Showing 66001 words to 69000 words out of 190498 words

Chapter 23 - Buzu Book 1 Complete

tun da ya ganta a gurin ai ya san tafiya za ta yi.

Sule ne ya nufo ta, hannunsa ri?e da kwanon abincin kare, ya ce "Malama kin fito?"

Nana ta ce "Eh, ina ta yi wa wannan Wan uwan naku magana, ya yi mini banza"

Sule ya kalle shi ya ce "Banza ya ce miki?"

"A'a ya yi mini shiru"

Ya ce "Auu shiru bai yi magana ba? Ba shi da lafiya ne, ki yi ha?uri"

Ta ce "Kurma ne?"

Sule ya ce "A'a yana ji, magana ce ba ya yi"

Maimakon ta tafi, sai ta ce "Bebe ne kenan?"

Sule ya ce "Bebe me kenan?"

"Ba komai, buWe mini na tafi"

Ya ajiye kwanon hannunsa ya buWe mata, ta Wauki kayan har za ta fita, sai ta waiwaya aikuwa karaf idanunta a cikin nasa.

Ta ja kayanta ta fice ta tafi gida.

*****

Cikin damuwa Mama take kallon su Jamila, Suwaiba jiki ya Wan yi kyau kwana biyu. "Jamila, wai haka za mu ci gaba da zama babu wani ci gaba? Kun san da an aurar da yarinyar nan kanku zai juyo, kuma haryanzu kuma babu wani tsayayye na kirki, duk sai takarce"

Jamila ta ce "TaS, ai wallahi babu wanda ya isa ya yi mini abin da ake yi wa Nana, wallahi bujirewa zan yi"

"Ke dalla rufe mini baki, kafin a kai ga hakan ba sai a samu mafita ba, na gaji da kashe kuWi a gurin malamai, babu wani saurayin kirki mai kuWi, duk sai gayyar tsiya".

Jamila ta ce "Ni fa auren nan ko na yi shi, ko kar na yi shi bai dame ni ba, ni damuwata na samu mai kashe mini kuWi, nima na Wana rayuwar jin daWin nan, wannan ba?in talaucin nan na gidan nan, idan ka biye masa, haka rayuwar ka za ta ?are, ka je kuma auri talaka irin Baba ka ci gaba da gyangyaWa rayuwa, jin daWi sai dai ka ga wasu suna yi"

Suwaiba ta ce "A ina za a samu mai kuWin, mu ba wani shegen kyau ba"

Jamila ta ce "Kanti za mu shiga wallahi, dan ni ina ganin allura ma zan yi"

Suna cikin maganar, Nana ta shigo da sallama, kasa amsa sallamar suka yi, sai bin ta da kallo, ganin kayan da suke jikinta, ga hannunta ta jakar kaya.

Nana ba wani shahararren kyau ne da ita ba, sai kyakyawan diri, domin jikinta shi ne babban rashin tsaronta. Idan ta taho ta gaba duk hijjabin da ta saka, baya Soye ?ir?irar ?irjinta. Ba?a ce mai matsakaicin tsayi.

Ta fito tsakar gida ta Webi ruwa ta yi wanka, ta yi alwala.

Jamila ta kasa jurewa ta ce "Nana ina ki ka samu wannan rigar? Ta yi miki kyau sosai" Nana ji ta yi tamkar ta share ta, saboda yadda suka haWa kai da babarsu, su ka wula?anta ta, suka Wauki gaba da ita.

Amma ta yi ya?i da zuciyarta ta ce "Da gaske?"

"Wallahi ta yi miki kyau sosai"

"Na gode" ta faWa a ta?aice.

"Waye ya baki?"

Nana ta ce "Gidan da nake aiki ne suka bani"

"Zan zo a din ga bani aro"

Ta jinjina kai ta ce "Idan ma so ki ke sai na baki"

"A'a aron dai" Nana na shiga Waki, Mama ta ce "Mara zuciya, me take da shi da za ta baki? Ba ga uwar Wakinki nan tana baki kaya ba"

Nana na saka ?afarta a Wakinsu, ta ganta a libraryn ?aisar.

"Meye haka kuma? Salla fa zan yi" ta yi magana tana waiwayen ganin ta ina za ta gan shi.

A kan kujera ta hange shi, yana rubutu a cikin wani littafi, ba tare da ya kalle ta ba ya ce "Ai ba a kira sallar ba ko?"

"To me ka kawo ni nan na yi maka, a yanzu? So nake na yi azkar kafin a kira sallar" Nana ta faWa a hasale.

"Wanda za ki aura ba shi da lafiya, an ce ki je ki duba shi kin ?i, me ki ke zato?"

?an shiru ta yi, sannan ta kalle shi ta ce "Kai ka saka shi ciwon ciki kenan?"

Ya ajiye al?alamin, ya rufe littafin, ya tashi ya ce "A'a, ba ni ba ne ba, miyagun ?wayoyin da yake sha ne kawai suke tambayarsa, duk ba wannan ba, haryanzu ba ki shirya barin gidan nan ba."

"Wai in bar gidan na je ina?"

Ya tura littafin hannunsa, tsakiyar wasu littattafai ya ce "Yanzu ba wannan ba tukuna, kin ga da kin yadda da sharaWinmu, da kin ceci Wan yaron nan da yake ta ?aunar ki"

A razane Nana ta ce "Wane yaron? Ba dai Haidar ba"

Ya harWe hannayensa a ?irjinsa ya ce "A'a ba shi ba, kalli mudubi da kin yarda ki na da halin ceton yaron nan, amma ba?in taurin kan ki ya sanya zai rasa rayuwarsa"

A gigice Nana ta ce "Wai wani yaron?" Da idonsa ya nuna mata mudubin. Muhsin ne a kwance, babu inda yake motsi a jikinsa, ga robar abinci, ga oxygen a hancinsa. Gefe mamansa ce, idanunta jawur saboda kuka. Ga kuma yar mahaifinsa Hajiya Sa'a a gefe.

Nana ta gigice ta ce "Muhsin"

"Eh, kin makara, an riga an bayar da jininsa ga wani aljani, mutuwa zai yi yaron"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, meyasa ba ka yi komai a kai ba?" Ta yi magana cikin kuka.

"Ina cikin aljanu masu son zaman lafiya, dama da zan yi wani abu a kai, sai dai ta hanyar ki, kuma farkawar sa ta ?arshe ma sunan ki yake ta kira. Kash Allah sarki, dama sunan uwarsa ya kira da take zaune kusa da shi, tna lissafa dukkanin numfashin da yake fitarwa, cike da ?auna da kuma fatan ya ci gaba da rayuwa, ba ke ba da ba ki sam ciwon sa ba" yayi maganar yana hura iska a jikin mudubin, a take komai ya Wauke.

Nana ta rikice cikin kuka, ta rasa abun yi gaba Waya.

"?anwar babansa ce ta bayar da jininsa, aka yi mata domin ci gaban samun duniyarta. Wadda dai ta bayar da turare a kawo miki. Shikenan mun gama je ki yi sallar ki"

"Nana" ta ji Baba ya kira sunanta da ?arfi. Ta Wago kai ta kalle shi, tana zaune a cikin Waki ta haWa kai da gwiwa tana ta kuka.

"Me aka yi miki? Ko wani ne ya mutu?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"To gidan aikin ne suka yi miki wani abu?" Ta girgiza kai alamar a'a.

Baba ya sake cewa "To kukan me ki ke yi, an ce tun da ki ka dawo ki ke abu Waya ko jikin ne?"

"Baba babu fa komai" ta yi magana tana tashi tsaye. Ta kalli gari ya yi duhu sosai, da alama isha ta wuce. Ta yi shiru ta tuna abin da ya sakata kuka, amma ta kasa tuna komai.

Ta yi alwala ta yi sallar magariba da isha'i, tana jin wata irin matsananciyar damuwa da tashin hankali a cikin zuciyarta, amma ta kasa tuna ko a kan mene ne. Abincin da ta zo da shi ta kasa ci, ta kira Nasiru ta bashi, ya karSa ya gudu waje kar Mama ta hana shi ci.

Sai dai tun da sanya ha?ar?arinta a ?asa take addu'a, amma bacci ya gagara, ta yi juyi, ta kuma amma ko alamar bacci babu a idonta, har aka yi kiran sallar farko, a kunnenta ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili ta zauna har aka yi sallar asuba.

Har gari ya yi shaa, tana zaune. Ta tashi zata fara shirin fita, kawai idanunta suka sauka a kan jakar da ta dawo da ita, daga gidan sarkin baka. Ta Waukko jakar ta hau buWewa. Sai dai ta zazzage jakar kaf babu komai a ciki.
Ta yi guntun tsaki, ta ajiyeta, sai dai ta yi shiru tana tuno abubuwan da suka faru a gidan sarkin baka. Ko ba komai ya karrama ta, ya mutunta ta, tana matu?ar son sanin halin da yake ciki a yanzu.

Ta gama shirinta, ta yi wa Baba sallama ta tafi gidan aikinta.

A Waki ta iske Haidar bai ko tashi ba, kasancewar ba ta samu bacci daren jiya ba, ya sanya ta nemi guri ta kwanta a ?asa, bacci mai nauyin gaske ya Wauke ta.

Ji ta yi tamkar wani abu ba dai-dai yake ba, ga baccin tana yi, amma ba ya mata daWi sam. A hankali ta buWe idonta, kawai ta ga Alhaji Zailani a cikin Wakin.
A mugun sukwane ta tashi, ta ja da baya ta kalle shi ta ce "Lafiya, me ya kawo ka nan?"

"Gidana ne" ya bata amsa.

"Eh na san gidan naka ne, amma a cikin gidan naka akwai inda shari'a ta yi maka iyaka, tun da ba duka mutanen gidan ne iyalinka ba"

Ba tare da ya amsa maganar da ta yi ba ya ce "Mun fara magana ba mu ?arasa ba, na zo mu ?ar?are ta yau"

Cikin takaici Nana ta ce "Wace maganar?"

Ya nuna mata gefen gadon Haidar ya ce "Zauna mu yi magana"

"Ni ba zan zauna ba, ka gaya mini ko ma mene ne a haka"

Ya nemi guri shi ya zauna, a gefen gafon Haidar yana tsareta da idanunsa.

"Bu?ata ce da ni a gare ki, wadda idan ki ka amince ke ma za ki samu biyan bu?atun ki"

Ta ce "Ni na ce maka ina da bu?atar wani abu ne?"

Alhaji Zailani ya ?ara tattara hankalinsa a kanta ya ce "Ko ba ki faWa ba, na san ki na da bu?ata kema. Kasuwancina ne ya fara yin baya, an ce mini muddin na yi tarayya da mace irin ki, taurarin ki za su haska nawa." Galala Nana take bin sa da kallo, yadda ya zauna babu kunya babu tsoron Allah, yana gaya mata maganganun banzar da babu komai a cikinsu sai jahilci da hauka.

Ko a jikinsa da kallon da take yi masa, ya ci gaba da magana. "Idan ki ka amince, zan baki kuWi, kuWaWe ba ?anan kuWaWe ba, kuWin da sai kin rasa yadda za ki yi da su"

Cike da takaici Nana ta ce "Kai yanzu bawan Allah, ka na da kuWin da zaka bani wanda sai na rasa yadda zan yi da su, me za ka yi da wasu kuma? Ai ina tunanin idan ka haWa ka ri?e sun wadace ka"

Ya mi?e tsaye ya ce "Ai ba a daina neman kuWi, ki amincewa bu?atata, zan baki kalar rayuwar da ba ki taSa tsammani ba a rayuwar ki"

Nana ta ja da baya ta ce "Ba na bu?atar kuWin ka, ko zan koma ga Allah a talauce ba zan abin da ka ke so ba, ko zan yi wannan mummunar Wabi'ar ba zan yi da mushriki irin ka ba, Allah ya tsare ni daga sharrin ka"

Alhaji Zailani ya ce "A'a ba ki da wani zaSi fa, tunda aka kasa ri?e budurwa kamar ki a gidanku, aka bar ki, ki ka fito yawon rainon yaro. Kuma na san tunanin ki bai wuce budurcin ki ba, babu lallai wani abu ya shafi nan gurin ma. Budurcinki ba zai taSu ba, kuma idan ki ka samu kuWi, za ki iya rayuwar ki ba tare da wani Wa namiji ba. Ki yi tunani a kai" ya nufi hanyar fita ya fice daga Wakin.

Jikin Nana ne yake wata irin tsuma, cike da tsoro da razani, ta dafe saitin zuciyarta da yake wani irin bugu tamkar ta fasa ?irjinta, ta fito.

Ta kalli Haidar da yake ta baccinsa hankali kwance. Jiki a sanyaye ta tashi Haidar, ta yi masa wanka ta fita da shi falo tana ba shi Abinci.

"Ke me ki ke bawa Wa na haka?" Ta ji muryar Shukura cikin Waga murya.

Nana ta kalle ta ta ce "?osai ne da kunun gyaWa"

"?osai? Ki ke ba shi, a gidan uban wa ki ka samo wannan tarkacen ki ke bawa yarona?"

"Kunun a nan na dama, ?osan kuma daga gida na taho da shi, shayi ba abincin yaro ba ne" Nana ta faWa kanta tsaye.

"Shut up malama, ki kwaso jagwalgwalo daga waje ki kawo shi kina bawa yarona kashe shi za ki yi? Na san wani concoction aka haWa a ciki ki ke ba shi, dan samun guri?" Nana kamar ta yaSa mata magana, mussaman da take cike da takaici, da mamakin abin da babanta ya yi mata, amma ta yi shiru, ta haWiye.

Haidar dai hankali kwance, yaka ta WaWWakar kunu a cikin feeder, ta tafi a fusace za ta fizge kwanon ?osan ta yi jifa da shi.
A zuciye Haidar ya buga mata feeder hannun sa, yana ihu.

Nana ta haWe rai ta kalle shi, sai ya nutsu.

"?aukko kwanon da ?osan, ka zo ka bata ha?uri, ko kuma yau na saka a kwano a kai wa kare ya cinye ka, sai wataran za a sake haifo ka"

A ruWe ya tashi ya Waukko kwanon ya kawowa Nana, yana cewa "Sorry Anty"

"Ba ni zaka bawa ha?uri ba, maminka za ka bawa ha?uri"

Mummy da take kallon duk abin da ya faru ta ce "Lallai tsakanin Haidar da Nana sai Allah. Sannan ke Shukura ban da abin ki, soyayya ce ta sanya har ta Wauki abin ta ta bawa Wanki. Sati biyun nan wallahi har ya yi kumari, ba nan ki ke complain na ramar sa ba? Malama ki wuce ki tafi makarantar ki, sannu da ?o?ari Nana"

"Yauwwa Mummy ina kwana?"

"Lafiya kalau Nana, ya Wan naki?"

"Yana nan lafiya ?alau"

Kasancewar a fusace yake, bai gai da Mummy ba, sai da Nana ta yi magana. Nana tana ganin mutuncin Hajiya Amina, tana da kirki sosai da sosai, Nana ta din ga mamakin yadda take zaune da Alhaji Zailani da wannan mummunar Wabi'ar da yake aitawa. Kodayake wata ?ila ba ta san yana yi ba. Wata zuciyar ta bata amsa.

Abin ya din ga damunta a zuciyarta, amma ta rasa wa za ta gayawa. Tare suka yi girki da Jummai. Har na dare suka yi bayan sun kammala yau ma Jumman ta ro?e ta, ta ajiyewa masu gadi Abinci kafin ta wuce gida.

Tun da ta tafi hanya take sa?awa tana warwarewa, idan ta ajiye aikin nan ba ta da wata makoma, yanzu Allah ya rufa mata asiri, ba ta da fargabar abinci ko kaWan, dama abinci shi ne babbar damuwarta, ga kuma albashi mai tsoka da take sanya ran fara karSa. Sai dai ga ?oshi ga kwanan yunwa, ko dai ta ci gaba da zuwa tana fuskantar barazana daga mai gidan, ko kuma ta koma zaman gida ba ta da abin yi, yunwa ma kaWai ta ishe ta.

Duk da akwai 'yar tazara kaWan daga gidan aikinta, zuwa gidansu, amma har ta je gida tunani take yi.

Tun a ?ofar gida ta haWu da Nasiru, ya ce "Nana kin dawo? Me muka samu yau?"

Ta yi murmushi ta ce "Ba komai"

"Bayan ga leda nan a hannun ki"

"Shinkafa ce, ka bari sai mu ci da daddare, ko an yi girkin dare ne?"

Nasiru ya ce "Tuwo ne, kuma tun da ga shinkafa ba zan ci tuwo ba, yauwwa ni na manta ma, Wazu Baba ya yi wasu ba?i, yana ta shiga yana fita yana faWa, ke yake jira ki dawo"

Ta yi sak, ta ce "Ni kuma?"

"Eh"

A Wan marairaice ta ce "To me kuma na yi?"

Ya Wan Wage kafaWarsa ya ce "Wallahi nima ban sani ba"

Ta kalli gidan ta ji gabanta ya faWi, sai ta ji sam ba ta ?aunar shiga gidan ma.

Ta daure a hankali, tana takawa da ?yar, cike da fargabar rashin sanin abin da za ta tarar.

Ta yi sallama babu kowa a tsakar gidan, ta shiga Waki ta ajiye ledar abincin hannunta.

Gaba Waya ta rasa abin da yake yi mata daWi, a zullumi take kawai Baba ya zo ya gaya mata me kuma ta yi a wannan karon.

"Laa Nana kin dawo?" Ta Wan zabura, ta kalli Jamila dan ba ta san ta shigo Wakin ba. Ta ce "Eh ya gidan?"

Jamila ta ce "Lafiya ?alau, ga kunun aya can da na ajiye miki a jug, a gidan maman khairat muka yi, na san ki na son shi, shiyasa na ce bari na ajiye miki"

Nana ta yi murmushin ?arfin hali, ta ce "Amma kuwa na gode sosai da sosai, bari na yi sallar magariba na haWa da abinci"

Jamila ta ce "To shikenan, ga shi can ma an yi kira"

Nana ta ce "Amm yauwwa Jamila, Nasiru ya ce mini Baba yana nemana, dan Allah ko kin san abin da na yi yake nema na?"

"A'a, ai ban daWe da dawowa ba nima"

"Ok to na gode" haka dai a Warare ta yi sallar magariba, duk da tulin damuwar da take ciki, ta Wauki jug Win kunun ayar nan, domin ta Wan sha ta bawa Nasir sauran, dan ko sha'awar abinci ba ta yi. Shi ma dan kar Jamila ta ji haushi ne, tun da ta ga neman shiri take yi da ita.

Ta buWe jug Win ta kai bakinta, ta ji an ce "Kar ki sha"

Ta waiwaya ba ta ga kowa ba, ta sake kaiwa bakin ta aka sake cewa "Kar ki sha" kawai ta Wauki fitila ta haska jug Win.

Jini ne a ciki yake ta tafasa, tamkar akan wuta. A razane ta saki jug Win kunun ayar ya zube. Ta din ga sauke numfashi, ta yi maza ta janyo zani ta goge gurin, dan kar Jamila ta zo ta tarar da abin da ya faru. Ba ta gama wannan taradaddin ba, Baba ya kwaWa sallama muryarsa a sama kamar tashin hankali.

Wani fitsarin tsoro ne ya kama Nana, tun kafin ta san abin da ta aikata.

"Nana ta dawo ne?"

Jamila ta ce "Eh tana Waki"

Cikin hargowa ya ce "Ki na ina fito ki zo nan, magajiyar tsiya da jaraba"

Dumm ?irjinta ya sake bugawa, a karo na babu adadi, jikinta ya din ga rawa yana neman gaza Waukarta, ta fito jiki a sanyaye tana jiran ji ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????abin da Baba zai ce.

"Ashe kin je gidan Ummi, ta ce miki ku je ku duba yaron nan, ki ka ce ba zaki ba, ki ka ?ara nanata mata ba kya son sa. To ?anin babansa ya zo nan Wazu, sun ce a tattara duk wani abu da ya san ya yi miki a mayar masa. KuWin aurensa dubu saba'in, kuWin da ya bayar aka kai ki gurin mai magani, da kayan shafe-shafe da ya kawo, ki na gidan mai magani aka yi amfani da su a gida, kusan lissafin dubu Wari da sittin, sun ce a mayar musu, kuma ni ban san inda zan je na nemo wannan kuWin ba, dan haka sai ki shiga ki fita ki san yadda za ki yi a nemi kuWinsu a ba su."

Ayshercool
08081012143
Page 21

Idan da sabo, Nana saba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login