Showing 21001 words to 24000 words out of 190498 words

Chapter 8 - Buzu Book 1 Complete

a hanya mana"

Nana ta Wan yi turus ta ce "Bakomai na gode, ai babu nisa sosai"

"A'a bakomai, ai ni na ce muje sai mu ajiye ki a hanya" sai ta ji mutumin yayi mata kwarjini, ta ci gaba da jayayya da shi, amma har cikin zuciyarta ba ta so hakan ba sam.

Su na tafe a hanya, yana yi mata tambayoyi, kan matakin karatunta, da makamantansu. Ta din ga bashi amsa sama-sama a tsorace, dan haka kurum ta ji ya takura mata da yawa.

Sai dai ya din ga yaba mata, da ?o?arin da take yi da yara. A bakin titi ta ce za ta sauka, ya Wauki kuWi dubu biyar ya ba ta, ta ce masa ba zata karSa ya ce ba zata sauka daga motar ba, sai da ta karSa, sannan ya buWe, ta yi masa godiya ta nufi hanyar gida.

A ?ofar gida ta hangi Baba, yana zaune a ?asan bishiya, sai hamma yake yi, idanunsa jawur.
Ta nufi inda yake, ta je ta dur?usa tana gaishe shi. Da ?yar ya amsa mata yana kawar da kai gefe. Ta Waukko dubu uku a kuWin nan ta mi?a masa ta ce "Baba ga wannan, yaran da nake kula da su ne, baban wani ya bani" sai ya waiwayo da sauri ya saka hannu ya karSa.

"Masha Allah, ai yakamata dai dama iyayen yaran nan, su din ga yi miki ihsani, tun da dai yaran nan na su da ki ke yi musu wahala, ba wani biyanki ake yi da kyau ba. Ko suturar jikinki suka kalla ai sun san mabu?aciya ce ke, ba sai an ce su baki ba"

Nana ta basar da zancen, dan ba ta son ire-iren waWannan zantukan na Baba, masu cike da son zuciya ta ce "Bari na shiga na shirya, na tafi Islamiyya"

"Zauna nan mu yi magana kafin ki shiga gidan" Nana ta zauna sosai tana sauraren Baba.

"Nana duk abin da ki ka ga ina yi, ?o?ari nake yi a kanki. Ki daure ranar talata ki je gidan yaya Atinen, a jarraba mai maganin wurinta ko za a dace. Idan bai yi ba sai fa mun dangana da mai maganin da Gaddafi ya bani labari, idan ba haka ba babu lallai ki iya zaman aure ki yi ha?uri? shi wancan malamin naku dama ba sonki yake ba, tun da ya gudu bai turo iyayensa ba. Tun daga wannan ba sai ki ha?ura ayi da shi ba, nima a rage mini Wawainiya ba. Yanzu ba a auren soyayya, ko wani zurfafa bincike duk bayi ake ba. Ki tashi ki shiga kar ki makara"
Ba ta ce uffan ba, ta tashi jikinta a sanyaye ta shiga gida, gaba Waya kalaman Baba babu na ?warara gwiwa sai na kashe jiki da cire wa mutum tsammani.

*****

Gaba Waya Auwal ya daina shiga makaranta, wanda hakan ya Wagawa Nana hankali, ta na ta son su haWu da shi, ta yi masa bayanin abin da ya gani ranar da ya je gidansu, amma ba ta samu ganinsa ba.
Ita ba waya ba balle ta kira shi, abin duniya duk ya dameta. Ranar asabar da sassafe, Baba da kansa ya tashi Nana, ya sanyata shiryawa, ta tafi gidan yaya Atine.

Babu yadda ta iya Baba, zuciyarta ta din ga raya mata, kar ta je, amma ta tabattar idan ba ta je ba, fushi zai yi da ita.

Tun da Allah ya sa ta je gidan, bayan sun gaisa yaya Atine take masifa, wai ta ?i tsayawa a nema mata magani ta wahalar mata da Wan uwa. Nana dai ba ta ce uffan ba, Yaya atine ta yi ta faWanta.

Ta shirya ta saka Nana a gaba, suka tafi wurin mai magani.

Ayshercool
08081012143

BUZU

Ayshercool

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA 002)

P8

Kallon farko da Nana ta yi wa mai maganin, takaici ya kama ta du?un-du?un da shi kamar wakilin sarkin dauWa. Yana zaune a cikin wasu tarin shirgi da ta rasa ko na uban mene ne.
?akin sai azabar ?auri yake yi, da tsamin wasu abubuwa da ta kasa tantance ko na mene ne.
Jikin bangon Wakin, an zana wasu irin hatimai, kuma an sa?ale ?ahunhuna da layoyi. A take zuciyar Nana ta bata wannan mutumin boka ne, ba malami ba, ko kuma malun malun.

Ya ?are wa Nana kallo, ta kawar da kai ta ?i kallonsa, Yaya Atine ta gyara zama za ta fara yi masa bayani, ya dakatar da ita, ya ce "?an saurara tukuna Hajiya. Ba ki ga ta kasa haWa idanu da ni ba? Ai sun zo shegun sun ?araso, tare ku ka shigo da su ai, ku na tafe su na biye da ita runduna guda, manya da yara tsofaffi da matasa, yanzu haka kusa da ke ma duk su ne a zazzaune makaran nata, sun cika gurin nan"
Yaya Atine ta zabura ta tattare ?afafuwanta ta ce "Innalillahi. A nan Win malam?"

"Eh fa, yi a hankali kar ki hau kan wani"

Nana kuwa waiwaya ta yi, domin ?ara tabattar da a kan wa yake maganar ne?.

Ya gyara zama, ya juya ya Waukko wani ruwa, a wata tasa ruwan duk yayi gansa kuka, ba?i ?irin da shi, ya Webo a hannunsa ya watsowa Nana. Take Nana ta Wan ja da baya, saboda idan wannan ruwan dauWar ya zuba a hijjabinta jirwaye zai yi.

Ya ce "Kin gani ko, ga su nan za su yi magana, sun ji ruwan azaba, wane su dan uban su. Waye ya zo kanta za ka yi magana ko kuwa?"

Nana ta Wago kai baki buWe tana kallon ikon Allah, tana tsoron ta yi wani abin, ya ce Aljanun ne suka zo, kar ta je ya zane ta. Sai dai ta ga idan ba ta yi da gaske ba, sai ya yi mata wanka da ruwan dattin nan, aikuwa ta tashi tsaye ta ja da baya.
Yaya Atine ta mi?e da sauri, ta yi baya cike da tsoro da fargaba.

"Ba za ku yi magana ba?" Yayi maganar yana zare mata ido, tare da mi?ewa.

Nana ta ce "Wai suwaye za su yi maganar ni ce fa"

Ya ce "Da alama wannan makaran nata, su na da azabar taurin kai, sai an yi aiki tu?uru a kansu. Yanzu zan yi mata wani ?aramin aiki, somin taSi idan kuma da kuWi a hannunki ki bayar da dubu goma sha biyar, za a sayo turarukan da za ayi mata aikin da su.
Ranar Litinin kafin hudowar alfijir, ake yin aikin, za ki kawo mana namijin goro guda bakwai, da zuma farar sa?a, kuma da wuya idan ba sai an yi yanka ba, kin ga sun ?i magana". Yayi maganar yana ?arasa she?a wa Nana ruwan hannunsa, hakan ya sanya hijjabin Nana, kwanciya a jikinta ya fito da surar da Allah yayi mata.
Takaici ya isheta, tun da suka zo, mutumin nan bai ambaci Allah ba, ko ayar Alqur'ani sai shirme da soki burutsu. Warin ruwan da ya zuba mata duk ya cika mata hanci. Kawai ta nufi hanyar fita ta bar Wakin. Yayi wuf ya ri?o hijjabinta.

A fusace Nana ta juyo ta ce "Meye haka, ka sakar mini hijjabina ba na son haka"

Mutumin ya dubi Yaya Atine da ke zare ido ya ce "Hajiya za su yi magana yanzu, ba ita ba ce ba" Nana ta saka ?arfinta za ta fizge hijjabinta, ya saka ?arfinsa ya hankaWata take ta faWa kan shirgin da ke cikin Wakin, wani azababben wari, kamar na ruSewar wani abu, ya daki hancin Nana, ga ?ume ?eya da ta yi, wanda gudun kar ta yi ihu, ya sake fakewa da haka ya yi mata wani abun, ya tilasta ta yin shiru. Tana ?o?arin Wagowa, ya sha?a mata wani abu a hancinta, ta kawar da kanta ba ta she?a da yawa ba, amma ta ji wata irin gigitacciyar azaba ta ratsa hancinta zuwa kanta. Ba ta san lokacin da ta kurma ihu ba, jin azabar ta danne mata hanyar fitar numfashi.

Ya kalli Yaya Atine ya ce "Hajiya jeki waje zan yi aikina"

Yaya Atine ta ce "Ka na ganin ba wani abu na je?"

"Eh mana, idan ma kin tsaya babu abin da za ki iya yi, idan ba haka ba idan suka zo fita su shige jikinki" ai cikin azama ta bar Wakin. Sai da ya le?a ya tabattar ta bar wurin, sannan ya dawo kan Nana, da take ta layi a ?asa.

Kan Nana ya yi, yana ?o?arin kai hannayensa ?irjinta duk biyun, ta yin?ura ta juya tana takaicin yadda Yaya Atine ta iya tafiya ta bar ta, daga ita sai wannan zindi?in mara tsoron Allah.

?o?arin juyo da ita yayi, yana laluben yadda zai saka hannu a cikin jikinta, tayi wani kyakyawan yin?uri, ta fizgo wani ?aho da ke rataye daf da ita, ta raWa masa a daidai tsakiyar kansa.

Afujajan ya tashi tsaye, yana zazzaro ido, ya gigice saboda yadda ta yi masa dukan a bazata, dan a zatonsa hankalinta ya gushe.

Ya kasa tsayuwa, ya nemi wuri ya zauna, saboda azabar raWaWi.

Ta tashi da ?yar, tana tangaWi, ya yin?ura ya yi kanta domin hanata fita, kar ta tona masa asiri. Amma ta sake Waukan wata ?warya wadda take cike da ruwa, yayi ba?i ?irin saboda tarkacen da yake ciki, ta she?a masa a fuska, sannan ta tattara Wan kuzarin jikinta, ta yi masa Sarin makauniya da ?waryar a fuska sai da ?waryar ta ragargaje.

Ganin Nana ta fito tana tangaWi, ya sanya Yaya Atine tashi ta nufe ta, mutanen wurin na ta yi mata sannu.

"Ke Nana lafiya, ke ce ko aljanun naki ne? Wani mugun kallo ta yi wa Yaya Atine, ta Wauki takalmanta a hannu ta ri?e.

Yaya Atine ta koma Wakin mai maganin, ta tarar da shi hanci na zubar da jini. Cikin tashin hankali ta ce "Malam lafiya kuwa?"

"Artabu muka yi da aljanun nata, ba aljanu ne a kanta ba, ba?a?en iblisai ne, shaiWan ne da zuriyar sa" ya yi maganar yana shafo jinin da yake fita daga hancinsa.

Sai hankalinta ya rabu biyu, tana ?o?arin ta tambaye shi, abin yi, kuma ga hankalinta a kan Nana. Ta koma in da ta bar Nana a tsaye, wanda suke zaune suka ce mata ai ta fita.

Ta fita da sauri, amma ko alamar Nana ba ta gani ba, ta bi hanya tana salati da fatan ba wani wurin ta yi ba.
Sai da ta ?arasa titi, ta hangota zaune a gefen hanya, takalmanta a hanunta tana ta layi.

Su na yin ido huWu, kafin Atine ta tsallaka, Nana ta tashi ta shige wani adaidaita sahu, ya ja sun tafi.

Salallami da salati, Atine ta hau yi, ta tari wani adaidaita sahun, ta tafi gidansu Nana.

Baba na ganinta a rikice ya ce "Atine yaya dai? Lafiya kuwa?"

"Ina fa lafiya Isa, mu na wurin mai magani, sun yi karambatta da aljanun nata, kawai ta fita ta haye adaidaita sahu, ai na za ta nan ta yo"

Gaddafi da yake wanki, ya ja tsaki ya ce "Wallahi lamarin yarinyar nan har da iskanci, kuma da gangan take ?in yin auren nan, a kaita gidan mutumin nan da na gaya maka Baba, idan ba gaske ne, idan ma ?arya take yi duk zai faWa babu wani aljani da ya gagare shi"

"To yanzu a ina za a ganota?"

Baba ya ce "To wa ya sani, kwanaki fa kwananta biyu ba ta nan, sai daga baya suka zo da Ummi, wai kawai ganinta ta yi a gidanta, idan ma da gaske take, idan ma ?arya suke yi oho musu. Ni wallahi na gaji da sabgar yarinyar nan shi yasa nake Alla-Alla a samu mai so ya aura na huta. Kuma ga wannan ?anin mijin Ummi ta tsaya tana iyayi"

Babu tsammani, sai ga Nana ta shigo, Jamila ta ri?ota tana ta tangaWi, da takalmanta a hannu.

Gaba Waya suka yi kan Jamila da tambaya "A ina ki ka ganta?"

"Gidan maman khairat zan je, kawai na hangota tana ta tangaWi kamar ma ta kasa gane hanyar gida ne"

Mama da take Waki, tana jin su, sai yanzu ta yi but ta fito ta ce "Jamila, ban hana ki nani?ar yarinyar nan ba, sai kin kwashi masifa da bala'i"

Atine ta ce "To 'yar nema, da ki na jin duk abin da ake yi, ki ka ?ule a Waki?"

Mama ta ce "Ya shafe ni ne da zan fito, ba zaki cikata ba?"

"Mama faWuwa za ta yi fa idan na cikata"

"Dan ubanki ki rabu da ita aka ce, duk ranar da ta ji miki rauni, ta sabauta ki ai kya shiga hankalinki" Gaddafi ya yi maganar cikin Waga murya.

Duk da abin da mai maganin nan, ya sha?a wa Nana, bai gama sakinta ba, amma tana jin duk abin da suke faWa.
Ta zame hannunta daga jikin Jamila, ta dafa bango ta nufi Wakinsu.
Tana jin Baba yana tambayar ta, dan me ta baro wurin mai magani, tayi masa shiru dan ko buWe baki, wahala yake yi mata balle doguwar magana.
Tana jin yadda Yaya Atine ta cafe, take yi masa bayanin, bataliyar aljanun da ke kan Nana, har da ?ara abin da ba a yi ba, kamar yadda mai maganin yayi mata bayani.

Tun tana jin su sama, har wani abu mai kama da bacci ya Wauketa.
Kamar a zahiri ta daina jin komai a duniyar da take ciki, ya zauna a gabanta yana kallonta, kafin ya ?ya?yace da dariya wani irin ba?in haya?i yana fita daga bakinsa.
Sam dariyar babu daWin ji, ta saka hannu ta toshe kunnuwanta, amma ba ta fasa jin dariyar ba.

"Igiyar ?addara, ta Waure ki ta ko ina, kuma kina da damar kwanceta, amma azabar ba?in taurin kanki, ya hana ki saduda ki karSi ?addararki"

Nana ta numfasa ta ce "Shirka ba ta cikin ?addarata, komai za ka yi mini, ba zan karSi abin da ka ke bu?ata na yi ba"
Ya Wago dogwayen yatsunsa, ya kai fuskarta ya lakuto gumin da take ta yi, ya kalli gumin a hannunsa ya ce "Ki daina cika baki, lokaci zai fayyace komai"
Daga haka ya Sacewa ganin Nana.

Bayan farkawar Nana, ta tashi da wata azababbiyar yunwa, ga sallolin da ake bin ta.
Ta tarar da Ummi ta zo, ta gaisheta amma ta amsa mata sama-sama. Ba a damu ba, ta yi sallolinta ta koma tsakar gida ta ce "Mama akwai abinci kuwa?"

"Babu" ta bata amsa kai tsaye.

Ummi ta ce "Mhmm Nana kenan, ai in dai irin wannan abubuwan ne, yanzu ki ka fara gani, tun da zaman gidan bai ishe ki ba, shi wancan na farkon Allah bai ?addara an yi da shi ba. Shi malamin naku an ce ya fito ya?i, amma duk da larurarki, Saleh ya ce yana sonki amma sai wula?anci ki ke yi masa. Ya je ai ya gaya mini duk abin da ki ka yi masa"

Nana ta yi kunnen uwar shegu da Ummi, kamar ba da ita take ba.

"Mun yi magana da Baba, aure babu fashi, ya ce a gaya masa iyayensa su turo"

Nana ta kalli Ummi ta ce "Yanzu za ki so hafsa ta auri mutum irin Saleh? Kin san fa Wan shaye-shaye ne, kuma a Lagos Win kin san ina ne wurin sana'arsa da suwa yake tare? Duk ba kwa duba mini wannan?"

"Nana ke ma fa kina da aibun nan, amma ya runtse ido ya ce ya ji ya gani, ita fa rayuwa yanzu idan ki ka samu mai sonki, duk wani tone-tone ba naki ba ne ba" ba ta sake kula Ummi ba, har ta gama abin da za ta yi ta bar gidan.

Tunanin yadda Allah ya ?waceta daga hannun mai maganin Wazu take yi, da tuni ya cuceta ya cuci rayuwarta, ita kanta ta san Allah ne kawai ya ?waceta, amma ya riga ya bugar da ita.
'wata?ila ga in da addu'oinki suke yi miki amfani, amma ki ke garaje da Sacin rai' wata zuciyar ta tunatar da ita, a take ta yi ta istigfari.

Sosai Baba ya Wauki maganar Saleh da muhimmanci, Nana kuma ta na ta kai kukanta ga Allah, duk da neman lafiya da take ro?a ya rinjayi duk sauran adduo'in da take yi.

Gashi duk da shirun da take yi wa Saleh idan ya zo, ba ya zuciya sai ya kuma dawowa, dan babban abin da yake saka shi zuwa ba yau ba gobe, bai wuce tozali da ?irar jikin Nana ba, da yake jin kamar zai Wimauce, idan bai kai hannunsa jikinta ba.
Ta kan ?are masa kallo, tana mamakin yadda Baba ya rintse ido, daga ganin aibun Saleh, kama daga kan askin banzar da yake kansa, zuwa suturar da yake sakawa da sunan gayu. Kodayake dama gayu idan ya haWu da jahilci hauka ne tuburan, duk soki burutsun da zai yi mata babu maganar Allah a ciki sai shirmensa.

Gefe guda ga kewar malam Auwal da ta dameta, tabbas ba dan mutunci da kamewarta, na Wiya mace ba da babu abin da zai hanata zuwa gidansu ta tuntuSi ko lafiyarsa ?alau. Sai dai duk da haka sai da ta tambayi abokinsa malam Nura, ya tabbatar mata da lafiyarsa ?alau ayyuka ne su ka yi masa yawa kawai.

Kimanin makwanni biyu kenan, ba ta ga malam Auwal ba, zuciyarta na raya mata, karSar lambarsa a wurin malam Nura, ta ari waya ta kira shi, amma ta kasa.
Kwatsam su na cikin karatu a aji, ta jiyo muryarsa a waje. Ta kasa ri?e kanta, ta tashi ta fita.

Kafin ta isa, har ya shiga cikin ofishinsa, yana cikin tattara litattafansa, kawai ya waiwayo ya ga Nana.

"Yaya Auwal meyasa ka ke guduna? Ina ta son mu haWu na yi maka bayani, amma ka daina zuwa ma gaba Waya"

"Babu malami a ajinku ne?"

"Eh, tilawa muke yi"

"Ki koma aji" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba.

Ta marairaice ta ce "Amma Yaya Auwal, magana nake son mu yi, dan Allah ka fahimce ni ba abin da ka gani, ba abin da ka ke tunani ba ne...

"Ki tafi aji na ce Nana, ba sai kin yi mini bayanin komai ba" yayi maganar cikin tsawa.

Tsayawa ta yi tana kallonsa, bayan tayi nasara sun haWa ido.

A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ba ta tafi ba kuma ba ta ce komai ba, sai dai idonta ya cika da hawaye.

Sai ya tausasa murya ya ce "Ki je aji Nana, ba na son gardama"

Ta girgiza kai ta ce "Koma me ka ke Soye mini ka gaya mini. Kai malamina ne, kuma abin koyi na, ka karantar da ni nagartattun halayen fiyayyen halitta Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Wanda ya haWa da gaskiya, da kuma ha?uri. Ka gaya mini ko ma mene

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login