Showing 6001 words to 9000 words out of 94381 words

Chapter 3 - Farar Wuta Complete

da nake dashi zai bani dama na iya cimma abinda ke gabana sai me idan na rasa hankalina?"

Sai ya girgiza kansa kawai yana cigaba da kallon

sa.

"Nasha gaya maka Ma'aruf ya mutu shekaru goma da suka wuce Ishaq, kaƙi ka yarda dani ne, amma Ma'aruf ya riga mutu, babu shi anan."

Ya ƙarasa yana nuna ƙirjinsa, daidai lokacin da labulen dakin ya bu

ɗ

e, wani bature ya leƙo fuskarsa a murtuƙe yace.

"

What the in the world are you two talking abou..."

Bai karasa ba sakamakon kallon da su duka biyun suka juyo suna yi masa kowanne ransa a

ɓ

ace, sai kawai yayi sauri ya maida labulen ya juya, dukkaninsu suka yi ajiyar zuciya alokaci guda.

Shiru ya ratsa w

ucewar sakan

ɗ

aya, biyu, uku... kafin Ishaq ya ƙaraso a hankali ya zauna a gefen sa.

"Kwana na nawa a asibitin nan?"

Ma'aruf ya katse shirun da sautin muryarsa da ya koma daidai, mai zurfi dake fitowa can kasa.

"Hu

ɗ

u, you were unconscious for three days

a Nigeria kafin mu taho."

A hankali ya ha

ɗ

iye yawu cikin maƙogwaronsa sannan ya ƙara tambaya.

"Me Baffa yace?"

"Ransa ya

ɓ

aci sosai, ransa ya

ɓ

aci fiye da duk yadda kake tunani, kullum sai ya kira waya ya tambaya idan ka farka, kuma yace da zarar ka da

wo hayyacinka mu koma gida."

Yaji lokacin da ya zuƙi numfashi ya fitar sannan ya koma da baya ya jingina da gadon bai ce komai ba, don haka shi ya cigaba da cewa.

"Mami kusan duk bayan awa guda take kira Ma'aruf, suna can ne amma hankalinsu anan yake, ko

wa ya damu, Hajiya tace hatta Abdurrahim jiya gidanka ya tafi ya kwana, dan Allah Ma'aruf, dan Allah ka taimaka ko don wa

ɗ

annan mutanen ka tallafi rayuwarka, dan Allah."

Kai tsaye maganganun suka shiga har wani waje dake can ƙasan zuciyar Ma'aruf, kuma ya

na jin yadda tasirin su ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinsa yana tafiya tare da gudun jinin cikinsu, sai kawai ya sake cusa yatsunsa cikin gashin kansa sannan ya runtse idanunsa.

Ishaq yana kallonsa, yana jin yadda tausayinsa ke bin zuciyarsa kamar kul

lum, ba sauki bane rayuwa da irin wannan cutar ya sani, ba sauki bane daurewa irin abinda ke zuciyar Ma'aruf din, ba sauki bane yadda yake iya daurewa abubuwa tsawon shekarun nan, ba sauki bane ba zama Ma'aruf din da yake gaba

ɗ

aya ya sani... Shi yasa fatan

sa a kodayaushe bai wuce Allah ya tallafi rayuwarsa ta wata hanya daban da take sabuwa ba, domin Allahn ya sani cewa su sun gwada duk wata hanyar da take a tunaninsu amma babu wani sauki.

Ya ha

ɗ

iye yawu a hankali cikin maƙogwaron sa yana cigaba da kallons

a yace.

"Nayi mana booking flight, gobe zamu koma."

Kuma ba don kallonsa yake ba ya tabbata ba zai ji sanda ya amsa da 'Allah ya kaimu' ba.

Saboda haka kai tsaye sai ya sake tambaya.

"Yaya kake ji?"

Ma'aruf yasa yatsu biyu ya shafo saman hancinsa har

a lokacin bai bu

ɗ

e idonsa ba yace.

"Ina ji ne kamar zan mutu saboda yunwa, nace ka taimaka min da abinci amma kana ta masifa, Idan na sake fita daga nan kar barni kawai kar kaje beli na."

Ba shiri wani guntun murmushi ya su

ɓ

uce a fuskar Ishaq

ɗ

in na tabb

as

ɗ

in da yake dashi cewar ya dawo daidai, don har abada irin Ma'aruf guda daya ya sani a duk tsayin rayuwarsa.

Ma'aruf yaji lokacin da ya fita amma duk da haka bai bude idanunsa ba, hoto

ɗ

aya ne ke yawo a cikin kansa, hoton

ɗ

akin bincikensa, yana hasko t

arin takardu da kuma hotunan da suke cikin

ɗ

akin nan, sannan yana hasko yadda hanya ta ƙarshe da yake tunanin zata kai shi ga nasara bayan shekaru hu

ɗ

u ta rushe har garinta, wanda takaicin haka shine sanadiyar tashin ciwon nasa da abinda yayi har suka taho

nan.

Wata jijiya daga gefen kansa ta bullutso cike da wani sabon takaicin da ya sake ratsa shi, sabon takaici... Don wannan

ɗ

auke yake da wani layi na fargaba da kuma tsoro, tsoron da bai taba ji a ransa game da ciwon nasa ba tsawon shekaru goma da suka

wuce, maganganun Ishaq suka sake haskawa a cikin kansa.

...idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya, kana gab da rasa hankalinka gaba

ɗ

aya Ma'aruf!

***

Alhaji Muhammad Mansour Bakori, sanannen mutum ne wanda yake da babban Kamfanin yin robobi

a garin Kano tare da ƙaninsa Alhaji Usman, wanda su biyu ne kacal a wajen iyayensu, mahaifinsu ya rasu shekaru da da

ɗ

ewa amma mahaifiyar su tana raye.

Alhaji Mansour Bakori yana da mata biyu da ƴaƴa goma sha

ɗ

aya, yayin da Alhaji Usman bai taba haihuwa b

a tsawon shekaru talatin da aurensa, wanda hakan ya faru ne sakamakon wani hatsari da yayi tun kafin tun yana saurayi har ya zame masa sanadin hakan, shi yasa kowa a danginsu yake girmama matarsa Hajiya Madina da kuma jinjina mata na zaman da take dashi a

duk shekarun nan alhali ita lafiyarta ƙalau.

Matan Alhaji Mansour biyu, Uwargidan itace Hajiya Maimuna, wata mata mai kirki da kuma alkunya,

ɗ

anta na farko Jamal ya rasu shekaru goma da suka wuce, daga shi sai Ma'aruf wanda shi a wajen kishiyarta ya girma

, sai Shukra, Munaya, Abdurrahim wanda shi tun yana shekaru biyu a duniya ya kamu da matsalar rashin magana amma yana ji kamar kowa, sai kuma autarsu Zahra.

Hajiya Kilishi itace mata ta biyu a gidan, wata mace ce mai tsananin kirki da kyautatawa, don fa

ɗ

a

ko da na rana guda bai ta

ɓ

a ha

ɗ

a su da Hajiya Maimuna ba tun zuwanta gidan, wani irin zaman lafiya da mutunta juna ne a tsakaninsu tun farkon zuwanta gidan, hakan yasa basu ka

ɗ

ai ba ko wanda yake nesa ba zai taba cewar su

ɗ

in kishiyoyin juna bane idan ya

gansu tare.

Ita ta raini Ma'aruf tun daga watannin da aka yaye shi har zuwa girmansa na yanzu. Hajiya Maimuna, mace ce mai hali irin na mutanen da, tsananin kawaici akan abinda suke ganin shine daidai, don haka tun daga ranar da Hajiya Kilishi ta kar

ɓ

e s

shi bata ƙara nuna cewa shi nata bane, a suna kawai Ma'aruf ya santa a matsayin mahaifiyarsa, amma a wajen Hajiya Kilishin da suke kira da Mami ya samu dukkanin wata kulawar da

ɗ

a ke samu daga mahaifiyarsa.

Ita ta raine shi da ƙarfin jikinta da kuma na zu

ciyarta, har zuwa girmansa kuwa ya zama tsakaninsa da Hajiya Maimuna gaisuwa ce kawai amma Mami ce komai

nasa, duk da ƴadda wasu daga cikin ƴanuwan Hajiya Maimunan suke nuna rashin jin da

ɗ

in su akan hakan a yanzu da ya zama shine ka

ɗ

ai namiji babba a gidan

.

Ƴ

aƴan Hajiya Kilishi biyar ne, dukkaninsu mata kuma dukkanninsu harafin sunansu ya fara ne da harafin S, Safiyya, Salma, Surayya, Samira da kuma Sahla kamar yadda take so, don a wajen Daddy babu ruwansa da ra

ɗ

in suna, duk wanda iyayensu mata suka zaba s

hi zai saka ba ruwansa. Zahra ce ma kawai taci sunan Inna Danejo 'Fatima' kamar yadda Hajiya Maimunan ta nuna tana so a saka.

Hajiya Maimuna ta sami matsalar shanyewar ƙafafu bayan ta haifi ƴarta ta ƙarshe Zahra, kuma babu irin maganin da ba'ayi ba a ƙasa

she daban- daban amma ba nasara, don haka a dole yanzu sai akan Wheelchair take yawo.

Gidan Alhaji Mansour dake unguwar NNDC quarters a garin Kano, ƙaton gida ne mai

ɗ

auke da bangare-bangare, akwai

ɓ

angaren iyalansa guda biyu wanda kowanne iri daya ne, ƙa

ton falo da

ɗ

akuna hudu kowanne da ban

ɗ

akinsa a ciki da kuma sauran wajaje irin Kitchen, store, courtyard da dai sauransu, sai bangarensa inda shine waje na farko a gidan mai

ɗ

auke da

ɗ

akuna biyu da falo da kuma wajen meeting

ɗ

insa inda yake ganin baƙi a g

ida.

Akwai bangaren boys quarters inda masu a gidan suke zaune sai kuma wajen Inna Danejo kakar gidan, wato mahaifiyarsu Alhaji Mansour inda itama take da ƙaton falo,

ɗ

aki

ɗ

aya da kuma toilet, sai

ɓ

angaren ƴan aiki, sai kuma bangare na karshe daga gefen h

agu na harabar gidan, wato bangaren Alhaji Usman da suke kira da Alhaji Baba, wanda shima da a gidan yake tare da matarsa daga baya sai ya siyi wani gida gaba dasu ka

ɗ

an ya koma, don haka wajen a ƙulle yake babu kowa.

Ishaq abokin Ma'aruf ne kuma

ɗ

an'uwan

sa, don da Mahaifiyar Ishaq

ɗ

in da Hajiya Maimuna iyayensu

ɗ

aya, asalin mahaifinsa

ɗ

an Kaduna ne kuma shi ka

ɗ

ai iyayensa suka haifa, mahaifinsa ya da

ɗ

e da rasuwa amna mahaifiyarsa sai da yazo matakin shiga Jami'a ne sannan Allah ya

ɗ

auki ranta, don haka da

shawarar Mami, Hajiya Maimuna ta tambayi Alhaji Mansour da kowa ke kira da Baffa, Ishaq ya dawo gidansu da zama daidai lokacin da Ma'aruf ke kokarin shiga Jami'a.

Mamin tayi haka ne don ganin ta samowa Ma'aruf sauki akan halin alhinin

ɗ

anuwansa da har a

lokacin bai gama warkewa daga ransa ba, don haka tare da Ishaq

ɗ

in Baffa ya

ɗ

auki nauyin karatunsu a wata Private University dake London har suka kammala, kuma hakan ya sanya shaƙuwa sosai a tsakaninsu duk da cewar

ɓ

angare daban-daban suka karanta. Ma'aruf

ya karanci harkar Kasuwanci ne yayin da Ishaq ya karanci

ɓ

angaren aikin lawyer kamar yadda yake da buri tun yana yaro.

***

Washegari...

No. 58 Mafara Street, NNDC Shara

ɗ

a Qauters.

.07:30 Pm.

Tun daga ƙofar gidan zaka gane cewar anyi wani taro ne a gi

dan an watse, don hatta gate din a bude yake gaba

ɗ

aya sannan ga motoci daga ciki suna kokarin fitowa.

Idan ka biyo ta cikin mutanen, zaka wuce ko'ina hanya ta kai ka har

ɓ

angaren Hajiya Maimuna inda taron mutanen yafi yawa musamman a ƙaton falon

ɓ

angaren

da zaka tarar wanda yake cike da tarin mutane gaba

ɗ

ayansu mata, kowa na zaune da abokin hirarsa yayin da ƙamshin turarukansu ya ha

ɗ

e da

ƙ

amshin dadda

ɗ

an abincin da aka gama ci a falon, don ga tarin plates nan wasu ma har da ragowar abincin sannan kuma a c

an gaban Tv stand na

ɗ

akin akwai wasu manya-manyan flasks cike da snacks kala-kala ga duk wanda yake so ya diba.

Sai dai duk wannan ba shine abin kallo a dakin ba, tarin akwatunan dake zube a makeken carpet din tsakiyar falon ne, an bu

ɗ

e kowannensu dake c

ike da kaya fal.

Lefen Babbar ƴar Hajiya Maimunan mace da suke kira da Shukra ne, amma ba zaka banbance adadin yawan ƴanuwan Hajiya Maimunan ko kuma na Hajiya Kilishi a falon ba, sun riga sun zama

ɗ

aya dukkanninsu don ko a sati biyu da aka karbi lefe biy

u na ƴaƴan Hajiya Kilishin Safiyya da Salma, duk sune dai a wajen, shi yasa a yanzu ma rabi hirarsu ta shirye-shiryen bikin da aka saka nan da wata guda mai zuwa ce.

Hajiya Kilishi ta ratso ta cikin mutanen, sanye take da wata doguwar rigar lace daya sha

adon stones sai wulgawar kyalli yake a cikin hasken fitulun dakin, ta karaso inda Hajiya Maimuna ke zaune akan kujerar Wheelchair dinta tana hira da wata ƴaruwarta, ta sunkuyo daidai saitin fuskarta sannan tace.

"Hajiya su Ma'aruf sun iso, yanzu na tura

Malam Sani (direba) ya

ɗ

auko su daga airpot, mukullin store dinki zan karba na ajiyemusu abinci

ɗ

azu, Hajiya Madina ce tace zata tafi nace idan direban nata ya sauke ta sai ya karasa ya kai musu abinci don na san baxa su shigo yau ba."

"Toh Alhamdlilah, M

uƙullin yana hannun Sameera ita ta karba dazu wai sun ajiyewa ƙawayenta abinci su ma."

Hajiya Maimunan ta amsa a hankali itama. Dukkaninsu sun sani cewa a duk tarin jama'ar gidan babu wanda bai san abinda Ma'aruf

ɗ

in yayi ba da kuma cewar baya ƙasar don l

abari baya taba

ɓ

uya, amma duk da haka gwara ace basu fallasa zancen ba duk kuwa da cewar duk ƴanuwa ne a gidan, amma hakan ba zai hana cece-kuce ba.

Daga nan

ɓ

angarenta ta nufa, inda babu mutane sosai, kuma ƴanmatan gidan da wasu kawayensu suka tare suna

ta hayaniyar da jiran a ragu don suma suje su bu

ɗ

e nasu babin kallon kayan. A falo ta tarar da Zahra da Sahla ƴan autan gidan kuma sa'annin juna sun baje litattafansu suna ta aiki kamar basu san da bidirin da ake yi a gidan ba, dama yayyensu sun riga sun

manna musu sunan Allazi boko 1 da kuma Allazi boko 2, don mayun karatu ne kamar ba gobe, yanzu suka shiga SS1 amma abinda suka sani ko Abdurrahim da yake SS3 bai sani ba, kwanaki har Surayya dake level three suka koyawa wani abu a Biology.

Har Hajiya Kili

shin zata yi musu maganar abinci sai ta kula da plate din snacks dake tsakiyar litattafansu, ta sana aikin Mama Rabi ne hakan, wata dattijuwa ma'aikaciyar gidan da har yanzu bata daina kula dasu ba kasancewar ita ta yaye su tun suna ƙanana.

Don haka ta am

sa sannu da shigowar da suka yi mata kawai ta wuce. Ta nufi kofar dakinsu Salma inda ƴanmatan suke, hayaniyarsu tun daga falon zaka ji ta, cike da raha da kuma nishadi kamar an fara bikin, kuma duka hirar da suke ta tsare-tsaren bikin ce da suka da

ɗ

e suna

yi tunda wannan shine karo na farko da za'a aurar da mata a gidan, kuma har guda uku a lokaci guda.

"A'a ranar kunshi ne fa za'ayi style iri daya, ranar Kamu kamar kowa zaiyi style dinsa ne ko?"

Muryar Munaya ta tambaya cikin hayaniyar.

"Ranar kunshi fa

shi babu anko Munaya kin manta ne kowa kayansa zai saka, da Kamu ne za'ayi har style

ɗ

aya."

Wata kawar Salma, mai suna Aysha ta bata amsa.

Hajiya Kilishi ta bu

ɗ

e kofar dakin daidai lokacin da Munayan ke gyara glass din idonta tana kallon wayar Sameera d

ake hannunta inda take ƙoƙarin banbace tarin atamfofi da kuma lesukan da zasu yi ankon dasu.

A ƙaton gadon

ɗ

akin gaba

ɗ

ayansu suke a baje dasu da tarin plate din snacks din da suke ci, sai wadanda basu sami waje bane suka zauna daga kan bedside drawers.

"

Ni fa wallahi gani nake kamar wata

ɗ

aya ba zai isa duk wannan shirye-shiryen ba."

Shukra ta fa

ɗ

a tana danna tata wayar.

"What?!" Salma ta mike daga kwance tana kallonta.

"... Ai Ya Shukra kar ma ki fara wannan zancen don wallahi Imran ba zai ta

ɓ

a yarda

a ƙara mana ko sati

ɗ

aya ba."

Salma ta fa

ɗ

a wanda hakan yasa dukkaninsu yin shewa a lokaci guda, don duk cikin amaren tafi kowa

ɗ

okin bikin, yayarta Safiyya ba ruwanta don ita dama ba mai magana bace tun farko, kuma wanda zata aura mai mata ne da ƴaƴan sa

biyu duk da cewar ba wani manyan ta yayi ba. Shukra kuma dake kan matakin masters dinta a bayyane yake cewa hankalinta yafi tafiya ga Project work din da take kan ga

ɓ

ar yi fiye da bikin, duk kuwa da irin rawar kafar da Suraj

ɗ

in da zata aura ke yi shi, w

anda dan wani abokin aikin Baffa ne.

Har Salma zata sake cewa wani abu Sameera dake gefenta ta daka mata duka, wani duka da idan zata yi

ɓ

aram-

ɓ

aramarta Mamin tazo wucewa suke yi mata shi, don haka a lokaci guda ta juyo ta kalli kofa inda Hajiya Kilishin

ke tsaye tana kallonsu da murmushi.

"Mami ina wuni..." Duka kawayensu na

ɗ

akin suka hada baki wajen gaishe ta don tun zuwansu basu ma ganta ba.

Da murmushin ta amsa musu sannan ta kira Sameera.

"Ina muƙullin store dinsu Munaya? Yayanku sun dawo yanzu,

kizo ki tayani mu debo abincinsu a saka a motarsu Hajiya Madina."

Da wani irin murmushi mai fa

ɗ

i Sameeran ta amsa, don Allah ya sani duk da kowanensu yayi waya dashi tun a jiya, da kuma hayaniyar gidan ta yau, suna cike da tunanin halin da Ma'aruf

ɗ

in ke

ciki, don abinda yayi wani abu ne da basu ta

ɓ

a gani ba tsawon rayuwarsu duk da sun san cewa kuwa yana da wannan cutar.

***

Mallam Aminu Kano International Airport

08:30 PM.

"Wata nawa aka saka bikin yaran nan ne Malam Sani?"

Ishaq ya tambaya a lokaci

n da yake kokarin saka jakar kayansu cikin boot

ɗ

in motar da Malam Sanin ya bu

ɗ

e.

"Wata

ɗ

aya aka saka wallahi, ai gidan ma har yanzu yana nan a

ɗ

inke, shi yasa Hajiya tace ba sai kunzo ba, kawai in wuce daku gida."

Ishaq ya gya

ɗ

a kansa yana rufe boot

ɗ

in

.

"Ai dama bamu da plan din zuwagidan nan yau, amma Lallai su Baffa sun shirya, har su uku ne fa a wata

ɗ

aya kawai."

"To ai rufin asirin Allah ake ciki kullum kuma shi ke rufawar." Cewar Malam Sanin yana dariya.

Duk maganar da suke yi, Ma'aruf na zaune

a cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login