin muryarta kadai ya doka wani abu a ƙirjinta tun kafin

ta fahimci abinda take fa

ɗ

a.

"Amina yi haƙuri, tun jiya bamu kira ki ba, muna asibiti ne sai da safen nan muka fara samun nutsuwa..."

"Asibiti? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!... Me ya faru Amma? Me ya faru?"

A yanzu ta tabbatar hannun nata rawa ya

ke, don tana jin yadda yake tafiya tare da bugun zuciyarta.

Daga cikin wayar Amma tayi ƙokarin gyara muryarta ka

ɗ

an sannan tace.

"Aminu ne mai mashin ya taka shi jiya da daddare a wajen aiki, amma sun ce jikin nasa da sauƙi kar ki

ɗ

aga hankalinki, yanzu

mu ma zamu shiga mu ganshi..."

Zancen ya katse a lokaci guda da Amina ta nemi wayar a kunnenta ta rasa. Hajiya Kilishin da a yanzu ke tsaye akanta riƙe da wayar tasa hannu ta

ɓ

are bayanta ta fito da batirin ta jefar dashi gefe, sannan ba tare da

ɓ

ata wani

lokaci ba ta karya wayar gida biyu itama.

Kuma taku biyu kawai ya mayar da ita baya kan kujerar da ta taso, ta cigaba da kallonta har a yanzu da ragowar murmushin nan a fuskarta kafin muryarta ta fito cikin wani irin sauti da yake ainahin halittar ta, sa

utin da yake manne a kirjinta tare da zuciyarta dake ƙawata mata tarin hanyoyin da kullum suke

ɓ

ullewa ga nasararta, sautin da a duniya kaf, mutum hu

ɗ

u ne kawai suke sanin da kasancewarsa, sai a yau da ta zabi Amina ta zaman cikon ta biyar

ɗ

in, cikon da ta

ke fatan zai zama mataki na ƙarshe da take da yaƙinin zai kai ga nasararta.

"Barka da shigowa cikinmu Amina."

Kalamai biyar

ɗ

in data furta kenan wanda ta lissafa cewa adadinsu ya dace da lambar matsayinta, murmushi kan fuskarta cika taf da tarin kalaman

da take shirin

ɓ

are mata a yanzu wanda zasu sa ta fahimci wacece Kilishi tun daga tushe da kuma dukkanin abubuwan data aikata a rayuwarta.

***

Wane shiri Ma'aruf ke yi akan ƴarsa Hameeda da kuma Ruƙayya?

Me ya yankewa zuciyarsa akan Amina da har Ishaq y

a fahimta?

Ku gaya min ina rayuwar gidan nan ke tafiya?

Munaya and Ishaq, me kuke tunani?

Hajiya Kilishi...

Ina gaya muku har yanzu sunan matar nan kawai kuke ji, next chapter zata bu

ɗ

e muku abubuwa da yawa game da ita...

Babi na gaba zai nuna muku me

ake nufi da ainihin kissa da kisisina irin ta mata kamar Kilishi, wanda suka yarda cewa kowacce mace zata iya samun duniyar da take so a tafin hannunta... Ba boka ba malam!

#Aysha shafi'ee.

#fikrawriters

#FararWuta.

BABI NA SHA UKU.

~~~~~~~

Ther

e's a part of me that likes to beleive everything will be okay, then there's another that breaks down every chance it gets.

- Unknown.

**

Dukkan wata ma'ana ta mamaki da kuma tashin hankali shine yadda fuskar Amina tayi a lokacin da take kallon Hajiya K

ilishi.

"Ta

ɓ

a Aminu dana sa akayi tsaraba ce ga ƙwaƙwalwar ki Amina don ki saurare dukkan abunda zan gaya miki da kyau, ki yarda da dukkan kalamaina sannan

kuma zuciyarki ta tabbatar da cewar Kilishin da zaki sani a yanzu da gaske take al'amuranta."

Tayi

shiru bayan ta fa

ɗ

i hakan hannunta na jawo wayarta da ta ajiye a gefe, babu ƙarar kiran dake shigowa alamun a silent ta saka ta.

"Ya akayi Awwalu?"

Muryar tata da ta canja tar ta tambaya cikin wayar bayan ta kara ta a kunnenta... Har a lokacin Amina bat

a motsa daga yadda take zaune ba, idanunta basu canja daga yadda suke kallonta ba, sannan ƙwaƙwalwar ta bata wartsake daga mamakin dake zagaye da ita ba, Ƙirjinta dake

ɗ

agawa cikin numfashi mai nauyi shine ka

ɗ

ai abinda zai sa ka san cewa idan ka ta

ɓ

a ta ba

zata tafi ta fa

ɗ

i ba.

Wataƙila magana guda

ɗ

aya aka fada a cikin wsyar wadda ta gamsar da Hajiya Kilishin, don bata ƙara cewa komai ba ta kashe ta kawai ta sake mayar da ita gefenta, sannan ta sake kallom Aminan, hasken fuskarta na yayewa alokaci guda

"

Duk abinda zaki ji a yanzu ya zama tsakani dake ne Amina, idan ba haka ba a ƙarshen zancena zaki gane abinda zai faru idan har kika sako mutum na ukun mu a wannan zancen koda kuwa mahaifiyarki ce.

Da farko mu bar duk wani kewaye-kewaye mu tafi ga abinda y

asa kika shigo gidan nan, tunda ni dake dama duk wani mai hankali mun san akwai dalilin aurenki da Ma'aruf..."

Ta gyara zamanta ka

ɗ

an sannan ta cigaba...

"... Cire mahaifinki ki ajiye shi a gefe, amma ko mahaifiyarki ta san ruwa baya tsami banza, a murya

rta kawai na fahimci cewa irin zurfin tunaninta kika

ɗ

auko Amina, ku duka kun san ba kowacce mace ce zata taka irin matsayin da kika taka a banza ba, zan ƙara tabbatar miki cewa shigowar ki cikin gidan nan dama cikin rayuwar Ma'aruf wani abu ne da ba don t

aimakona ba, ba zaki ta

ɓ

a samunsa ba ko zaki mutu sau

ɗ

ari ki dawo, saboda a rana guda zamu iya samun mata dubu da zasu yarda da auren Ma'aruf ko da kuwa ciwon da yake dashi yafi haka tasiri, don ba'a wayewar kowacce rana mata ke samun namiji irinsa ba.

Kuma shi kansa Amina, da an bashi za

ɓ

i na sani tsaf zai kawo macen da zata fi ki a komai don irinsu kawai ya sani kuma yake mu'amala dasu, amma sai nayi amfani da ƙarfina da kuma ikona nace ke ka

ɗ

ai za'a bawa wannan matsayin wanda dole kowa ya yarda da hak

an, don haka duk wata soyayya da kika ga kina samu daga mutanen gidan nan dama shi Ma'aruf

ɗ

in da ya fara saurarar ki duka saboda ni suke miki ba don komai ba, ni na

ɗ

ora su akan turbar zuciyarsu ta so ki kuma hakan ya zame musu kar dole."

A yanzu Amina t

ayi ƙoƙarin sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta dake faman rawa suna kakkarwa akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login