Showing 141001 words to 144000 words out of 190498 words

Chapter 48 - Buzu Book 1 Complete

yi ta yi mata nasiha, har aka yi sallar la'asar. Su na yin sallar la'asar, su ka ce za su tafi, saboda kar su yi dare a hanya.

Nana ta ce "Bari ya dawo daga masallaci, sai na raka ku" Duk s karSi lambobin wayar su, su ma suka karSi ta ta.

Suka shirya tsaf za su tafi, Nana ta fito ta tarar ya dawo daga masallacin.

Ta ce "Sayyid, za su tafi zan raka su ko bakin titi ne, su hau adaidaita sahu, su je tasha".

Ya ce "Bari mu je tare"

"Idan mutanen gidan su na neman ka fa?"

"Wata ta ?one a gidan, sun tafi kai ta Asibiti"

Nana ta waro ido, ta ce "Wace ta ?one?"

"Ban sani ba, kawai na buWe gate sun ce mini za su Asibiti, wata ta ?one da ruwan zafi"

Nana ta ce "Ikon Allah, Allah ya sauwwa?e."

Su Adda Saude, su ka fito, suka tafi raka su tare da Sayyid.

Su na tafe su na ci gaba da yi musu nasiha, a bakin titi, suka tarar musu adaidaita sahu. Nasiru dama tun da ya raka su, gida ya koma saboda zai je makarantar Islamiyya.

Nana ta tambayi mai Napep ta ce "Nawa za ka kai su tasha" hararta Buzu ya yi, ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu, ya bawa mai adaidaita sahun.

Ya sake Waukko ba?ar leda, ya ajiye wa Anty Fati a kan cinyar ta, ya ce "Mun gode sosai"

"A'a ba zamu karSa ba, Wawainiyar ta yi yawa"

Nana ta ce "A'a Anty Fati, ba zai ji daWi ba. A ce ina gaida Mama, ina kewar ta sosai da sosai" ta yi magana idanunta na cika da hawaye.

"A'a Nana, kar fa ki je ki zauna ki yi ta koke-koken nan, idan haka ne, za mu daina zuwa"

Ta goge hawayen ta ce "Na daina, ku gaida gida"

Sai da su ka ja motar su ka tafi, sannan su ka dawo gida.

Nana ta zuba masa Abinci, ya ce "A'a ba na jin yunwa yanzu"

"Sayyid ina jin daWin yadda ka ke mutunta 'yan uwana idan sun zo, kuma na ji daWin yadda yau ka yi magana da su, har ka yi raha, har cikin zuciyata na ji daWi sosai da sosai. Allah ya nuna mini 'yan uwanka haka, zan yi iya yi na, na kyautata musu nima, Allah ya sa su amince su karSe ni a matsayin Waya daga cikin ahalainsu".

"Na ji kin ce a gaida Mama, mamanki na nan ta bari, a ka aura miki ni?"

Ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ba ga Maman nawa nan ka gani ba, ranar da mu ka je duba Baba?"

"Ba maman ki ba ce, kuma ko mamanki ba ta so na, ba za ta din yi mana irin kallon da waccan matar ta yi mana ba. Amma wannan da su ka zo, na ga su na murna sosai da sosai da ganina, har suka yi mana addu'a, duk da ban san me yasa ki ka yi kuka ba da suka zo"

Nana ta haWiye abu mai Waci da ya tsaye mata a wuyanta, ta san yanzu ba ta da wani mutum mafi kusanci da ita, sama da shi, dan haka babu bu?atar Soye masa komai, dan haka ta numfasa ta ce "Tabbas ba Mamana ba ce wadda ka gani a gidanmu. Mamana sun rabu da Baba, tun ban fi shekaru tara ba. Ba komai nake iya tunawa ba, kawai dai na san Mama ba sa jituwa da dangin su Babanmu, su na yawan samun saSani. Har dai suka rabu. Ta ce Baba ya bata mu, ni da yayana amma ya hana ta. Ba ta daWe da rabuwa da shi ba, ta yi wani auren. Abin ya Sata wa Baba rai sosai da sosai, ya ce kamar ta sane ta kashe auren dan ta fita ta auri wani, wanda ta aura Win kuma an ce ya taSa son ta, ba ta aure shi ba.
Adda Saude ta zo ta Wauke ni ta ?arfin tsiya, ta tafi da ni, amma da ?yar na kwana a gidan da Mama take, mijinta ya ce sai an fita da ni. Abin dai duk babu daWi, aka sake mayar da ni gidan Baba. Na fi shekara bakwai ban ganta ba, ina kewar ta sosai da sosai" ta yi maganar tana fashewa da kuka.

Ya rungume Nana a jikinsa yana shafa bayanta a hankali.

"Ki daina kuka, za mu je mu ganta in sha Allah, ke gara ke a kan ni ai. Ban sani ba ma ina da maman ko ba ni da ita, ni ke kaWai na sani"

Ya jima yana rarrashinta, sannan ta Wan tsagaita da kukan da take yi. Ta fara buWe kayan da suka kawo mata. Ba masu tsada ba ne ba, amma ta yi ?o?ari. Bedsheet kawai biyar ne, huWu na gida, Wan waje Waya. Ga kwanuka har da kayan sakawa.
Sai da ta bari an kira magariba ya fita, sannan ta sake fashewa da kuka, ta yi kuka sosai sai da kanta ya fara ciwo,? sannan ta ha?ura ta yi shiru.

*****

Jikin Shukura ya yi kyau, ta warware, wannan kumburin duk ta sace, aka rubuta mata sallama.
Doctor Sharif ya sha jinin jikinsa, dan sai da ya tsorata ya fara wasi-wasin ko dai Shukura ta san abin da ya aikata mata, saboda yadda ta canza gaba Waya. Wasa da dariyar ma da suke yi, gaba Waya ta daina, da ya shigo sai ta tsuke fuska. Sai dai wani sashi na zuciyarsa ya din ga ba shi, kawai yanayin da take ciki ne, na rasa Wan ta da ta yi, ya sanya duk ta canza ta daina walwala.

Hajiya Amina ta dube ta, ta ce "To Shukura yaya? Gidanki zan mayar da ke, ko gida za ki taho?"

"Mummy mu je gida na Wan huta tukuna"

Sagir ya harari Shukura ya ce "Mummy, a dawo da ita kawai, ke ma ki huta da Wawainiya tun da ta samu lafiya"

Su na cikin mujadalar, Alhaji Zailani ya kira waya, ya ce "An sallame ku ne ko kuwa? Ya ce mini yau za a sallame ku"

"Eh, an sallame mu, ta ce gidan zata taho, mijinta ya ce ta koma gida"

"Saboda me? Ta koma ta yi masa me? A dawo mini da 'ya ta gida ta huta, kafin ta koma, me za ta je ta yi masa da yanka a jikinta".

Hajiya Amina ya ce "A'a kar a yi haka, mijinta ne fa"

"Ni kuma ubanta ne, ki ce masa na ce a kai mini 'ya ta gida ta huta, idan ba za ki faWa ba, ni zan kira shi"

Sagir yana ji yana gani, haka ya ha?ura, aka mayar da Shukura gida, maimakon gidansa.

****

Nana ta kira su Adda Saude, suka tabattar mata da sun je Bauchi lafiya, ta yi musu bangajiya.

Yana ta shirin kwanciya, Nana kuma ta ?ura masa ido, zuciyarta ta yi mata nauyi, ba ta jin daWin komai.

Ya zo kusa da ita, hannunsa ri?e da kofi ya mi?a mata. Ta saka hannu ta karSa, tana kallon sa.

"Na ga ba ki ci abinci ba, madara ce na kuma karSo miki"

Ta buWe kofin, ta kalli madarar, da wani ba?in abu a kai.

"Habattussauda ne a ciki, ko na fara sha ne?" Ya yi magana yana mi?a hannunsa zai karSi kofin.

Ta kafa kai, ta fara shan madarar, sai da ta shanye ta ajiye kofin.

Ta dube shi ta ce "Me yasa ka ke bani madarar nan?"

"Na ji wani likita ya faWa a radiona, yana ?ara wa mata lafiya sosai"

Ta Wan yi murmushi, sannan ta numfasa ta ce "Sayyid, da gaske ?abilarku, ba sa auren macen da ba ta su ba?"

Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sannan ya ce "Duk abin da zai fito daga bakina a yanzu, ?arya zan yi miki, saboda ba zan iya tuna komai a kan ?abilar tamu ba"

Cikin rawar murya ta ce "To yanzu idan Allah ya sa ka tuna waye kai, da asalin rayuwar ka, ni mece ce makomata? Za ka karSe ni a matsayin matarka kuwa?. Idan kuma aka samu akasi ka manta da ni baki Waya fa? Yaya zan yi? Mece ce makomata?"

Ayshercool
08081012143
41


Ya yi shiru yana nazarinta, hawaye ya wanke mata fuska, har cikin ranta maganganun da suke fitowa daga bakinta. Tabbas! Tambayoyin nata a kan hanya suke, kuma sun cancanci ta samu amsar su, amma ta yaya zai bayar da amsar abin da shi kansa bai sani ba?

Ya dake ya tattaro nutsuwar sa, ya Wago fuskarta, su ka haWa ido.

"Ba na so, ganin wannan na Waya daga cikin abin da yake tayar mini da hankali, na rasa nutsuwa, hawayen ki zafi yake haifar mini a zuciyata, kuma yau wuni ki ka yi kuka" ya yi maganar yana share mata hawayen da yake kan fuskarta.

"Sayyid ka bani amsa, zuciyata ta cika da tsoro da fargaba, da kuma wasi-wasi"

Ya sassauta muryarsa ya ce "Ma vie. Idan har tunawa da rayuwata da waye ni, zai sanya na manta da ke a cikin rayuwata, ina fatan na dauwwama ba tare da na tuna waye ni ba. A jikina ina jin rayuwar da nake yi tare da ke, ita ce rayuwa mafi aminci da kwanciyar hankali. Ba ki yadda ba da na ce miki rayukanmu na cikin na juna ba? Muddin ruhinki na yawo a doron duniya, ba zai taSa barin ruhina cikin nutsuwa ba, saboda abokan rayuwa ne"

"Sayyid"

"Duniyata"

Wani kyakyawan murmushi ne ya suSucewa Nana, ta ce "Kalaman ka na ?ara mini ?warin gwiwa, har ba na son na ji muryar ka ta Wauke ko sau Waya"

"Da gaske?"
Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya sumbaci goshinta yana murmushi, mai ?ayatarwa.

Sai da zuciyarta ta motsa, wani irin shau?i ya mamaye ta, ji take tamkar ta furta abin da take ji a cikin zuciyarta, amma ta danne, sai kallonsa da take yi.

Ya ce "FaWi mana, ki furta"

"Me zan furta?"

"Abin da yake zuciyar ki, da ki ke son faWa" ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"A'a, ruhina ne a jikinki fa, ko in gaya miki abin da ki ke son cewa?"

Ta girgiza kai alamar a'a. Ya saki wani irin murmushi, mai cike da ?asaita yana kallon fuskarta.

Haka ya sakankance, ya tattara duk hankalinsa da lokacinsa a kan Nana, sai da ya mantar da ita damuwar da ta shiga, wani nannauyan bacci, ya sace ta.

*****

Hajiya Sa'a ce take mita iya yin ta, "Wallahi Jamila, ban da yayan ki ne ya yi miki wannan dukan, da sai na rufe shi, wannan ai take ha??in Wan Adam ne. Tun da kin kai shekaru goma sha takwas, ai kin sa abin da ya dace da rayuwar ki".

"Wallahi haka Mama ma ta faWa, da police station za a kai shi, Baba ya yi ta bata ha?uri, nima na ce kar a kai shi, ta yi ha?uri"

"Saboda me ki ka hana a kai shi, ai gara a kai shi, ya san cewa ke da shi akwai bambanci yanzu"

Jamila ta ce "Kaii babban yayanmu ne fa Mummy"

"Shi Win fa, shi ba dukan ki ya yi ba?"

"A'a ai bai kamata ba, da kunya abun"

"Ke Jamila, kalle ni da kyau. Irin wannan lamarin, dole ki sakawa kowa tsoron ki idan ki na son ki zauna lafiya ki taka duk wanda ki ke so. Ba a tausayi ba kuma a tuna danganta kan ki kawai za ki kalla, ki gina rayuwar ki. Babu wani abu da dangantaka ke ?ara wa banda koma baya da hassada da fitintinu"

Jamila ta jinjina kai ta ce "Haka ne"

"Dan haka duk wanda ya yi yin?urin taSa ki, ki yi maganinsa kawai. Ni zan fita ba daWewa zan yi ba amma"

"To a dawo lafiya" Jamila ta yi maganar tana kashingiWa a jikin kujerar 3 seater da ke Wakin.

Har bacci ya fara Waukar ta, ta ji ana sallama, ta buWe idonta ya ce "Yi ha?uri na tashe ki, Mummy ta fita ne?"

Ta jinjina masa kai tana ?o?arin mayar da kai ta kwanta.

"Ta daWe da fita ne?"

"A'a"

Ya ce "Ok thanks " ta mayar da idonta, ta lumshe shi kuma ya Wan ?ura mata ido, kan ya fice.

****
Alhaji Zailani na zaune, yana jiran ta gama haWa tea ta ba shi, kiran wayar Hajiya Sa'a ya shigo wayarsa. Ya Waga su ka gaisa. Ta ce "Zailani, matarka ta fi ?arfin ta je duba Hanifah a Asibiti, har an sallame su sun koma gida"

"Dan Allah ki daina kamabama abu, wane irin fin ?arfi, ni na je, su Rauda su je, maman su ta je, duk bai isa ba? Ba ta da lafiya ne, mu na ta yawon asibiti"

"Ba ta da lafiya me ya same ta?"

Ya ce "We are expecting another Muhsin in sha Allah, cikin yana ta ba da matsala ne yana neman ya fita, so an bata complete bed rest ne, kin ga ba zai yiwu ta din ga yawo ba"

Hajiya Sa'a ta Wan yi jimm sanan ta ce "Yayi Allah ya raba lafiya"

Uwargidan sa da ke ?o?arin haWa masa tea kuwa, ji ta yi tamkar ta kurma ihu. Da ta ji batun cikin Fadila, kuma wani namijin ne. Ita nata yaran biyar duk mata ne.

"Ya dai lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallon ta.

Ajiye masa tea Win ta yi, ta bar falon saboda takaici, dan kuwa ji ta yi, tamkar ta watsa masa shayin a kansa.

Ya karya abin sa a nutse, yana yi yana communicating da mutane ta waya.

Tashi ya yi zai je ya duba Fadila, dan ba a gurin ta ya kwana ba, kuma ba ta jin daWi sosai. Sai dai ya ji tamkar an Wora masa dutse a kansa, kuma an saka igiya an Waure shi. Ya yi mi?a ko zai ji dai-dai, amma ya kasa jin ya dawo normal.

Ya lallaSa ya fita, kansa na sara masa ya nufi sashin ta. Ya yi iya ?o?arin sa, bai bari ta fahimci wani abu ba, saboda kar ya ?ara mata damuwa, ya zauna har su ka yi hira, sannan ya fita.

****
Ya na zaune yana kallon Nana, ta na ta fafutukar yin breakfast, saboda ?o?ari meatpie ta tsiri yi da safen.

Ta kammala ta zuba masa nasa, ta haWa masa tea. Ta zuba masa ido. Ya saka hannu ya Wauka ya kai bakinsa ya ci, ya yi murmushi ya sake kaiwa bakinsa.

Ta ce "Da daWi?"

Ya Waga mata babban yatsansa, alamar jinjina.

"To ka ce Allah ya yi mini albarka"

Murmushin sa ya ?ara faWaWa ya sumbaci goshinta, sannan ya shafa gashinta ya ce "Allah ya yi albarka"

"Amin Shugabana" ta yi maganar tana dariya.

"Ga Nonon can a kan mudubi, ki fara sha kan ki karya"

Ta tsuke fuska ta ce "Nonon ra?uma dai ba nawa ba" A tare su ka tuntsure da dariya, har ya kusa ?warewa, ta Waukko ruwa ta ba shi ya sha.

Ta ce "Ba ruwana, kar ka ?ware ka ce ni ce"

Duk da ba ta da cikakkiyar masaniyar dalilin ba ta Nonon ra?umin, amma ta fara jin daWin sa sosai da sosai a jikinta.

"Sayyid, bari na kaiwa ?awata ko za ta ci"

"Wa?"

"Yusra" ya jinjina kai. Ta fita ta shiga cikin gidan.

Ko da ta yi sallama, a falo ta tarar da Siyama, hannunta duk ya ?one, a Sare mata ?unar.

"Sannu ina kwana?"

Ta kalli Nana ta amsa ciki-ciki. Ba ta sake bi ta kan Siyama ba, ta haye benen. ?akin Yusra ta shiga da sallama.

Yusra ta Wago, amma ba ta amsa ba. Ta ganta a zaune a kan gado ta yi tagumi, amma tana ganin Nana ta saki murmushi.
Nana ma ta yi mata murmushi ta ?arasa ta zauna a kusa da ita ta ce "Yayata, kin tashi lafiya?"

Yusra ta ce "Lafiya ?alau"

"Abinci na kawo miki, ko kin karya?" Ta ce "A'a"

"To ga wannan" ta saka hannu biyu ta karSa ta ce "Na gode" Nana ta din ga yi mata hira, har ta cinye meatpie Win.

Ta Wan numfasa ta ce "Dan Allah Nana, kema ki na jin kin gaji da duniya, idan ki ka ga wu?a ki ji kamar ki cakawa kanki, ko ki faWo daga saman bene ki mutu? Irin duniyar babu daWi Win nan?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Sosai, na taSa yin?urin kashe kaina ma, amma addu'a nake yi sosai da sosai. Ina ro?on Allah ya kiyaye ni. Kuma nake yin alwala sosai nake zama da ita"

"Kin tabattar idan na yi hakan zai daina ji, idan na yi addu'a Allah ba ya karSa, salla ma kamar ba daidai nake yi ba." Nana ta rufe mata baki ta ce "Ki daina faWar haka, nima da ina wannan tunanin amma na yi ta istigfari. Allah ya na karSar addu'armu, ba dan haka ba da wata?ila haukacewa zamu yi gaba Waya"

Yusra ta ce "Haka ne, wallahi na ji daWin zuwan ki gidan nan, duk kin san me nake ji, kuma kin san abubuwan da nake ji ba ?arya nake yi ba"

"Ai kamar yadda na gaya miki ne, mukaWai mu ka san abin da muke ji. Ki daina damuwa sai kowa ya san halin da ki ke ciki, an fahimce ki an daina cewa ?arya ki ke yi. Idan an kai ki gurin likita ya baki magani, ki din ga sha. A gefe kuma ki din ga addu'a ki na fatan Allah ya yaye miki"

Ta girgiza kai ta ce "Ba na son maganin likitan nan, bacci suke saka ni, kuma ba na iya baccin sam, sai dai jikina ya mutu, kuma damuwa ta ?ara yi mini yawa". Nana ta din ga rarrashinta da ba ta ha?uri.

Sun yi hira sosai, sannan ta ce za ta raka Nana bakin ?ofa.

Su na tafe ta ce "Kin ga Siyama ta ?one ko? Tana shiga kitchen za ta juye ruwa a flask, na she?e mata shi a hannunta. Nana ta tsaya cak ta ce "Saboda me?"

"Ta Sata miki rai, ni kuma muddun aka Sata miki rai na san zuciyar masoyina sai ta sosu, ni kuma ba na fatan hakan. Dan da na ?yale ta ma, ban san shi wani matakin zai Wauka a kan ta ba"

"Ba zaki ?yale matar nan ta huta ba ko Haula? Ki ji tsoron Allah"

Ta maze ta ce "Ai ko dan saboda ke, ina sassauta mata, ba har hira ku ke yi ba? Ina dattijon arziki?"

Nana ja ta tsaya, ta ce "Me yasa ki ke kiran mijina da dattijo, alhalin matashi ne?"

Ta yi dariya, ta naWe hannunta a ?irjinta ta ce "Ni ina ruwana da mijinki? Ba da shi nake ba, duk da na san ki na ganin komai wasu lokuta."

"Ki gaya mini, me ki ka sani game da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login