Showing 27001 words to 30000 words out of 190498 words

Chapter 10 - Buzu Book 1 Complete

gidana?" Tsuke fuska ya yi ya ce "Kamar yaya? Ya ka ke magana kamar wani shege ba kai ka haife ni ba? Gidan ubana na zo, kuma wurin 'yar uwata na zo"

"Ban yi maka iyaka da gidana ba? Ki na me ki ka bari ya shigo mini gida?" Yayi maganar yana kallon mama.

A ?ufule ta ce "Au to kokawa ka ke so na yi da shi? Ko saSa shi zan yi na jefa waje, tun da kai ka dawo sai ka fita da shi ai"

Ya sake kallon imrana ya ce "Ba magana nake yi maka ba? Ban hanaka zuwar mini gida ba?"

Cikin rashin Wa'a Imaran ya ce "Sai ka ce wani gidan kirki, to ka mayar da ni in da na fito, cikin uwata ta mayar maka da ni"

Nana ta ce "Imarana Baba ne fa"

"Shi Win, shekaru uku ba ka ga Wanka ba, da haka yakamata ya karSe ni komai girman laifin da na yi masa? Ba azabtarwa da ake yi mana ne ya tilasta mini barin gidan nan ba"

Gaddafi ne ya shigo, bayan dawowarsa ya jiyo hayaniya daga cikin gidan ya shigo, domin duba abin da yake faruwa.
Shi kansa mamaki ne ya kama shi, ganin Imran a gidan.

Baba kamar ya fashe da kuka ya ce "Imrana ni ka ke gaya wa haka? Ka tashi ka fita ka bar mini gida na ce maka"

"Idan na bar gidan shege nake, wallahi sai na gama kwanakin da zan yi. Ke Nana ga jakata nan zan je na dawo.

Nana ta tashi ta Wauki jakar, ta nufi Wakinsu da ita, Baba ya daka mata tsawa ya ce "Bashi jakarsa ya bar mini gida"

Cikin kuka Nana ta marairaice ta ce "Dan Allah Baba ka yi ha?uri, tun da ya ce idan ya gama kwanakinsa tafiya zai yi. Shekara uku ban ganshi ba, dan Allah ka yi ha?uri"

"Au Nana kin fi son Wan uwanki da ni ko? Amma yana sane da mu, ya kama gabansa ya tafi gantalinsa har shekaru uku, yana gararamba bai waiwayo gida ba, sai yanzu saboda ya mayar da ni Wan iska zai dawo mini gida?"

Imaran ya nufi Nana, ya karSi jakarsa, ya kaita wani Wan lungu ya ajiye, ya fice ya bar gidan. Shi kansa Gaddafi kasa magana ya yi, saboda tsagwaron zunzurutun tsageranci kawai yake iya ganowa a cikin idon Imran Win.

*****

"Hajiya Sa'a aiki ya lalace fa"

"Ban gane ba, kamar yaya?"

"Akwai wani hatsabibin shaiWani a tattare da yarinyar nan, ya lalata mana aiki gaba Waya. Ba a samu adadin jinin da ake bu?ata a jikinta ba"

Dafe kai Hajiya Sa'a tayi, ta ce "Yanzu mene ne abin yi, ka ce akwai sa'a a tattare da yarinyar yanzu babu wata dabarar kuma? Yarinyar ce wata irin majanuniya, har kaya na bayar a kai mata, babu yadda ban yi a sake kawo mini ita gidan yarinyat Safiyya ba, dama a can na ganta wai ta ?i yarda. Ni kuma na abin na je gidansu ba, ba na son zargi da saka ido"

"Aikuwa neman mafita ya ganki, domin wani ba?in sheWani ne a tattare da ita, babu lallai ya bari wani ya raSe ta, saboda wasu dalilansa, 'yar aiken tamu ma ya ?ona ta. Yanzu dole ki san yadda za ki yi, a sake ba ta maganin zamu sake tura wani Wan aiken"

Hajiya Sa'a ta jinjina kai ta ce "Amma, ba yadda za ayi a samo jininta nata, dole sai an bata wani abin ta ci?"

"Eh dole ne, idan ba haka ba babu ta yadda za a samu jininta, ba zai bari a tunkare ta ba. Kuma ko ba haka ba, idan ba ta hanyar abincin da za a bata ba, ba kowane aljani zai iya raSarta ba, saboda tana zama da alwala, kuma tana adduo'i shi kansa aljanin jikin nata, ba ?aramar azaba yake sha ba. Dan haka yanzu ko dai a samu jininta ta wannan hanyar ko kuma ki janyo ta ?ungiya"

Hajiya sa'a ta ce "Ba abu ne mai sau?i ba hakan, muguwar miskila ce, ba kamar 'yar uwatta ba, da Wayar ce ko nan ka ce na kawo maka ita, zan kawo ta, amma babu komai zan san abin yi, dole ha?ata ta cimma ruwa"

"Babu laifi"

****
A hankali jikin Nana ya ci gaba da yi mata raWaWi, tamkar ana kunna mata wuta, ta daure ta din ga nanata suratul jinn, tun daga farko har ?arshe a zuciyarta.
Imaran ne ya dawo bayan sallar isha'i, hannunsa ri?e da ledoji.

"Nanawo, sannu ya jikin?" Yayi maganar bayan ya ja kujera ya zauna.

"Jiki Alhamdilillah"

"Kai Nasiru Waukko faranti" yayi maganar yana kallon Nasir.

Ya je ya Waukko faranti, ya zazzage musu gurasa da nama fal a kai.

Ya kalli Nana ya ce "Ina Jamila ne? Tun da na dawo Suwaiba kawai na gani, ko an yi mata aure ne?"

Nana ta ce "A'a tana ma?wabta"

Ya tsuke fuska ya ce "Har bayan sallar isha'i, kamar gidan ubanta?" Yana rufe baki ta yi sallama.

Sai dai ta tsaya da ta ga Imaran, ta ce "Imran dan Allah kai ne ko gizo idona yake yi mini?"

"Ban sani ba, tun la'asar ba kya gida kina can kina gantali a gidajen mutane"

"Haba ai ka bari mu gaisa, ina ka tafi shekara uku ba wanda ya san inda ka ke?"

"In da ki ka aike ni. ware ki wanko hannu ku zo mu ci abinci"

Ta ce "Yanzu ma kuwa"

Cikinsu ya shiga, suka rufarwa gurasar, yana kallon Nana, da ?yar take ci. A haka Gaddafi ya shigo Waukar abincin dare ya tarar da su.

Imran ya kalli Nana ya ce "Wai ba za ki ci ba ne?"

"Imrana ba a Webarwa Baba ba, Mama ba a bata ba"

Haushi ne ya kama shi ya ce "Wallahi ba zai ci ba, da na zo ko ruwan gidansa ya bani, ba kora ta ma ya yi ba? Kar Allah ya sa ki mayar da hankali ki ci"

Abinka da 'yan uwa, haka suka kewaye Imran.

Jamila ta ce "Wai dan Allah tsawon wannan lokacin, ina ka tafi?"

"Duniya na shiga mana, tun da an kore ni an ce ba a bu?ata ta a gidan"

Baba yayi sallama, suka amsa masa gaba Waya.

"Imarana ban ce ka bar mini gida ba wai?"

"Wallahi Baba ba zan bar gidan nan ba, sai na gama abin da nake yi"

A fusace Gaddafi ya ce "Wai kai baban? ka ke yi wa magana a haka?"

Imran ya kalle shi ya ce "Kai kuma ina ruwanka da ni? Kai a yaya ne baka yi masa magana, ya taSa korarka ne? Ka ga tun da na zo ban kula ba kar ka shiga harkata ehee"

A fusace Gaddafi ya yo kan Imran, Imaran ya mi?e tsaye ya ce "Wallahi yanzu ba da ba ce, wallahi ka taSa ni sai na soka maka ?arfe".

Baba ya tare Gaddafi ya ce "Rabu da shi, kar ya yi maka rauni, alamu sun nuna haryanzu yana shaye-shaye"

"Wallahi Baba ko uban me yake sha, dai-dai nake da shi, ka bari na sauke masa tsagerancin da yake kansa"

"A'a gara dai ya ri?eka, dan wallahi ka taSa ni sai na buga ka da ?asa ba abin da ya dame ni" ya kaWe rigarsa ya fice.

Nana ta dafe kanta, ta rasa abin da yake yi mata daWi, tun tsaowar su Baba ba sa shiri da Imran ko kaWan, tabbas a baya babu wanda suke tsoro sama da Gaddafi sun daku a hannunsa, saboda ya ce babar su ce ta yi sanadin da aka saki babarsa, kuma har ta mutu Baba bai dawo da ita ba.

Ta yi alwala ta yi sallar isha'i ta kwanta, ba dan tana jin bacci ba.

Kwanciyarta ke da wuya, ta lumshe idanaunta, ta lula duniyar tunani, ta buWe idonta domin juyi ta gyara kwanciyarta, kawai ta ganta a bakin wani ruwa a zaune.

Ta Waga kai ta waiwaya, ba kowa a wurin, sai dogwayen bashiyu koraye shar, ruwan gabanta kuma sai tambal-tambal yake yi tamkar zai yi ambaliya.

Ta kalli jikinta, ta ga babu kaya a jikinta, sai wani Wan mayafi da aka rufe mata ?irjinta, zuwa al'aurarta.
Jikinta duk ya Wuri ruwa, ya kwaile saboda ?una.

Ta yin?ura za ta ja ?afafuwanta, ta tashi ta gansu Waure a jikin sar?a.

Free pages na daf da ?arewa. Contact me to subscribe yours.
Ayshercool
08081012143
BUZU
YOTA/002
AYSHERCOOL

P10

Ta waiwaya jin maganganun su Suwaiba, a kusa da ita, har su na faWa a kan charger, amma ba ta ganinsu sai ita ?wal a wurin.

Ta rintse idanunta, tana faWin "La haula wala ?uwwata illa billah"

Ji ta yi an taSa ta, ta buWe idonta tana tsammanin ganinta a Wakinsu, amma ta ganta dai a wurin a zaune.

Ya dur?usa ya kwance sar?ar ?afarta, sannan ya kalleta, ba ta iya kallonsa, duk da a suffar mutum ya bayyanar mata, duk da dogwayen yatsunsa masu Wauke da za?o za?on farata sun fallasa bambancin da yake da shi da bil adama.

"Kalli jikin ki, kalli irin raunukan da suke jikin ki, saboda azabar taurin kan ki da dan halin ki zan bi, da sai dai ciwon nan yayi ajalinki"

Nana ta Wan kalle shi, ta kawar da kanta ta ce "kai ne fa ka yi mini raunin, da tartsatsin wutar da ya din ga fitowa daga bakinka"

Ya dube ta ya ce "Ba zan yi miki irin wannan illar ina sane ba, kafofin da za a din ga zu?ar jininki ake so. Ina sake jaddada miki ki karSi abin da ?addara ta zana miki. Ni hadiminki ne zan zama mai biyayya a gare ki, idan kuma ki ci gaba da bujirewa zan ci gaba da azabtar da ke, dan rayuwata ba za ta salwanta a banza a kan ?o?arin kare ki da baiwarki ba, ba wannan aikin na karSi yi daga wurin kakaninki ba".

Ta Wan Wago ta ce "Wani irin aiki ka karSa a kaina, kuma meyasa ka dage lallai ni zan yi harkar bori? Kai ba ka ga ilimin addini ya yawaita ba yanzu? Su ma na yi imani da Allah, rashin ilimi ne ya sanya su ka yi wannan harkar. Kuma duk sauran mutanen dangin babu wanda za ka matsawa ya yi harkar shirka sai ni?"

"Ba ni da lokacin da zan tsaya yi miki wani dogon bayani, amma ina mai tabbatar miki tashin hankali da masifun rayuwa yanzu a ka fara, ko ?afa ba ki saka ba domin ba ayi komai ba".

Nana ta ce "Abin da Allah ya ?addara ya zai same ni ne kawai zai faru da ni, na zan taSa yadda da duk wata tatsuniya da za ka karanta mini ba"

"Shikenan, ba na bu?atar dama ki yarda, zan cire hannuna na ja da baya na zura miki ido, da kan ki za ki neme ni".

"Da ni da kai duk bayin Allah ne, dan haka babu yadda za ayi na nemi taimakon ka. Ko da ka tare mini wani abu, Allah ne ya tare mini kai sila kawai za ka zama" Ta yi maganar cike da ?warin gwiwa.

Yayi mata shiru, ya juya ya kalli ruwan nan, ya fara fito da wata ba?ar iska daga bakinsa yana hurawa ruwan. A take iskar ta dinga tafasa ruwan har da tururi. Ya kwantar da Nana, ita kuwa ta zuba wa sarautar Allah ido.

Ya ce "Maganin da matar nan ta baki ki ka sha, ta samu damar tsinka wata jijiya a mararki, shi ne ki ke wannan fitsarin jinin kuma sun samu sun tara, duk da bai ishe su ba.
Wannan ciwon na jikinki, ba ?onuwa ba ce ramuka suka yi miki, jininki na zubowa ta ramukan sai dai ba za su iya amfani da shi ba, saboda yana jikin fatarki ne kuma ba za su iya raSarki a haka ba" Nana jin sa kawai take yi, ba wai dan tana yadda da maganganun na sa ba.

Ya din ga Webo ruwan tekun nan, yana zuba wa Nana a jikinta. Ta rintse idanunta tana jin yadda wani irin zafi yake ratsata har cikin ?ashinta.
Ya zira hannunsa a cikin bakinsa, ya zaro wata doguwar allura, ya shammaci Nana ya caka mata a mararta. Ta kurma ihu sai da gaba Waya dajin ya Wauka.

A zahiri kuwa, tun da ta lumshe idonta, jikinta yake rawa ha?oranka suna karo da juna, idanunta suka kakkafe.

Su Jamila suka fito suka bar mata Wakin, zuba mata ruwan nan da ?aisar yake yi, a zahiri ihu take yi.
Gaddafi ya je ?ofar Wakin ya tsaya yana bala'i.

"Wallahi ko ki rufe mana baki, ko na yi miki mugun duka, dan abin naki zunzurutun iskanci ne na za ki hana mutane bacci ba". Amma a banza dan ba ta san ma yana yi ba, sai wani irin gurnani da take yi kamar an yanka sa.

Ya nufi wurin da aka sayo ice aka ajiye, ya samo wata sanda dai-dai lokacin ta fito daga Wakin za ta fita waje.
Babu tausayi babu imani, ya fara shirga mata icen nan a jikinta.

Nasiru tun da Nana ta fara wannan gurnanin, ya fita majalissar da ya ga Imarana, ya ce masa ya zo ya ga abin da Nana take yi, zuwansu yayi daidai da dukan da Gaddafi yake yi wa Nana.

Imran ya hankaWe shi ya ce "Kar ka sake dukanta, wani irin azzalumi ne kai, da wanne za ta ji? Dama abin da ku ke yi mata kenan" hankaWe shi Gaddafi ya yi yana ?o?arin sake dukan Nana, Imran ya Waukko ?aton itace a murhu yana wuta yayi kan Gaddafi zai jirga masa gadan-gadan.
Da ?yar Baba ya raba faWan ya ce "Gaddafi na ce ka daina dukan yarinyar nan, tun da ka ga nima na saduda ba ciwon ?arya take yi ba, ba ta da lafiya da gaske. KuWin auren da na ce yaron nan Saleh ya kawo, su nake jira mu kaita can in da ka ke ba ni labarin nan, amma tun da abin ya kai haka ma dole ko rance ayo a kaita wannan jaraba ta ishe ni.
Kai kuma jarababbe Wan nema, kai ba aljan ba amma ka fi sheWan shaiWanci, wallahi aljanun Nana sun fiye mini hatsabibancin ka nesa ba kusa ba Imrana."

Imran bai kula Baba ba, ya dur?usa ya Wago Nana, matsanancin tausayinta ya mamaye zuciyarsa.
Suka ci gaba da hayaniyarsu, shi kuma ya mayar da hankali kan tofa wa Nana ayatul kursiyyu, a fuskarta.

Mi?a ta yi a hankali, sai kuma ta ri?e hannunsa tana ajiyar zuciya.

"Nana"

"Na'am Imran, ka tsaya a kusa da ni, tsoro nake ji"

"Na sha gaya miki, ki daina jin tsoro, kar wani abu ya din ga ba ki tsoro. Babu wani abu da ya isa ya cutar da ke sai abin da Allah ya ?addara zai same ki" Ta jinjina masa kai, tare da ?ara jin ?warin gwiwa.
Ya Waukko ruwa pure water ya bata ya ce "Yi bismillah ki sha ruwa" ta karSa ta yi bismillah ta fara sha.

Ta kammala sha, ta ce "Alhamdilillah"

"Amma Nana ki na addu'a kuwa?"

Ta jinjina masa kai ta ce "Eh"

"Lamarin nan yana damuna Nana, da kafin na tafi kamar abin ya lafa miki"

"Eh, tun da aka saka mini rana ta farko abin ya dawo, har zuwa yanzu"

Imran ya ce "Ba komai akwai Allah"

"Imran" ta kira sunansa a hankali.

Ya amsa da "Na'am"

"Tun da ka tafi, ka je wurin babarmu ne?"

Tsuke fuska ya yi ya ce "Ai ni da sake zuwa in da take har abada"

Cike da damuwa Nana ta ce "Saboda me? Mahaifiyarmu ce fa, ni ko a waya ba na samunta, ga Baba ya hana duk wata hanya da za ta sada ni da ita"

"Nana, ki yi focusing a kan rayuwarki. Duk duniya babu wanda dan ya cire hannunsa daga rayuwarki za ki kasa rayuwa. Uwa na haifar jariri ma, ta mutu a take ya girma ya rayu, balle ke da wayon ki da girman ki, ki ci gaba rayuwarki kawai. Ta fi son mijinta da yaran da ta haifa yanzu a kanmu, ban da haka ai ya kamata ta waiwayo mu, ta ji halin da muke ciki, amma tana can tana rayuwarta cikin kwanciyar hankali"

Hawaye na bin idon Nana ta ce "Ba haka ba ne Imran, babarmu tana sonmu, Mijin da take aure ne ba ya son mu je in da take, nan ma idan ta zo ka san Baba wula?anci zai yi mata".

"Kin ga mu bar wannan maganar, ki je ki yi alwala ki nemi wuri ki kwanta kawai" fafur Imran ya ?i yarda su ci gaba da maganar.

*****

Buzaye ne su uku, zaune a cikin jeji, mai Wauke da manyan bishiyu, iska sai kaWawa take yi. Dukkaninsu sanye da rawani. ShikaWai ne a gefe, ya zuba shayi a kofi , yana sha yana lumshe idanunsa, alamar yanayin yana yi masa daWi.

Cikin damuwa Habu ya ce "Souley, na rasa abin yi, kaina ya kulle fa"

Souley ya ce "Nima hakan take Habou, anya ba za ka mayar da shi Nijar ba, tun da an kasa samun magani?"

Da sauri Habu ya girgiza kai ya ce "A'a, ba zan mayar da shi Nijar ba yanzu, akwai wani mai magani da na ji labari, har kwantar da mutane yake yi, ina jiran cikakken adireshin gurin ne, shi ma za mu jarraba"

"To ai ni tsoro nake ji ne Habou, kar a garin yawon neman maganin nan a samu mushikila, ka na kallo kullum abin nasa babu wani ci gaba, duk in da aka je sai dai ace mana babu mafita. Kawai ka tsinci mutum ka yi ta wahala da shi, ka je in da ka tsinto shi ka mayar da shi kawai mu huta"

Habu ya kalli Sule cike da takaici, kawai ya tashi, ba tare da ya sake tanka masa ba ya nufi in da Wayan yake.

"Taso mu tafi" yayi maganar yana kallonsa.
Sai dai bai motsa ba, ya ci gaba da tsiyayo shayin da yake cikin buta yana sha.

Habu ya mi?a masa hannu, ya sake cewa "Taso mu tafi" sai a lokacin ya Waga kai ya kalli Habu, ya ?arasa shanye shayin, ya tashi tsaye.

Sule ya ce "Habou kalli fa ko magana a 'yan kwanakin nan ba ya yi, sai a shafe kwana da kwanaki bai ce komai ba, haka zamu ci gaba da wannan aiki haka?" Habu bai tanka masa ba, ya ri?e hannunsa suka yi gaba.

*****
Dawowar Imran gidan malam Isa, ya sanya kullum cikin rigima ake da shi, kullum sai sun yi faWa da Baba ko Gaddafi.
Ba ya kwana a gidan, amma garin Allah na wayewa zai zo. Nana ta samu afuwa sosai da dawowar Imran. Saboda ba ta taSa zama da yunwa, sau ukun nan sai ta ci abinci a rana.
Sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login