Showing 30001 words to 33000 words out of 190498 words

Chapter 11 - Buzu Book 1 Complete

dai ta kasa tunanin Auwwal, tun ranar da suka rabu, ba ta sake ganinsa ba.
Ga Baba ya fara addaba mata da maganar Saleh, wanda ko sunansa ba ta ?aunar ji.
A can makaranta da take koyarwa, mahaifin Walibinta Muhsin, ya fara damunta, kullum ya zo Waukar Muhsin, sai ya ce zai rage mata hanya. Ga shi ba ta da damar tafiya, sai an gama zuwa Waukar yaran gaba Waya, kuma kullum Muhsin ne ?arshen zuwa Wauka.

Yau bayan ta dawo daga islamiyya, Yamma li?is, Baba ya shigo fuskarsa Wauke da fara'a ya ce "Ke Nana, ki je ga Saleh can a waje yana jiranki" gaban Nana ya faWi.

Imran ya tashi ya nufi hanyar fita, Baba ya ce "Kai malam ba kai fa kai na ce ba"

Ya waiwayo ya kalli Baba ya ce "Ni akwai gurin da zan je" ya fice.

"Ke kuma Nana ba magana nake yi miki ba?"

Jiki a sanyaye ta ce "Ina zuwa, kaya zan canza"

Imran kuwa yana fita ya tsaya ya ?arewa Saleh kallo, ya ce "Kai ai kamar na sanka a gidan Ummi"

Saleh yayi murmushi ya ce "Ba kama ba ce ba ni ne ai"

Imran ya ce "Bala'i ashe idan na je neman aure nima za a bani, duk da ana ganin ba ni da saiti. Kai yanzu saboda ka raina wa kanka hankali gurin ?anwata za ka zo neman aure a haka? Kalli wani shegen wando a jikinka ba ka san saukakkiyar Alqur'ani ba ce, kuma mahaddaciya ba?"
Saleh yayi saroro yana kallon Imran.

"Eh kalle ni da kyau, wallahi sai na je har gida na kasa wa Ummi warning, mai ku ka mayar da Nanan, wallahi ta fi ?arfinka me za ta yi da Wan jagaliya kamar ka?"

"Saboda na zo ?ofar gidanku neman aure, ka ke gaya mini abin da ka ga dama?"

Imaran ya ce "Malam gaskiya nake gaya maka, ba ka cikin irin mutanen da Nana za ta so da aure, a tsarinta tana son mutum mai kamala da sanya manyan kaya kuma...

Shiru ya yi, ganin Nana ta fito fuskar nan babu walwala.

Maimakon ya tafi sai ya ja ya tsaya, takaici ya hana Saleh magana, a girme ya girmi Imran amma ya tsaya yana gaya masa magana dan ya zo wurin ?anwarsa.

Ya maze ya kalli Nana ya ce "Gimbiyata barka da fitowa"

Imran ya kwaSe baki yana jiran me Nana za ta ce. Ta Wago suka haWa ido.

"Amma ko za ka bamu wuri mu yi magana" Saleh yayi maganar yana kallon Imran.

"In ba ku guri na je ina? Ka zo wurin ?anwata zance da crazy jeans, meye banbanci na da kai, da ake cewa ba ni da hankali?. Kai wallahi ba za ayi zancen nan ba, ke koma gida ranar da ya shirya neman aure, yayi shigar mutunci ya zo"

Babu musu Nana ta shige gida, dama haka take so. Baba na ganin ta dawo ya tambayi ko lafiya?.

"Imaran ne ya ce na dawo gida"

"Ki dawo ki yi masa uban me? Idan ba ki yi aure ba zai aure ki ne?"

Ya nufi waje yana faWa, ya tarar da Imran ya tare ?ofar gida yana cewa Saleh idan gidan ubansa ne, ya ture shi ya shiga da wannan shigar tsiyar.

"Imrana wai ba ka da hankali ne? Meye haka?"

"Baba, wai ya za a Wauki aure a ba wa mutumin da zai zo neman aure, yayi ido huWu da sirikinsa da yagaggen wando, da tarin suma kamar shekararren zakara. Kuma a gaya masa gaskiya Nanan nan fa ba son sa take yi ba"

Baba ya ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Imrana yaushe ka yi hankalin da ka fi ni sanin dai-dai? Shigar mutum ake dubawa ko halin iya ri?e auren? Ita Nanan ba taimaka mata zai yi ba, tun da ba lafiya ce da ita ba"

Imran ya ce "Baba neman kan da ka ke yi da Nana ba daidai ba ne ba, Allah ya Wora mata larura alhakinka ne nema mata magani, ba neman kai da ita ba, amma shikenan 'yar ka ce, duk matakin da ka Wauka a kanta daidai ne" yayi maganar yana barin gurin.

Baba ya kalli Saleh ya ce "Dan Allah malam Saleh ka yi ha?uri, yaron nan ba cikakken saiti ne da shi ba, ka san idan mutum yana shaye-shaye sai a hankali ka yi ha?uri. Nana 'ya ta ce kuma na isa da ita, ka je ka turo magabatanka kawai kar ka Sata lokaci kamar yadda wancan yayi"

Saleh ya ce "In sha Allah Baba na gode sosai"

"Yauwwa yi tafiyarka, kar ya zo ya yi maka wani haukan a ka" Saleh ya so keSewa da Nana, amma Imran ya wargaza komai.

An fara kiraye-kirayen sallar magariba, Jamila ta shigo Nana ta fara nema, Nana ta ce "Wannan kiran fa ta samu ne?"

"Wai dan Allah ina kayan da Hajiya ta bani na kawo miki, ko sau Waya ba ki saka ba, balle na yi miki hoto na tura mata, tun da na san ba za ki je ta gani ba"

Nana ta ce "Zan saka ne, kawai ni ban san dalilin da ya sanya ta bani kayan ba ne, amma zan saka in sha Allah"

Jamila ta ce 'Ai mace ce mai kyauta, babbar 'yar kasuwa ce fa, kwanan za ta fara bani kaya ina Wora nawa nima, kin ga turare ta bani na kawo miki " ta yi maganar tana mi?a wa Nana wani turare.

Nana ta karSa tana murmushi, kasancewar tana son ?amshi sosai. Ta sunsuna turaren ta kalli Jamila cikin mu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????rmushi ta ce "Amma ?amshin turaren nan yayi daWi sosai, ki ce mata na gode sosai"

Nana ta fara ?o?arin fesa turaren a hannunta, amma idan ta fesa babu abin da yake fitowa, ga kuma turaren tana gani cikin kwalba. Tayi tayi amma abu ya gagara.

Suwaiba da ta fito daga banWki ta ce "Wai ke Jamila ba ki gaya wa hajiyar, ki na da 'yar uwa da ku ke uwa Waya uba Waya ba, ni ba zata bayar da komai a kawo mini ba sai wata Nana da uba kawai ku ka haWa?"

Suwaiba ta ?araso, ta karSi turaren hannun Nana, ta fesa a hannunta ta sunsuna.
Wurin da ta fesa turaren Nana ta ga duk ya SuSSule, kamar an caccaka allura jini ya fara fitowa. Sai dai ta ga Suwaiba normal, ba ta nuna wata alama na ta ga abin da ya faru ba, hakan ya tabattar wa Nana, ita kaWai take gani.

Suwaiba cike da mugunta, ta feshe rigar material Win jikinta milk. Nana ta Wan ja da baya ganin jini, ya Sata rigar maimakon ruwan turare.

Suwaiba kuma ta ce "Amma turaren yayi ?amshi" tana sake feshe jikinta da shi. Sai dai duk in da turaren ya taSa a fatarta Sulewa yake jini ya fara zubowa.

Ta gama fesawa, ta bawa Nana turaren ta ci gaba da sabgoginta.
Mama ma masifa ta hau yi, wai tana uwar Jamila ba a bayar da komai a kawo mata ba sai wata Nana.

Jiki a sanyaye Nana ta shiga Wakinsu, tana sake kallon kwalbar turaren. Ta buWe ta ?ara fesawa a jikinta da hannunta, amma ya?i fitowa.

Ta ajiye turaren tana tunanin ko sharrin ?aisar ne.

Ta sake fitowa yin alwala, Baba ya zaunar da Gaddafi yana ta gaya masa abin da Imran yayi, tare da ?orafin ya gaji da rashin mutuncin da yake aikatawa.

Nana hankalinta ba ya kan abin da suke faWa, hankalinta yana kan Suwaiba, da jini yake ta gangarowa daga hudar jikinta, kuma rigar jikinta ta rine zuwa jini. Amma normal suwaiba na ta ayyukanta.

Nana ta ware a gefe, tana ta jan "wa hifzan min kulli shaiWanin marid"

Sam jikin Nana ba ?wari ta kwanta, duk addu'a da ta zo bakinta yi take yi, ta waiwaya ta kalli in da Suwaiba take, ta ji?e jagab da jini ga ?arnin jinin ya cika Wakin babu daWin ji.

Suwaiba na ta kallon kaWe-kaWenta a waya, har bacci ya kwashe ta. Nana ko kyakyawan ?ifta ido ta kasa yi, ganin yadda jinin ya ji?a katifar da Jamila da Suwaiba su ke kai, ya gangaro ?asa.

Ana haka Suwaiba ta kurma wani irin uban ihu, Nana ta razana, ganin wannan bararojin da ta ba ta magani ta lasa, jikinta ba?i ?irin ta koma kamar gawayi, fuskarta ce kawai ba a ?one ba sai gashinta, ta tsaya a kan Suwaiba ta kafa ha?oranta a wuyan Suwaiba tana zu?ar jini. Maimakon Nana ta yi addu'a kawai ita ma sai ta saka ihu ta suma a gurin.

Cikin ihu da kururuwa Suwaiba ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Mama Baba ku taimake ni, Nana za ta kashe ni, Nana tana shan jinina dan Allah ku yi mini rai Nana na shan jinina!!!


Ku tuntuSe ni kai tsaye, domin fara biyan naku kuWin littafin.
https://wa.me/2348081012143
Ayshercool
08081012143
Ko kuma ku kasance da ni a kan manhajar arewabooks @ayshercool7724
BUZU
AISHA ADAM AYSHERCOOL
YOTA/002

P11

?ungurungum, page Win yau naku ne, YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION, Tare da 'yan Ayshercool media, ina godiya sosai da sosai.

A wannan karon Mama ce ta fito da gudu, jin muryar Suwaiba tana ihu.

Sai dai ta tarar da Nana a gefe, tana bacci.

Ta Wago Suwaiba tana kiran sunanta, sai dai Suwaiba ta rirri?e wuyanta, tana numfashi da ?yar tana cewa "Nana ce, Mama ki taimake ni za ta kashe ni"

Cikin kuka maman ta fara ?walawa Baba kira "Malam Isa ka zo Nana za ta kashe mini 'ya, na daWe ina faragbar kar ta cutar mini da yara, gashi za ta kashe Suwaiba"

Jamila ma tuni ta tashi, ta ja gefe, domin ita ma a tsorace ta tashi, saboda mummunan mafarkin da ta yi da Hajiya sa'a tana ?o?arin sha?e ta, ta caka mata wata wu?a.

Baba ya ce "Wani irin Nana za ta kashe ta kuma? Ba ga Nanan a gefe tana bacci ba?"

Cikin fushi da tsawa ta ce "To ka ?araso mana ka ga abin da take yi"

Ya ?arasa ya ga Suwaiba, ta rirri?e wuyanta, idanunta duk sun fito waje sai kakari take, da ?yar take furta Nana za ta kasheta.

Baba ya ce "Suwaiban Baba, buWe ido ki ganni, Nana bacci take yi me ki ke gani?"

Cikin kuka da kakari Ta ce "Baba wallahi Nana ce, jinina take sha, ka hana ta zan mutu"

Baba ya koma gurin da Nana take, ya kai hannunsa ya juyota, idanunta a buWe, amma babu ba?ar ?wayar idonta, sai farar kawai. Jikinta kuma sanyi ?alau kamar gawa.

"Ni wannan wane irin abu ne haka?"

"Ke Jamila, je ki ki taso mini Gaddafi" Jamila ta tashi jiki a sanyaye ta fita ?ofar gida, ta ?wan?wasa wa Gaddafi Waki.

Tare suka dawo, yana tsaki yana bala'in shi tattarawa zai yi ya koma in da ya fito, ya gaji da wannan bala'in na gidan.

?an tsayawa yayi yana kallon in da Nana take, ga gefe Mama ri?e da Suwaiba tana kuka.

Ya ce "Mutuwa Nanan tayi ne na ganta a haka?"

Cikin kuka Suwaiba take mi?a wa Gaddafi hannu ta ce "Yaya ka taimake ni, Nana za ta kashe ni, jinina take sha" tayi maganar tana kuka.

"Wane irin shan jini kuma?"

Nana kuwa tuni ta lula wata duniyar a yanayin da take ciki.

Domin kuwa ?aisar take gani. Ya ce "Kin ga da kin sake kin fesa turaren nan a jikinki, da jininki za a sha ba nata ba. Aike ne na musamman domin ke, da na bari kin fesa turaren nan da sai dai wata ba ke ba"

Nana ta kalle shi ta ce "To ni me za ayi da jinina? Kuma meyasa ba ka hana wannan mummunar matar shan jinin Suwaiba ba?"

Ya tan?washe ?afafuwansa ya kaWa kai ya ce "Saboda ke ce uwar gijiyata, alhakin kula da ke ne kawai a kaina. Duk da ba jininta suke bu?ata ba, amma idan 'yar aiken ta ji daWin jinin na ta, to fa ta samu wurin zama. Ko da su can jinin bai yi musu amfani ba, to ita za ta ci gaba da amfani da jininta, domin ta warke daga ciwon jikinta, idan ba ayi wasa ba hakan zai yi ajalinta."

Cikin damuwa Nana ta ce "To ka yi wani abu a kai mana"

Yayi murmushi ya ce "Zan iya wani abu a kai tabbas, amma daga lokacin da ki ka fara bani umarni hakan yana nufin kin karSi gadon gidanku. Kuma zamu yi aiki tare"

Da hanzari ta ce "A'a ni ba zan iya shirka ba na gaya maka. Amma ba zan zuba ido komai ya tafi a haka ba. Idan haka ne anya ba wannan matar Hajiya sa'a da ta kawo turaren babu masaniyarta a kan wannan abun?"

Murmushi ya yi ya shafi gefen fuskar Nana ya ce "Ban sani ba, amma ke ma zan shafe komai daga kanki yanzu wani binciken ba shi da amfani sam. Mussaman ke da ba za ki yi abin da ya dace ba, idan ki na tsananta bincike wataran za ki shiga gurin da ba zan iya ciro ki ba.
Kalli nan ki ga, ta waiwaya domin ganin abin da yake nuna mata.

?akinsu ta gani, Suwaiba ta samu bacci, Jamila kuma ta ce Allah kar ta, ba zata kwana a Wakin nan ba tsoro take ji.
Mama ta ce su tarkata su koma Wakinta, su kwana tare da yaranta a bar Nana ta ci kanta.
Baba ya kalli Gaddafi ya ce "Gaddafi, gobe in Allah ya kaimu dole mu yi sammako, mu kai yarinyar nan gurin da ka faWa Win nan. Ni kaina na fara jin tsoron abubuwan nan".

Gaddafi ya ce "Allah ya kaimu"

Nana ta dubi ?aisar ta ce "Ni dama gurin mamana ka nuno mini, na ganta ko na ji daWi"

"Idan na fara karbar umarninki, haka yana nufin kin amince da sharaWina, ni kuma zan yi miki mubaya'a na zama mai hidima a gare ki"

"A'a bari ba na so" tayi maganar tana girgiza kai.

Ya saka dogwayen yatsunsa yana ci gaba da shafa kumatunta ya ce "Alamu na nuna, sar?ar ?addara ta mayen ?arfe na ?o?arin janmu wani wuri, ta yi wani Wauri mai wahalar kwancewa. Ko na ce sar?ar na ?o?arin sar?e ki. Gobe za a wuce da ke gurin mai magani, 'yar uwakki ta shafa miki mugun tabo, tun da ta ce kina sha mata jini, babarta ba za ta yi shiru ba, za ta yi ta gaya wa mutane ne. Ga yayanki can ya sha ?wayoyi yana ta bacci, gobe har ku tafi ba zai farka ba, domin na ?arawa abin da ya sha ?arfi. A duniya zan ga wanda ya isa ya raba ni da ke. Zan ga mai karambanin mai maganin da zai jarraba hakan".

"Allah ne zai raba ni da kai" ta yi maganar a hasale.

"Da zai rabani da ke, da bamu haWu ba" ya bata amsa.

Nana ta waro ido ta ce "Kaii zaka yi saSo, ki ba musulmi ba ne? Ko da yake musulmi ba zai yi abin da ka ke yi ba"

?aisar ya yi dariya ya ce "Kamar ba musulmin ne ke neman jininki su yi tsafi da shi ba"

Ya koma ta bayanta, ya zuro kansa gefen fuskarta, hakan ya ?ara adadin bugun zuciyarta, jikinta yayi sanyi ?alau kamar wadda aka saka a cikin firinji.

Ya ce "Bari na sake nuna miki wani abu, amma akwai bu?atar na tsaya kusa da ke, idan ba haka ba, wannan 'yar ?aramar ?wa?walwar ta ki bugawa za ta yi. Kalli can" ya nuna mata wani mudubi. Ta Waga kai ta kalla.

Kawai ta ga Auwwal a kwance ana yi masa wankan gawa, gefen cikinsa na ta zubar da jini.

Razana tayi za ta mi?e, amma ya ri?e ta ya ce "Kar ki zarge ni, babu sanya hannuna a cikin wannan abin, ya gama shirinsa gobe zai tafi Abuja, Wazun nan masu ?wacen waya suka tare shi, suka karSi wayar suka caka masa Wan buda.
Yaran kuma da suka yi, abokan yayanki ne, nan da 'yan kwanaki idan bincike yayi nisa shi ma za a kamo shi".

Wani irin yin?uri Nana ta yi, domin ta ?wace daga jikinsa amma ta ji an ri?eta. Ta Waga kanta kawai ta ganta a ana kiciniyar shiga taxi da ita, ta waiwaya ta ganta a tare da Yaya Atine da Baba.

Ta ja ta tsaya ta ce "Wai ya na ga haka?"

Baba ya ce "Ba ki da lafiya, gidan mai magani za mu je"

"To Baba ai ban yi sallar asuba ba"

Yaya Atine ta ce "Mu je, idan an je gidan mai magani sai ki yi sallar"

Nana ta kalli sama yadda gari ya fara haske, ta ce "A'a ni a bari na yi salla"

Baba ya ce "Ta dawo hayyacinta, a ?yale ta tayi sallar"

Nana ta shiga gida Yaya Atine ta bita, ta yi alwala.

Yaya Atine ta ce "Rabi ki bari a tafi da Suwaiba gidan mai maganin nan a duba ta ita ma"

Mam ta ce "Eh ko ba gidan mai magani ba, ta je ta ?arasa lasheta a hanya ta kashe ta, babu in da za ta je, kuma wallahi kurwar Suwaiba ta fi ?arfinki" ta yi maganar tana hararar Nana.

Nana dai ta yi alwala, ta gabatar da sallar asuba, aka saka ta a cikin taxi, aka ja aka tafi, ba tare da ta san ina suka dosa ba.

Suwaiba kuwa ba ta tashi daga bacci ba, sai bayan ?arfe tara na safiya, kuma babu wanda ya tashe ta, domin ta yi salla. Sai a lokacin ta yi salla, ta nemi abin karyawa.

Jin Mama na ta jera mata sannu ya sanya ta ce "Wai mama sannun me ki ke yi mini ne?"

Mama ta ce "A'a abin da ya faru da ke jiya mana, wannan azzalumar tana neman kar ki"

Cikin rashin fahimta Suwaiba ta ce "Wace ce? Ni fa ban gane ba"

"Jiya kururwar da ki ka din ga yi ki na Nana za ta kashe ki, tana miki jini, ba mu yi bacci ba fa" Suwaiba ta zaro ido ta ce "Ni Win?"

Jamila ta ce "Eh mana, kasa numfashi ki ka yi fa, kina ta kuka wai Nana tana sha miki jini"

Jikin Suwaiba ya yi sanyi, ta ce "To ai ni tun da na kwanta, ko juyi ba na tunanin na yi, sai yanzu na tashi daga bacci"

Jamila ta ce "Ikon Allah, kin ga kururwar da ki ka din ga yi kuwa, wai Nana na sha miki jini?"

"Ni dan Allah ku daina wannan zancen tsoro ku ke bani wallahi kar na je, aljanun nata ne nima su ka shafe ni"

Muryar Imran ce ya dawo da su kan tsakar gidan, yana ta kwaWa wa Nana kira.

Nasiru ya ce "Nana fa sun tafi gurin mai magani, bayan sallar asuba"

"Kamar yaya ita da wa?"

"Asubar farko, aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login