Showing 81001 words to 84000 words out of 190498 words

Chapter 28 - Buzu Book 1 Complete

koma Wakinta ta Wauki wayarta ta kira Malam Wayyabu.

Sai da ta kusa tsinkewa ya Waga, "Malam yaya a ke ciki? An gama aikin ne?"

"Eh a kan aikin muka kwana jiya"

"To shikkenan, na gode sosai da sosai, baban nata fa ka yi aikin a kansa?".

Ya ce "Kar ki damu, ba wanda ban yi ba fa"

Ta ajiye wayar, tana kuma tunanin me yakamata ta yi.

Kafin azahar Wan aiken Alhaji Zailani ya zo, ya kawo uban kayan abinci kamar za a buWe ?aramin shagon sayar da kayan abinci. Bakin Baba ya ?i rufuwa, sai shiga yake yana fita yana washe baki, yana ?iyasata irin abin da zai yi wa Nana muddin ta bijirewa auren Alhaji Zailani.
Yaron nasa ya sanar da Baba cewar, tafiyar gaggawa ta kama Alhaji Zailani, washegari zai dawo, amma ko baya nan bai dawo a goben ba, za a Waura auren nan ranar Juma'a, kuma ba ya bu?atar taron jama'a, waliyyai kawai sun isa.
Baba yana tsuma ya tabattarwa da yaron Alhaji Zailani, mai suna Sani cewa ya tabattarwa da Alhaji Zailani ba za a samu wata matsala ba.

Nana kuwa gaba Waya ji ta yi jikinta ya ?ara sanyi, tun da garin Allah ya waye, komai ba ya yi mata daWi, tamkar ta mutu ta huta.
Duk mutanen gidan sun koma baccin safe, ta shirya ta fice daga gidan.

A hanya gari ya ?arasa wayewa Nana, ta je ta din ga bubbuga gate Win, aka zare sakata aka buWe. Sai dai maimakon ya ba ta hanya, sai ya zura mata idanunsa yana kallonta. HankaWa ?ofar ta yi ta shiga a fusace, ta tsani wannan Wan iskan kallon da yake yi mata, shi kuma kullun fuska a rufe, ba a ganin fuskarsa sai dai ya yi ta kallon mutane.
Burki ta ja ta tsaya, tana kallon yadda ?osassun karnukan nan, suke safa da marwa a harabar gidan. Ta waiwayo ta kalle shi, ya kawar da kansa kamar bai gan ta ba, ya mayar da gate Win ya rufe ya saka mukulli, ya nufi Wakinsu na masu gadi.
Karnukan suka yi cirko-cirko suna kallon Nana, su na haushi.

"Dan Allah ka raka ni bakin ?ofar shiga" ta yi maganar a marairaice. Bai kulata ba ya cigaba da tafiya. "Dan Allah idan ba za ka raka ni ba ka buWe mini ?ofa na koma". Ganin da gaske ba zai rakata ba, kuma ba zai buWe mata ba, ga karnuka su na nufo ta, kawai ta rufa masa baya da gudu. Ya tsaya ya waiwayo ya kalleta. Ta ja ta tsaya cikin tsananin tsoro.

Sule ne ya fito yana mi?a da alama a lokacin ya tashi, ya kalle su ya ce "Nana lafiya na ganki da sassafen nan? Kuma ya na ganku a tsaye haka lafiya dai?"

"Tsoro nake ji, na ce ya raka ni ya?i, kuma ya kalle ?ofa ya ?i buWe mini na koma gida, kuma so suke su biyo ni su cije ni" ta yi maganar idanunta na cika da hawaye saboda tsoro.

Sule ya yi dariya ya ce "yi ha?uri, ni ban san dalilin da ya sanya ku ke yawan samun saSani da Buzu ba. Jira ni na Waure karnukan sai ki wuce"

Ta goge hawayen ta ce "To na gode sosai" Shi kuwa tuni ya shige Wakin su, ya bar ta da Sule.

Ko da Nana ta shiga cikin gidan, Wakin Haidar ta nufa kai tsaye, yana kwance yana ta baccinsa. Ajiyar zuciya ta?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? din ga saukewa, ta dur?usa a gabansa ta dafa kansa, tana karanto masa addu'oin da suka sauwwa?a a bakinta. Tana Wan tofa masa. Wata irin razana ya yi a baccin, har da Wan ihunsa, Nana ta rungume shi, ya ?an?ameta ta cigaba da yi masa addu'a.

Yau Shukura ta na gida, sun yi hutun makaranta. Har mamaki take yi yadda Nana ba ta gajiya da abin da Haidar yake yi mata na hayyata irin ta su ta yara.
Duk motsin da ya yi, ta san me yake nufi, zuwan Nana gidan ya yi ?iba ya zama ?ato saboda yadda yake cin abinci. Ga kuma karatu da take koya masa, har da addu'oi.

Nana ta ce "Shukura" karon farko da ta taSa kiran sunanta, Shukura ta kalli Nana da mamakin tsaurin idon da ta yi.

"Na san ba zan dauwwama ina kula da Haidar ba, amma dan Allah ina son ko yaya ki ajiye a?idar boko, ki din ga jansa a jiki, kuma ki tsayawa azkar Win sa da kula da yi masa addu'a. Ke kanki ki ?ara ?aimin addu'a sosai da sosai, ka na da ido ne kawai amma ba na ganin gari ba, abin da Allah ya so kawai shi muke gani"

"To da na ce miki ba na addu'a ne, da za ki buWe ?azamin bakin ki, kina kiran sunana haka kai tsaye ni sarki ce?"

Nana ta kalli Shukura ido cikin ido ta ce "Ni ki ke cewa mai ?azamin baki! To kar ki yi abin da na ce, idan kin ?i ji ai ba za ki ?i gani ba"

Babban abin da ya bawa Shukura mamaki, bai wuce yadda ta ji tamkar an saka mukulli an rufe mata baki ba, bayan sun haWa ido da Nana ba, ta yi gum ta kasa cewa komai.

Gaba Waya Nana ta manta da wani sharaWi da Baba ya kafa mata ma, hatta batun auren Alhaji Zailani ma sai ta daina jin ya dame ta, mummunan mafarkin da ta yi da su Shukura ne kawai yake damunta. Sai kuma wata irin fargaba da ta rasa ko ta mece ce.
Domin ragewa kanta damuwa, tare suka yi girkin dare da Jummai. Hajiya Amina ce ta ce "Nana ki zo ki tafi, na ga alamun hadari a garin nan, kuma tun da ba abin da ki ke yi"

"A'a kar ki tafi" Haidar ya yi maganar yana ri?e rigar Nana.

Nana ta kalle shi da murmushi a fuskarta ta ce "Idan na zauna zaka goya ni?"

"Eh zan goya ki, ki yi bacci" ya yi maganar cike da shirirtar su ta yara.

Da ?yar a ka yi masa wayo, Hajiya Amina ta Wauke shi, Nana har za ta fita, Jummai ta biyo ta da kular abinci ta ce "Dan Allah Nana ki ajiyewa masu gadi, na san yanzu su na can waje shan wannan shayin nasu na ibada, ba za su dawo ba sai cikin dare. ki Wan tura Wakinsu ki ajiye musu, idan ba su san an ajiye ba, karnuka ne suke zubar musu. Jiya da na ajiye musu a waje ba su sani ba, su ka kwance karnuka, aikuwa su na sako su, suka je in da aka ajiye abincin suka kifar, suka hau ci" Nana ta Wan yi Jimm sannan ta karSa ta fita.

Kamar yadda Jummai ta faWa kuwa, Nana tun kafin ta ?arasa bakin gate Win, take jiyo hayaniyar buzayen a ?ofar gida, alamun duk su na waje a ?ar?ashin bishiyar da suke zama da yamma su sha shayi, su yi wasan takobuna.
Amma duk da haka sai ta tsaya a ?ofar Wakin nasu tana sallama, ko za ta ji an amsa, amma ta ji shiru. Sai ta Wan tura ?ofar Wakin, wani irin ?amshin turare ya kawo wa hancinta ziyara.
Ta zura flask Win abincin, ta yin?ura za ta tashi, kawai ta ji kukan Haidar a cikin Wakin yana kiran sunanta. "Anty Nana, ki zo)
Ba ta yi nazarin komai ba, balle tunanin ta baro Haidar Win a cikin gida ba, kawai sai ta Wimauce ta hankaWa ?ofar Wakin ta shiga.
Cak ya tsaya ya waiwayo ya kalli inda take tsaye. Daga shi sai dogon wando, hannunsa ri?e da mataji, yana taje dogon gashinsa da ya kwanta a kan kafaWarsa zuwa dokin wuyansa. Gefensa butar shayi ce, take ta dahuwa a kan wuta, kuma da alama a cikin wutar aka zuba turaren wutar da yake tashi.
Cikin matsanancin tashin hankali tsoro da razani, ta yi yin?urin juyawa ta fita, amma ?ofar Wakin da tagogi suka kulle, sautin wata irin guguwa ya karaWe Wakin. A take ya rikiWe daga kamaninsa zuwa wannan tsohon mai kama da ?aisar, ya bayyana cikin suffa mai matu?ar ban tsoro, ya buWe ?aton bakinsa mai kama da bakin tsohuwar rijiya, ya fara fito da wata irin wuta Jawur tana wani irin haya?i, lamar gobarar tankar mai.
Iya ?arfinta ta dafe kanta, ta ?wala ihu ta faWi a gurin sumammiya. Jin ihunta ya sanya ya sake waiwayawa ya kalle ta, ya ganta a ?asa ba ta ko motsi. Ya ?arewa Wakin kallo domin ya ga abin da ya razanata amma bai gani ba.
Ya mayar da hankali ya ?arasa taje gashinsa, ya tufke abinsa, ya zira rigarsa, ya shafa turare sannan ya kawo rawaninsa ya naWa. Ya zauna a gaban shayinsa, ya fara tsiyayowa yana kurSa a hankali tamkar shikaWai ne a cikin Wakin babu wata halitta kuma.

Gidansu Nana tun da aka yi sallar magariba, Nasiru ya shigo gida yake tambayar ko Nana ta dawo.
Suwaiba ta ce "wai kai Nasiru Nanan nan uwarka ce ne?"

"Ban sani ba, idan ma uwar ta wa ce ina ruwan ki?"

Cikin hasala ta ce "Idan na kama ka wallahi sai na gwara kanka"

"Ba ki da wannan ?arfin wallahi" ya yi maganar yana fita. Ya zauna a ?ofar gida yana kallon hanya, amma babu Nana babu alamar ta. Tsoro ne ya fara kama shi, kar ya je ko ta sake Sata aljanun nata sun kai ta wani gurin.
Yana zaune ya hango Baba ya nufo gida, hannunsa ri?e da manyan ledoji.
Nasiru ya tashi ya karSo masa kayan suka shiga gida.

Su na shiga Nana ya fara tambayar Mama, amma ta ce ba ta dawo ba. A take hankalin Baba ya tashi, ya fara tunanin ko dai ta gudun ne?
Sai a lokacin ya fara binciken ina ne gidan da Nana take aiki, tun da take zuwa bai taSa bibiyar ina take zuwa aikin ba.
Gaddafi baya nan, dan haka ya Wauki Nasiru, suka fita neman Nana.

Gurin ?arfe tara na dare, Gaddafi ya dawo gida, ya shigo cikin gida zai wanke kayansa, yana neman Nasiru zai aike shi. Suwaiba ta gaya masa halin da ake ciki. Ya yi saroro ya ce "Yanzu har ?arafe tara ba a san inda take ba? Kuma babu wanda ya san gidan aikin nata?"

Jamila ta ce "Ni dai ta taSa kwatanta mini, can wajen quarters Win markaz ne, wai gidan Alhaji Zailani"

"Sako hijjabin ki mu je, mu duba"

Mama ta ce "Ku je ina? Babu inda za ta je"

Ya haWe rai ya kalli Jamila ya ce "Ba magana nake yi miki ba, sai na taka wuyanki tukuna?" Ba Jamila ba ita kanta Mama sai tsuke bakinta ta yi, dan iya ashariyar Gaddafi ta ishe su.

Sam ba su sha wahalar gano gidan ba, kasancewar Alhaji Zailani sanannen mutum, saboda yawan kyautar da yake yi da taimakon al'umma.
A tsatstsaye suka tarar da mutane a ?ofar gidan, buzaye sai magana suke yi da yaren su.

Kai tsaye Gaddafi ya kutsa suka shiga cikin gidan, mutane ne a tsaye a ?ofar Wakin masu gadi, ga matar gidan a tsaye fuskarta Wauke da damuwa.

Gaddafi ya nufe ta, suka gaisa ya ce "Dan Allah ni yayan yarinyar da take yi muku aiki ne, Nana tun da ta fita tun safe bamu ganta ba, shi ne muka zo nan ko ta zo?"

Hajiya Amina ta ce "Alhamdilillah mu na ta tunanin yadda za a yi, tun bayan la'asar muka yi sallama, ta tafi gida. yanzun nan yarona ya shigo yana gaya mini wai masu gadi sun ganta a Wakinsu a sume, su suna waje, mutum Waya suka bari a Wakin, shi kuma ba shi da lafiyar ?wa?walwa, ya ?i magana an rasa wanda zai taSa ta ma. Yanzu nake tunanin ya za a yi a samo wani daga gidansu, dan ni ban san gidansu ba"

Gaddafi ya ce "?akin masu gadi kuma?" Ya juya ya nufi Wakin.

Nana na sume a tsakar Wakin, gefe guda shi kuma yana zaune yana kaWa ?afafuwan sa, tamkar ba ya jin hayaniyar da ake yi.

Gaddafi ya nufi Nana da sauri, ya Wago ta, yatsun hannunta da na ?afarta duk sun ?andare kamar wadda ta daWe da mutuwa, ga jikinta sanyi ?alau.

Ya Waga kai ya kalli Buzun nan da duk abin da ake yi, sabgar gabansa kawai yake yi, ya kalli Nana. Duk da ba shiri suke yi da ita ba, amma ya san Nana ba ta cikin jerin yara marasa ji, amma me ya kawo ta Wakin masu gadi?.

Hajiya Amina ce ta saka Yusuf ya Wauki su Gaddafi ya tafi kai su gida.

Cikin damuwa Habu yake dubansa ya ce "Buzu, ya aka yi yarinyar nan ta shigo Wakinmu, me ya same ta? Me yasa kuma ba ka kira wani daga cikinmu ba?" ?aga idanunsa ya yi ya kalli Habu, a dole Habu ya ja bakinsa ya tsuke, duk da tarin tambayoyin da suke bakinsa.

Cike da takaici, da matsananciyar tsana da damuwa, Baba yake kallon Nana yake maimaita a Wakin masu gadi ka gano Nana?"

"Idan an yi magana a ce aljanu ne suka hanata aure, ga ha?i?anin abin da ya hanata aure nan ai" Mama ta din ga faWar maganganu. Jamila ta ce "Mama ba lallai abin da ki ke tunani ba ne ba, kin san ba ta da cikakkiyar lafiya"

"Eh ban sani ba sai yanzu da ki ke gaya mini, rashin lafiya ne za a ganta a Wakin masu gadi da wani?"

"To ai an ce mahaukaci ne, har fa muka taho yana kallon dandazon mutane, bai yi magana ba, kuma bai fito ba" cewar Jamila, dan ta ?i yarda zuciyarta ta bata wani mugun abin Nana take aikatawa.

Kawai Baba ya tafi Waki, Mama ta bishi tana faWin "Yanzu baban Jamila, baka gudun a zo a ji kunya? Wallahi tun da ta fara haka, ko an yi auren nan ba za ta zauna ba, kunyata ka za ta yi, tun da ta furta maka ba ta son auren nan, take ta wannan iskancin. Maza nawa ta ce ba ta so? ko dai ka san abin yi ko kuma abin da za ta yi a gaba sai ya fi na yanzu muni"

Wata irin tafasa zuciyar Baba ta din ga yi, tafasar da tun da yake bai taSa jin zuciyarsa ta yi ba, wata irin matsananciyar tsanar Nana ta mamaye zuciyarsa.
Kamar mahaukaci haka ya fito fiuu ya yi waje.

Ayshercool
08081012143
25

Ko da Baba ya fita Gaddafi ya nemo, a gurin masu shayi.

Gaddafi ya ce "lafiya kuwa?"

"Ofishin 'yan bijilanti zaka raka ni"

"Amma a daren nan? Me ya faru?"

"Mu je za ka gani"

Gaddafi ya bi Baba zuwa gurin 'yan bijilanti.

Baba ya shigar da ?orafi, a kan zargin yin lalata da yarinyar sa.

Gaddafi ya ce "Baba, babu tabbacin abin da ka ke faWa fa?"

"Babu tabbaci, aka same ta a Waki tare da shi sama da awanni?"

Gaddafi ya ce "Amma ai ka san ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba"

"Ka rufe mini baki Gaddafi" Gaddafi ya yi shiru, 'yan bijilanti suka bayar da mutum biyu, tare da Gaddafi aka tafi taho da Buzu.

Hankalin Habu ya yi mummunan tashi, ganin wai an zo a tafi da Wan uwansu gurin hukuma. Cikin damuwa ya ce "Wallahi ina da tabbacin babu abin da ya yi mata, ba shi da cikakkiyar lafiya ?wa?walwa ne, amma ba wani abin ya yi mata ba, ai mutane sun ga a yadda muka tarar da su"

Jami'in bijilanti ya ce "To ka Waukko takardar shaidar ba shi da hankalin, ka haWo da ita mu tafi, ko ce maka aka yi mahaukaci ba zai iya wani abun ba" sauran buzayen ma duk hankalinsu a tashe.

Haka aka tasa Buzu da Habu, da wasu daga cikin buzayen, suka tafi ofishin 'yan bijilanti.

Shugaban gurin ya ce "Waye daga cikin su, aka tarar da su a Wakin? Ina kuma ita yarinyar?"

Baba ya ce "Tana gida a sume"

"A sume kuma? Shekararta nawa?"

"Shekara ashirin da Waya"

"Ikon Allah, to waye a cikin su?" Gaddafi ya nuna Buzu.

"Kai malam ya aka yi aka tarar da kai daga kai ita a Waki, tsawon awanni, sauke rawanin nan na fuskarka ina magana kana kallona"

Habu ya ce "YallaSai ba shi da cikakkiyar lafiya fa, wallahi taSin hankali ne da shi, ina da tabbacin babu abin da ya haWa shi da yarinyar nan"

Sule ya ce "Ba ma sa shiri da ita, wallahi rashin fahimta aka samu, na ga kwanon abinci a Wakin, ina kyautata zaton ma abinci ta kai mana, akwai dai abin da ya faru tabbas"

"Ba da ku nake magana ba, ka buWe baki ka yi mana bayani, ko kurma ne?" Shugaban bijilanti ya yi maganar yana kallon Buzu. Amma bai ko motsa ba, balle ya yi magana.

Ya sake tsuke fuska ya ce "Sauke rawanin nan kafin na saka a sauke maka shi yanzun nan, ka ?unshe fuska kamar Wan taliban" ?ura masa ido ya yi bai yi magana ba.

Habu ya ce "Ka cire rawanin dan Allah, ka yi maganar abin da ya faru"

Sule ne ya kai hannu zai sauke masa rawanin, amma ya ri?e masa hannu.

"Dattijo, alamu sun nuna fa mutumin nan da gaske mahaukaci ne"

Baba ya ce "Wallahi ko dawanau ce a kansa sai an bi mini hakkina, dama 'yan kwanakin nan shi ne yake hure mata kunne, sai ta kai bayan magariba a waje ba ta dawo ba. Ta ?i aure fafur kowa ya zo ba ta so"

"To kai Baba ya ka ke so a yi? Kana gani ya ?i magana, ita yarinyar ba ku zo da ita ba, ni wannan case a bari gobe in Allah ya kaimu ku tafi gurin 'yan sanda".

Baba ya ce "Duk fa wata shaida da ake nema, ta tabatta tun da abin da suke yi kenan, sai ya aure ta ya je su ?arata" gaba Waya suka kalli Baba. Cikin tashin hankali Habu ya ce "Dan Allah dattijo ka yi ha?uri, wallahi ba su saba yin komai ba, wannan karon ma rashin fahimta ne, Nana mutuniyar kirki ce, shi kuma ba shi da cikakkiyar lafiyar ?wa?walwa, dan Allah ka yi ha?uri"

"Wallahi ba zan ha?ura ba, daga nan har kotun ?oli mu je, a karSa mini hakkina na ci mini mutunci ta hanyar yin lalata da 'ya ta, ana daf da Waura mata aure" Gaddafi dai ya yi shiru yana kallon ikon Allah, bai ta taSa tunanin Baba zai Wauki irin wannan matakin ba.

"Dan Allah ka yi ha?uri, ka ga nan ba ?asarmu ba ce ba, idan aka kai mu gaban shari'a wahalar da mu za a yi, dan Allah ka yi ha?uri"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login