Showing 42001 words to 45000 words out of 94381 words
mutanensa sai faman gaisawa yake dasu fuskarsa
ɗ
auke da
ɗ
imbin fara'ar da ya kasa auna nauyinta dana ku
ɗ
in sadakin auren dake cikin aljihunsa, dubu
ɗ
ari cif!
A cikin ƙwaƙwalwar sa lissafi yake cewar ko da kudin zasu iya ninka adadinsu sau
goma baya jin zai ta
ɓ
a iya bada ƴarsa aure ga mutumin da akace yana da matsalar ƙwaƙwalwa, tunda gashi tun a yanzu sun fara gani, in ba haka ba wane ango ne yake ƙin halartar wajen
ɗ
aurin aurensa?
***
Motar ta shigo kamfanin da saurin da ya saka maigadin
da ya bu
ɗ
e gate
ɗ
in juyowa yana kallonta, kuma duk saurin nata sai da ta isa ga layin da ake ajiyar motoci ta tsaya sannan ƙofar mazaunin direba ta bu
ɗ
e.
Ishaq ya fito sanye da wasu kaya kalar sararin sama, wayoyinsa rike a hannu ya rufe ƙofar sannan ya
tunkari cikin ginin dake kallo shi, wani gini mai hawa uku da yasha adon gilasai tun daga samansa har ƙasa. Security
ɗ
in daya bude masa ƙofa har sunkuyawa yayi bayan ya gane shi yana fadin.
"Yalla
ɓ
ai sannu da zuwa."
Kuma maimakon ya amsa sai kawai ya tam
baye shi.
"Ma'aruf yana ciki ko?"
"Eh tabbas, ai tun safe ya iso yallabai"
Jin haka yasa Ishaq
ɗ
in yin gaba zuwa hanyar matattakalar da zata kaishi sama, wata receiptionist (mai karbar baki) a wajen mai suna Rafi'at ta shiga gaishe shi tana murmushin da
ke manne cikin tsarin ayyukanta, kuma da mamakin yadda akayi bata manta fuskarsa ba duk da karancin zuwansa wajen ya
ɗ
aga mata hannu yana zarcewa zuwa saman.
A hawa na farko can ƙarashe ofishin Ma'aruf
ɗ
in yake, don yana tuna lokacin da yake gaya masa ce
wa ya canja office, ya isa ƙofar daidai lokacin da sakatariyar Ma'aruf
ɗ
in mai suna Martha ke fitowa riƙe da wasu files a hannunsa.
"Sannu da zuwa yallabai, yana tare da wasu baki ne a ciki, ko zaka jira su kammala."
Martha ta fada da murmushin dake nuna
masa da gaske take, kuma ya san lallai baƙin masu muhimmanci ne don babu ta yadda za'ayi ta tsaida shi idan ha haka ba.
Gyada kansa kawai yayi alamar ya fahimta sannan ya ƙarasa kofar ya bu
ɗ
e ta, idonsa ya gane masa wasu inyamurai biyu da kuma wani
ɗ
an c
hina, dukkansu suna zaune a kujerun dake tsallaken teburin Ma'aruf
ɗ
in, kuma budewar kofar tasa dukkaninsu suka juyo suka kalle shi, Ma'aruf na sanye da wani bakin yadi mai sealed
ɗ
inkin da ya fito da tsarin jikinsa, hular kansa ma baka ce data dace da shi
gar da ita kadai ya kamata ta tabbatarwa da Ishaq cewar abinda yake tunani tabbas haka ne, dama baiyi niyyar zuwa wajen daurin auren ba.
"Bismillah, ka shigo mana."
Ma'aruf
ɗ
in ya fa
ɗ
a yana kallonsa, sannan a lokaci guda ya maida kansa kan takardar dake
gabansa yana ƙarasa rubutun da yake yi, ya kuwa karaso cikin daidai lokacin da ya rufe takardun ya miƙowa mutanen tare da murumushin daya dace da fuskarsa.
Ɗ
aya daga cikin inyamuran ne ya karba tare da yin godiya kafin dukkanninsu suka mike a lokaci guda,
Ma'aruf
ɗ
in ma ya mike yana miƙa musu hannu,
ɗ
aya bayan
ɗ
aya suka gaisa kowanne da murmushi yayin da yake sake yi musu alkawarin cewar kar suji komai, suyi aikin da zasu yi kawai babu abinda zai gifta a tsarinsu.
Kuma watakila yanayin fuskar Ishaq
ɗ
in su
ka kalla don babu wanda yayi masa magana a cikinsu suka yi hanyar kofar suka fita.
"Wanne za'a kawo? Tea ko Coffee"
Muryar Ma'aruf
ɗ
in tasa hankalinsa dawowa daga rakiyar da yayiwa mutanen nan, ya juyo ya kalle shi.
"Kaima ka san ba abinda ya kawo ni ba
kenan."
"Na sani..." Ma'aruf ya fa
ɗ
a yana komawa kan kujerarsa.
"Shi yasa na tambaye ka hakan ai, don idan ka fara muryarka zata fi fitowa idan da abu mai zafi a kusa."
Sai kawai ya girgiza kansa, yace.
"Wane irin rashin mutunci ne wannan B? Ya za'ay
i ranar da za'a
ɗ
aura maka aure guda ka taho Office? Ka san tarin mutanen da suka neme ka a wajen nan?"
"Really? Ai da ka sani kawai su biyo bayanka ku same ni anan sai su ganni."
Wani irin abu ya sake tasowa Ishaq, sai kawai ya karaso gaban teburin nasa
ya zube wayoyinsa sannan ya kalle shi sosai yace.
"Abinda kake yi ba daidai bane Ma'aruf, me yasa ko sau
ɗ
aya a rayuwarka ba zaka yi abu irin na mutane ba? Ka nuna baka son auren nan da farko, daga baya kazo ka nuna ka yarda saboda Baffa, to idan haka ne
me yasa zaka kunyata shi a yau? Me yasa baka je wajen ba alhali ka san rashin zuwan naka zai iya haifar da wani abu?"
"Me zai haifar?" Ya tambaya alamun hankalinsa a kwance, kafin ya cigaba.
"Zai haifar da rashin faruwar auren ne? Kana tunanin akwai abi
nda zai saka Baffa ya canja maganarsa? Na gaya maka na yarda da auren ne saboda naga ba zan iya karewa ba, naga babu abinda zanyi wanda zai canja ra'ayinsa, yanzu ka gaya min da ban je ba ya fasa
ɗ
aurawa?"
Ishaq yayi shiru kawai yana kallonsa, sautin numf
ashinsa na fita da yawan da ya zarce daidai, don akan fuskar Ma'aruf din yake gane cewa abinda ya fada ba haka bane, dole akwai wani dalili daban da yake dashi game da auren nan, saboda abinda ya fa
ɗ
a da farko gaskiya ne.
Su biyun sun sani cewar wannan au
ren ba ƙaramin ha
ɗ
ari bane, abu ne da bai kamata ya faru ba, don haka ba saboda Baffa ya ture hakan ba ya sani, shi yasa babban tsoronsa shine abinda zai iya yi, don shi shaida ne akan tarin abubuwan da suka faru a baya, abubuwan da basa furtawa har yanzu
balle na ukunsu ya sani, abubuwan da ba wai sunyi shawarar
ɓ
oyewa bane kawai akwai su ne amma kamar babu su
ɗ
in.
Ya ha
ɗ
iye wani abu a ƙirjinsa yana jin yadda shakka da kuma tsoron abinda Ma'aruf din zai iya ke bin koina a jikinsa, bai san yarinyar nan ba,
bai ta
ɓ
a ganinta ba amma yana tausayinta tun yanzu, don ya san wani rauninta a rayuwa aka kalla aka ha
ɗ
a wannan auren, tunda a bayyane yake ga kowa cewar ba kowanne uba ne zai iya
ɗ
aukan ƴarsa ya bawa mutum irin Ma'aruf ba, kamar babu banbanci ne da ka tu
ra ƴar taka cikin dokar dajin da babu ranar fitowa.
Sai kawai ya zaro wallet
ɗ
insa daga aljihu, kuma har a lokacin Ma'aruf
ɗ
in na kallonsa da nasa idanun dake danne tarin abubuwan da yake dannewa, a cikin wallet din Ishaq ya zaro ID Card
ɗ
insa ya nuno mas
a shi, kuma da ganin haka Ma'aruf ya san me yake nufi, ya san cewa da gaske ransa ya
ɓ
aci, don rana ta ƙarshe da ya fito da ID card
ɗ
insa yana tuna masa cewa shi lawyer ne zai iya
ɗ
ora aikinsa sama da alaƙarsu shine ranar da aka kai Baffa asibiti saboda c
iwon zuciyarsa da ya tashi ta dalilinsa.
"Ban san me kake shiryawa ba Ma'aruf, amma na yarda cewa ba ka yarda da auren nan saboda Baffa ba, akwai wani abu da kake
ɓ
oye min..."
"Jamal ya san yarinyar."
A lokaci guda muryar Ma'aruf
ɗ
in ta katse shi yana k
allonsa.
"Me kace?" Ya tambaya idanunsa na shaida rashin ganewar.
Ma'aruf ya gyara zamansa, ya ƙifta idanunsa yana kallon Ishaq
ɗ
in sannan ya sake maimaitawa.
"Jamal ya san yarinyar Ishaq, so nake na san yadda akayi Jamal ya san yarinyar, wataƙila hakan
zai iya bani damar da zan iya gano mutanen da suka sa na kashe shi!"
Ya rufe bakinsa daidai lokacin da Faruk ya shigo Office
ɗ
in yasha adon wasu fararen kaya har da babar rigar, bakinsa a bu
ɗ
e yace.
"Wai da gaske baka je
ɗ
aurin auren ba?"
****
Kayan j
ikin Amina wani farin Lace ne wanda aka
ɗ
inka daga cikin kayan lefen, ta yafa farin mayafin da shima a cikin kayan yake, hannayenta sun sha ƙunshin da suka je har zoo road tare dasu Ummi suka yini ana yi,
ɗ
aurin
ɗ
ankwalin da Momi tayi mata yayi baya da yaw
a ta yadda hakan ya fito da gashinta ta gaba, akwai fararen awarwaro a hannyenta har da wani zobe mai kyalli ma.
Babu ko kwalli a idanunta amma ita kanta ta sani cewa kamanninta ba
ɗ
aya suke da sauran ranaku ba, watakila suna da kuma matsayin aure yana zu
wa ne da tasirin dake banbanta kowacce amarya da sauran fuskoki, don ita kanta ta sani cewar fuskarta tayi wani irin fresh da kuma kyan da kowa ke gani tare da fararen idanunta, fatar fuskarta har maiƙo take saboda yadda take tas babu ko
ɗ
igon ƙananun ƙura
jen da ta saba fama dasu.
"Fatee, ina gurasar? Jiranki fa muke yi!"
Wata Shukra
ɗ
aya daga cikin kawayenta a islamiyya ta kwallawa Fatiman dake can cikin hayaniyar tsakar gida kira, a cikin
ɗ
akin nasu ƴanmata me fal da suka ha
ɗ
a da kusan duka ƙawayen su n
a islamiyya da kuma na makarantar boko wanda duk a ƙoƙarin Fatima ne ta tattaro su, sannan ga su Ummi ma da tasu tawagar ƙawayen, don haka
ɗ
akin ya cika taf sai faman hayaniya suke wadda ke sajewa cikin tarin ta gidan gaba
ɗ
aya.
Don ko'ina a cike yake taf
da mutane sai faman rabon abinci kawai ake, babu wanda yayi tunanin za'ayi wannan taron, Amma bata taba lissafa cewa yawan wa
ɗ
annan mutanen zasu taru ba, amma ance wai biki dama ba'a masa gayya da kansa yake fallasa kansa, musamman ga su
ɗ
in da kusan duk
wanda suka mu'amalanta yana jin da
ɗ
in zama dasu.
A lokacin Maryam ta shigo
ɗ
akin riƙe da wani faranti da aka cika da ƙullin zobo. Ummi da tasha kwalliya cikin ankon atamfar nan tace.
"Yawwa Mary, matso ta nan, tun dazu dama Aunty Safiyya ke cewa mu jira
a kawo."
"Ta
ɓ
! Wallahi na wannan ƙawaye na ne suna can a dakin Aminu, plate nazo nema idan kun gama zan zuba gurasa."
"Au ba zaki bamu ba?"
"Waashi can fa ana ta
ɗ
iba a
ɗ
akin Amma, kuje ku
ɗ
ebo naku kafin ya ƙare don wallahi har yaje rabi."
Ummi ta miƙ
e da sauri tace.
"Mu nawa ne a dakin?"
"Ai kawai je ki
ɗ
ebo ashirin, in ma da saura ma kara." Cewar wata a cikin ƙawayen Aminan suna ƙyalƙyalewa da dariya gaba
ɗ
ayansu.
Ummi ta fita daidai lokacin da Fatima ta shigo rike da plate guda biyu na ban
ɗ
ashen g
urasar, Maryam kuma ta juya ganin ba zata samu abinda tazo nema ba.
"Wallahi kowa ya
ɗ
auke hannunsa kafin in ajiye." Cewar Fatiman ganin yadda kowannensu yayi shiri da hannunsa.
"Dalla malama ki ajiye kawai meye haka wai?" Cewar Shukra.
"Wallahi sai kow
a ya
ɗ
auke hannunsa, salon ina ajiyewa in rasa."
Ta fa
ɗ
a tana dariya, yayin da hayaniyarsu ta ƙaru kowa na fadin ta ajiye, ai kuwa tana dire farantin kafin ta mika nata hannun ta nemi gurasar ta rasa, sun wawushe ta tsaf suna ƙyalƙyala dariya, kuma yanayi
n fuskar Fatiman yasa Amina dake daga gefensu yin dariyar itama, lebbenta yayi talewar da har haƙoranta suka fito, don abu ne da ba yau suka saba ba, tun a makaranta sun saba irin wannan abin da an kawo abinci kawai wanda ya samu ya samu.
Kuma dariyar taj
i tana tafiya har ciki ƙirjinta, tana ta
ɓ
o wani abu da ya kamata dama ace yana nan, wannan farin cikin da mace ke ji a lokacin aurenta.
A cikin hayaniyar da
ɗ
akin ya ƙara ru
ɗ
ewa dashi Aunty Ma'u tazo ta kira ta, tana fita taga Aminu ne yazo da mai hoto, a
ka shiga
ɗ
aukar hoton kowa da ƙungiyarsa, Aminu na tsaye shine mai bada umarnin dake sa kowa yin dariya, don haka kusan duk a hotunan an
ɗ
auka ne Amina na dariya, tayi kyau a cikin kayan da suka zauna a jikinta sosai ga kuma skirt
ɗ
in kayan daya bu
ɗ
e ta ƙa
sa, ita kanta ta yarda cewa telan nasu Ummi ya iya
ɗ
inki ba'a banza suke ta yabonsa ba, kuma a kowanne hoto ita idonka zai fara gani saboda shigar kayan nata farare tas da kuma baƙin gashinta daya fito ya ha
ɗ
u da baƙin ƙunshin hannaye ta yana ƙara haska fa
rin.
Hatta Amma tayi kyau cikin shigar wani lace da ya dace da maman Amarya, itama tana ta dariyar da har ta mantar da ita haushin da zuciyarta ke ciki game da kayan jere da suka kai aka ƙi karba.
Ranar da su Tanti suka tafi za'a fara jeren nan, ranar zu
ciyarta ta sake yin baƙi game da al'amarin auren, don a waya Hajiya Kilishi ta kira tana gaya mata cewar ai su basu ce su kawo kaya ba, wai mahaifin yaron daya bada kudi ayi gyaran gida ya bayar har dana komai don haka su sun riga sun gama jeran su amarya
kawai suke jira.
Sai da ƙyar bayan Tanti ta dage cewar baza su kawo ƴarsu haka ba sai da abinda zata kalla itama ta san cewar iyayenta ne suka yi mata kamar kowacce ƴa, sannan Hajiya Kilishin tasa aka fitar da kayan gado guda daga wani
ɗ
aki suka jera nasu
, kayan Kitchen kuwa suka zube mata gaba
ɗ
aya don shi dama abubuwan da aka ajiye basu da yawa, sai a sannan ne zuciyar Amman ta
ɗ
anyi sanyi, amma har a wayewar garin yau bata dawo dai-dai ba sai a yanzu da Aminu ya saka ta yin dariyar dole.
Kuma duk yadda
bikin ya kai ga zuwa a ga
ɓ
ar da kowa ke ganin ba'a shirya ba, yayi mutuƙar yin da
ɗ
in da wataƙila ko da sun shekara ne suna tanadi haka komai zai kasance, banbancin kawai na farin cikin da za'a samu a zuciyoyinsu ne.
Wajen yamma, Adam ya kawowa Amina saƙon
wata sallaya mai kyau da kuma alƙur'ani daga Abdallah, a hannayenta Amina ta rungume ledar ba tare da tace komai ba, idanunsa kawai take hangowa a ranar da ta gaya masa aure zata yi, yana kallonta da yanayin da bata iya fassara shi ba.
"Dama na gaya miki
, ba wani son ki yake yi har cikin zuciyarsa ba."
Haka Fatima tace lokacin da ta gaya mata yadda suka yi, amma sai ta girgiza kanta ta bata amsa.
"Cewa yayi dama ya sani ba lallai ya iya aurena bane Fati, yace ya san ba lallai ni ko iyayena mu iya jurewa
tazarar dake tsakani na dashi ba."
Da yamma Fatima dasu Ummi suka sa ta canja zuwa wani material kalar ruwan madara, a lokacin kuma kusan duka ƙawayen nasu na nesa sun tafi sai mutum uku kawai da kuma wasu daga cikin ƙawayen su Ummi, kalar kayan ta ƙara
fito da hasken fararen idanunta, suka saje sosai cikin wani
ɗ
auri mai kyau da Momi ta sake yi mata.
"Kece amarya ta farko a wannan lokacin da naga anyi bikinta bata yi make-up ba Amina, Allah ya shirya miki halinki."
Cewar Momin sanda take
ɗ
aura mata
ɗ
an
kwalin, sai kawai tayi wani murmushi tana kallon ƙunshin hannunta yayin da wata ƙawarsu ta ke cewa.
"Amma kuma tayi kyan da wasu amaren ma da yawa basu yi ba, kin san natural look ƙarshe ne."
Da haka sai hirar
ɗ
akin ta koma kan kwalliya, kowa na fa
ɗ
in ko
a kwalliya simple make-up tafi kyau, wasu kuma na lissafo masu kwalliyar da ko heavy make-up
ɗ
in suka yi tana yin kyau. Ta sani itama da aurenta bai zo a karkace ba zata yi kwalliyar, amma babu kalar tanadin data shiryawa wannan, ƙunshin ma don su Momi su
n takura ne kuma ta san shine abinda kowa zai fara lura dashi akanta.
"Dama da kika ha
ɗ
a kayanki baki
ɗ
ebi wa
ɗ
ancan litattafan ba?"
Fatima ta tambaya daga gefenta sanda idonta ya kai kan wani kwali a can saman durowarsu na litattafan makarantar ta, litat
tafan da ta san ba zata taba rabo dasu ba, don kullum cikin bitarsu take yi.
"Maryam ce ma ta ha
ɗ
a kayan ai, ni ban san me da me ta ha
ɗ
aba, kawai dai tace min ta hada su ne tare da sauran kayan akwatunan."
"Allah yasa dai bata ha
ɗ
a miki da kayan sawa da
yawa ba, don yawa zasu yi miki idan aka hada da sababbin, gwara ita a ta
ɗ
an ƙara akan nata. Ina ledar su sallayar da aka kawo, bari na ha
ɗ
a na kaisu kusa da akwatunan, kar a manta."
Fatiman ta fa
ɗ
a tana ƙokarin miƙewa, sai dai kafin ta kai ga miƙewar Ami
na ta jawo hannunta da sauri, ta juyo ta kalle ta, idanunta sun ka
ɗ
a daga farinsu ta girgiza mata kai.
"Ki zauna kawai Fatee, ki bari ko anjima sai ki
ɗ
auko su."
Muryarta da ka
ɗ
an tafi