Showing 174001 words to 177000 words out of 190498 words

Chapter 59 - Buzu Book 1 Complete

ta tafi da sauri gurin karSo kati.

Shi kuwa Sayyid, ?arnin da gurin yake yi, da warin gyambo kala-kala da yake gurin, ya sanya jin numfashinsa zai Wauke.
Ya zaunar da shi a hankali a kan wata kujera, ya ce masa "Sannu"

Sayyid ya jinjina kai, Nana ta dawo hannunta ri?e da kati, idanunta sun yi ja, alamu suka nuna, da ta tafi karSo katin, kuka ta yi a hanya.

Mai Adaidaita sahun ya ce "Tsaya da shi a nan, bari na duba idan da alfarmar da za a iya yi mana, a shiga da shi ya ga likita.

Ta ce "To na gode" ya karSi katin ya yi gaba.

Sayyid ya ri?o hannun Nana a nasa, ya kwantar da kansa a jikinta, yana murza hannunta a hankali.
"Sannu Sayyid" ya Waga mata kai kawai.

Mintuna biyar, sai ga mai adaidaita sahun ya ce "Yauuwa bari na shigar miki da shi"

Ya sake kama Sayyid, ya kai mata shi har gaban likita. Ya zaunar da shi sannan ya kalle su ya ce "To ni na tafi Allah ya ?ara afuwa."

Nana ta ce "Na gode bawan Allah, Ubangiji Allah ya biya maka bu?atunka na alkhairi, ya ji?an magabatanka, Allah ya buWa maka na gode sosai da sosai"

"Amin bakomai, ai yi wa kai ne, Abokina Ubangiji Allah ya baka lafiya"

Sayyid ya Waga masa hannu, ya jinjina kai.

Ta ce "Ya ce ya gode"

"Ba wani abu" ya fice ya bar Wakin likitan.

Nana ta yi wa likitan bayanin abin da ya faru, ya kalli Buzu ya yi masa tambayoyi. Ta ce "Ai ba zai iya magana ba"

Ya ce "Ok, to ya sauke rawanin, zan duba shi" Nana ta sauke masa.

Likitan ya sanya stethoscope Win sa a ?irjin Sayyid, ya saurara. Sannan ya Waura masa BP.

Ya din ga kallon fuskar Sayyid, ya kama hannunsa ya duba pulse Win sa. Nana kuma ta zuba masa ido, kamar ta shiga cikin kan likitan, ta ji mai ya gano.

"Hajiya tun yaushe yake da hawan jini ne?"

Cikin mamaki Nana ta ce "Hawan jini kuma?"

"Eh mana, jininsa ya hau fiye da kima, ko ba ki san yana da shi ba?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ban sani ba. Sayyid ko dama ka na da hawan jini?"

Yanayin kallon da ya yi wa Nana, yasa ta kalli likitan ta ce "Shi ma bai sani ba"

Likita ya ce "Gaskiya dai jininsa ya hau sosai, kuma zuciyarsa babu lafiya. Bradichadia nake ji a pulse Win sa. So yanzu za mu yi managing jininsa da ya hau. Zan rubuta allurai da magunguna, ki sayo a yi masa.
Zan rubuta muku gwaje-gwaje, idan an yi za ku dawo ranar Monday mu gani"

Jikin Nana ya yi sanyi a raunane ta ce "Likita ba za a ba shi gado ba? A haka zamu koma gida har Monday, ka ji fa zuciyarsa ba ta bugawa sosai"

"Ki yi ha?uri. Abin da zan iya yi masa kenan, ko na ce a ajiye ku babu gado a nan. Kuma dole sai an yi gwaje-gwajen nan tukuna, sannan zamu san abin yi. Ki yi ha?uri ki kwantar da hankalinki. Maybe ma hawan jinin ne ya kawo rashin bugawar zuciyar sosai, amma da ya sauka za a iya samun ci gaba"

Ta jinjina kai ta ce "To shikenan, na gode sosai Likita"

"Babu wani abu kar ki damu, zai samu lafiya in sha Allah"

Ta ce "Allah yasa, kuma Likita zai iya warkewa? Na ji an ce har abada ba a warkewa daga matsalar hawan jini da matsalar zuciya."

Cikin ?warin gwiwa likitan ya ce "A kimiyyance, sun ce ba su da magani, sai dai a yi managing symptoms kuma a canza life style. A addinance kuma mun san babu abin da ya fi ?arfin Allah. Babu wata cuta da ta gagari Allah ya yaye wa bawansa"

Wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi, bayan samun ?warin gwiwa daga bakin likitan. Ya rubuta allurai da magungunan da za a yi masa. Ta karSa ta yi masa godiya.

Da ?yar Sayyid ya taka ya bar ofishin, Nana ta zaunar da shi a kan benci, ta fita ta sayo alluran da za a yi masa. Amma duk Nurses Win sun yi busy, aiki ya yi musu yawa.
Nana ta koma gurin likitan, ta gaya masa, ya taso da kansa ya zo ya zauna ya yi wa Sayyid alluran.

Yana yi yana yi wa Nana nasiha. Bayan ya gama yi masa allurar, ya saka ta bashi maganin, ya ce bayan awa Waya zai sake duba bp Win sa.
Likita ya koma office, Nana ta fita ta sayo masa abin da zai ci, dan bai karya ba ga shi an fara kiran Azahar. Da ?yar ya Wan ci kaWan, ya ce mata salla zai yi. Ta kai shi waje, ya yi alwala ta shimfida masa Wan kwalinta, ya hau ya yi sallar. Bayan ya idar ita ma ta raSa ta yi. Baya ta idar, ta mi?e masa ?afafuwanta, ya kwanta a kai. Tana son taSa ?irjinsa, amma tana tsoron ta taSa ta ji zuciyarsa ba ta bugawa sosai.
Sai da suka yi kusan awa biyu, sannan Likita ya sake duba jininsa. Ya ce "Alhamdillah jininsa ya sauka, ba kamar yadda ku ka zo ba, zuciyar ma ta fi da bugawa. Yanzu ku je idan an yi wannan gwaje-gwajen, zuwa Monday sai ku kawo, ko ba ku same ni ba, za a duba shi in sha Allah"

Nana ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "Mun gode sosai da sosai Likita, Allah ya sa ka ajiye aiki lafiya"

"Amin Allah ya sauwwa?e" ya mi?e ya tafi.

Nana ta kalli Sayyid cikin tausayawa ta ce "Rayuwata, ya ka ke ji yanzu?"

"Alhamdillah" murmushi ta yi, jin ya yi magana.

"Ma sha Allah, sau?i ya samu, zaka iya tashi mu je gida?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Ta tashi shima ya yin?ura, cikin ikon Allah, babu wanda ya ri?e shi har suka fita titi, duk da a hankali dai yake tafiyar.

Su na zuwa gida, ta dafa ruwa ta yi masa wanka tsaf, ta canza masa kaya. Ta lallaSa shi da ?yar ya Wan ?ara Abinci.

Cikin damuwa ta ce "Sayyid, wai ya aka yi ka samu hawan jini dan Allah, ko wani abun nake yi maka da baka jin daWinsa?" Ya girgiza kai alamar a'a.

"Amma na yi mamaki. Saka mini lambar Habu, ai ya kamata na sanar masa" ya karSi wayar, ya dannan mata lambobin, ya mi?a mata. Ta karSa tana jiran wayar ta shiga, amma waya ta ?i shiga. Wai layin a rufe yake.

Cikin damuwa ta girgiza kai ta ce "Layin a rufe yake, bari zuwa anjima sai na sake gwadawa.

Horn Win motar Hajiya Halima ne ya cika layin, Nana ta Wauki hijabi ta fice. Yana ?o?arin yin magana amma ba ta tsaya ba.
Ta le?a ta tabattar Hajiya Haliman ce, sannan ta buWe gate Win.

Hajiya ta shigo da motar, Nana ta rufe ?ofar, ta dawo ta nufi motar Hajiyan, ganin ta tsaya ba ta wuce ciki ba.

Nana ta ce "Hajiya sannu da zuwa"

"Meye haka? Ina mai gadin da ba zai fito ya buWe gate Win ba? Ina ma ku ka tafi ne, babu wanda ku ka sanarwa, ku ka bar mana gida a haka, wane irin wula?anci ne haka?"

Cikin girmamawa Nana ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri. Wallahi ba shi da lafiya ne, hankali a tashe muka tafi Asibiti. Mun yi kuskure ki yi ha?uri dan Allah"

"To dole ne? Idan ba zai iya ba ai sai ya ajiye aikin ko? Amma ba zai yiwu na Wauke shi aiki, ya din ga bar mini gida haka ba. Kwanaki ma haka ku ka yi mini, ya ce ke ce ba ki da lafiya, shikenan ku kullum cikin ciwo ku ke, idan ba zai iya ba ku ajiye mini aikina, na nemi wani" gaban Nana ya yi mummunar faWuwa, jikinta ya yi sanyi sosai. Ta ce "Ki yi ha?uri dan Allah" Hajiya Halima, ta fizgi motar, ta yi cikin gidan.

Tun da Nana ta koma Wakin, ya ?ura mata ido, amma ta basar ta ce "Sannu Sayyid" kawai ya kawar da kansa ya lumshe idanunsa.

****
Cikin damuwa Fadila take yi wa Hajiya Suwaiba magana, duk da yanayin fuskarta cikin ko in kula take amsa mata.

"Ni gani nake kamar za mu Wora wa Alhaji Zailani Wawainiya a ce mu koma Asibitin da yake da file, ya Wauki nauyin Daddy. Kin ga haryanzu kashe kuWi ake yi, ba ma a gano me yake damunsa ba. Amma shi Alhaji Zailani ya dage, kina ganin babu matsala?"

"To da da matsala zai ce, a kai shi ne? Tun da mun kasa affording nan Asibitin, kuWinmu ya ?are, idan muka koma na gwamnati, ai dariya za a yi masa. Gara mu koma can Win".

Raudah da a baya, take biyewa mahaifiyarta ita da ?annenta, suke zabga wa Fadila rashin kunya son ransu, yanzu gaba Waya ta saduda. Musamman ganin yadda Fadila ba ta da nutsuwa duk ta rame, saboda damuwa saSanin da da suke tunanin, kuWin mahaifinsu ne kawai ya sanya ta aure shi, kamar yadda mamansu ke nanata musu.

Ta ce "Mummu Anty fa gaskiya ta faWa, nima gani nake yi, tamkar Wora wa Daddyn su Shukura nauyi ne, ba fa mu san ranar barin Asibiti ba"

"Na saka baki da ke ne?" Rauda ta girgiza kai tare da yin shiru.

Fadila ta sake cewa "Ni kuwa ya maganar kuWaWen kuwa? An gama biya ko haryanzu da saura?"

"Da an gama biyan ai za ki ji"

Fadila ba ta ha?ura ta sake cewa "Dama gidan da Umma take ciki ne, shi ne ya bata, mun yi magana da ita, a sayar da shi za ta koma gidan Yaya da zama. Sai kuma gwala-gwalaina na aure, duk su na nan. A sake rage bashin, a kuma biya kuWin makarantar su Hibba. Jiya da ya Wan farfaWo sai da ya yi maganar su. ?uri Hajiya Suwaiba ta yi mata da ido, domin ta tabattar da gaske take yi, ko kuma makirci ne kawai da iya Duniya.
"Fadila" ya kira sunanta da ?arfi.

Gaba Waya suka nufe shi, saboda tun jiya bacci kawai yake yi, kamar sumamme.

"Kar ki sayar da gidan Umma, ba ta na yi. Ni Allah zai kawo mini Wauki" Ya yi maganar tamkar yana magana da kurame, saboda yadda yake Waga murya.

Fadila ta ce "To, ba sayarwa za a yi ba"

"Kin haihu ne?"

Ta ce "A'a"

"To Allah ya raba lafiya. Dan Allah ku cewa likitan nan, ya zo ya cire mini robar fitsarin nan, ta dame ni wallahi"

Rauda da idanunta suka cika da hawaye ta ce "Daddy ka yi ha?uri, ka ga ba iya tashi ka ke yi ba, zuwanka banWaki zai baka wahala. Ka yi ha?uri ka bar robar fitsarin nan "

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan Raudana, na gode"

"Sannu Daddy" ta yi maganar idanunta na zubar da hawaye.

A ranar Alhaji Zailani ya aiko da mota, aka mayar da Alhaji Fatuhu Asibitin su Doctor Sharif.

A gaban iyalan Alhji Fatuhu, ya din ga jaddadawa Doctor Sharif, a kula da amininsa, duk abin da ya kama a yi masa, shi zai din ga biya. Suka yi ta godiya.
Daga bisani ya bi bayan Doctor Sharif, suka fita.

"Ka na ji na Sharif?"

"Eh Alhaji"

"Wannan mutumin ko me za a yi masa, ba zai taSa warkewa ba. Kawai dai ku din ga yi masa abin da ya sauwwa?a da duk wani abu da zai ?ara rikita masa jiki. Ka sanya ido sosai a kansa, zan din ga kiran ka, ina jin halin da yake ciki. Zan tafi umara ne."

"Ba ka da matsala Alhaji"

"Shikenan, za ka ga sa?o in sha Allah"


****

Nana kuwa tun tana kiran lambar Habu, tana sanya ran za ta same shi, zai Wauka har ta sare.

Ga jikin Sayyid sai godiyar Allah, babu wani ?arfi a tattare da shi. Sai dai akwai ?arfin hali, a haka wasu lokutan yake fita buWe gate.

Jiki a sanyaye take kallon shi, ta ce "Sayyid, gobe in Allah ya kaimu, Litinin za mu je gwaje-gwajen da aka bamu, ga shi haryanzu ban samu Habu a waya ba. Ko gidan zan je na duba ko lafiya?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a" ta yi shiru tana kallonsa, dabara ta faWo mata, ta Wauki wayarta ta fara duba lambar Hajiya Amina. Amma ko sama ko ?asa ta nemi lambar a wayar ta rasa. Ta duba iya in da za ta iya dubawa amma ba ta samu lambar ba.
Ta Waga kai ta kalle shi, ta ga ya lumshe idanunsa, jikinta ya ba ta shi ne ya goge lambar ba wani ba.

Ta koma gefe ta yi shiru, ta rasa abin da yake yi mata daWi a ranta, gaba Waya a tsorace take da ciwon nan nasa. Cikin dare ba ta iya bacci, da ta fara bacci, sai ta tashi, ta duba ta ga ni ko yana numfashi, ta Wora hannunta a kan ?irjinsa, ta ji ko zuciyarsa na bugawa, gaba Waya ba a nutse take ba.

Daren ranar Lahadi, Nana ta tafi cikin gidan, domin sanar da Hajiya Halima, batun komawa Asibiti da za su yi da safe.

Siyama ta tarar a falo, tana kallo tana ciye-ciye.

Nana ta ce "Dan Allah gurin Hajiya na zo" ko inda Nana take ba ta kalla ba, ta ci gaba da kallon Tv. Ganin Siyama ba ta da niyyar kula ta, ya sanya ta nemi guri ta zauna, ta fara zaman jira.
A?alla Nana ta shafe awa Waya da rabi, ?arshe ma Siyama ta tashi ta bar mata falon. Har Nana ta yanke tsammanni, sai ga Hajiya Halima ta saukko daga kan bene.

Nana ta yin?ura ta ce "???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Hajiya ina wuni"

"Lafiya ?alau" ta nemi guri ta zauna.

Ya kalli Nana ta ce "Ya aka yi?"

"Dama Hajiya zuwa na yi na gaya miki dan Allah gobe in Allah ya kaimu, za mu yi sammako, mu je Asibiti ne an bamu gwaje-gwaje, shi ne na ce bari na zo na gaya miki kar mu yi laifi".

Kamar Hajiya Halima ba za ta yi magana ba, sai kuma ta kalli Nana ta ce "Shi kuma gadin, da buWe gate Win ni zan? je na zauna na yi?"

Nana ba ta yi tsammanin jin haka daga bakin Hajiya Halima ba, amma ta dake ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri Hajiya, in sha Allah ba zamu jima ba, ki yi ha?uri"

"Ni fa kin ga Nana, idan abin nan ba zai yiwu ba, a ha?ura kawai. Na nemi wani, ku je ku nemi lafiya babu yadda za a yi ga aiki, sai dai ku bar mini ?ofa ku na can yawon Asibiti, ba fa zai yiwu ba"

Nana ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri, na sani amma in sha Allah zai samu lafiya ya ci gaba da aikin, ki yi ha?uri"

Hajiya Halima dai, ba ta cewa Nana su je ko kar su je ba, Nana ta tashi ta koma Wakinsu, duk jikinta a sanyaye.

Wayewar garin Litinin, Nana ta kammala komai da wuri, ta tafi cikin gidan, domin sake gaya wa Hajiya Halima, amma ta tarar ba su ma tashi daga bacci ba.

Ta ga idan ta tsaya jira, za su iya makara, dan haka ta fice, ta samu abin hawa suka tafi.

Nana ta Wauka abin mai sau?i ne, amma wuni suka yi yawo, daga nan zuwa nan, wasu gwaje-gwajen, aka ce ma ba za su fito a ranar ba, sai bayan kwanaki biyu. Ga shi duk kuWin hannunta suka ?are. ?arshe ba su samu ganin likita ba, da tasa tasan da suke hannunsu ba, saboda sai bayan la'asar li?is sannan suka samu teses Win.

Su na komawa Nana, ta Wora girki, zuciyarta ta yi ta raya mata, ta je ta gurin Hajiya Halima dai, ta ?ara ba ta ha?uri, amma ta fasa saboda ba ta san me za ta tarar ba, kar ta yi mata wula?anci.

Nana ta ci gaba da bashi magungunansa, tana kula shi, zuwa kwanaki biyun da aka Wibar musu, komawa karSar sakamako. Idan ana bu?atar buWe gate, ita take zuwa ta buWe, idan kuma ya ji jikin nasa da sau?i, sai ya je ya buWe da kansa.

Nana ta sake zuwa ta sanar da Hajiya Halima za su koma Asibiti, nan ma ta din ga ?anan maganganu, Nana dai ta yi ta ba ta ha?uri. Ta fito suka fita da Sayyid.

Suka fara zuwa, suka karSo gwaje-gwajen, suka koma Asibiti. Sai dai wani likitan suka gani daban.
Likitan ya ce ba za su iya kula da case Win sa a nan ba, saboda akwai matsala a zuciyarsa, dan haka aka tura su Asibitin gaba.
Can ma da suka je, aka yi masa hoton ?irji, aka yi masa ECG, shi ma da ?yar suka samu, dan sai da Nana ta bayar da cin hanci, sannan aka yi cuku-cuku, aka ba su result Win a ranar, sai dai shi ma da suka koma likitan da zai duba su, ya tafi. Nana tamkar ta Wora hannu a ka ta fasa ihu, gaba Waya ma ta rasa abin yi, ga shi dakiya kawai take yi, ba ta son ta yi kuka ya gani, ta san yana yin kuka, za ta Waga masa hankali. Kawai ta zauna ta yi shiru ta rasa abin da yake yi mata daWi.

"Mu tafi gida"

"Sayyid ba mu ga likitan ba zamu koma?"

"Eh mu tafi" jiki a sanyaye Nana ta tashi, suka nemi abin hawa suka koma gida.

Sai dai su na zuwa gidan, suka din ga bugu, amma gate Win a rufe. Tun Nana tana sanya ran za a buWe har ta sare. Ta zauna a kan Wan dakalin da Sayyid ya zauna, ta rasa abin da yake yi mata daWi.

Ta sake jarraba kiran wayar Habu, amma still ba ta shiga, ta damu sosai da rashin jin Wuriyar su Habu. Ta samo ruwa suka yi salla a ?ofar gida, tana ta tunanin mene ne abun yi? Har magariba ta yi, sauro ya fara bin su, Nana tana bugun gate Win, amma shiru.

"Sayyid yanzu mene ne abin yi?" Bai yi magana ba, sai ga motar Hajiya ta dawo, tare da Siyama.
Nana ta yi ajiyar zuciya, ta tashi ta nufe su fuskarta Wauke da murmushi ta ce "Hajiya ashe fita ku ka yi, kawo mukullin a buWe" ta mi?a wa Nana mukullin, ta buWe musu gate Win. Wani abu mai Waci ya War su a zuciyar Sayyid, ganin yadda Nana ke kokawa da ?aton gate Win da ya fi ?arfinta.
Ba su damu da tambayar Nana ya mai jiki ba, amma Siyama? ta ?ura masa ido, tamkar idonta zai faWo.

Suka wuce da mota, Nana kuma su ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login