Showing 171001 words to 174000 words out of 190498 words

Chapter 58 - Buzu Book 1 Complete

ya din ga yi, da jin abin da ta faWa ya ce "Sayyid, shugaba, ko kin manta sunan da ki ka saka mini ne?".
"Shugaban da babu masarauta"
"Ai a cikin Duniyata masaurata take"
Nana ta ce "Wai me yasa sai dare, ka fi sakar mini fuska, ka yi ta magana ka na raha"
Ya gyara kwanciyar sa, ya Wago daga kwanciyar da ya yi ya ce "Na gaya miki?"
Da sauri ta ce "A'a bar shi, ba sai ka faWa ba"
Kawai ya tuntsure da dariya, ta ce "Hmm za ka yi dariya ne, Allah ya dauwwamar da wannan kyakyawan murmushi a fuskar gangar jikin da ke Wauke da ruhina"

"Ashe ke ma kin iya, abin cikin film Win"
Suka yi dariya tare, ya fara kashe Nana da salon soyayyarsa mai tsayawa a rai, tare da haWa yaren Hausa da fransanci, gurin gaya mata kalamai masu motsa zuciya.

Cikin rawar murya ta ce "Sayyid"ya Waga kai ya kalle ta.

"Kana ganin abin da nake gani?"

"je l'ai vu(Na gani) amma kar ki tsorata. Yi kamar ba ki gani ba"

"A'a ina ne nan Sayyid? Ina yawan ganin gurin nan, ina yawan ganinmu tare a nan."

Y girgiza mata kai ya ce "Nima ban san ina ne ba"

"Kuma ba mafarki ba ne?"

"Zahiri ne" ya amsa mata a ta?aice.

"Amm..." Bai bari ta sake magana ba, ya rufe bakinta da nasa, saboda tambayoyinta ba sa ?arewa.

Bayan wani lokaci, ya rungumota daga banWaki, sai rawar sanyi take yi.

"Ba ki da lafiya ne?"

Ta kalle shi ta ce "Me ka gani?"

"Kamar ki na jin sanyi, kuma na da ruwan Wumi muka yi amfani"

Ta jinjina kai ta ce "Ina jin sanyi kam, mu je ka bani Wumi"

Da sauri ya ce "To mu je"

"A'a ba fa abin da ka ke tunani ba ne"

Ya yi murmushi ya ce "To ma na ce miki ina tunanin? Zo na baki Wumin jikina"

"Ba na so, ?ona ni ka ke yi"

Kawai ya yi dariya, ya ce "Daga ni har ke, Allah ya yaye mana abin da yake damunmu"

"Amin Sayyid, dama ka na ganin Wakin nan kai ma?".

"Eh amma a mafarki galibi"

"To akwai ranar da ka ce azumina zai karye, na ganmu a Wakin kuma na tashi, na ga ya karye Win"

Kawai ya shafi ji?a?iyyar kalbar da take kansa, yana dariya ?asa-?asa.

"Ya ka ke dariya? ka bani amsa mana"

"Na saka ki bacci ne, sai na taSa ki kaWan"

"Ka yi mini me?"

"Abin da muka yi yanzu" sai kuma ta yi saroro cikin jin kunya, ta kwanta za ta juya masa baya, amma ya juyo da ita, ya kwanta shi ma. Gaba Waya yau ya fi kullum ba ta mamaki, hirarsa ta fi ta kullum yawa, zolaya da nishaWinsa ya fi na kullum. Duk a 'yan kwanakin nan, sun ?ara samun nutsuwa da kusanci da juna sosai da sosai.

"Shugaba"

"Rayuwata"

"Ya ake ka ke saka ni bacci mai nauyi"

Ya yi shiru bai ba ta amsa ba, ta Wan jijjiga shi, kawai ta ga ya yi bacci.

Sai dai tana sakankancewa bacci mai nauyi ya Wauke ta, ya ?ara farkawa ya tashe ta.

"Sayyid gaskiya ?asa zan koma, na bar maka katifar nan, halak malak haba, kwata-kwata ban yi bacci ba. Kaina har ya fara ciwo. Ga zuba ruwa ga rashin bacci haba Shugaba"

Bai ce mata uffan ba, ya rungume ta, ta baya, ?irjinsa a bayanta. Ji ta yi zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri. Har za ta yi magana sai kuma ta fasa, jin jikinsa ya saki alamar ya yi bacci.

Siyama kuwa bayan ta farka ta ganta a gida, sai ta kasa tuna komai. Tayi-tayi amma ta kasa tuna komai. Ta tambayi Maminsu, me ya same ta, ta gaya mata a mota aka tsinto ta a sume
Abin ya Waure mata kai ya ba ta mamaki, a iya saninta, ta haWu da mai gadi, sun yi magana daga haka ba ta sake tuna komai ba. Abu kamar wasa sai ta din ga zabura tana tsorata haka kawai.
Ta kasa zama a Wakinta itakaWai, ta tashi ta koma Wakin mahaifiyarta.

*****
Alhaji Zailani ne a zaune a kan kujera, yana kallon Alhaji Fatuhu, da yake zaune, ya jingina da pillow, Fadila na ta ?o?arin ba shi Abinci.

"Sannu Fatuhu"

Alhaji Fatuhu ya ce "Yauwwa Alhaji Zailani, na gode" ya furta cikin ?arfin hali.

Ya kalli Fadila, zaune ciki ya tsufa sosai da sosai. Ya ce "Babu wanda yake kula da shi, ke ga larura ga kuma Wawainiyar jinya".

"He deserves it, Daddy shi mai kulawa ne a gare mu" ta yi maganar hawaye ns zirarowa daga idanunta.

"Allah sarki, sai ha?uri, ki yi ha?uri. Allah ya ba shi lafiya" kasa ci gaba da ba shi Abincin ta yi, ta ?ara fashewa da kuka.

A hankali Alhaji Fatuhu ya ce "Za mu yi faWa idan kina kuka, ai na samu sau?i"

Alhaji Zailani ya ce "Look, kukan nan ba abin da zai amfana muku. Ki yi ha?uri ki yi masa addu'a, kin ga juna biyu ne da ke. Ba zai so wani abun ya faru da ku ba, daga ke har abin da yake cikinki ba. Kin ga Shukura irin haka aka yi, ta saka damuwa mara dalili a zuciyarta. Ta zo ta haifi yaronta babu rai. Kuma ta zo ta sake shiga damuwa. Ki yi ha?uri dan Allah" Cikin rauni ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, na gode sosai da sosai"

"Yauwwa babu komai, idan Hajiya Suwaiba ta zo, ta kira ni a waya, ku koma Asibitin Doctor Sharif,a din ga yi masa komai a can. Ba zai gagara ba in sha Allah"

Fadila ta ce "Kar mu Wora maka Wawainiya, nan ma su na ?o?ari Alhamdillah"

Alhaji Zailani ya ce "kai, Fadila. Kin san waye mijin ki kuwa a gurina? Da Suwaiba ce ma ba za ta yi jayayya ba na sani.
Dan Allah ku haWa kayan ku, zan turo direba ya mayar da ku can zuwa dare in sha Allah. Abokina Ubangiji Allah ya ?ara afuwa"

Ya mi?a wa Alhaji Fatuhu hannu suka gaisa, Alhaji Fatuhu ya ce "Na gode sosai da sosai, da Wawainiyar da ka ke ta yi, na gode sosai da sosai"

"Ai ka san babu godiya tsakaninmu, Allah ya sauwwa?e". Bayan ya fito harabar Asibitin, ya din ga wata irin dariya. Ya hau motarsa yana faWin da sauranka, tun da har yanzu ka na magna. Wannan matan ma duk sai sun gudu sun bar ka, abin da za ka ci ma sai an taimaka maka da shi. Ya ja motar ya bar harabar Asibitin.

*****
Gidan su Nana kuws, duk wanda ya yi surutun, gyaran da aka yi wa gidan, da yawon da Jamila take yi. Sai Mama ta ce Maman Khairat ce ta haWa Jamilan, da wata Hajiya 'yar kasuwa, Jamila take taya ta aiki a kasuwancinta, tana biyanta.
Suwaiba kuma, abu kamar wasa jiki ya ?i daWi sam. Kullum cikin ciwo take, yau ciwon kai, anjima ciwon ?afa da ciwon baya. Ga shi ta auri zaman Waki ba ta son fita. Idan ciwon kan nan ya tayar mata, tamkar za ta haukace, ta din ga burgima kenan tana ihu da kururuwa. Mama ba ta wani mayar da hankali ba a kan ciwon na Suwaiba, saboda hankalinta na kan abin duniyar da Jamila take kawowa, shi yasa ba ta damu sosai da sosai ba. Duk inda ta kai Suwaiba neman magani, wasu su ce Aljanu ne da ita, wasu su ce Asiri aka yi mata. Wasu su ce kambun baka ne da baki. Gaba Waya Suwaiba, ta rame ta yi ba?i. Idan abin ya motsa ko abincin kirki ba ta iya ci, sai aikin kuka sai bacci.

*****

Can gurin su Nana kuwa, fito daga gaba Waya Sayyid jikinsa yake yi tamkar an zare masa laka, wata irin mutuwar jiki da ta ?aru a kan ta jiya da yake ji.

Nana ta fito daga wanka, ta Wauro zani ta fito tana Wigar da ruwan wanka. Ta yi fari da idonta, ta ce "Shugabana"

Yayi murmushin da ya saba, tare da sunkuyar da kansa, yana kallon wayarta da ke hannunsa.

Ta buWe drowern mudubi, ta Waukko kibiya da comb, ta nufo shi, ya kalle ta ya tsuke fuska.

Ta kwashe da dariya, ta ce "Mutumina akwai shagwaSa, kalbar kanka ta tsufa sosai, ka bari a tsefe dan Allah. Idan ya so ma yi kitson gobe"

Ya girgiza kai ya ce "A'a"

"Gaskiya sai na tsefe ta, na yanke maka farce, ka yi wankan juma'a ko Rayuwata"

Yana hararta, ta kwantar da kansa a kan cinyarta, tana yi masa dariya.

"Rigimammen Shugabana"

Tana tsifar tana yi masa hira. Yana ta shiga yana fita a cikin wayarta, ya kunn wa?r kewa, ta wani mawa?i Wan nijar ta kewa.
Cikin nishaWi,take bin wa?ar, ta ri?o tafin hannunsa cikin nata, tana bin, baitukan wa?ar.
Kowa tsaneka, ni na tsane shi sanya a ranka...
Zuciyata na baka, duk masu ?in ka su daina shakka...
Rayuwata na baka...
Ni ta ya zan guje ka...
Ka dawo gare ni dan Allah, zuciya ta bar kewa...

Murmushi ya gaza barin fuskarsa, fararen ha?oransa a waje, ya juyo gaba Waya ya ?an?ance idanunsa, yana yi mata wani irin kallo cikin nishaWi.

Ta ci gaba da bin wa?ar, tana Wan jan kunatunsa "Mallakina ne, kai zan kira da sheriena...
Ko iyayena sun ce na bi ka mai so na...
Kai jinina ne...
MahWina ne...
?addarata ne
Mai yabona ne...
Ashe kai ne, ashe kai ne, ashe kai ne abin so ne, abin so ne, abin so ne.
Dan Allah ka dawo gare ni mai so na ina kewa...

Ya Wago hannunsa ya kalli azurfofin hannunsa, ya ciro Waya ya kamo hannunta ya dam?a mata. Tana dariya ta ce "Iyee gaskiya na iya wa?a, har da kyauta? Amma ya yi mini yawa ai"

"Ki samo zare ki zura a ciki ki yi sar?a da shi" Nana ta din ga tuntsura dariya. Ta ce "Riba biyu, ga tsifa na yi ga kuma kyauta an ba ni.

Ya din ga kallon dariyar da take yi yana murmushi.

Can zuwa la'asar Nana ta fuskanci jikinsa gaba Waya a sanyaye yake, kamar babu kuzari haka yake gudanar da komai.

Sai dai ba ta tambaye shi ba, saboda tana tsoron ya zamana wani abu ne yake damunsa, ba ta son ganinsa a cikin damuwa sam.

Su na cin abincin dare, tana yi masa hira yana amsawa muryarsa a sanyaye.

Wayarta da ke caji a Wakin, ta cika Wakin da ?ara. Nana ta duba ta ga Hajiya Amina.

Cikin rawar jiki ta Waga tana murmushi ta saka a hansfree ta ce "Hajiya tuba nake yi, kwana biyu ma ban kira ki na gaishe ki ba".

"Alhajin ne, ba Hajiyar ba"

Wata irin mummunar faWuwar gaba, ta riski Nana, ta kalli Sayyid. Ta ga bai ko kalle ta ba, yana cin abincin sa a nutse.

"Wa..wa..wane Alhajin ya aka yi? Ina mai wayar?"

Zailani ya ce "Mai waya tana nan ?alau, na ji kin saka wayar a blacklist ne, shi ne na ce bari na biyo ta inda dole ki Wauka. Me ki ka yanke game da maganarmu? Idan kin amince zan turo miki inda zamu haWu, mu gama na baki kuWin ki na sallame ki, babu wanda ya ji babu wanda ya sani. Idan kuma ba haka ba zan Wauki mataki na gaba"

"Na shiga uku, zaka kashe mini aure, wannan wace irin masifa ce, ban yadda ina budurwa ba sai da na yi aure" Sayyid ya mi?a hannu ya katse kiran, ya kashe wayar gaba Waya.

Cikin kuka ta ce "Dan Allah Sayyid ka fahimce ni, zan yi maka bayani"

Ya girgiza kai ya ce "Babu bu?ata, ci abinci"

Sosai Nana take kuka ta ce "Wallahi Sayyid"

"Don't talk.(Kar ki yi magana)"

Gaba Waya hankalinta ya yi mummunan tashi, duk jikinta ya mutu. Amma bisa ga mamakinta, ta ga ya ci gaba sabgoginsa ko ta kanta bai bi ba.

A tsorace ta raSa shi ta kwanta, tana tsoron kar ya sha?e ta.

Ya kamo hannunta, ya Wora kan tsefaffen gashinsa ya ce "Ki yi mana addu'ar bacci"

Ta yi ajiyar zuciya, ta fara karantowa a hankali. Suratul fala?i, Nasi, ayatul kursiyyu da ayoyin farko na Suratul Ba?ara. Sai dai tana karantawa muryarta na rawa. Ta idar ta busa masa a fuskarsa. Kamar yadda ta kan yi musu, ranar da take cikin ?oshin lafiya.

Gani duk ta takure ta ?i sakin jikinta, ya sanya ya yi ?o?arin kawar da damuwar da take ciki. Amma ya ji jikinsa ya ?ara nauyi, yana jan numfashi da ?yar. Duk ?o?arin da ya yi, ya kasa komai, sai kokowa da yake yi da numfashi.Nana kuwa jin ya ?yale ta, ya sanya ta yi bacci.

Hatta sallar Asuba, a gida ya yi, a Waki. Ta sab wasu lokutan idan ba ta tashi da wuri ba, sai dai ta tashi ta ga ya sayo ?osai ko buredi, amma yau har ta makara, ta tashi ta yi abin karyawa yana kan katifa bai tashi ba.
Ta tsaya a gaban mudubi ta shirya, ta yi kwalliya.
Vibrating wayarta take yi, sai da gabanta ya faWi, saboda tana tsoron kar ta je ko Alhaji Zailani ne. Jiki a sanyaye ta Waukko wayar, ta kalli Sayyi, ta ga bacci yake yi.
Ta Waga kiran gabanta na faWuwa, ta saka a kunnenta.

"Nana ba faWa me ya kawo gaba?"

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Jamila, yau ke ce da kira na?"

"Eh, tun da ba kya neman mutane ba. Rannan na wuce ta wajen gidanku, kamar na biyo na ce kar na je, na takura muku"

Nana ta ce "Kashh, amma ba ki ji daWin halinki ba, dan wula?anci?"

"Ba wani wula?anci, lokacin ma Ummi ce ta ce kin yi Sari, ai an kwana biyu da na wuce Win ai"

"Kai Ummi sai da ta faWa? Ina su Mama, ba ta taSa zuwa gidana ba, Yaya Atine ma haka"

"Aikuwa na ji Yaya Atine tana ta masifar, ba ki je mata ba."

"Wallahi ba ya bari na fita ne, sai na yi ta fama. Ina suby ne?"

"Tana gida babu lafiya, tana ta fama da matsanancin ciwon kai"

Cikin damuwa Nana ta ce "Subhanallah, in sha Allah zan samu dai na zo gidan, ba ni ita dan Allah na yi mata sannu"

"A'a ni ba na gida ma, na fita tun safe"

"Zuwa ina?"

"Gurin neman halal mana. Kin san Hajiya Sa'a nake yi tayawa saye da sayarwar kaya tana biyana".

Nana ta yi murmushi ta ce "Jamila kenan, ni dai wallahi matar nan ba ta yi mini ba, ba zan Soye miki ba, ina iya jin alamun rashin gaskiya a tattare da ita. Na san yanayin gidanmu, dole ka nema idan kana so ka rayu. Amma Jamila ki san abin da za a saka ki ki yi, duk wani abu da zaka tara a duniya koma bayan imaninka da mutuncinka ne. Ubangiji Allah ya kawo muku mazaje na gari, masu tsoron Allah masu wadata."

Jamila ta ce "Hajiya Nana sarkin manyance, dama kuma ga shi an yi aure, sai abin da ya yi gaba. To na gode sosai na ji ana sallama"

"To ki gaida su Mama da Suwaiba kafin na zo"

"To shikenan, sai anjima" ta kashe wayar, ta ajiye ta shashshafa turare.

Ta juyo ta kalli Sayyid ta ga idanunsa kar a kan ta.

"Shugaba ya dai? A tashi a zo a ci Abinci"

Murmushi ya yi da ?yar, amma bai yi magana ba, kuma bai motsa ba.

"A taso mana ranka ya daWe" ya yi shiru dai yana kallonta.

Nana ta yi murmushi ta ce "Yau mulki ake ji kenan, bari na zo na Waukko ka, tun da tashi ya gagara" ta ?arasa ta Waukko kayan abincin, ta jera a inda suke ci. Ta kunna turaren wuta, Wakin ya gauraye da ?amshi. Ta ga dai da gaske ya ?i tasowa, ta nufe shi tana rangwaWa.
Ta sunkuya a gabansa, ta yi masa kiss a goshi ta mi?a masa hannu, ta ce "Bismillah taso Shugaba"

Bai kama hannun ba, ya ci gaba da kallonta, sai kuma jikinta ya yi sanyi, da kallon da yake yi mata.
Jiki a sanyaye ta ce "Wai Sayyid lafiya kuwa? Ko maganar ce ta Wauke?"

Ya mi?a hannunsa, ya kamo nata, ya Wora a saitin zuciyarsa.

Ta yi shiru, ta ji zuciyarsa ta buga sau Waya, sai kuma ta yi shiru ba ta sake bugawa ba, sai bayan wasu sakanni, sannan ta sake bugawa.

A razane Nana ta kalle shi jikinta na rawa ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid meyafaru? Me ya same ka haka?"


Ayshercool
08081012143
48


Bai ce uffan ba ya ci gaba da sauke numfashi. Tashi ta yi a matu?ar rikice, ta zari hijjabinta ta yi waje, cikin matsanancin tashin hankali da kuma damuwa.
Ta kai a ?alla mintuna ashirin, sannan ta dawo a rikice, ta tarar da shi a zaune ya jingina bayansa da jikin bango, ya lumshe idanunsa.
"Sayyid na samo abin hawa, Asibiti za mu tafi"
Ya buWe ido da ?yar ya kalle ta. Ta nufi wardrobe ta duba ta Waukko irin kuWin da Imran ya bata. Ta buWe wardrobe Win sa, ta Waukko masa riga jallabiya. ya tashi da ?yar, su ka shiga banWaki, ya wanke bakinsa. Ya fito ta naWa masa rawaninsa, ba ta damu da ko rufe Wakin ba, suka yi waje.
?arfin hali kawai Nana take yi, amma zuciyarta ta gama tsinkewa, ta karaya a mugun tsorace take.
A cikin adaidaita sahun ma, a jikinta ya kwanta ya yi lamo, ya yi shiru ba ya cewa komai.
Addu'a kawai Nana take yi, da fatan Allah ya kawo musu Wauki. Amma a yanayin yadda zuciyarsa take bugawa ta yi mugun tsorata.
Asibitin da suka je aka saka mata ruwa, suka je, amma aka ce musu ai weekend ne, kuma ?aramin Asibiti ne ba sa aiki weekend.
Hankalin Nana ya yi mugun tashi, yana son ya yi mata magana, amma ya kasa.
Sai suka bawa Wan sahun tausayi ya ce "Ko na kai ku Asibitin cikin gari emergency, ko wani taimakon a yi masa"
Muryar Nana na rawa ta ce "Yauwwa malam, na gode kai mu dan Allah" ya ja babur suka tafi.
Ya kamo hannun Nana, ya danne saitin zuciyarsa da shi, ji yake numfashinsa ma na neman ya ?wace masa.
"Sannu Sayyi, Allah ya baka lafiya, Ubangiji Allah ka dube mu, babu mai kawo mana Wauki bayan kai, Allah ka yi mana ba dan halinmu ba" muryar Nana na rawa, take wannan addu'oin, har suka ?arasa Asibitin.
Mai adaidaita sahun ya yi mata mutunci, har zai ja babur Win, ya ga yadda Sayyid ya kasa tsayuwa,yana neman faWuwa Nana kuma ba zata iya ri?e shi ba. Ya kashe babur Win ya fito ya ce "?anwata, bari na ri?e miki shi, ba za ki iya ba"

Ya sa?ala hannun Sayyid a kafaWarsa, suka taka a hankali zuwa Sangaren emergency.

Matashin ya kalli Nana ya ce "KarSo kati, ki dawo"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login