Showing 165001 words to 168000 words out of 190498 words

Chapter 56 - Buzu Book 1 Complete

saSanin da ya shiga tsakaninsu.

(BAYAN MAKONNI BIYU)

Gaba Waya Fadila ta rasa abin da yake yi mata daWi, hankalinta ya ?i kwanciya, tun da aka fara zaman kotu ta ji halin da ake ciki ta rasa abun da yake yi mata daWi, yanayin yadda shari'ar ke gudana, za ka san da gayya ake yi, kawai shi ake son ya tozarta.
Dan tashin farko Al?ali cewa ya yi a tsare shi, sai an ajiye wasu miliyoyi da kadarori, za a sake shi.
Wasu tuhume-tuhumen ma, bai san da su ba, sai ranar da aka fara zaman kotun, sannan ya san da su. Har wasu ma?udan kuWin, da ake zarginsa da sama da faWi da su, a lokacin da yake shugabanci.
Haka aka sayar da wasu daga kadarorinsa, aka bayar sannan aka ba da belinsa.
Kotu ta yi umarnin a yi gwanjon kadarorinsa a sallami mutane kuWinsu.

*****
Alhaji Zailani, tare da Malam Gambo suka koma gurin da suka binne, jaririn nan, su ka tono ?warangwal Win sa, duk ya zagwanye. Suka saka a akwati, suka tafi da shi.
?akin da Malam Gambo yake tsaface-tsafacensa su ka je. Ya Waukko ?warangwal Win jaririn, aka babbaka wata irin wuta, aka Wauki ?warangwal Win jaririn nan, ya rubuce jikin da sunan Alhaji Fatuhu, ya zana wasu hatimai, ya nannaWe su a jikin ?warangwal Win aka saka a cikin wutar nan.
Malam Gambo ya din ga zuba wani magani a cikin wutar, ya kawo wasu irin layoyi da ya zana hatimai daban-daban, ya din ga jefawa a cikin wutar. Alhaji Zailani kuma yana kiran sunan Alhaji Fatuhu.
Sai da ?warangwal Win nan ya yi ba?i ?irin, zaren da aka naWe ?warangwal Win, ya kama jikin sosai. Ya kuma naWe shi da wani zaren, sannan ya naWe da likkafani, su ka je suka samu wata tsohuwar rijiya, suka jefa a ciki.

Alhaji Zailani ya koma gida, kulle kansa a cikin Waki, ya din ga SaSSaka wata irin mahaukaciyar dariya, tamkar zai haukace.

Ya ce "Alhaji Fatuhu ka gama yawo, yanzu sai na ga wanda za ka hura wa hanci, wai ka ga mai kuWi kuma mai tsoron Allah, mu zuba mu gani. Wannan burin nawa ya cika, saura kuma waccan yarinyar"

Alhaji Fatuhu kuwa, sun dawo daga kotu, Yayan Hajiya Suwaiba, lauyan da ya tsaya masa, yana ta yi masa nasiha a kan ya karSi ?addara.

Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi Barrister, na karSi ?addarata. Na kuma gode wa Allah. Abu Waya nake tunani iyalina na saba musu da rayuwar jin daWi da kwanciyar hankali. Ina jin tausayinsu fiye da abin da ya same ni"

Cikin tausaywa Barrister ya ce "Na sani Alhaji, tabbas kai mutum ne mai kyautatawa iyali. To yanzu ne ranar da za su nuna maka halacci su ma, a yi ha?uri"

Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, mun gode Allah"

Ji ya yi tamkar ana ?o?arin fizgo ?wa?walwarsa. Ya yi wata irin zabura, ya ri?e kansa gam. Barrister ya ce "Alhaji lafiya dai?"

Ya girgiza kai ya ce "Zafi nake ji" kafin ya kuma wata maganar, ya yanke jiki ya faWi a gurin.

Nana tamkar tana kallon talabijin, haka ta ga komai a cikin mudin da ?aisar yake nuna mata.

Yana gefe yana rubutunsa, ita kuma ta zuba uban tagumi tana kallon mudubin.

"Shigen irin wannan sihirin aka yi wa mijinki, shi ne wannan wutar da yake cewa tana ci a jikinsa. Sai dai shi nasa ya sha bamban da wannan ta wasu fannukan"

Nana ta zabura ta kalle shi ta mi?e tsaye ta ce "?aisar ka yi mini bayani, waye ya yi masa asirin? Kuma daga ina yake? Suwaye iyayensa?"

Ya Wago ya kalle ta ya ce "Kin manta sharaWin ne?"

Ta yin?ura za ta yi magana, ta yi ido huWu da Sayyid, yana kusa da ita, ya zuba mata ido.

Ta yi ajiyar zuciya.

"Waye ?aisar?" Ya jefo mata tambayar babu zato babu tsammani.

Ayshercool
08081012143


CHAPTER 46.

Hantar cikinta ce ta kaWa, ta kalli cikin ?wayar idonsa, jin yadda ya jefo mata tambayar, babu tsammani ba tare da ta shirya hakan ba.
Wani irin gumin tsoro da fargaba, ya fara tsatstsafo mata, saboda ba ta san ta ina yakamata ta fara yi masa bayani ba, ba ta san ma me za ta ce masa, da zai gamsar da shi, amsar da za ta ba shi ba. Sai dai a ina ya san ?aisar, har yake tambayarta waye shi? Ta tambayi kanta.
Ga mamakinta, sai ta ga ya tashi ya yi mi?a, ya fice daga Wakin ba tare da jiran amsar da za ta ba shi ba, ko kuma bayanin da za ta yi masa ba.
Ta tashi ta kimtsa jikinta, babu jimawa sai ga Habu ya zo, Sayyid ne ya fara Waga labule, ya ganta a kintse a cikin hijjabi, sannan ya ba wa Habu damar shiga.
Sama-sama suka gaisa da Habu, ita ?asan zuciyarta tana tsoron kishin Sayyid, shi ma Habun haka.

Ya ajiye wani galan a gaban Sayyid, ya ce "Sa?onka nan, an kawo shi Wazu fresh ne"
Sayyid ya ce "Na Husnah ne" Nana ta saci kallonsa, ko za ta ga ya canza mata, saboda tambayar da ya yi mata, kuma bai jira ta amsa masa ba, amma ta ganshi normal.
Ta Wan yi murmushi ta ce "Me na samu?"
Habu ya ce "Nonon Ra?umi ne da ake kawo miki, ga kuma dabino da zuma, fresh masu kyau da aka kawo daga Nijar"
Nana ta ce "To Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai da sosai. Habu wai kai ka ke ba shi kuWi? Na ga kuWi masu yawa a kayansa, ya ce kai ne ka ba shi"
Habu ya yi murmushi ya ce "Ba ki yadda da abin da ya faWa ba ne? Ai mutum mai iyali dole sai da kuWi, kuma na gaya miki mu na harkar kawo dabino, zuma, cukui kayan shayi, asuwaki mazar?waila daga can Sahara.
Nana ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta ce "To ya batun binciken da ka ke yi, a kan danginsa, ya ce mini ka na bincike a kai."
Ya Waga kai, suka yi ido huWu da Sayyid sannan ya ce "Ina nan ina yi, kuma in sha Allah duk bayanin da na samo zan sanar da ke"
Nana ta ce "Ma sha Allah, kuma Habu duk 'yan garinku Buzaye, su na jin Hausa? Idan ba sa ji da yaya za mu yi magana idan an gano su?"
Habu ya yi murmushi ya ce "Mu ba ga shi mu na ji ba? Hausa na cikin manyan yaruka a Nijar, da kusan kowa yana jin yaren. Dan haka kar ki damu, tun da yana jin Hausa, danginsa ma na san su na ji"
"To Allah ya sa su karSe ni, idan an gano su. Ina Sule kwana biyu?"
"Ya je gida, ai shi ya taho da wannan kayan ma"
A wannan karon Sayyid bai kula su ba, kuma bai sanya musu baki a hirar ta su ba, har suka yi suka gama. Ta tashi ta tattaro masa kayan wankin Sayyid ta ba shi, ya yi musu sallama. Bayan ya tafi, Sayyid ya Wauki kayan shayinsa ya koma bakin gate. Nana ma ganin babu abin da za ta yi, kawai sai ta bi shi.
Ta samu guri ta zauna a gefensa, ta Wan zuba masa ido, amma bai kula ta ba, ya mayar da hankali a kan shan shayinsa.
"Sayyid" ya Wago ya kalle ta.
"In tambaye ka?"
Ya jinjina kai alamar eh.
A Wan sanyaye ta ce "Yau na yi magana da Habu, na ga ba ka yi fushi ba"
Kawai ya yi murmushi ya ce "Kina so na yi ne?"
Ta ce "A'a, dama bai kamata ka din ga yi ba, tun da sukaWai mu ke gani a matsayin danginka. Su Habu 'yan Aljanna ne, ina yabawa Wawainiyar da suke yi da mu, mussaman shi, alhalin ba ku da ala?a"
"Ke ma 'yar aljanna ce, in sha Allah "
"Kai ma haka" ta faWa tana murmushi.
Sai kuma fuskarta ta bayyanar da damuwa, ta ce "Sayyid, ciwon nan naka yana bani mamaki, ka san komai na rayuwa na yau da kullum amma sanin waye kai kawai ka manta. Dan Allah idan ban takura maka ba, ka gaya mini abin da za ka iya tunawa, bayan da ka buWe ido ka ganka a wannan yanayin "
Ya Wan yi shiru na Wan lokaci, sannan ya kalle ta ya ce? "Kawai na ji abu ya sar?e mini numfashi,? tari ya kama ni, ?ura tana shigar mini hancina da bakina. Na yi ?o?arin buWe idona, amma abu ya gagara, saboda wata irin ?ura da na gani ta turnu?e gurin,, da wani irin sauti da tashin ?urar yake bayarwa. Ba na iya gane komai. Na takure jikina na lokacin da ban san adadinsa ba, daga bisani na ji shiru. Na sake buWe idona a hankali, sai na ga ?urar ta lafa, na ganni a cikin sahara, da wani tsoho mai matu?ar tsufa, hannunsa ri?e da sanda, gemunsa fari tas har cikinsa, ga wasu irin kaya da suka yi mugun tsufa a jikinsa.
Nan na fara tunanin waye ni, ya kuma aka yi na ganni a wannan gurin, amma na kasa tuna komai.
Na yi ?o?arin tuna sunana, da inda na fito, amma ban ji ko kusa da tunawa na yi ba.
Na kalli tsohon nan, da niyyar na tambaye shi, amma na kasa magana, na yi, nayi amma na kasa ce masa komai, shi kuma bai daina kallona ba.
Wata irin ?ishirwa ta kama ni, ga yunwa ina ji, amma na kasa magana. Can na hango wani mutum ya nufo ni a kan ra?umi, ya saukko daga kan ra?umin ya nufo ni da sauri. Yana ta yi mini magana, amma ba na gane abin da yake faWa. Ya Wago ni ya bani ruwa na sha.
Sai na fuskanci kamar ba ya ganin tsohon nan, nikaWai nake ganinsa. Ban san meyafaru ba. Na buWe ido na ganni a wani guri, ya ce mini Nigeria ce, tun? daga nan yake ta Wawainiya da ni" Duk wannan bayanin da yake yi wa Nana, daki-daki yake yin sa, yana yi yana hutawa, kuma a nutse babu gaggawa.
Ta jinjina kai ta ce "Kenan mai ka na ganin, wannan tsohon kenan?"
"Ki na ganinsa ne ke ma?"

Ta jinjina masa kai, sannan ta ce "Me yasa ka tambaye ni waye ?aisar?"

Ya yi murmushi tare da sunkuyar da kansa, ya kalle ta ya ce "Tambayoyinki sun yi yawa Rayuwata"

"Dan Allah ka bani amsa Sayyid, wasu lokutan ina shiga ruWu a kan abubuwan da suke gudana, ba na ganewa sosai, sai na ga kamar taSin hankali ne da ni"

"A'a lafiyarki ?alau, ni ne mai matsala, ni nake da taSin hankali na sani"

"A'a lafiyarka ?alau"

Ya Wan kurSi shayin hannunsa ya? ce "Ai na san gaskiya, ana kuma faWa ina ji, ba ni lafiyar ?wa?walwa ina da taSin hankali"

Ta gyara zamanta, ta ce "To wai gurin masu magani da ku ka je, babu inda aka yi nasara, ko alamun nasara?"

"Eh" ya amsa a ta?aice.

"Amm Sayyid"

"Kaiii na gaji, dan Allah ki daina tambayar nan, ba kya gajjya ne?"

Ta yi murmushi ta ce "Idan zan kwana ina magana, in dai da kai ne, ba zan taSa gajiya ba. Sannan ka yi ha?uri abin da na yi maka dan Allah, na zubar da abin da ka shiga da shi Wakinmu, raina ya Saci ne, kuma na ga ban kyauta ba"

"Kuma ke ta ce na kaiwa, shi yasa na karSa"

Ta ce "Makirci ne kawai na mace, amma? na ga alamar ta girgiza da ganinka, kamar ta fara son ka ne ma"
Ya yi shiru bai ce komai ba. "Ba zaka kula ni ba?"
"Me zan ce?"
"To kar ka kulanin, kuma wallahi naga abin da raina zai sosu, sai ka neme ni ka rasa"
Kawai ya sunkuyar da kai yana murmushi.
"Dariya ma na baka ko? Amma idan ni ce sai ka wani haWe rai, ka yi ta yi mini faWa"
"Ki yi shiru, ki huta"
"Na ?i yin shirun, wallahi idan sonka take yi, sai kun ga abin da ba ku zata ba"
Ya ce "Ai na ma gani"

Siyama ce ta nufo su, Sayyid ya yi hanzarin mahar da takunkumin fuskar ya rufe fuskar sa.
Ba ta kula Sayyid ba ta ce "Nana, yau girki nake son yi, ki zo mu je mu yi"
Nana ta yi murmushi ta ce "Ma sha Allah, bari na zo" ta yin?ura ta tashi, Sayyid ya bi ta da kallo. Suka shige cikin gidan tare da Siyama.

Siyama na matu?ar jin daWin hira da Nana, gani take kamar ta samu sau?i, tun da Nana tana jin irin abin da take ji. Kuma tattaunawar da suke yi.

"Kamar haka da nake yi wa Sagir girki, na zo ba na iya yi, saboda zuciyata raya mini take, na cakawa kaina wu?a, ko na ?ona kaina da ruwan zafi"

Nana ta ce "Subhnallah. Yaushe wai ki ka fara ciwon nan ne?"

Ta Wan yi shiru sannan ta ce "Lokacin da su Mami, suka tare a gidan nan, na zo ganin gida, lokacin na dawo daga umara. Kawai daga tafiyata gida, na din ga jin tsoro cikin dare. Dama da ciwon kai na tafi gida. Ina bacci sai na ji ana shafa ni da daddare. Sosai fa nake jin ana taSa ni, idan na faWa ba a yadda. Lokacin mijina yana neman aure. Aka ce kishi ne ya sa? dan Allah ba zan yi kishin mijina ba ina son sa Nana?"

Nana ta ce "A'a dole ki yi kishi mana, tunda ki na son sa"

"To daga ?arshe, mamansa ta ce sai ya rabu da ni, wannan kishin idan ban kashe kaina ba, zan kashe shi ko matarsa. Aikuwa ya sake ni"

Nana ta numfasa ta ce "Ki yi ha?uri ki ci gaba da addu'a, idan ki? na da rabo sai ki ga kin koma"

"Anya kuwa Nana? Mami ta ce babu ni babu shi, ba shi da mutunci da shi da iyayensa da 'yan uwansa"

"Kar ki damu fa, idan da rabo sai ki koma, amma a yanzu dai, ki fauwwala wa Allah komai" Ta jinjina kai ta ce "Haka nex

Muryar Hajiya Halima suka ji, tana ?wala wa Yusra kira. Yusra ta amsa da "Na'am, gani nan"

"Me ki ke yi a kitchen ne?" Ta yi maganar tana shigowa kitchen Win.

"Girki mu ke yi, ni da Nana"

Nana ta ce "Hajiya ina wuni?"

"Lafiya ?alau Nana, lallai taku ta zo Waya da Yusra, na ga tana Wan sakin jiki ta yi walwala da ke, dan Allah ki kula saboda kar ta yi wani abin da zai cutar da ita, ba ta da cikakkiyar lafiya. Ni fita zan yi"

Nana ta ce "Tom, a dawo lafiya"

Ta amsa da Allah ya sa, ta bar kitchen Win.

Suka girka faten dankali da kifi, yanayin yadda Yusra ke girki, ya tabattarwa Nana, yana daga cikin abubuwan da take son yi. Su ka yi lemon mangwaro, suka saka a fridge ya yi sanyi.
Bayan sun kammala, ta kalli Nana ta ce "Ki zuba kai kai wa mijinki, kar ya huce"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a mu ci kawai, zai iya gwale ni ya ?i ci"

Yusra ta ce "A'a, zai ci. Duk abin da ki ka ci, ki din ga ba shi, za ki ga ya ?ara son ki sosai da sosai. Da haka muke yi ni da Sagir" cikin tausayawa Nana take kallonta, alamu, sun nuna har da zafin rabuwa da mijinta ya sanya larurata yin gaba. Saboda aljani ya fi samun damar shafar mutum, a lokutan fushi, damuwa, ko kuma najasa.

Haka ta takura wa Nana, ta zuba abincin a flask, ta fita. Yana zaune yana facing hanyar shiga gidan, ta tsaya cak tana kallonsa, hakan ya sanya shi tasowa ya nufo ta.

Ya ?araso, ta nuna masa guri ta ce ya zauna, ya zauna ya dube ta ya ce "Kin bar ni, nikaWai"

Ta buWe faten dankalin, ta ce "Abinci zan baka"

Ya kalli harabar gidan ya ce "A nan?"

"Eh mana, ba kowa ai. Bai kamata a ce kullum daga Waki sai bakin gate ba, canza abubuwa yana sanya nishaWi a zukata"

Ta sauke masa rawaninsa, ta Webo dankalin a cokali, ta kai bakinsa. Ya buWe ta saka masa.

Bayan ya haWiye ya ce "Ba ke ki ka yi ba"

"Ni na yi "

"Ba ke ba ce. Babu yaji, babu tafarnuwa, bai ji maggi sosai da sosai ba"

Ta kwashe da dariya, ta ce "Sayyid ko numfashi na yi, sai ka gane, ka haddace komai nawa. To na ji amma tare muka yi ai" ya ci gaba da buWe bakinsa, yana karSar Abincin. Tana yi tana cire masa ?ayar kifin da ba ta fita ba.
Ya gama ta ba shi lemon ya shanye, ya ce "Na gode sosai"

Ta kalle shi ta Sata fuska, ta ce "Ba ka ce ba"

Fuskarsa Wauke da murmushi, ya kamo fuskarta, ya sumbaci goshinta ya ce "Allah ya yi wa rayuwata albarka"

"Wannan ai wayo ne, amma shikenan na gode" gani ta yi ya tsaya cak, yana kallon guri Waya. Ta waiwaya sai ta ga Siyama ce a bayanta, hannunta ri?e da wayarta ta kara ta a kunnenta. Wani abu ya soki zuciyar Nana,ganin kallon da take yi masa. Bai yi magana ba, ya nufi gurin da yake zaune da farko.
Nana ma ba ta kalli Siyama ba, ta wuce ta, ta shige. Hira ta je suka ci gaba da yi da Yusra. Sai dai duk wata hirar ta Yusra shirme ce, amma ta fitowa da Nana abubuwa da dama, da suke damunta.
Sai dai galibin hirar ta ta,na zamanta da mijinta ne, da irin son da take yi masa. Sai da ta ji tamkar ta ce wa Hajiya Halima, su haWa wa Yusra maganin da na gargajiya bisa doron addini. Amma yanayin yadda take ganin gidan, sun ginu a kan doron a?idar boko, babu lallai su amince da hakan.

Sai da ana daf da fara kiraye-kirayen sallar magariba, sannan Nana ta fito.

Har ta wuce lungun da shuke-shuke suke, ta koma da baya ta le?a, ta ganshi a gaban famfo, yana alwala. Ta cire takalmanta, cikin sanWa ta nufe shi, tana zuwa daf da shi ta faWa bayansa, ta ma?ale wuyansa.

"Ya aka yi ne?"

"Wai ba ka ji tsoro ba?"

Ya yi dariya, ya ce "Tun lokacin da ki ka fito daga cikin gidan, nake jin kina kusanto ni a jikina"

"Ka daina tsorata ni, da wannan maganganun na ka"

"?aga ni, alwalata za ta karye"

Ta no?e kafaWa ta ce "A'a"

"Dan Allah"
Ta sake cewa "A'a" ya saka hannunsa ya jawo ta daga bayansa, ya tara hannunsa a famfon, ya taro ruwa ya watsa mata a fuska. Ba shiri ta mi?e tana ajiyar zuciya. Ba ta farga ba ya Wauki tiyon da yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login