Showing 90001 words to 93000 words out of 190498 words

Chapter 31 - Buzu Book 1 Complete



"Ko za ka sauke rawanin naka mu yi magana?" A hankali ya juya ?wayar idonsa, yana kallonsa amma bai yi magana ba.

"Magana nake, ka sauke rawanin fuskarka mu yi magana" still bai sauke ba, kuma bai yi magana ba, sai ma yin?urawa da ya yi, ya juya zai fita" cikin azama ya tashi ya sha gabansa ya ce "Ya mu na magana za ka tashi ka tafi?"

"Me yasa ka kira ni?" Ya yi maganar yana tsare shi da ido.

"Bu?ata ce"

"Ta me?"

"Ina so ka gaya mini ko nawa ka ke bu?ata, ka saki yarinyar nan Nana da babanta ya aura maka"

Ya gyara tsayuwarsa sosai yana kallon cikin idanun Alhaji Zailani, ya ce "Je devrais divorcer?" Alhaji Zailani ya yi ?uri da ido yana kallonsa, dan bai gane me ya ce ba.

Ya taka a hankali ya je gaban Alhaji Zailani ya tsaya, sannan ya ce "Me yasa ka ke so na sake ta?"

"Saboda na fi ka bu?atar ta"

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Ka ce ka fi ni bu?atar ta?" Kafin Alhaji Zailani ya ba shi amsa, kawai ya gansu a tsakiyar dokar daji.

Ya saka hannu, ya sauke rawanin fuskarsa, kyakyawar fuskarsa ta bayyana ya ce "Ka ce ka fini bu?tarta? Har ka manta da abin da na yi maka a wancan lokacin?, shi ne ka sake biyo ni da wannan maganar?"

Ya saka hannunsa a wuyan Alhaji Zailani, wasu irin dogwayen farata suka tsiro a yatsunsa, a hankali kamaninsa suka gushe, fuskar wani tsoho tukuf ta bayyana.

Ya ?ara tsananta sha?e Alhaji Zailani ya ce "Ni na fika bu?atar ta, fansa ta zan Wauka a kanta. Mallakina ce, fansa zan Wauka, dan haka na fika bu?atar ta!!

Jin numfashin sa ya yi, ya dawo iya ?irjinsa, jini ya fara zubowa daga gurin da ya huda shi da faratansa.

Ayshercool
08081012143


Page 27


"Wayyo Allah, Amina tashi Amina zai kashe ni" a razane Hajiya Amina ta tashi zaune tana waige-waige ta ce "Waye zai kashe ka?"

"Haska mini wuyana jinina ya na zuba, duba mini da sauri" A sukwane cikin matsanancin razani, ta sauka daga kan gadon, ta kunna ?wan lantarkin Wakin.
Alhaji Zailani na ri?e da wuyansa, ya haWa uban gumi ta ko ina. Ta ?arasa gabansa tana kallon wuyansa ta ce "To ai Alhaji ba komai a wuyanka"

"Kin tabatta?" "Wallahi wuyanka babu komai, sauke hannun mu gani" ya sauke hannunsa a hankali. Ta ce "Shafa ka ji, babu komai a gurin fa" ya gyara zamansa yana ajiyar zuciya cike da razani, saboda yana jin sha?ar nan har a lokacin.

"Mafarki kawai ka yi, ka yi addu'a ka kwanta"

Ya ce "Ko ma ki kwanta kawai" ba ta matsa masa ba, ta gyara kwanciyarta ta kwanta.
Shiru ya yi ya dafe kansa yana tunani, tabbas ya ?uduri aniyar kiran wanda aka aura wa Nana, ya biya shi kuWi ya sake ta, amma ya kasa tunawa ya kira shi Win sun yi maganar? Ko kuma sharrin mafarki ne kawai?. Tabbas ya ?allafa rai a kan burin cikar muradinsa, dan haka ko da tsiya, ko da tsiya-tsiya sai ya yi tarayya da Nana burinsa ya cika.
Bacci bai Wauke shi ba, sai gefin sallar asuba.

****

Ummi na ta shirya yara, tana Waukar musu kayan da za su yi amfani da shi, saboda gida za su tafi saboda wunin bikin Nana, dan a washegari za a kai ta gidanta, an samu da kyar Baba ya bayar da wani abu, a yi girki a yi mata wunin biki, shi ma sai da Yaya Atine ta saka baki, da Anty Saude 'yar autar su, ta haWa da dubu hamsin Win da buzayen nan suka bayar, ta yi mata sayayya.

Saleh ne ya faWo gidan, yana ?wala mata kira, kamar mara hankali.

"Lafiya ka ke yi mini wannan kiran haka?"

"Wai da gaske an Waura wa Nana aure?"

Ummi ta Wan taSe baki ta ce "Eh, gobe ma za a kaita gidan mijinta"

"Lallai ma, wato saboda an samu wanda ya fi ni kuWi, shi yasa ta yi ta wula?anta ni?"

"Ai Saleh na gode Allah ta wani fannin da ba ta aure ka ba, da na ji haushin ta, amma tun da ka iya kai Babanmu gurin 'yan sanda ba kunya babu tsoron Allah, na ce lallai ka ri?a idan aka yi auren sai abin da Allah ya yi"

Ya sassauta murya ya ce "Wallahi Ummi ba a son raina ba, Hajiya ce ta dage sai an fasa an karSo kuWin nan, kuma na din ga ciwon cikin nan, ina mugwayen mafarkai, Hajiya ta ce dama an ce mata duk wanda zai aure ta mutuwa yake yi"

Ummi ta ce "koma dai mene ne, ai yanzu ka rasa, kuma kai ka san babu inda za ka je neman aure a baka a arhar da Baba ya so baka Nana" ya zauna a tsakar gidan cike da dana sani, ya gama zamansa ya tafi ba tare da ta sake kula shi ba.

*****

Kallonsa ta yi a lokacin da yake ?o?arin fita daga bedroom Win, ta tsuke fuska ta ce "Wai ina za ka je ne?"

Ya kalle ta ya ce "Eh, da wuri zan fita ne, yakamata na je na duba Fadila kafin na fita"

"A'a ka na azarSaSi dai yau ita ke da kai, jeka a sauka lafiya"

Kamar wanda ya aikat laifi ya yi sororo ya ce "Haba ke kuwa? Haryanzu tana cikin jimamin mutuwar yaron nan, tun da ya rasu take fama da rashin lafiya, tana bu?atar a rarrashe ta, amma kin saka kishi a gaba ai yakamata ki tausaya mata"

"Wai dan Allah a kanta aka fara mutuwar Wa da ba za ta yi tawakalli ba? Ko ni ma ba gani da 'yar ba mara lafiya. Kullum na yi magana sai ka ce kana gurinta ka na rarrashinta, ka na lallaSawa dai ka yi mata wani cikin, ku ?arata"

Ya Wage kafaWarsa ya ce "Eh haka ne maganar ki, dama yakamata a yi hakan, kuma mu haWa da addu'a sai ki ga an dace" ya fice ya bar ta. Wani irin gululun takaici ya tsaye mata, kawai ta ja guntun tsaki.

A gefen gado ya tarar da ita a zaune ta yi shiru. Sallamar da ya yi ne ya dawo da ita hayyacinta, ta amsa masa. Sannan ta Wora da "Good morning Daddy" bai amsa ba ya ?arasa ya zauna a kusa da ita, jakar makarantar Muhsin ce a gefenta, hannunta kuma littafin sa ne. Ya saka hannu ya zare littafin ya duba bangon littafin. Ya yi zanen mace a gaban allo, ya rubuta Anty Nana, duk da spelling Win bai fita ba, a ?asa kuma ya zana wata ya rubuta mom sai kuma babansa. Jiki a sanyaye ya kalli Fadila da tuni idanunta suka cika da hawaye.

"Haba babyna, anya Fadilana ce wannan ko dai an canza mini da wata? Ya kamata a ce mun yi tawakalli. Haryanzu ina jin raWaWin mutuwar boy, amma wallahi wannan yanayin da ki ke ciki ya fi Waga mini hankali, dan Allah ki kwantar da hankalinki ki yi ha?uri mu ci gaba da addu'a".

Tamkar ya fama mata ciwon da yake cikin zuciyarta, ta ce"Daddy"

"Na'am Fadila"

"Ina addu'a, ina son yin tawakalli but am missing my son" ta yi maganar cikin sheshshe?ar kuka. Ya rungume ta a jikinsa, idanunsa na cika da hawaye, saboda tamkar bai taSa haihuwa ba sai a kan Muhsin.

"Ki yi ha?uri ki kwantar da hankalinki, kin ga yanzu idan ba ki kwantar da hankalinki ba, ta yaya zamu samu nutsuwar samo wani babyn?" Ya yi maganar da sigar wasa. Haka ya din ga rarrashinta, har ta Wan nutsu, ya tattare kayan Muhsin, ya ce "Duk tattare kayansa zan yi na mayar site Wina, tun da su suke Waga miki hankali ki ke kuka". Ba ta ce komai ba ta yi shiru.

Ya dawo ya kwanta a jikinta ya ce "Yauwwa tun da na gama rarrashin ki, nima a rarrashe ni" a dole sai da ya saka ta dariya, dama hakan yake so.

Hajiya sa'a ce ta yi sallama a falon, ta amsa mata da kyar tana cika tana batsewa.

"Ke kuma lafiya ki ke ta huci haka? Ko ke da yaran ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a"

"Ina fatuhun yake? Ganinsa nake son yi, Allah ya sa bai fita ba.

"Yana can yana lalata"

Cikin rashin fahimta hajiya Sa'a ta ce "Lalata kamar yaya?"

"Gurin 'yar gwal mana, tun ?arfe takwas ya bar sashina, ya tafi gurin matarsa wai rarrashinta yake yi, saboda a kanta aka fara mutuwar Wa, ya ce da wuri zai fita, amma har sha Waya yana gidan nan, babu inda ya je yana gurinta"

A fusace Hajiya Sa'a ta ce "Ni kaina fa iskancin yarinyar nan ya fara isa ta, tun lokacin zaman makokin yaron nan take ta wasu abubuwa, babu alamar tawakalli a tattare da ita, bari na je za su gane ba su da wayo"

A falo ta tarar da su, Alhaji Fatuhu ya shirya zai fita, amma su na zaune a kan 3seater, sai magana yake yi mata ?asa-?asa yana murmushi, ita ma Fadilan tana ta murmushi tana rufe fuska kamar wasu saurayi da budurwa.

"Fatuhu meye haka? Aka ce ka na nan ka na rarrashinta, ta ?i sakin jiki ta kwantar da hankalinta a kan mutuwar yaron nan, to idan ba za ta ha?ura ba ta bi shi lahirar mana saboda ?auna"

Alhaji Fatuhu ya kalle ta ya ce "Haba Yaya sa'a, ke ma fa uwa ce, kin san dole ta shiga damuwa, kuma na san ba zai wuce Maryam ce ta zauna ta gaya miki abin da aka yi da wanda ba a yi ba"

Hajiya sa'a ta ce "Wanda dai aka yi, tun da ga shi ina gani"

Fadila ta kalle ta cikin mamaki, ta rasa abin da ta yi wa matar nan, tun Muhsin yana gadon asibiti tayi ta hantarar ta, wai duk ta damu mutane dan Wan ta ba shi da lafiya . Haka da ya rasu, ta din ga hantarar ta a cikin mutane wai ba ta da tawakalli. Dama tun can ba wani shiri suke yi ba, amma abubuwan da ta din ga yi mata, sun Waure mata kai kuma sun saka ta ?ara tsanarta, saboda babu alamun tausayawa a tattare da Hajiya Sa'a.
Tsam ta mi?e ta ce "Daddy a dawo lafiya, i will call you"

Ya ce "Ok dear"

"Au Fadila kin fi ?arfin ki gaishe ni?"

Alhaji Fatuhu ya ce "Dan Allah yaya ki daina yawan ?orafin nan, ta yaya za ta gaishe ki, daga shigowar ki an zigo ki kin zo ki na faWa"

?o?arin hayayya?o masa ta yi, ya haWe rai yana kallonta, ta sani sarai idan ya buWe baki ba zai raga mata ba, hakan ya sanya ta bar maganar, ta shiga abin da ya kawo ta.

*****

Sauri-sauri ya shirya, ya nufi gurin da yake ajiye mota, ya fito da motar zai fita.
Sannu a hankali ya buWe gate Win, komai a nutse yake abin sa, babu gaggawa ko rawar jiki kamar yadda sauran 'yan uwansa suke yi.

Hankalin Alhaji Zailani yana kan waya, babu tsammani ya Waga kansa suka yi ido huWu da shi, ya buWe fuskarsa. Hantar cikinsa ce ta kaWa gabansa ya faWi.

Shi ma ya ?ura wa Alhaji Zailani ido, da kyar ya iya jan motar ya bar gidan.

****
Gidan su Nana kuwa, ranar ta kasance ranar da za a kaita, sai dai babu wanda ya san ina za a kai ta, kuma ko katifa Baba bai saya ba. Da Ummi ta yi masa magana sai cewa ya yi ba shi da kuWi, ita ta yi mata. Abin ya Sata mata rai, babu wanda ya san wani irin guri za a kaita, idan babu labule da katifa a ?asa za ta zauna? Ga kuWin sadakin Nanan har dubu Wari biyu a hannunsa.

Nana kuwa kawai dai ga ta nan ne, hankalinta ya kasu kashi-kashi, tana tunanin maganganun da ta ji da wannan muryar, ga kuma abin da ?aisar ya gaya mata. Duk da wani Sangaren na zuciyarta na gargaWinta da yadda da maganganun Aljanu, wata?ila kawai wasa suke yi mata da hankali. Tana jiyo Mama tana SaSSaka dariya tana cewa yanzu idan buzayen su ka ?i zuwa, su nuna in da za a kai Nana, ko kuma suka gudu shikenan Nana ta zama bazawara.
Maganar ta sosawa Nana rai nesa ba kusa ba, wato duk bayan abubuwan da ta yi mata a baya, har ma tunani take yi, ta yi zawarci. A take Nana ta yi wa kanta alwashin ko bangon duniya wanda aka aura mata, zai Wauke ta ya kai ta, za ta bi shi ko da kuwa zai din ga azabtar da ita ne, ta gwammace hakan da ta sake dawowa gidan nan da sunan zawarci tun da dai ibada take yi.
Abubuwan da suke damunta kuwa, ta fauwwalawa Allah, ta dake ta je ta yi wanka. Ta yi kwalliya da wannan shaddar, da kayan da aka kawo mata.
Kasancewar Nana tana da fata mai kyau, 'yan kayan da Ummi ta haWo ta yi mata gyaran jiki na kwana biyu, ta yi kyau fatar ta ?ara haske. Ga zanen lalle an yi mata. Gashin kanta ma ya yi kyau, komai kyau ne da shi idan ya sha gyara.

Sai da Mama ta yi saroro, da Nana ta fito cikin kayan nan, tamkar matar wani hamsha?in mai kuWi. Duk da ta rame sosai, amma kayan sun zauna a jikinta, tamkar tela ya gwada ta. Fuskarta babu yabo babu fallasa ta fito tana gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki.

Nan gida ya Wauki guWa, aka din ga yi mata fatan alkhairi. Duk da ga a yadda auren ya zo mata, kuma har a lokacin ba ta tantance waye ma mijin nata ba. Amma ganin mutanen da suke ta shiga su na fita, ana cin abinci, a dalilinta. Kawai ta dur?usa ta yi sujudu shukur, ko ba komai wannan wata rana ce da kowace mace da ta san ciwon kanta, take fatan gani a rayuwarta.

"Allah ga Nana, Allah ga baiwar ka. Ina godiya da tarin ni'imomin ka a gare ta" ta Wago fuskarta duk hawaye. Suwaiba ta ce "Ji wata gulma, har da sujjada kamar auren gaske, wai a dole sai an raina wa mutane hankali. Mu dai a hanzarta a yi a bar mana Waki"

Nana ta kalle ta ta ce "Suby kenan, ai duk ci gaba ci gaba ne, ba Waki ba gidan zan bar muku baki Waya ku sake, ina fatan aniyar kowa ta bi shi"

Suwaiba ta ce "Aniyar kowa ta bi shi kamar yaya, me ki ke nufi?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ba zan biye miki ba, ni yau ina cikin farin ciki ne a gare ni, ba zan biye miki ki lalata mini ita ba" Suwaiba ta ci gaba da faWar maganganu. Nana kuma ta fice ta bar mata Wakin.
A hakan an sassamu wanda suka bayar da gudummawa sosai da sosai, domin kowa yana yabon Nana da halaye na gari, dan duk 'ya'yan malam Isa babu mai ha?urinta da biyayya, duk da wasu lokutan ita ma tana da faWa, amma akwai ladabi. Ummi ta kasa ta tsare tana karSar kaya da kuWin gudunmawar da kanta,
Ta kuma din ga ?o?arin, duk wani yin?urin kawo hargitsi da Mama take ?o?arin yi a gurin taron ta hana.
Nana ta samu kayan kitchen, da kuWaWe daga hannun jama'a da dangi.

Da yamma sai ga Yusuf da mota, tare da Sule, Hajiya Amina ta ce a Wauki Nana a ciki.

Yaya Atine ta ce a fara zuwa su ga gurin, su san abin da za su saya, amma Yusuf ya ce babu bu?atar hakan, amarya za su Wauka.

Gaba Waya jikin Nana a sanyaye yake, su Yaya Atine suka saka ta sake wanka, Ummi ta bata wata lafaya da ta saya mata, ta saka ta feshe ta da turare.

Ana ta rangaWa guWa, aka kai Nana gurin Mama wai ta yi mata nasiha.

Mama ta ce "A'a ni me zan ce, ai ta san komai ba abin da ba ta sani ba, a sauka lafiya"

Nana a ranta ta ce "Ko ba ki faWa ba lafiya zan sauka, kuma sai Allah ya kunya ta ki".

Baba yana ?ofar gida, aka kai masa Nana ya yi mata nasiha.

Ya ?are mata kallo ya ce "Yanzu kin ga abin da ki ka janyo wa kan ki ko Asma'u? To ki buWe kunne ki saurare ni, babu zawarci a gidana, duk Wan da zan aurar kin san ina jaddada wannan, ba zawarci babu yaji a gidana. Allah ya rufa miki asiri da miji na gari, amma fafur ki ka ?i. Je ki Allah ya ba da sa'a ya baku zaman lafiya" Nana ta daskare a gurin ta kasa motsi balle ta tashi.

"Na ce ki je Allah ya sanya alkhairi" ya maimaita mata.

Ta Wago idanunta a hankali ta ce "Baba... Sai kuma maganar ta ma?ale ta ?i ?arasa fitowa, saboda kuka da wani abu mai nauyi da ya danne mata ma?oshinta.
Ta yin?ura ta tashi, har sun kai bakin motar, ta waiwaya, kawai ta ga Baban ya zubo mata ido, idanunsa cike da hawaye.
Kawai ta yi bismillah ta shiga motar.

Ba Nana ce yarinya ta farko da Baba ya aurar ba, amma har cikin zuciyarsa ya ji rabuwa da ita, duk da tarin haushinta da yake ji. Wani sashen na zuciyarsa kuma ya fara tunatar da shi, da jin kamar bai kyauta ba abin da ya aikata.

Kasancewar mota Waya tak aka kawo, daga Yaya Atine, Anty Sa'a sai Ummi suka tafi raka Nana.

Su na tafe a hanya su na ta hirar su, Nana kuwa zubar da hawaye kawai take yi.
Sosai Yusuf ya ji tausayin Nana, shi kansa ya jinjina girman wauta da rashin sanin ciwon kai da mahaifin Nana ya yi.

"Kai wannan wace irin unguwa ce duk babu mutane, wannan ai sai a yanka mutum a binne ba a sani ba"

Ai kuwa babu shiri Nana ta Wago, tabbas haka ne, unguwar manyan gidaje ne sosai awon gwamanti, sai dai babu alamar akwai jama'a da yawa a unguwar.

Gaban wani gida suka yi parking, mai Wauke da doguwar katanga.

Ko da suka fito, Yaya Atine ta ce "Aka ce mai gadi ne, ya na ga katafaren gida haka?"

Sule ya ce "Eh gidan da zai yi aikin gadin ne, a Wakin masu gadi za su zauna"

Ta ce "To ikon Allah" ya buWe gate Win suka shiga.

Akwai ?atuwar haraba a gidan, ta ko ina shuke-shuke ne, main gidan kuma yana can nesa da gate Win gidan. Daga nan kusa da gate Win kuma wani wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login