Showing 84001 words to 87000 words out of 190498 words

Chapter 29 - Buzu Book 1 Complete

Sule ya yi maganar cikin magiya. Baba ya fututtuke ya din ga bala'i, buzayen nan su na ba shi ha?uri.

"Payer la dot" ya furta cikin harshen faransanci yana kallon Habu. Habu ya waro ido, shi ma ya juye harshe, suka koma magana da french.

Jiki a sanyaye Habu ya kalli Baba ya ce "Nawa ne sadakin?"

Gaddafi ya ce "Baba wai da gaske aura masan ita za ka yi?"

"Eh mana, tun da haka ta zaSa. Ai wallahi ba za ta zubar mini mutunci a idon duniya ba, dan na san tun da Rabi ta san maganar nan babu wanda ba zai ji a ciki da wajen unguwar nan ba, har a dangi sai ta yi ta yamaWiWi, tun da haka ta zaSa ta samu"

Baba ya mayar da idonsa kan Habu ya ce "Ko ma nawa ne, ku bayar da sadaki da safe ya zo ya Wauke ta".

Habu ya sake kallon Buzu, cike da damuwa ko zai canza magana, amma ya ga babu alamar hakan.

Hatta 'yan bijilantin, sai da su ka ba shi ha?uri, da rarrashi amma fafur Baba ya ?i yarda kamar wanda ake ?ara zugawa.

Habu ya ce kuWin hannunsa ba su da yawa, bari ya kira waya a kawo kuWi.

Shugaban bijilanti ya ce ba za Waura auren nan a ofishin bijilanti ba, sai dai a tafi gidan mai unguwa, a yi a gaban jagororin unguwa.

Haka kuwa a ka yi, abin da Baba bai sani ba, da kansa ya ?ara tagayyara Nana, da yayata maganar.

Naira dubu Wari biyu Habu ya bayar, a matsayin sadakin auren Nana Asma'u ?arfe sha biyu saura na dare.

Gaddafi dai Baba ya ?ure masa mamaki, duk da ya san har da ziga a cikin lamarin na Baba.

Sai dai kuma Gaddafi ya yi mamakin yadda buzaye, masu gadi suka iya biyan har Naira dubu Wari biyu a take matsayin sadaki. Nawa ake ba su kuWin gadin da har su ka ci suka tayar da kan biyan wannan kuWin haka?.

Can gida kuwa Nasiru ne yake ta tattaSa Nana cikin tsoro, saboda sanyin da jikinta ya yi, kamar gawa.
Sai can wajen ?arfe goma na dare ta farka. Ta saka Nasiru ya kawo mata ruwa ?ofar Waki. Da rarrafe ta fito bakin ?ofar ta yi alwala. Ko yin?urawa ba ta iya yi balle ta tashi, saboda wani irin jiri da take yi. Da jikin kaya ta jingina daga zaune ta yi salla. Ta idar ta sake kwanciya.

Nasiru ya ce "Nana ba za ki ci abinci ba? Ga awara na sayo miki mai zafi" amma ya ji shiru. Ya duba sai ya ga ta koma yadda take da farko, hannunta zuwa ?afafuwan ta duk sun ?andare sun lan?washe.

Sha biyu da rabi Baba suka nufo gida, Gaddafi ya ce "Amma Baba ba a yi ganganci ba kuwa? Kawai ka aura mata mutunen da baka san ma wani iri ba ne ba, dubu Wari biyu fa suka bayar na sadaki ba ka tunanin ma ko wasu marasa gaskiyar ne?"

"Gaddafi wannan abin da na yi shi ne kawai maganin abin da yarinyar nan take aikatawa. Sau nawa ana yin?urin aurenta tana ?i? Mutumin nan da ya fito fa cewa ta yi za ta gudu, ko kuma ta kashe kanta a kan auren, amma ta san ta je Waki gurin namiji. Wannan ne kawai hanyar da zan bi na aurar da ita. Muddin za a din ga saka lokaci ba za ta taSa bari a yi ba".

Gaddafi ya numfasa ya ce "Haka ne, amma ba na tunanin za ta bi maza ko makamancin haka."

"Ba a shaidar Wan yau Gaddafi. Allah ya zaunar da ita lafiya"

Gaddafi yana son sake yin magana, amma ya fasa ya yi shiru.

Mama tamkar ta zuba ruwa a ?asa ta sha, haka ta ji bayan da Baba ya yi mata bayanin abin da ya faru. "Wallahi ka yi dabara baban Jamila, wallahi da haka za ta ci gaba da zubar mana da mutunci a idon duniya, kuma auren ba za ta yi shi ba, duk wanda ya zo haka za ta ci gaba da korarsa. Kuma shi kansa Alhajin idan ya ji abin da ya faru ba zai yarda ya aure ta ba, ba ma ita kaWai ba, duk wanda ya ji maganar nan ba zai yadda ya aure ta ba, amma tun da aka yi haka ka ga an yi maganin kowa ma. Kuma asiri ya rufu, tun da ta yi i?rarin kashe kanta, ko guduwa muddin aka yi mata wannan auren".

"Ai yanzu sai ta yi duk abin da ta ga dama, na yi wa tufkar hanci. Har Gaddafi yana wani cewa ba za ta aikata ba, ba zata aika ta ba uban me ya kaita Wakin masu gadi? ?ila ma Allah ne ya tashi tona mata asiri hakan ta faru"

Mama ta ce "To Allah dai ya kyauta"

Jamila kuwa jikinta ya yi sanyi sosai, sam ba ta taSa tunanin Baba zai Wauki wannan matakin ba. A yanayin yadda suka tarar da Nana, bai yi kama da wadda ta aikata wani rashin gaskiya ba.

****

Cikin matsanancin Sacin rai sule yake magana, "Habu yanzu da ka yarda aka yi wannan auren ya zamu yi da su gaba Waya?"

Habu ya ce "Amma ai ka na ji, da kansa ya ce a biya sadakin ko?"

"A'a ni ya za ayi na sani, tun da ba iya faransanci na yi ba, kuma da ya ce ka biya masa sadakin sai ka biye masa? Mutumin da ba hankali ne da shi ba, kai yanzu idan aka saka maka takobi a wuya, za ka iya nuna danginsa ko ahalinsa ne? Daga taimako sai jajubo mana wahala? Aure ai Wawainiya ne, shekarata nawa a Nigeria iyalina su na can sahara, ban kawo su nan ba, yanzu ya ka ke so mu yi?"

Habu ya kwantar da murya ya ce "Dan Allah Souley ka yi ha?uri, duk ba abin Waga hankali ba ne ba, idan aka samo wani gidan gadin, sai ya fara aikin gafin kafin a san abin yi"

Tamkar ya gaurawa Habu mari ya ce "A haka zai yi gadin? Mutumin da sai ya yi sati bai ce uffan ba, aikin gadi fa ba buWewa da rufe ?ofa ba ne kawai"

"Ai ba hauka yake tuburan ba, kuma ko a nan ai mu na tafiya mu bar shi, kuma ya yi gadin, dan Allah ka yi ha?uri ka daina Waga muryar nan, zamu san abin yi da yardar Allah"

"Ni wallahi har mamaki ka ke bani Habou, daga tsintar mutum sai wahala ka ke da shi, kamar wani tsohonka, na ga yadda za ayi ai da wannan bada?alar"

Habu ya dafa kafaWar Sule ya yi murmushi ya ce "Babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah, kuma Allah ya na gani taimako muka yi, ba zamu wula?anta ba". Da ?yar Habu ya samu ya shawo kan Sule.

*****

Nana ba ta sake tashi ba, sai washegari ?arfe bakwai na safe, shi ma Nasiru ne ya tashe ta, kamar jiya a bakin ?ofar Wakin su ta yi alwala, ta yi sallar asuba a zaune. Yana zaune ta idar, tana idarwa ya ce "Nana kar ki kwanta, ga kokona ki sha ki daina wannan baccin, jikin ki fa sanyi yake yi"

Ta girgiza kai ta ce "Na ?oshi Nasiru, jikina babu ?wari nima ji nake kamar mutuwa zan yi"

Da sauri ya ce "Ba mutuwa za ki yi ba, yunwa ki ke ji, ki sha kaWan" ganin yadda ya damu sosai da sosai, ya sanya ta karSa ta sha kaWan, ta ajiye ta fara ?o?arin kwanciya.

Suwaiba ce ta shigo Wakin, tare da rangaWa guWa ta ce "Amaryar tsakar dare, mai doki ya koma kuturi, ba a auri mai gida ba an auri mai gadi, to Allah ya sanya alkhairi".

Nana ta Waga jajayen idanunta ta kalli Suwaiba, ta mayar da idonta kan Nasiru ta ce "Nasiru mafarki ne wai?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a a zahiri ne"

"To me Suwaiba take cewa ne?"

Cike da ?uruciya ya ce "Wai jiya da daddare aka yi auren ki"

"Aurena kuma? Kamar yaya?"

Ya ce "Wallahi nima ban sani ba" Suwaiba ta cigaba da dariya, tana Waukar jakar kayan kwalliyar ta.

Baba ne ya shigo Wakin, ya tarar da Nana a zaune, ga Nasiru a gabanta da kofin koko.

"Yauwwa kin tashi kenan? To ki buWe kunnen ki da kyau, ki saurare ni"

Ta zubawa Baba manyan idanunta, da suka yi kama da na Japanese sai dai nata manya ne.

"Nana kin bani mamaki nesa ba kusa ba, duk iya ?o?arin da nake yi a kanku, amma ki ka zaSi ki zubar mini da mutunci, nayi nayi kin ?i yin aure, duk wanda ya zo sai kin kore shi kin ce ba kya so. Mutumin kirki ya fito da rufin asirinsa yana son ki da aure, amma ki ka buWe baki ki ka iya gaya mini idan na aura miki shi, za ki kashe kanki ko ki gudu, ?arshe kuma saboda abin kunya aka gano ki a Wakin masu gadi Nana. Dama 'yan kwanakin nan ba na gane kanki, ba kya dawowa gidan nan sai dare. To kin kyauta sai dai nima na Wauki matakin da ya dace, saboda mutuncina ba zai zube a idon duniya ba, na aurar da ke ga abokin lalacewar ta ki, su buzayen da ki ke zuwa Wakinsu, idan da kun yi ba lada yanzu sai ku yi mai dalili" Jin Nana ne ya Wauke baki Waya, ta daina tantance komai, bakinta tamkar an saka mata sakata, jikinta ya ?ara wani irin sanyi, sannan ya yi mata nauyi, ta kasa motsa kowace gaSa ta jikinta." Idonta kar a buWe ko ?iftawa ba ta yi, hawaye ya din ga zirarowa.

Baba ya ?arasa maganar, ba tare da Nana, ta iya gane me yake faWa ba. Idanun Nasiru ya cika da hawaye saboda tausayin Nana. Duk da ?an?antar shekarunsa yana fuskantar wasu abubuwan, kuma ya san ba a haka ake yin aure ba.

"Nana ki daina kuka" yayi maganar cikin matsananciyar damuwa, yana kallon fuskarta. Kawai ya ga ta nemi guri ta kwanta.

Baba kuwa zuwa aka yi, aka ce ana sallama da shi. Ya fita sai ya tarar da Habu da wasu buzaye guda biyu. Ya wani haWe rai yana muzurai ya ce "Kun zo ku tafi da itan ne ko kuwa?"

Habu ya girgiza kai ya ce "A'a, zuwa muka yi mu nemi alfarma"

"Ta me?" Ya faWa yana ?ara tsuke fuska.

"Muna son a bamu ko mako guda ne, mu samu gurin da za su zauna, kuma a sama masa Wan wani abin yin, yanzu idan muka Wauke ta, babu gurin da za mu ajiye ta"

Baba ya ce "Mako guda kawai, idan ku ka ?ara fiye da haka, sai na kai ku ?ara gurin hukuma"

Habu ya ce "Ba za a yi haka ba da yardar Allah, mun gode sosai" suka yi wa Baba sallama suka tafi. Habu ya kasa daina ta'ajibin abin da ya faru daren jiya. Yana mamakin yadda Baba ya iya Waukar 'yar sa ya aura musu, ba tare da sanin ma daga ina suka fito ba, kuma har a yanzu bai tanbayi daga ina suke ba, kuma su waye danginsu ba.

***
Hajiya Amina ce a zaune, tana shan tea ta kalli Shukura ta ce "Kin ga haryanzu layin Nana ba ya shiga, ina son sanin halin da take ciki, wallahi jiya ban yi bacci ba"

Shukura ta kalle ta ta ce "Ba ki yi bacci ba?"

"Wallahi Shukura, hankalina a tashe yake gaba Waya, ban takamaiman abin da ya same ta ba"

Yusuf ya yi sallama, ya shigo falon ya ce "Mummy, wai buzayen nan ne, suke son magana da ke"

Ta ajiye kofin hannunta ta ce "Ka ce su shigo"

Ya fita ba a jima ba, sai ga shi tare da Habu da kuma Sule.

Suka zauna a ?asa suka gaisheta ta amsa musu, cikin sakin fuska.

Habu ya ce "Hajiya jiya fa da daddare, an zo tafiya da Wan uwan nan namu, mahaifin Nana ya ?i yarda, sai da aka Waura mata aure jiya da Wan uwan nan namu" ba Mummy ba hatta Shukura sai da ta zaro ido.

Mummy ta ce "Saboda me?"

"Ya ce lalata suke yi, kuma wallahi Wan uwan namu ma ba shi da cikakkiyar lafiya, ai kina ganinsa kullum a gefe shi Waya. Shi ne dai na zo na sanar miki, kar a yi abu ba ku sani ba"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, me yasa ba ku zo kun sanar da ni ba? Haka ake yi kawai sai a Waura wa mutum aure a kan abin da ba a tabattar da faruwarsa ba? Yarinyar nan nutsatstsiyar yarinya ce, akwai abin da ya faru ba na tunanin Nana za ta aikata wani abu irin haka. Yanzu to ya za ku yi can ?asarku za ku kai ta ko kuma ya ya?"

Habu ya girgiza kai ya ce "A'a, zamu samu gurin da za su zauna ne, kafin mu je gida a yi wa magabatan namu bayani"

Cikin damuwa Hajiya Amina ta din ga nanata "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ikon Allah wannan wane irin abu ne haka? Matakin ya yi tsauri da yawa, ai sai a fara bincike tukuna a tabattar idan ma wani abun yake zargi"

Shukura duk da ba wani shiri take da Nana ba, amma al'amarin ya daki zuciyarta, a yadda take ganin Nana ta yi kalar nutsuwa sosai da sosai, sam ba ta ji a ranta Nana za ta iya aikata abu makamancin haka ba.

****
"Jamila" Nana ta furta da ?yar, saboda yadda take jin tamkar an Wora mata wani ?aton dutse a kanta.

"Na'am"

"Da gaske Baba yake yi, an Waura mini aure, ko kuwa mafarki ne?"

Jamila ta Wan taSe baki ta ce "Da gaske ne mana, zai yi miki ?arya ne?"

Ta sake cewa "Kuma da buzayen nan?"

"Eh fa"

"Waye a cikin su?"

Jamila da ta fara ?osawa da tambayoyin Nana ta ce "Ni fa ban sani ba, tun da ba taSa zuwa na yi ba balle na san su. Ke ma Nana me ya yi miki zafi, da za ki je Wakin masu gadi me ki ke yi a ciki? Dama ana i?rarin kin ?i yin aure, yanzu ga abin da ki ka ja wa kanki nan"

Sanin ko ta yi bayani ba fita za ta yi ba, ya sanya ta jan bakinta ta tsuke. Ta ci gaba da sauke numfashi da ?yar. Tiryan-tiryan ta shiga tuno abin da ya faru, sai dai tunaninta ya tsaya cak a daidai lokacin da ta ga wannan mutumin a cikin Wakin, har ta razana ta ?wala ihu.

Cike da dana sani take raya, da lokacin da ta firgitan nan addu'a ta yi, da wata ?ila hakan ba ta faru ba.

Ta Waga kai a hankali, ta ?urawa ?ofar da Jamila ta fita ido. Wani irin huci haWi da nishi ta din ga ji, ba tare da ta san daga ina yake fitowa ba.
Wata irin narkekiyar macijiaya ce, ta fito daga cikin roofing Win Wakin, tana tsartuwa ta yo kan Nana. Tamkar an Waure ta, ta kasa motsi, kuma ta kasa magana kawai ta zubawa sarautar Allah ido.

Ta ci gaba da nufo ta tana tsartuwa, sai kuma Nana ta ga macijiyar ta ?ame a guri guda, tana ta wutsul-wutsul tana fasa kai, tana neman hanyar guduwa.

Wani dogon hannu ta ga an zuro ta taga, an dan?i kan macijiyar, an janye ta, sai da aka janye ta, sannan Nana ta razana ta iya tashi zaune tana maimaita "Innalillahi wa innalillahi raji'un"

Tagar Wakin ta kalla, ta ga ?aisar a tsaye, ya tattare macijiyar, ya zura ta a cikin wata 'yar mitsitsiyar kwalba. Har yanzu hannunsa Waya da rauni.

Ya dubi Nana ya ce "Wannan ma 'yar aike ce, aka kuma aikota jininki ake so ko ta halin ?a?a, kuma 'yar uwakki aka bawa abin da ta zo ta ajiye a Wakin nan, da zai bayar da damar samo jinin naki. Sai dai waccan jakar ce ta hana macijiyar ?arasowa inda ki ke" ya ?arasa maganar yana nuna wa Nana, jakar da sarkin baka ya bata.

"Duk ba wannan ce ma ta saka na zo da kaina gurin ki, rana tsaka ba. Ina mai tabattar miki da wannan auren da mahaifin ki ya yi miki, ya jefa rayuwar ki a cikin sabon babin ?addara da ?alubalen rayuwa, ba kuma ke kaWai ya jefa ba har da ni. Sai dai na yi alwashin ba zamu wahala muka Wai ba, sai na yi masa mafi munin azabtarwa a kansa da kuma iyalansa, duk wani farinciki da yake tunanin samu a duniyar nan, sai ya yi hannun riga da shi, ke kuma ki shirya tsaf dan wanda aka aura miki ko dai ya yi ajalina ko na yi ajalinsa!

Ayshercool
08081012143
26

Jin abin Nana ta din ga yi tamkar tunani, kuma tamkar mafarki, domin da ta tashi zaune, ba ta ga ?aisar Win ba, kuma ba ta ga macijiyar ba.

Muryar Yaya Atine ta jiyo a tsakar gida tana faWin "Wanda ya ?i ji ai ba ya ?i gani ba, sam ban ga laifin Isa ba abin da ya yi, wannan hukuncin shi ne ya dace da ita, babu irin rarrashi da ban bakin da ba a yi wa yarinyar nan, amma kowa ya zo sai ta yi burus fafur ta ?i yarda da maganar aure, hankalinta ba ya kwanciya sai maganar ta lalace, idan wani abin da aljan wani abin tsagwaron iskanci ne kawai, dan a iya adadin yawon nema mata magani da aka yi, ai ya ci a ce ta warke"

Mama kuwa tamkar ta taka rawa dan murna, duk yadda take ?o?arin Soyewa, sai da farincikin ta ya kasa Suya.

Ta yi caraf da maganar Yaya Atine ta ce "To ai yanzu an yi mai Wungurugum, haihuwa da hanji, ko in ce mai doki ya koma kuturi, tun da babban mutum ne mai rufin asiri ya fito yana sonta, amma fafur ta ?i, har tana i?irarin za ta gudu, ko ta kashe kanta, ashe ita gurin wasu take zuwa lalacewa" saurin katse maganar ta yi, bayan da suka yi ido huWu da Nana a tsaye a ?ofar Wakin su.

"Rabi, duk abin da za ki ce na yi, ba zai dame ni ba, dan na riga na saba da duk wani ?azafi da cin mutunci da ki ke yi mini, har ?azafin maita kin yi mini duk abi dame ni ba, kuskure ma fi girma da za ki yi shi ne, yi mini ?azafin zina, babu wanda ya kama ni ra'ayil aini, ina yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login