Showing 45001 words to 48000 words out of 190498 words

Chapter 16 - Buzu Book 1 Complete

ke, bayan ka na da magungunan su?"

"Ban gaya miki a cikin aljanu irin ?aisar ba su da yawa ba? Yanzu ki je zan kwanta in huta ne"

Ta jinjina kai, ta tashi ta nufi ?ofa, har ta kusa fita ya ce "Ki na ji?"

Ta waiwayo ta ga har ya kwanta.

"Ki ci gaba da addu'a da karatun Al?ur'ani, duk da idan kin yi kin fi shan wahala, kar ki daina. Kuma kar ki yadda wani abu ya baki tsoro, wasu lokutan da tsoron ka ake amfani a cutar da kai, ki cigaba da addu'a duk tsanani akwai sau?i a biye. Wata?ila tsanani da ?addarar gobe ta fi wadda ki ke ciki yau" ta yi shiru tana jinjina maganganun sa.

Ta Wago ta ce "To na gode sosai da sosai. Ka ajiye mini naman maciji an jima zan zo in gwada ci" ya yi dariya ya ce "Kamar gaske. Zo mu ga tafin hannunki"
Ta koma gurin da ta bar shi, ta dur?usa ta nuna masa tafin hannunta hagu da dama. Ya yi shiru yana kallo sannan ya ce " Ki kula sosai zanen X Win da yake kusa da layin zuciyarki na nuni da tsagwaron gwagwarmayar rayuwa. sannan layukan ?asan babban Wan yatsanki suna nuni da za ki yi wasu tafiye-tafiye, wasu daga ciki na jin daWi wasu na wahala. Sai kuma alamar ido, da ke babbar Wan yatsarki da alamar sar?ar da ke jikin babban yatsan akwai wani abu amma ba zan gaya miki ba, shi ma wani karatun ne daban, yana da ala?a da aure da kuma matsalar iyali"
Ta kalli Sarkin baka ta ce "Abin mamakin? ka ba ya ?arewa sarki, bayan layuka ban ga komai a hannun nawa ba, ko kana ganin wani abu da bana gani a hannun, kuma dai sanin gaibu sai Allah ai"

Ya kwashe da dariya ya ce "Wani karatun ne daban, duk da na san ji na kawai ki ke yi ba yarda ki ke yi ba. Je ki an jima ki zo ki ci naman. Na so na je da ke taron wasan maharba da muke yi duk shekara, ni ke Wauke da kambun har yanzu, sai dai ba na iya tunanin bana za ayi wasan da ni, ?aisar ya yi mini illa. Maza je ki sai an jima" ta tashi tsam ta nufi hanyar fita tana kallon hannunta. Wannan tsohon mai kama da ?aisar ta gani, cikin wannan fararen kayan nasa, tamkar yanar gizo gizo saboda tsufa.

Sai kuma ya Sacewa ganinta, a hankali ta ?arasa ?ofar Wakin ta ga baya nan, sannan ta fita, tana tafe a hankali tana duba tafin hannunta tana kallon zanukan da sarkin baka ya faWa, da tunanin shi kuma wani kalar siddabarun ne. Ji ta yi zafin rana ya ?aru kamar lokaci Waya temperature ta canza. Ta Waga kai kawai ta ganta a bakin layinsu. Ta waiwaya da sauri ta ga ba ta cikin gidan sarkin baka. Ta sake dubawa ta ga dai bakin layinsu ne dai.

Hatta kayan jikinta ba su bane ba, dogon hijjabi ne da aka ba ta take sakawa lokacin salla, sai kuma wata jaka da take rataye da ita ta fata. Ta din ga ?ifta idanunta domin ta ji ko bacci take yi amma ta ga ido biyu ne, kawai ta nufi gida.

Ko da ta shiga gidan da sallama, babu kowa a tsakar gidan. Ta sake yin sallama Nasiru ya shigo gidan da gudu ya dawo daga aike, ya ce "Laa mama Nana ta dawo"

Hakan ya yi daidai da fitowar Mama daga Waki, hannunta ri?e da tsintsiya da abin kwashe shara.

Sakin tsintsiyar ta yi tana kallon Nana kamar ba?uwar halitta.

Nana ta ?a?alo murmushi ta ce "Mama sannu da gida?"

"Uban me yasa ki ka dawo gidan nan yanzu?" Cikin mamaki Nana t tsaya tana kallonta.

"Ke idan ki na da kunya ma kya dawo gidan nan, duk da ta'asar da ki ka yi?"

Cikin mamaki Nana ta ce "Wace ta'asar?"

"Ban sani ba" ta yi magana tana Waukar wayarta a kan taga"

Nana ta nufi Wakinsu, amma Mama ta dako tsalle ta tare ta, ta ce "Ai kuma zamanki ya ?are a gidan nan, abin da na yi na ri?on ki Allah ya ba ni lada. Ba za ki ci gaba da zama ki kashe mini 'ya 'ya ba"

"Mama kisa kuma? Wa na kashe?"

Ba ta kula Nana ba, ta fara magana a waya "Ko ma ina ka tafi, ka dawo ka zo ga Nana ta dawo, ka zo ka fitar mini da ita daga gida, dan wallahi ba zan zauna da ita ba" ta kashe wayar.

Nana ta tsaya tana kallon ikon Allah, Fafur Mama ta hana ta shiga Wakinsu, ba a fi mintuna goma sha biyar ba, sai ga Baba ya dawo gida.

Cikin mamaki yake kallon Nana ya ce "Ina Gaddafin yake?"

"Gaddafi kuma Baba?" Nana ta tambayi Baba cikin mamaki.

"Eh mana, ba wancan jarababben Wan nema ya kai ?arar mu ba, wai mun kai ki inda ba a sani ba, aka haWa Gaddafi da jami'an tsaro a je a taho da ke"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ni da kaina na dawo, ban ga Gaddafi ba"

Suwaiba ce ta fito daga Wakin Mama, sai da Nana ta tsorata, ta yi wani irin haske, duk da tana shafe-shafe, amma hasken da ta yi, da gani na rashin lafiya ne.

"Ka fa san yadda za ka yi da ita, dan wallahil azim ba zan ci gaba da zama da masifa da annoba ba, shi kansa wanda aka ce an kashe Win nan, ina kyautata zaton ma ita ce ba wani ba, to wallahi jinin 'ya'yana ba zai shawu a sha banza ba"

Baba ya ce "Wai Rabi me yasa ki ke haka? Idan ta bar gidan nan ta je ina?"

"Ta koma gurin uwatta, ta je ta sha nata jinin"

"Ba zai yiwu ba, har duniya ta naWe, ba zan bawa maijidda Wa na ba."

Nana ta yi ajiyar zuciya cike da tsantsar damuwa da ba?in ciki.

Ya sake kallon ta ya ce "Wai ba makonni biyu aka ce za ki yi ba, me ya dawo da ke gidan nan yau?"

"Shi ne ya sallamo ni" ta amsa a hankali.

Baba ya ci gaba da faWa "Wallahi Ina takaicin haihuwar Imarana, ya haWa Gaddafi da jami'an tsaro, shi kuma an zo nemansa a kama shi ya gudu, yanzu ma kalli 'yan sandan ne suke kirana ga kuma wannan masifar"

"Baba a kama shi kuma? Me ya yi?"

"Eh ai ke ce mai jin tausayinsa dama, sun haWa kai da 'yan iskan abokansa, sun kashe wannan malamin naku, ana ta nemansa ruwa a jallo"

Nasiru ya yi farat ya ce "Baba ba fa Yaya imarana ne ya yi kisan ba, abokansa ake nema, shi ne ake nemansa dan ya nuna inda suke"

"Duk ba abu Waya ba ne dai?" Baba ya faWa cikin takaici.

Jikin Nana na rawa ?irjinta na dukan uku-uku ta ce "Wai wani malamin namu?"

Nasiru ya yi farat ya ce "Malam Auwal aka kashe da daddare, ya fita sayayya ana gobe za a kai ki gidan mai magani"

Kanta ne ya yi wata irin sarawa, ta yi saurin dafe kanta tana tunanin kamar ta san zancen amma ta manta a ina.
Iya ?arfinta take kokowa tsakanin ?wa?walwarta da zuciyarta a kan sai ta farka daga nannauyan baccin da take yi.

Ayshercool
08081012143.

15

Suwaiba ta shiga banWaki ta koma Waki, babu wanda ta kula a tsakar gidan.

Mama kuwa bala'i ta ci gaba da yi. "Wallahi baban Jamila ba zan zauna da Nana ba, idan ta gama da yaran nan kaina za ta dawo, shi kansa wannan yaron an fara maganar saboda ya?i aurenta ya rasa ransa".

Baba ya ce "A'a Rabi, wannan dai zance ki ne, idan da wanda zai mutu dan bai aureta ba ai Suleiman ne, kuma duk abin da ake yi mata a gidan nan babu wanda ya mutu, dan Allah ki daina wannan maganar"

Kamar ta mari Baba ta ce "Abin da ya samu Suwaiban bai ishe ka hujja ba, sai ka buWe ido ka ga gawar ta tukuna? Ni fa wallahi sai dai ka zaSa, ko ta bar gidan nan ko ni na bar gidan"

"A'a ba za ayi haka ba, yanzu idan ki ka ce ta bar gidan nan ina za ta tafi? Haba Rabi Nanan nan fa 'ya ta ce ita ma. Kuma idan kin kwantar da hankalinki, kin san na karSi kuWin auren ta, nan da sati biyu za a Waura mata aure, ta bi mijinta Ikko, duk mene ne abin tayar da jijiyar wuya?"

Nana tun da ta dafe kanta, ta sunkuya ba ta ko motsa ba, sai yanzu da ta Wago ta fara magana iya ?arfinta "Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah ku tashe ni daga baccin nan, ya za ayi malam Auwal ya mutu? Dan Allah ku tashe ni kafin ?wa?walwata ta samu matsala, dan Allah ku tashe ni daga baccin nan" ta Wago da idanunta suka yi wani irin ja kamar za su kama da wuta, hawaye ne tare da mijina suke rige-rigen zuba a fuskarta.

Baba ya ce "Nana meye haka? Zuwa islamiyyar na banza dama ki ke yi? Ko ni na mutu ai ba kya yi haka ba" jefar da jakar hannunta ta yi, tai waje.

Baba ya bita da sauri, amma tamkar wal?iya bai ga ko sahunta ba.

Kai tsaye Nana rukunin ofisoshin malamai ta nufa a islamiyyar su.
Malam Nura ta tunkara, babban abokin malam Auwal.

Cikin yanayi na Wimuwa ta ce "Wai an kashe malam Auwal? Dan Allah kai ma ka iya ru?iyya ai ka na yi mini, dan Allah ka karanta mini koma mene ne ko zai sake ni na tashi daga wannan baccin."

Ya ?arewa Nana kallo, da gaske a Wimauce take, cikin sigar rarrashi ya ce "Zauna mu yi magana"

"Ba zan zauna ba, kawai ka yi mini ru?iyya na tashi. A nan fa na same shi a ofishin sa, muka yi magana, ya gaya mini gaskiya ba zai iya aurena ba, kuma duk na fahimce shi, ya ce mini zai tafi Qatar, to kuma daga na yi tafiya sai ace mini ya mutu?"

"Al mautu ha??un Nana Asma'u, mun yi rashin Auwal. ?ata gari ne suka soka masa makami su ka ?wace masa waya kafin a kai shi Asibiti rai ya yi halinsa, ki yi masa addu'a"

Jikinta na karkarwa ta ce "Ya sayyadi Nura. Na yi rashi ba zan manta Yaya Auwal ba, yanzu waye zai din ga bani addu'oin? Waye zai yadda da abubuwan da nake ji a jikina na ciwo, ba tare da ya ?aryata ni ba?" Tuni malamai suka cika ofishin, kowa da abin da yake faWa, wasu na kuka domin mutuwar ta dawo musu sabuwa. Da yawa ba su san ya so ya auri Nana ba sai yanzu.

An daWe ana rarrashin Nana, da yi mata nasiha, ba a taSa yi wa Nana mutuwa mai shiga jiki ba sai a wannan lokaci, Alkhairinsa kawai take tunawa.

Halin da take ciki, bai hana kunnuwanta jiyo maganganun wasu malaman, su na cewa yayanta ake nema ruwa a jallo shi ya kashe Auwwal. Sauti komai ?an?antarsa Nana na iya jiyo shi, wasu lokutan da haka take gane ?aisar na daf da ita.

Malam Nura ya saka ta a gaba, ya tafi raka ta gida, suna tafe yana yi mata nasiha.

A ?ofar gida malam Nura ya yi mata sallama, ta shiga cikin gida tana taku da ?yar.

Ko sallama ba ta iya yi ba, ta nufi ?ofar Wakinsu, ta ga an saka tsumma an Waure ?ofar Wakin. Ta Wauki jakar da ta dawo da ita daga gidan sarkin baka, duk da har a wannan lokaci ba ta san mene ne a ciki ba.

Ta fara ?o?arin kwance ?ofar Wakin, jin motsi ya sanya Mama sake fitowa, tana ?o?arin nufo Nana tana bala'i. Nana ta Wago a hankali ta kalli Mama, sai kuwa ta ja ta tsaya, dan ba ta taSa ganin Nana ta yi mata irin wannan kallon ba. Gani ta yi tamkar wal?iya idanun Nana suka yi. Ta buWe Wakin ta shiga ta kwanta.

Aka jima Baba ya dawo, dan yawon neman in da Nana ta yi ya yi. Yana dawowa suka ci gaba da faWa da Mama a kan lallai sai ya fitar da Nana daga gidan.

Nana tana ji Baba ya kira Yaya Atine yana ro?onta. Baba ba ya iya waya sai ya saka ta a hansfree, kuma sai ya ta Waga murya tamkar yana magana da aradu.

"Atine dan Allah idan da hali Nana ta zo gidanki, ta zauna kafin a Waura mata aure. Rabi ta?i yadda ta zauna da ita, kin san halin da Suwaiba take ciki"

"Wace Nana kuma? Ba tana gidan mai magani ba?"

"Ta dawo Wazu, wai mai maganin ne ya sallamo ta, kuma ga 'yan sanda sun tafi da Gaddafi a taho da ita, shi kuma Imarana ya gudu nemansa ake yi ana zargin sun kashe wannan yaron da ake ta magana a kansa a radio, wanda ya ?i auren Nanan"

Nana na jiyo Yaya Atine, kasancewar wayar Baba a ragargaje take kuma China ce ta na cewa "TaS lallai Isa Allah ya jarabce ka, wannan masifar duk a gidan ka? To mai magani ma ya kasa ya sallamo ta balle kuma ni, ya zan yi da ita ina ma na ga gurin ajiyeta? Ka yi ha?uri ta zauna a gurinka kafin lokacin bikin nata"

Ya marairaice ya ce "Me nake da shi, ba wani biki aure kawai za a Waura su tafi, ai kin san ba shi ne da ni ba"

Yaya Atine ta ce "To ai shikenan, amma ka ri?e 'yar ka, ba zan je nima na gogi bala'i ba, dan ni na fara tsorata da al'amuranta"

"Amma yay... Ba ta bari ya gama maganar ba, ta kaste kiran.

"Ka gani ko? Ita ba za ta karSi bala'i ba, ni kuma a bar ni da bala'i ya ci gaba da kashe mu ba zai yiwu ba"

Sallamar da ake kwaWawa a waje, ya sanya Baba fita, ya tarar da 'yan sada tare da Gaddafi.

?aya daga 'yan sandan ya ce, "Yauwwa barka malam, zamu tafi da kai station ne"

Baba ya ce "Saboda me?"

"Mun je in da aka ce an kai yarinyar Wanka ya yi ta raina mana hankali muna yawo, babu wani a gurin nan, kuma ga wanda ya kawo ?arar ana nemansa ruwa a jallo"

Baba ya ce "Ai bayan tafiyar ku ta dawo"

Gaddafi ya ce "Ta dawo kuma? Ni fa har gurin da muka ajiye mota muka shiga, bamu ga gidan nan ba"

"Wallahi ta dawo, tana cikin gidan nan"

Sai da aka tafi tare da Nana har police station, aka yi rubuce-rubuce sannan aka saki Gaddafi suka taho gida. Tana jin yadda Gaddafi yake rantsuwa shi da sake shiga duk abin da ya shafe ta har gaban abada.

Kwanaki biyu suka shuWe, Nana ko rintsawa ba ta iya yi, sai da ta gwammace dama a gidan sarkin baka ta yi zamanta.
Mama kuma ba su fasa faWa da Baba a kan lallai ya nemi in da Nana zata zauna ba. Dama normally ma ba abinci ake ba ta ba sai an ga dama, yanzu kuwa tun da ta dawo Baba ne ma ya kan bayar a sayo mata kunu ko awarar naira Wari, shi ma ba iya ci take yi ba.
Dama ba su fiye shiri da Suwaiba ba, sun fi shiri da Jamila, sai dai a wannan karon tun da ta dawo, babu wanda yake shiga sabgarta, hatta Wakin da take ba sa shigowa. Tana jin yadda idan aka yi ba?i, ko aka zo duba Nana mama take muzanta ta, tana cewa aljanunta ne suka halaka Auwal, wanda ya fasa aurenta kuma suke ?o?arin kashe Suwaiba.

Nana tana ganin yadda wasu daga hudar jikin Nana suka fara warkewa, sai dai wasu ba su fasa zubar da jini ba.

Turaren da Jamila ta kawo mata ta gani a kan tagar su, an feshe fiye da rabi. Ita dai ta san turaren nata ne, amma ta kasa tuna yadda aka yi ta same shi.

Cikin dare ta kasa bacci, ta tashi zaune ta haWe gwiwoyinta ta kifa kanta, har yanzu gani take kamar za ta farka daga bacci, ace mata Auwal bai mutu ba.
Kwanakin nan da aka Wauka kuma, ta gazagata da gaske malam Auwal ya rasu. Tana so ta je ta yi wa mahaifiyarsa ta'aziyya amma ba ta sani ba ko ta santa, ga kuma surutun da ake ta yi a kanta.

"Ya Allah ka yafe mini rashin tawakalli da na yi, na bari Wimuwa ta sanya ni yin abin da bai kamata mai imani ya yi su ba. Ya Allah Auwal bawanka ne, mai kwaWaitar da al'umma bin ka da manzonka, mai hidima ga addini, mai ?aunar Manzon Allah ma'abocin Alqur'ani ya Allah ka yafe masa ka yi masa rahama" ta yi maganar kuka yana ?wace mata.

Dariyar da ta ji ne, ya sanya ta Waga kanta. Ta ganta a zaune jikin wata bishiyar tsamiya, ita kaWai ?wal a daji.

"Iska na wahalar da mai kayan kara, yanzu duk saboda soyayyar ki ka koma haka? Kamar gaske mutumin nan ya riga ya mutu, kuma ba fa wai son shi ki ke yi ba, sha?uwa da tausayi ne a tsakanin ku" tashi ta ya tsaye a fusace tana waiwayen in da za ta ga ?aisar. Domin kuwa sai a lokacin ta tuna ya nuna mata mutuwar malam Auwal, amma da ta tashi a wancan lokacin ta manta da komai.

"Kai ne ka kashe shi ko?"

"Idan zan kashe shin ne zan soka masa wu?a? Kwanansa ne ya ?are ba zan iya kashe shi ba ai, ni ba na kisan kai sai an dame ni, kamar yadda Sarkin baka ya taSo ni, nima na taSa shi wata?ila na karya alkadsrinsa wannan maitar wata?ila ita ce ajalinsa"

Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Kenan kashe shi za ka yi? Wai kai wani irin halitta ne azzalumi mara imani? Duk wanda na mu malanta sai ka cuce shi?"

"A'a ni ba na taSa kowa sai ya taSa ni. Ba ya fara lallaSa ki ki sadaukar masa da ni ba? Ba ki yi tunanin ta wace hanya zai yi amfani da ni ba, kawai saboda ki rabu da ni, ki ka amsa masa kuma ke ba ki san ya ake sadaukarwar ba, ki ka amsa. Ya shiga gonata ni kuma na shata masa layi" yayi maganar yana bayyana a gabanta.

Cikin kuka Nana take faWin "Allah ya yi mini maganin ka ya saka mini, idan ka fi ?arfina ba ka fi ?arfin Allah ba ai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login