Showing 96001 words to 99000 words out of 190498 words

Chapter 33 - Buzu Book 1 Complete

shi kuWi ya sake ta, sai dai ban san meyafaru ba na kira shi Win a zahiri, ban kira shi ba na kasa tunawa, ni dai kawai na ganshi a mafarki ban ma san meyafaru ba kawai na farka na ji tamkar an sha?e ni, da ?yar nake numfashi"

Malam Gambo ya yi shiru ya ce "Kuma ka tabattar ba ka yi maganar da shi a zahiri ba?"

"Wallahi na kasa tunawa"

"Hakan na nufin da akwai matsala kenan, ka Wan bani lokaci zan yi bincike"

Cikin damuwa ya ce "Zuwa yaushe kenan? Ni fa duk abin da za ayi sai dai a yi, fatana kawai burina ya cika"

"Kar ka manta burin naka ba Waya bane ba, kar ka manta bayan burinka na son haska taurarinka, na mallakar dukiya mai tarin yawa da kujerar siyasa, akwai burinka na son kawar da babban amininka, idan ka yi wasa za mu yi jifar gafiyan Saidu, dole ka tattara hankalinka a kowane Sangare, muddin ba ka dur?usar da shi ba, taurarinka ko sun haska ba za ka taSa shan gabansa ba, dan haka ka kula da kyau"

Ya yi ajiyar zuciya ya ce"Na fahimta, shi ma ba mantawa na yi da nasa Sangaren ba, shi ma na shirya komai, amma ina sauraren ka abin da binciken naka ya baka sai ka sanar da ni. Dan ko ya kama na zubar da jininsa ne zan yi domin na samu cikar muradina"

"Ka dai dakata, zuwa lokacin da zaka ji daga gare ni tukuna"

Da ?yar ya lallaSa Alhaji Zailani ya kwantar masa da hankali.

*****

Cikin tsananin tsoro da razani Jamila take kallon hajiya Sa'a, jikinta na wata irin tsuma cikin faragaba da tashin hankali. Yawun da za ta haWiye ma ya gagare ta, saboda tsoron da ya mamaye ta.

"Jamila, na gaya miki sirrinmu, idan kin ga dama ki yi shiru da bakin ki, ki tara arziki ki bar shi, idan kuma kin so ki fallasa, ba ki da hujjar kare kanki, kuma sai na ?arar da zuriyar ku, ta hanyar bayar da jinin ku Waya bayan Waya.
Abin farko da nake bu?ata ki taimaka mini, shi ne mu na bu?atar jinin yayar ki Nana, a baya na sha baki abu ki bata, ba tare da kin san dalilin hakan ba, to yanzu na gaya miki abin da nake so. Dan haka za ki taimake mu muma"

Jamila na jan numfashi da kyar cikin rauni ta ce "Amma ba za ta mutu ba?"

Safiyya ta ce "Ke ina ruwan ki da zata mutu ko ta rayu, idan aka so har babanki za a iya nema ki bayar, to dan dai wannan da ba uwarku Waya ba"

Hajiya sa'a ta Waga mata hannu ta ce "?yale ta, dole za ta ji banbarakwai abin, ina ga sai dai mu sanya ta a wani Sangaren, tana da tsoro sosai da sosai. Yanzu dai ki fara yi mana wannan aikin tukuna"

Jamila cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Hajiya a canza mini wani, tausayinta nake ji" har maman khairat ta hasala za ta yi kan Jamila da masifa, hajiya Sa'a ta Waga mata hannu. Ta dubi Jamila ta ce "Ba fa kashe ta za a yi ba, Wan kaWan muke son jinin nata"

"To ai ta yi aure, babanmu ya aura mata wani buzu" ta yi maganar hawaye na cika mata idanu.

"Eh na san ta yi auren, na ga duk kin tsorata kin damu, bari na kawo miki lemo ki sha" ta tashi ta ?iftawa maman khairat ido, ta fice daga Wakin.

Ba a jima ba ta dawo da lemo a cikin glass cup, ta mi?a wa Jamila. Jin sa da sanyi, ya sanya ta karSa kai tsaye ta fara sha. Sai dai tun kafin ta gama shan lemon, jiri ya fara Wibar ta.

Maman khairat ta karSe kofin lemon, Jamila kuma ta silale, cikin fita hayyaci.

Suka sassaki labulaye, suka kashe fitila, duhu ya mamaye Wakin, ta kunna kyandira, ta bawa maman khairat ta ri?e mata, ta Waukko wata jakar fata ta zazzageta.

Wani irin tarkace ya zubo daga ciki, tare da layoyi, ta cire wa Jamila kayan jikinta, ta din ga sha mata wani irin mai jawur da shi. Bayan ta gama ta Waukko wata allura a cikin wata laya, ta sokawa Jamila a wuyanta. Aikuwa ta zabura jikinta ya yi wata irin girgiza. Ta juya bayanta ta kuma soka mata a ?eyar ta. Nan ma jikin nata ya sake girgiza.
Ta sake saita ?ahon zuciyar ta, ta sake soka mata. Jikinta ya din ga tsuma ba tare da ta tsaya ba. Hajiya sa'a ta din ga karanto wasu abubuwa cikin wani irin yare, jikin Jamila na ci gaba da rawa tamkar ana girgiza ta.
Ta kama hannunta, ta saka mata wasu awarwaraye, sannan ta kawo wani bargo ta rufe ta da shi.

****

Tamkar mujiya haka Nana take zaune a Wakin nan, duk abin duniya ya ishe ta, yamma tana yi ya Wauki radiyo ya fice ya bar ta a Wakin ita kaWai.

Ta tashi ta kwance kayan da Ummi, ta yi mata sayayyar su.
?an kayan shafe-shafe ne, da turaruka sai under wears, duk da masu arha ne Nana ta ji daWi sosai da sosai.
Duk da tana jin haushinta, amma ta san idan ba Ummin ba, babu wanda zai tsaya tsayin daka ya yi mata wannan abin. Ta haWa da na gurin Hajiya Amina, duk ta jere. Ta janyo drower mudubin, ta ga burshes ne da comb a ciki. Ta mayar ta rufe.

Ta janyo jakar kayanta, ta buWe wardrobe Win, ta ga Sangare Waya sha?e da kayansa, sai da abin ya bawa Nana mamaki.
?angare Waya ta jere kayanta, ta tsaya tana kallon kayan, duk da galibi wanda hajiya Amina ta ba ta ne, ba ta san lokacin da murmushi ya suSuce mata ba. Ta daWe tana burin ganin kayanta a cikin wardrobe. Dan a gida, a wata tsohuwar adakar kakar su take zuba su, ?arewa wataran talauci ya ishi Baba ya ce ta zazzage kayanta, ta ba shi. Haka ta ba shi ya sayarwa 'yan gwangwan ya sayo mata viva ya bata wai ta zuba kayan a ciki, tun da tsummokaran nata ba su da yawa. Daga baya ta koma zubawa a kwalaye, daga ?arshe dai Jamila ce ta samo mata ghana must go ta bata, take saka kayan ta a ciki. Amma yau ga kayanta a wardrobe, kuma kaya kusan set goma sha uku, sababbi da tsofaffi, ga atamfofinta uku da ba a kai ga Winkawa ba.
Ta ninke bargonta, da bedsheets da Shukura ta bayar a bata, ta saka su a saman wardrobe Win.
Drower ?asan wardrobe Win kuma, ta saka takalmanta guda biyu, da jakar gidan sarkin baka, da pad Win ta. Ta gyara kan katifar ta Wame ta da bedsheets. Ta tashi tsaye tana kallon katifar, ita ma tsawon rayuwarta a kan wani tsohon bargon Baba take kwana, shi ma dai na kakar ta ta ne, bargon nan tamkar ya koma audigarsa saboda tsufa, amma yau albarkacin aure, ga ta da ?atuwar katifa.

Wani murmushin ne ya sake suSuce mata, ta juyo kawai ta yi karo da shi a tsaye a bayanta.

Ba ta san lokacin da ta ?wala ihu ba, dan sam ba ta ji alamun mutum a bayanta ba.
Kuma kasancewar ta ?ure da jikin katifar, razanar da ta yi, sai ta faWa kan katifar.

Taku Waya ya ?ara, ya tsaya a kanta yana kallonta.

Ayshercool
08081012143

29

?ara rikicewa ta yi, ta kasa tantance abin da take gani daga cikin idanunsa.

Ya sauke rawaninsa, ya saka hannu a aljihunsa, ya Waukko wayarta ya ajiye mata a gefen ta. Tashi ta yi zaune tana kallon wayar, gaba Waya ta manta ma tana da wata waya, a ina ya samu wayata? Ta tambayi kanta.

Ta bi wayar da kallo, ta kasa taSa ta. Ya sake zura hannunsa a cikin aljihunsa ya ciro wata roba, ya ajiye mata, ya juya ya fita. Sai da ya fita ta Wan samu ta nutsu, ta kai hannunta ta Wauki wayar ta duba ta ga a kashe take, sai ?amshi take yi. Ta kalli robar da ya ajiye mata, dabino ne fal a cikin robar lubiya.

Gefe kuma ga kwanukan abinci, fulasan kawai ta kalla ta san daga gidan Hajiya Amina suke.

Tana cikin tunani, ta ji sallamar mace. Ta amsa tare da kallon ?ofar Wakin. Wata mata ce ta shigo, Nana ta yi mata maraba, ta shimfiWa mata sallaya ta zauna.

Bayan sun gaisa Nana ta ce "Ban gane ki ba"

"Eh ai ba ki sanni ba, a nan baya muke, aka ce ai an kawo amarya na ce bari na zo mu gaisa"

Nana ta ce "Allah sarki, dama da mutane a nan haka? Shiru nake jin unguwar duk da jiya na zo"

Matar ta ce "Eh, ai a nan baya nake, sunana na Haulat, amma kin je kun gaisa da mutanen gidan"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ai ban san da mutane a gidan ba"

Haula ta ce "Ai ba su fiye zama bane ba, kullum cikin yawo suke, amma yau ko gobe za su dawo."

Zuwan Haulat sai ya Webe wa Nana kewa, su ka yi ta hira.

Sun daWe su na hirar, sannan ta yi wa Nana sallama, ta rako ta har bakin ?ofar Wakin ta ce "Idan na fara fita, nima zan kawo miki ziyara"

"To shikenan, ai a nan baya muke"

Nana ta ce "Kuma da gidaje a gurin? Na ga duk kangwaye ne?"

Haula ta ce "Gamu kuwa, akwai gidaje a gurin"

"Allah sarki, to na gode sosai ki gaida gida"

Yana zaune a kan benci, yana shan shayi a cikin Wan ?aramin kofin nan nasu, Nana ta jima tana mamakin kofin da suke shan shayin nan, tamkar wasan yara. A ganinta sai mutum ya sha goma bai ?oshi ba.
Tana hango shi su na fitowa da Haulat, ya rufe fuskarsa.
Ta zo za ta fita ta tsaya tana gaishe shi, amma ya yi shiru, kuma bai Waga kai ya kalle ta ba, ta fita.

Sai da Nana ta ji babu daWi, haryanzu ita ba ta ga wata alama ta hauka a tare da shi ba, kuma jiya ya yi magana ba kurma bane ba, tsagwaron wula?anci ne ya sanya sai a yi masa magana amma ya yi shiru.

Da daddare ma, zuwa ya yi ya saka ta a gaba, yana kallonta yana kallon kwanukan abincin da ba ta san waye ya kawo ba, ta san dai na gidan Hajiya Amina ne.

Haka ta zuba masa ya ja gefe ya sauke rawaninsa ya ci abinsa, sai dai da ya gama ci, yake Waukar kwanon da ya ci abinci ya fita ya wanko ya zo ya ajiye. Abin da ta lura da shi, shine mutum ne mai tsafta sosai.
Ita dai tana gefe sai dai ta saci kallonsa, sai dai ?asan zuciyarta tana mamakin yadda yau ba ta jin bugun zuciyar, sai dai sanyi da take ji.

Bayan ya ajiye kwanukan, ya tashi ya kwance rawanin sa, duk da wayarta take Wan dannawa, sai da ta saci kallon gashin kansa, kawai ta ji tana son ya ware shi, ta ga adadin tsawonsa.
Ya rage kayan jikinsa, ya Wauki radion sa, da kayan shayinsa ya fice daga Wakin.
Yana fita ta ja ajiyar zuciya, ta tashi ta shiga banWaki, ta yi wanka ta wanke bakinta, tayi alwala, ta fito ta shirya ta kwanta.

A iya saninta, wayarta take Wan duddubawa tana tunanin yadda aka yi ya samu wayarta.

"Amarya ba kya laifi, ko kin kashe mai gida?"

"Meye haka wai?"

"A ina?"

"Ni fa yanzu matar aure ce, ya zaka din ga kawo ni nan, duk lokacin da ka ga dama?"

Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Ina ruwana da auren ki? Auren jeka na yi ka? Auren da haryanzu ba ki da tabbas a kansa? Haryanzu ba fa ki san me ki ka aura ba, kuma kamar an ce ma mahaukaci ne ko?"

A ?ule Nana ta ce "Ko ma dai mene ne ina ruwan ka? Zan gano da kaina, koma wane ne, idan ma mutum Win ne ko akasin haka"

?aisar ya ce "Jiya fa ki ka zo nan ki na yi mini kuka, ki dai san iya abin da yakamata ki yi, da inda yakamata ki tsaya kar allura ta tono garma"

"Eh, haushi ka ke ji na yi aure, ba tare da tsammaninka ba, balle ka sake hanawa"

Kawai ?aisar ya bushe da wata irin dariya, da sai da ta tsorata ya ce "Ke haryanzu ba ki san ina ki ka dosa ba, ni ba jinnil ashi? bane da zan hana ki aure, na baya ma mazan naki ne ba su yi mini ba, duk da wannan ma da na farga da wuri sai na ruguza shi, sai dai idan na matsa za ki iya rasa rayuwar ki baki Waya, shi yasa na ?yale"

Nana ta ce "Saboda me?"

"Kawai" ya bata amsa.

"Amma wai da gaske aljani yana auren mutum?"

"Eh"

"To ku ina naku matan ku ke auren na mutum?"

Ya ce "To ai ni ba aljanin soyayya ba ne ba da za ki tambaye ni."

Nana ta ce "Amma ka hana ni aure? Me yasa ka saka Saleh ciwon ciki?"

"Ke ko duk matan bil'adama sun ?are zan auri masifaffiya ne mai azabar taurin kai kamar ke ne?"

"Eh abin nan ne, da ake cewa makaho ga ido, ya ce wari yake, na fi ?arfin ka ne kawai"

Ya ce "Ko?"

"Eh mana, dan Allah ka gaya mini ya ake yi ku ke auren bil adama"

"Ni ma ban sani ba, sai dai zan baki wani littafi ki karanta, soyayyar Aljani Ridwan, da bil adama" Nana ta zabura ta ce "Dan Allah, ya sarkin baka, a wane hali yake yanzu? Kuma ni ba littafin soyayya nake so ba, wannan littafin na Jaddul jinn nake so ka bani na ?arasa karantawa"

"Ba zan bayar ba, kuma ba wannan ne ya sanya na kira ki ba, duba jikin mudubi, ki zo ki gaya mini abin da ki ka gani"

Nana ta ce "Wallahi ba zan kalla ba, masifa da bala'i kawai ka ke nuna mini a cikin mudubin nan, Allah ya sa ya tarwatse...

"Wallahi sai kin kalla, wata?ila zuciyar ki ta saduda, ki yi abin da ya dace"

Kawai ta ganta a gaban mudubin, Jamila ta gani a kwance tsirara, Hajiya Sa'a na ta tsira mata allurar nan. Tsigar jikin Nana ta tashi, ta rintse idanunta ta ce "Dan Allah me take yi mata? Jamila ce fa"

"?warai ita ce, Matar ta umarceta ta kawo mata jininki, ta ce ba za ta iya ba, shi ne ta bi ta bayan gida, yanzu haka ta gama mallake ta, duk abin da ta ce ta yi shi za ta din ga yi, ba za ta taSa kaucewa maganar ta ba"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu ya zan yi, kar ta cutar da Jamila, shiyasa ni tun farko ba na son yawon ma?wabtan nan da take yi. Wannan matar ba ita ta bayar da Muhsin ba?"

?aisar ya ce "?warai ita ce, kuma ba wannan ba, bayan cin moriyar ganga, yada ?wauron ta za ta yi. Ba wannan ba bayan Walibin ki da ki ka rasa, babansa ma an sako shi gaba, wata?ila nan kusa ko nesa kaWan ya bi Wan nasa".

"A'a ba gaskiya ba ne ba ?aisar, hakan ba zai taSa yiwuwa ba"

"Dama ai ba gaya miki nake yi domin ki yadda ba"

Ta Wan yi shiru cikin jimami da tashin hankali, ta ce "Yanzu meye abin yi, ba na son Jamila ta faWa ga halaka" ta yi magana cikin kuka.

"Kin fi ni sanin abin yi ai Nana Asma'u"

"A'a ban da wannan, wannan ba mafita ba ce ba, na gaya maka ba zan yi wannan ba"

Ya ce "To shikenan, sai ki zura ido mutane na cutuwa alhalin ki na da yadda za ki yi, ki taimaka musu"

"A'a ?asair" kawai ta ga tamkar ya wurgota waje.

Ihu ta saka ganin tana faWowa daga sama, za ta faWa cikin ruwa. A razane ta tashi tana faWin "Ya Allah" ta dafe saitin zuciyarta tana haki.

Ita kaWai ce a cikin Wakin, ta janyo wayarta ta duba lokaci, ta ga uku da rabi na dare. Ta yi shiru domin tuna abin da ya razanata daga baccin, amma ta kasa, kawai faWowarta daga dogon tsaunin da libararyn ?aisar zuwa ?asan ruwa ta iya tunawa.

Ta kalli Wakin, fitila a kunne, amma ba ya ciki.

Ta tashi a hankali, ta nufi ?ofar Wakin, ta le?a harabar gidan.

Yana kwance a kan benci, yana bacci ya tada kansa da hannunsa. Gabansa Wan murhun dafa shayinsa ya mutu, ga butar shayin da kofinsa.

Wasi-wasi ta shiga yi, a kan ko tashin sa za ta yi. Wutar gurin ce ta Wauke gaba Waya, gurin ya gauraye da duhu, aka yi wata irin wal?iya mai hasken gaske, kawai ta ga wannan tsohon a tsaye a kansa.
Tamkar an dasa ta, ta kasa motsi ta kasa gaba ta kasa baya, aka sake wal?iyar nan, ta sake ganin tsohon nan a tsaye a kansa, sai dai wannan karon ya feso wani irin tartsatsin wuta da ya tilasta mata yin baya cikin matsanancin tsoro.

A hankali ta buWe idonta, kawai ta ganshi a tsaye yana kallonta, kamar taSaSiyya haka ta zura da gudu, ta koma kan katifa ta kifa kanta tana haki, saboda tsoro da razani. Maganganun ?aisar suna nema su fara zama gaskiya a kan mutumin nan. Tabbas ta fara tantamar kasancewar sa mutum. Duk da ta san ba ta da cikakkiyar lafiya ?aisar ya saba tsorata ta, amma ya za a yi a ce mutumin da ta hango yana bacci, cikin abin da bai fi ?ifta ido sau biyu ba, ta gan shi a gabanta.
A Sangaren sa shi ma mamaki yake yi, me take yi a tsaye a bayan labule a wannan tsohon dare haka?.

*****
Hajiya Sa'a ce take kallon Jamila, tana wani irin mugun murmushi ta ce "To jamsy me ki ka ce yanzu?"

Jamila ta ce "Ta yaya zan samo miki jinin nata?"

"Yauwwa Jamila, ba wani abu ne mai wahala ba, magani zan baki a abinci, ki kai mata ta ci, sai kuma abin da za ki ajiye mata a Waki"

Jamila ta ce "To shikenan, babu damuwa an gama"

"Kin tabattar za ki iya?"

"Eh mana, me zai hana?"

Hajiya Sa'a da Maman Khairat suka kalli juna, suka she?e da dariya, Hajiya Sa'a ta ce "Yauwwa jamcy, zan gaya miki duk yadda za a yi " Jamila ta gama wuninta a gidan, sannan ta tafi gida. Sai dai gaba Waya ta din ga jin ta wani iri, tamkar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tattare da ita.

****
Tamkar bakin mama ya taSo ?eyarta, haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login