Showing 48001 words to 51000 words out of 190498 words

Chapter 17 - Buzu Book 1 Complete

Kuma kana kallo aka kashe malam Auwal ba ka yi komai a kai ba, banda zalunta ta ta azabtar da ni ba abin da ka ke yi"

Ya yi murmushi ya ce "Zuwa islamiyyar ta ki ba shi da amfani ashe, ai idan abin da ya fi haka za ayi masa ba ruwana, azabar da ya din ga saka ki na bani, na yi farin ciki da mutuwarsa, ki ro?a masa Allah gafara, dan wasu lokutan idan damuwa da gajiya ta yi masa yawa, yan shan ?wayoyin gusar da hankali ya yi bacci mai tsawo. Sannan akwai tarin hotunan 'yan mata a wayarsa, ke har ma hirar tsakar dare a dandalin sadar da zumunta yana yi na rage zafi da 'yan mata..

"?arya ka ke yi, wallahi ?arya ne ba dai malam Auwal ba... Nana ta katse shi cikin ?arji.

?aisar ya ce "Ai dama ban ce ki yarda ba, ku bil adama ma akwai wanda ya kai ku ?arya ne. Sarkin baka kuma zan kasa zan tsare sai na ?arasa shi, saboda ba neman sadaukar masa da ni ne kawai ya sanya na yi masa wannan hukuncin ba, wani gagarumin laifi ya taka mini da sai na ga bayansa"

"Dan Allah kar ka kashe shi, mutumin kirki ne, kuma mutane wasu sun yi imani da maganinsa, marasa ?arfin da ba za su iya jelen Asibiti ba, yana taimaka su babu ko kwabonsu"

A hankali ya fara zagaya Nana ya ce "Gaba Waya halayyarki ba ta da saiti, kin gama kushe abin da yake yi, yanzu kuma kin ce a ?yale shi, mutane na amfana. Idan ya mutu sai ki je ki gaje shi, tun da dama ya kai ki ya nuna miki magunguna. Kwanta ki yi bacci kafin ?wa?walwarki ta samu matsala, ki shirya tarar sabuwar matsalar da take tunkarar mu daga ni har a dalilin zuwan ki gidan wannan mutumin.

Za ta yi magana kawai ta daina ganin komai, sai juyi da ta yi a Wakin da take, cikin magagin bacci. ?o?arin yin?urwa take yi ta tashi, amma wani irin bacci mai kama da fita daga hayyaci ya yi awon gaba da ita.

Bayan kwanaki uku, jami'an tsaro ba su fasa zarya a gidan su Nana ba, a kan neman Imran. Ga fitina da mama take yi a kan zaman Nana, abu ya ?i ci ya ?i cinyewa, sai da ma?wabta har da mai unguwa su ka shiga lamarin, aka din ga rarrashinta, aka din ga janyo mata ayoyi da hadisai, a kan tauhidi da Wayanta al'amura. Nauyin manyan mutanen da suka haWu, ya sanya ta ce ta ha?ura Nana ta zauna, zuwa lokacin da za a Waura mata aure.

Nana gaba Waya lamarin da yake faruwa a gidan na su baya gabanta, har da batun Waurin aurenta da ake yi, sati biyu masu zuwa. Rashin samun Abincin nan da ba ta yi, ya fara damunta dan sannu a hankali mutuwar malam Auwal ta fara sakinta, sai dai duk lokacin da ta tuna shi sai ta yi masa addu'a.
Tana zaune a tsakar gida da yamma, Suwaiba na tsakar gida tana ta jin kaWe-kaWe a wayarta, kanta ko Wan kwali babu.
Bararojin nan ce a zaune a kusa da Suwaiba, jikinta duk ya ciko ta warke, ta zura kanta kusa da Suwaiba tana le?a wayar ita ma.
Nana ta yi shiru tana kallon Suwaiba, tana son ta yi magana, amma tana tsoron abin da ka iya biyo baya.

"Ke Suwaiba, tashi ki shiga Waki, dan jaraba kalli yadda ta zura miki idanu, kar ta ?arasa tanWe ki" Mama ta yi maganar cikin haWe rai.

Suwaiba ta kashe wayar, ta yin?ura ta tashi, aikuwa matar ta haWe rai, kafin Suwaiba ta kai Waki, ta hankaWeta ta faWi ?asa.

"Kin gani ko? Abin da nake faWa ko? Dama na ce ba zan zauna da yarinyar nan ba, gashi dai sai ta kashe mini 'ya hankalinta zai kwanta"

Kawar da kai Nana ta yi gefe, ta ci gaba da zancen zucinta, dan ba hatsaniyar gidan ce a gabanta ba yanzu.

Da daddare Nana ta tsaya tana ?arewa jakar da ta zo da ita daga gidan sarkin baka kallo, tun da ta zo da ita, ba ta buWe ta ga abin da yake cikin jakar ba.

Yau ma kwanan ihu Suwaiba ta yi, cikin ikon Allah Nana kuma, tun da ta dawo ba ta ihun nan da take yi da daddare sai Suwaiba.

Washegari Monday, Nana ta shirya domin jarraba zuwa makaranta, duk da ta san za ta sha bala'i gurin director, na rashin zuwanta tsawon lokaci, amma ta tafi cike da fatan Allah ya sassauta zuciyarsa ya sanya ya karSe ta, ya biya ta Albashinta, kuma ta ci gaba da aikinta.

Sai dai ta tarar da saSanin abin da take ta fata, domin kuwa ta tas director ya yi mata, ya ci zarafinta ya ba ta takardar kora. Jiki a sanyaye ta karSi takardar ba tare da ta buWe ba ta ce "To sir salaryana ka taimaka ka bani na last month"

"Ba za a bayar ba, shi ma last month Win wani zuwan kirki ki ka yi, kullum ba ki da lafiya"

Nana ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah ko rabi ne, ka taimake ni"

"Ba zan bayar ba, asarar da ki ka janyo mana, na wahalar neman wata malamar a kuWinki" Nana ta ji zafin korar da aka yi mata, duk da ta san laifinta ne, amma dai yakamata a bata hakkinta.

Ko sallama ba ta yi da sauran malaman ba, dama ba cikinsu take shiga ba, saboda yadda suke yi mata kallon Nanny kawai.

Dama da ?afa ta zo makarantar, dan haka yanzu ma ba ta da kuWin abin hawa, da ?afarta ta mi?i hanya.

Horn Win da aka ishe ta da shi ne, ya sanya ta tsaya, ta waiwaya. Motar baban Muhsin ta gani. Ya ?araso gurin da take ya ce "Anty kwana biyu lafiya kuwa? Muhsin na ta rikici ba kya zuwa makaranta shi ba zai zo school ba"

"Wallahi na Wan yi rashin lafiya ne"

Cikin tausayawa ya ce "Eyya Allah ya sauwwa?e, mun yi magana da director ya ce sallamarki zai yi, ba yadda ban yi ba, amma ya ?i yarda ya ha?ura" Nana ta yi guntun murmushi da iyakarsa laSSanta ta ce "Ba wani abu, rabona ne ya ?are a gurin kawai".

"Eyya babu daWi, to hawo na sauke ki a gida"

Ta girgiza kai ta ce "a'a ba komai na kusa ?arasawa ai"

"A'a da saura ai na sani, hau dan Allah" ya yi maganar yana buWe mata ?ofar gaban motar" ta yi bismillah ta hau.

"Wallahi ban ji daWin sallamar ki da director ya yi ba, ki na da ?o?ari matu?a gaya." A wannan karon ma murmushin dai ta yi tana wasa da yatsun hannunta.

"Ki bani takardun ki, na nema miki admission a school of legal studies, ko koma makaranta mana"

Ta girgiza kai ta ce "A'a na gode sosai"

"Me yasa? Karatun ne ba kya so? Nana ba zan cutar da ke ba. Ba na wasa da duk abin da ya shafi yarana, yanzu haka Muhsin ne ?arami, amma duk lokacin da nake gari ni nake kai shi makaranta, saboda yana son hakan. Da Wa da dukiya ba ayi musu mugunta ba ka san wa zai amfane su ba. Amma ki yi tunani idan kin amince zan samar miki admission ba, ko ba duka ba zan Wauki Wawainiyar karatun naki."

Cikin girmamawa ta ce "Ka na cikin mutanen da ba zan manta da su ba a rayuwata, ba zan so ka Sata kuWin ka ba, ina ga nan da wani Wan lokaci za a Waura mini aure, kuma garin zan bari gaba Waya"

"Allah sarki, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Bani wayar ki na saka miki lambata, idan lokacin bikin ya yi ki sanar da ni, zan halarci Waurin aure in sha Allah"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ni da waya ai, ka yi mini addu'a na gode sosai da sosai. Sannan a cewa Muhsin ya yi karatu da kyau, Allah ya yi masa albarka" jiki a sanyaye yake kallon Nana, haka kurum take ba shi tausayi gaba Waya yanayinta ya nuna akwai labari mai ban tausayi a tattare da ita.

Ya yi parking daidai gurin da take sauka, tana kiciniyar buWe ?ofar motar, ya mi?a mata kuWi, ya ce "Ga wannan ba yawa, Allah ya baki wani abin yin." Za ta yi magana ya girgiza mata kai. Ta saka hannu biyu ta karSa ta ce "Na gode sosai da sosai"? ya daWe yana kallon yadda take tafiya da ?yar ta shige cikin layuka.

*****
Malamin Hajiya Sa'a yana zaune, ya duba wurin da yake gabansa, ya kalle ta ya ce "Hajiya a wannan karon ma babu sa'a fa, 'yan aikenmu sun makara, domin fafur sarkin baka ya hana yarinyar nan, ?arshe ma ya mayar da ita gida, ya ce mu je can mu Wauke ta, yanzu haka tana can"

"Kai wannan wace irin masifa ce? Ni an taSa bani aiki mai wahalar wannan ma kuwa?"

Ya yi dariya ya ce "Ai na gaya miki hatsabibin aljani ne a tare da ita, kuma mutane irinmu, mu na burin mallakar aljani irinsa, domin kaf jinsin babu aljani mai tsananin juriya da kasada kamar sa, tun da sarkin baka ya mayar da ita ba tare da ya mallaki aljanin ba, na san akwai matsala. Yanzu ki bar wannan mu jingine ta zuwa wani lokaci kaWan. Yanzu ga wani aiki mai Wan sau?i, 'yar aikenmu na kan waccan yarinyar da ta yi amfani da turare kuma ta warke ma. Ki duba dangi wanda yake jininki ki samo yaro da bai wuce shekara biyar ba, a sadaukar mata da shi, domin ta ?ara samun kuzari zan sanya ta yi miki wani aiki"

Hajiya sa'a ta Wan yi shiru ta ce "Akwai Wan wa na, ba zai gagara ba"

"To shikkenan, tashi ki je, Sa'a na tare da ke Hajiya Sa'a tun da ki na bibiya ga duk abin da aka saka ki. Ki je za a sanar da ke lokacin da ake bu?ata" tashi ta yi tana jin daWin yabon da ya yi mata.

*****
Nana da ta koma gida, ta tarar an kai Suwaiba asibiti, daga gurin masu magani, wai jikinta babu jini an ri?e ta a asibiti.
Sam Nana ba ta yi gigin bin su ba, ta dai yi wa Suwaiba Addu'a. Ta duba kuWin da baban Muhsin ya bata dubu goma cif. Addu'a ta din ga kwarara masa da shi da zuriyarsa, saboda ta ji daWin kuWin nesa ba kusa ba.

Da yamma Ummi ta zo gidan, ta tarar da Nana a gida.

"Nana ke ba ki je asibiti duba Suwaiba ba?"

"Hmm kin san da yadda ta yarda nake zaune a gidan nan ne ma? Su na cewa ina ?o?arin kashe Suwaiba, wai ina sha mata jini.. sauran maganar ya kakare mata saboda kukan da ya kufce mata mai taSa zuciya.

Jiki a sanyaye Ummi ta ce "Yanzun ma da na je, su na ta maganganu amma dan Allah ki manta da su. Ke dai Allah ya baki lafiya. Na zo ne a kan batun shirin bikinki, Baba ya ce ba za ayi taro ba. Amma ko ba za ayi taro ba ai kya fara gyaran jiki dai ko?"

"Me zan gyara? Ni dan Allah ki rabu da ni"

Ummi ta ce "Kamar yaya na rabu da ke? Aure fa za ki yi."

"Auren jeka na yi ka ba? Ai kun san ba so nake yi ba, amma babu yadda na iya ne, shi ne sauran mafitar da ya rage mini"

"Au Nana ba za ki daina maganar ba kya so Win nan ba ko? Ke ba kya tausayin kanki da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wannan wahalar da ki ke ciki ko? Ki je ki ki yi ta yi, sai mutum ya tausaya miki, idan ki ka tafka wani rashin mutuncin zai gane ke ba abar tausayi ba ce. Ki je ki yi abin da ki ka ga dama, ni na cire hannuna a kan ki"

"Allah yana tare da ni, na san shi ba zai cire hannu daga kaina ba" Nana ta yi maganar hawaye na gangarowa daga idanunta.

Ayshercool
08081012143

P16

Sosai Ummi ta fusata, da yadda ?arara take nuna ?iyayyarta ga Saleh.

Bayan tafiyar Ummi da magariba sai ga Saleh, Nana tana iyakar ?o?arinta duk da ba ta son Saleh, ta saka wa zuciyarta son aurensa, ko dan samun sassauci daga wannan takurarriyar rayuwar da take yi. Sai dai fafur ta kasa jin komai game da shi balle auren. Ga gefe tana fargabar kar shi ma wani abin ya same shi, ko ?aisar ya cutar da shi.

Har ya yi kiWansa ya yi rawarsa, Nana ba ta tanka masa ba, har ya yi ya gama ya gaji ya tafi.

Washegari da safe tana bacci, Baba ya je ?ofar Wakinsu da kansa yana ?walawa Nana kira. Ta yin?ura ta taso da kyar ta fito ya ce "Nana, tun da Allah ya yi miki dawowa ba za ki koma gurin koyarwar taki ba ne? Na ga tun da ki ka dawo, ba ki je ba sai jiya, yau kuma kin naWe a gida, ai kya gurgura ki ?arasa ki samu Wan abin kashewa a hannun ki, ke da za ki yi doguwar tafiya ki bar gari, duk da na san mijin naki ba zai bar ki haka ba, alamu sun nuna mutum ne mai kyauta da kirki." Tun da Nana ta ji yana ?ara yabon Saleh, da cewar yana da kyauta, ta san Baba ro?e-ro?e yake yi wa Saleh, kuma yana ba shi.
"Ina magana kin yi shiru?"

"Baba an kore ni" ta amsa a ciki.

"Kamar yaya an kore ki?"

"Baba daga makarantar mana"

Sak ya yi ya ce "Ikon Allah, ke kuwa me ki ka yi haka?"

"Korata kawai suka yi " ta bashi amsa tana komawa cikin Wakin saboda wani irin azababben bacci da take ji, duniyar har juya mata take yi.

Nana ta koma ta ci gaba da zuwa islamiyya da take yi, duk a fakaice tana fuskantar tsangwama, saboda yadda ake zargin da saka hannun Imran a kisan malam Auwal, wasu kuma suke zargin aljanunta ne suka yi ajalinsa.
Gefe guda ta kan shiga matsananciyar damuwa, a duk lokacin da ta zo makarantar, domin kuwa yana tuna mata da malam Auwal, idan ta kalli bugiren da ya kan zauna sai ta ga kamar za ta ganshi.

Dama ba sakin jiki take yi da mutane ba, dan haka nesa da ita da mutane suka ?ara yi da ita bai dame ta ba. Sai dai cikin malaman makaranta babu wanda ya canza mata.

Aka sallamo su Suwaiba daga Asibiti, ta sha jini a ?alla leda biyar, sai dai an kasa gano dalilin da ya sanya jininta yake ?onewa. Dama zaman su a Asibiti babu ko kwabon Baba, 'yan uwar babar su Suwaiban ce kawai suke Wawainiya da ita.
Bayan sun dawo gida, yadda Mama ke tattalin Suwaiba da sauran yaranta, abin ya yi ta burge Nana yana ba ta sha'awa, ba ta damu da ?yamar da suke nuna mata muraran a fili ba, wannan soyayyar da kulawar kawai take ?awa.
Da tuno ta su mahaifiyar sai ta ji zuciyarta babu daWi, sam kamar ta manta da haife su a duniya, ko waiwayen in da suke ba ta yi. Duk da Baba ya ?ara yi mata gargaWi a kan kiran mahaifiyar tasu, ta sake lalubar waya ta kira layinta amma a kashe.
Yanzu wai shirin aurenta ake yi, amma Baba bai tuntuSi kowa daga Sangaren mahaifiyar su ba. Da akwai wata ?anwarta da take zuwa duba su, tare da kakar su, Mama ta shiga ta fita ta saka Baba ya ci musu mutunci suka daina zuwa.

Nana tana Waki, tana duba muktaril hadis, ta jiyo Baba a tsakar gida, rai a Sace yana gaya wa Mama iyayen Saleh sun zo, sun nemi a sake ?ara musu sati huWu, wai bai gama shiryawa ba haryanzu bai samu Wakin da zai ajiye Nana a can Lagos ba.

"To kuma ka yarda da hakan?"

Ya ce "To ya zan yi? Ni da cewa na yi ko a Wakinsa na samartaka a can ikkon, ya saka ta kafin ya samu Wakin, suka ce mini a suna da yawa wanda suke kwana a Waki Waya. Na ce musu a Waura ko a gidan 'yan uwa sai ya ajiye ta, kafin ya samu gurin sun ?i yarda"

"Lallai ma, wannan ai zancen banza ne, amma dai ka san cewa sati biyu muka yi da kai ko? Kana kallon wahalar da nake ta fama da Suwaiba babu ko sisin ka, sai ta halaka Suwaibar sannan zaka san abin yi ko?"

"Ba zata halaka Suwaiba ba, abubuwan da suke faruwa ba yin kanta ba ne na ba ita ma, kuma Suwaiba ma, wata?ila kawai zafin ciwo ne".

"Au haka ka ce? Zafin ciwo ko? Wallahi duk abin da ya samu yarana ya rataya a wuyanka da nata".

Zuciyar Nana na yawan ingiza ta, ta yi wa Mama martani, amma wata zuciyar sai ta hana ta.

****

Kamar ba?uwar halitta haka suka zuba masa ido. Yana kwance yana sauke numfashi a hankali. Goshinsa ya haWa gumi, idanunsa a rufe.

"Da alama ya samu sau?i, bacci ya Wauke shi sosai"

"Eh nima na gani"

"To yanzu shikenan haka zai rayu, ba za a samu maganin larurar nan ba balle ya iya tuna waye shi?"

Habu ya girgiza kai ya ce "A'a souley, mai rai ai baya fitar da rai, a duk inda yake. Zan ci gaba da nema masa magani, da yardar Allah na san za a dace. Yanzu idan na rabu da shi ban yi masa adalci ba, ina zai je? Kuma hannun wa zai faWa? Duk ba mu sani ba. Gara na ci gaba da zama tare da shi, zuwa lokacin da za mu dace da maganin"

Sule ya jinjina kai ya ce "Shikenan, amma ni ina jin tsoro ne, na ga hatta magana ma ya daina yi, abin gaba yake yi"

"Eh duk da haka ba zamu karaya ba akwai Allah. Za mu biku na ga yanayin gurin, idan zai yiwu mu ci gaba da zama tare da ku, shikenan idan ba zai yiwu ba zamu bar gurin"

"A'a babu wata matsala ma, za ku ji daWin zaman gurin".

*****

Sannu a hankali take tafiya a cikin Wakin karatun, da ke Wauke da tarin littattafai, kundi kundi.
Ta Waga kanta litattafai ne iya ganinta a cikin Wakin, sai dai sun sha ?ura, wasu ma gizo-gizo ya yi musu yana mai yawan gaske.
Ta ?arasa gaban wani tebur, ta ga wani ?aton littafi a ajiye,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login