Showing 39001 words to 42000 words out of 190498 words

Chapter 14 - Buzu Book 1 Complete

taf. Ya dubi Salamatu ya ce "Salameme zuba wa Fulani a randarta" Salmatu ta karSa, ta je ta buWe randar da bafulatanar nan ta Wqzu sha wannan ba?in abun ta juye a ciki.

Ya kalli Nana ya ce "Za ki iya tuna daga wani lokaci, ki ka fara ganin uban du?usa a bacci?"

"Waye hakan?" Nana ta tambaya cikin rashin fahimta.

"Aljanin da yake zuwar miki"

"Wai ?aisar?"

Ya yi murmushi ya ce "Shi"

"Ba zan iya tunawa ba" ta bashi amsa.

"Ina kallonsa a tare da ke Wazu, shi ya yi wannan tsawar mahaukatan nan suka yi shiru, so nake ya bayyana a jikinki mu yi magana da shi, amma ya?i. Masu ihun nan da ki ka gani, duk masu ba?a?en aljanu ne masu taurin kai, wanda ko an ba su magani, suke lafawa su dawo daga baya. Nan gurin Waure su na yi, nake hukunta su da azaba kala-kala, a matsayin gargaWi da kashedi. Akwai haya?in da ake yi musu safe da yamma an gama haya?in muka je, amma ?aisar ya ?i bayyana. A duniya aljanun da suke irin sa ba su da yawa". Nana ta yi tsuru tana kallonsa da saurarensa, tare da kallon maganganun sa a matsayin soki burutsu.

"Amma ke me yasa ba zaki yadda ki karSi abin da yake gadonku ba, ki ka gwammace ya yi ta azabtar da ke?"

Take Nana ta tsuke fuska, ta tsani ta ji an danganta ta harkar bori da gadonsu, kamar wani abin arziki.

"Ni ba zan yi shirka ba"

Sarkin baka ya ce "Ba shirka ba ce ba, bayar da magani, idan bayar da magani shurka ne, Asibiti ma shirka suke yi. Ki amince sai mu haWu mu ci gaba da gudanar da taimakon al'umma"

Ta girgiza kai ta ce "Ni ba zan yi ba ba na so"

"Anya? Ki yi tunani kar ki zo nan gana kina nema ido rufe fa" tayi shiru ba ta yi magana ba.

"Salamatu mayar da ita Wakinta, a bata abinci, idan tana bu?atar wani abin a bata"

Salamatu ta jinjina kai, daga nan ta jagoranci Nana suka bar Wakin.

****

Zaune take a katafaren falonta, ta hakimce a kan kujera tana amsa waya "Hajiya Sa'a, ya mu ka ji da iftila'in nan da ya tinkaro mu, coustom sun ri?e mana kaya a Abuja?"

"Aikam, mu na nan muna ta up and down, Allah ya sa su sakar mana a kan lokaci"

"Amin ya rabb, wallahi hankalina duk a tashe yake, na haWa kuWin mutane da jarina duk na zuba na sayo kayan nan, ni dai fatana Allah ya sa kar su yi condeming Win kayan nan wallahi ban san in da zan saka raina ba, ga mutane sun fara ?orafi"

Hajiya Sa'a ta ce "Ahha haba Sadiya, babu abin da zai faru fa, ki kwantar da hankalinki ki yi addu'a"

"To shikkenan Hajiya, na gode sosai da sosai" bayan sun yi sallama, Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta kalli maman khairat ta ce "Safiyya mutuniyarki ce fa, Sadiya"

"Ohh Allah sarki"

"Duk hankalinta a tashe yake, batun kayan da coustom suka ri?e, ni ba ta son ko kaWan kayan nan ba a gabana suke ba"

Safiyya ta yi dariya ta ce "Haryanzu ita kanta a tukunya yake kenan, ba ta san dawar garin ba?"

"Ina fa ta sani, a zatonta business yake tara mini kuWi, duk wannan abin shige mini take son yi, ta ji sirrina".

"To hajjaju a shigo da ita sabgar mana"

Cikin sauri ta ce "A'a tana da surutu, ga ?aryar ri?on addini, kin san kuma ?a'idarmu, muddin aka samu mushikila akwai matsala. Ai zatonta business Win nan na ri?e, har take neman yin takar da ni a wasu abubuwan. Ba ta san kare yawa ne kawai ba, da kawar da hankalin mutane".

"Gaskiya ne, sabgar tana bu?atar sirri sosai"

"Safiyya kin ga an sake samun matsala, yarinyar ba ta yi amfani da turaren nan ba, wanda ya yi amfani da shi daban, ya ce wani aljani ne a kan yarinyar hatsabibin gaske ba zai bari komai ya yi tasiri ba. Kuma wallahi ya tabbatar mini idan aka yi amfani da jininta, za a samu alkhairi sosai taurarinta masu haske ne. Kuma idan aka yi wannan aikin ba za a ?ara bamu wani aikin mai wahala ba. Mun riga mun wuce gurin mun samu sa'a, sai da na ce anya ba sato ta zan saka ayi ba?"

"Na shige su ni Safiyya, kuma Jamila ta tabattar mini da ta ba ta turaren har ta na murna"

"Wallahi ba ita ta yi amfani da shi ba, an yi amfani da turaren amma ba ita ba ce ba"

"Kai wannan wace irin jaraba ce? Ga shi kuma wai ba ta nan an kaita gidan mai magani an barota a can" da sauri Hajiya Sa'a ta ce "Haba dai? A ina ne na ji ko da yadda za mu yi mu samu gurin?"

Maman khairat ta ce "Wallahi ban sani ba, sai dai idan ta zo na tambayeta"

"To ki yi mata cikin hikima dan Allah, ki nuna mata wata 'yar uwakki za a kai, kar mu bar wani trace da za a gane wani abu"

"To shikenan hajjaju bari ta zo, it ma ina daf da jawota cikin ?ungiya, za ta yi mana amfani saboda tana da mugun kwaWayi daga ita har iyayenta"

"Aikuwa nima na gani, yanzu dai a far wannan Win"

****
?angaren Nana, ta ga abubuwan al'ajabi kala-kala a gidan sarkin baka.
A kwana uku da ta yi, tana iya fita da kanta ta zagaya tana ganin marasa lafiya har ma ta yi magana da su, ta basu shawarar su din ga zuwa asibiti. Tana yawan zuwa ganin Kubra, sai dai yanayin da take tarar da ita a ciki, ba ya yi mata daWi, saboda wataran da sau?i wataran kuma hauka take yi tuburan.

Kullum idan Sarkin baka zai zagayen ganin marasa lafiya, da waWanda ake kawo masa su ganshi, tare yake yi da ita.
Aka kawo wata mata da tsohon ciki tana tafiya da ?yar, cikinta har rinjayarta yake yi, wai shekarar cikin goma a jikinta, wasu lokutan ya tashi, wasu lokutan ya kwanta a neme shi a rasa.

Su na gama yi wa sarkin baka bayani, Nana tayi farat ta ce "Ba ku je asibiti ba?"

"Mun je, duk gwajin da aka yi sai ace babu ciki" babar matar ta ba wa Nana amsa.
Sarkin baka ya bushe da dariya ya ce "Asma'u ma'u, su Asibiti duk abin da suka zo muku da shi, za ku karSa ku ce technology ne, mu kuma namu da muke yi, shi ne shirka a gurinki. Shi maganin baturen kin san da me da me ake haWawa? Kin tabattar da ingancin halaccin sa a addinance? Shi fa ilmi siffa ce ta Ubangiji, kuma yana bayar da ita ga wanda ya so, bai keSantar da baiwarsa ga farar fata ba kawai, ku ba?a?en fata ne ku ka raina abin da Allah ya baku na ilmi, ku ka yi amanna da bature ne kawai ya iya"

Ya mayar da hankalinsa kan mara lafiyar ya ce? "Hajiya a da idan ki na al'ada ba ruwanki, duk gurin da ki ka samu yarda ?unzugun jinin ki ke yi. Da ?unzugun jinin hailarki aka yi miki sihiri, saboda a raba ki da mijinki, idan ba ki manta ba, kin yi ta zubar da jini tun yana taya ki neman magani har ya gaji ya yi aure ya rabu da ke. Da ki ka ce ki na da ciki ma rigima ku ka yi ta yi ya ce ba nasa bane ba" cike da amanna Wari bisa Wari suka gazgata sarki.

Nana ta ce "To kai ya aka yi ka sani, bayan baka nan aka yi?"

Ya kalli Nana bai ce mata komai ba ya tashi ya nufi kan matar. Ya saka Salamatu ta Webo ruwan magani, aka bawa matar ta sha.
Ya dun?ule hannunsa ya buWe tafukansa aska ta fito, ya saka aka buWe cikin matar, ya din ga yi mata ?ananan tsagu da askar. Wannan karon sanho ne a jikinsa, (jakar magunguna) zabira (Jakar wanzamai ta kayan aski)

A wannan ?aramar jakar, ya ciro garwashi jawur, ya Wora a kasko ya zuba wani magani a kai.

Take matar ta hau tari, ya kama cikin ya lailaya ya tattara shi guri guda, sai ga wani jini ba?i ?irin guda-guda yana fitowa daga cikin.
Sai da jinin ya gama fita, ya tattare guri guda ya zama wani ba?in muzuru. A take cikin ya baje, Sarkin baka ya dan?i muzurun ya jefa a cikin sanhonsa ya ce "Aljani ne yake ta yi mata wannan siddabarun. Salamatu a kaita gurin su 'yar ?ashi Waya, a tsumata zuwa jibi a sallame ta" Sai da Nana ta razana da abin da ta gani.

Bayan fitarsu ya kalli Nana ya ce "Idan ki ka kuma ?aryata ni a gaban mutane, sai na je na Waure ki a cikin mahaukatan nan kema"

Nana ta ce "Amma ka ce ?aisar ba zai kamu ba"

Ya ce "Zai kamu, ban yi niyyar kama shi bane"

Ta sake cewa "Amma ya ake ka ke wannan abubuwan haka? Ta ya ya ka ke sanin abin da baka nan aka yi?"

"'yan aike ne suke gaya mini "

"Aljnu kenan ko? Haramun ne fa hakan shirka kenan"
"Ba shirka ba ne, taimakon al'umma muke yi"

"Wallahi shirka ce, har fa tsafi ka ke yi "

Dariya ya yi ya ce "A ina na yi tsafin?"

"Ga shi nan ina gani kana yi, ya aka yi mage ya fito daga cikin mutum, kuma ya ake yi ka ke tura abubuwa da yawa a cikin 'yar ?arama jakar nan?"

Sarki ya ce "Aljihuna ne da yawa a cikin jakar"

"To buWe in gani" ya yi murmushi ya mi?a mata jakar ya ce "BuWe da kanki" cike da ?warin gwiwa ta karSi jakar, babu fargabar komai ta fara dubawa. Ya zuba mata ido yana dariya.

Sai dai ta zazzage jakar babu komai a ciki.

Ta kalle shi ta ce "Wallahi tsafi ne ina magen da ka saka a ciki ya tafi?" Ita kanta Nana tana mamakin yadda ta daina kewar gida gaba Waya, take jin kamar ta daWe da sanin sarkin baka.

"Idan kin yadda ki bayar da magani, zan nuna miki yadda nake komai, ki koma gida ki taimaki mutane"

Ta girgiza kai ta ajiye masa jakarsa.

"Ki je ki huta, anjima tare za mu fita farauta da ke, ki je ki yi bacci yanzu"

Ta waro ido ta ce "Da wa za ayi farautar? Amma dai ba ni ba ko?"

"Eh ba ke ba" ya bata amsa

Ta juya da baya da baya, ta fita. Tana zuwa Wakin da take, ta ga haya?i da wani irin ?auri mara daWi, cikin abin da bai fi mintuna uku ba, bacci ya kwashe ta.

Da ?aisar ta fara tozali, zaune a kan wani dutse a cikin wani rafi, ya mi?e ?afafuwansa a cikin ruwan masu azabar tsayi kamar itacen dogon yaro.
Duk da ta riga ta saba da ganinsa, ba ta fiye razana dan ta gan shi ba, amma biyo bayan tuna mafarkin da ta yi da shi, a cikin sahara ya sanya ta zura da gudu tana neman hanyar guduwa.

Ta yi gudu mai nisan gaske, ta ga wani gida, kawai ta faWa gidan, tana addu'a a zuciyarta amma ta kasa furta ta, a bakinta.
Sai dai bayan shigarta gidan, ta nemi hanyar fita ta rasa, kofofi kashi kashi a gidan, duk ?ofar da ta bi babu hanya sai dai ta sake dawowa guri Waya.

Ta dinga buWe ?ofofin amma ta rasa hanya.

"Ina za ki ne?" Ya tambayeta bayan ya ajiye wata kwalba, jikinsa sanye da fararen kaya yana Wigar da ruwa.

"Yau kuma tsoro na baki? Ko ba ki yi zaton ganina yanzu ba?"

Kuka Nana ta saka ta ce "Dan Allah ka yi ha?uri, kar ka ?ona ni yau ma, dan Allah"

"Yaushe na ?ona ki?"

Nana ta ce"Ranar da ka zama tsoho ka koma ra?umi, ka yi ha?uri dan Allah"

Ya girgiza kai ya ce "Ba ni bane"

"Wallahi kai ne"

"Ni ban yi wannan tsufan ba ai, ba ni bane"

Cikin kuka ta ce "Kai na gani a sahara, ka zama ra?umi kana feso mini wuta"

Ya sake cewa "Ba ni bane ba, tawagar buzayen da ki ka gani ne lokacin da ku ka shiga gidan. Ni ban yi wannan tsufan ba dudu sheruna nawa ban fi Wari biyar da goma ba, yaro ne ni"

Galala Nana ta saki baki tana kallonsa, shekara Wari biyar da goman ne yaro. Tambayoyi ne fal a cikinta amma tana tsoron ta tambaye shi ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta.

Ya ce "Kalli can" ta kalli gurin da ya nuna mata.

Suwaiba ta gani tana ta ihu ana danneta, mama na kuka tana tofa mata addu'a, sai fizge-fizge take yi tana kiran sunan Nana.

Cikin damuwa Nana ta ce "wai me ya sa take kiran sunana, ba fa ni ba ce ba, ni me na yi mata?"

Ya watsa wani abu daga hannunsa a gurin da take ganin su Suwaiba, sai ga wannan bararojin, tana ta zu?ar jinin Suwaiba, sannan jikin Suwaiba na ci gaba da zubar da jini ta huda-hudar nan da jikinta ya yi da ta fesa turare.

?if ta daina ganinsu, ta juyo gurin ?aisar cikin damuwa, sai dai ba ta yi magana ba.

"Kin san dalilin da ya sa na ?yale mutumin nan, da ki ke gidansa? Wasu dalilai ne, ki gaya masa har yanzu bai san ni ba, duk hatsabibancinsa akwai sararin da bai isa ya jefe ?afarsa ba. Na zuba masa ido ne na ga iya gudun ruwansa, amma dole sai na nuna masa iyakarsa, kuma zan gani tsakanin ni da shi waye zai yi maganin wani, kuma wannan abubuwan da yake yi miki akwai wani abu a ransa za ki ce na gaya miki "

"Mene ne a ran nasa?"

"Za ki gani, ya ce yau zai tafi da ke farauta, zai ci gaba da nuna miki magunguna. Zan ga iya ?arshen hatsabibancinsa"

Nana ta yi sororo tana kallonsa, duk da tana son tambayarsa, amma tana tsoron ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta.

Ya ce "Wuce ki tafi"

"Ai na rasa ?ofar fita"

"Bi waccan" ya yi maganar yana nuna mata hanya. Tana fita ta ganta a tsaye a ?ofar Wakin da take tare da sarkin baka. Yana sanye da shigar hargi(irin shigar da maharba suke yi)
Bayansa rataye da kwari da baka.

Ba ta iya musa masa ba, ko jin tsoro ko makamancin haka ba, kawai ta saka kai ta bi shi. Daga shi sai ita yana gaba tana bin sa a baya hannunsa da fitila.
Wata ?ofa suka je, ya Waga asabarin ya shiga, Nana ma ta bi bayansa. Suna shiga ?ofar ta gansu a dokar daji.

Sai a lokacin jikin Nana ya hau rawa, tsoro ya kama ta, ta ja da baya ta domin koma amma ta ga babu ?ofar da suka shigo.
Ya kalle ta ya ce "Kar ki tsorata, babu abin da zan yi miki, bari na Waure dajin"

"Ina ne nan?" Tayi maganar cikin tsoro.

"Dajin igbele ne, na jihar delta"

Ta waro ido cikin kiWima ta ce "Delta kuma? Daga Kanon mu ka zo delta?"

Sarki ya ce "Eh, wata kububuwa nake son kamawa zan yi magani da dafinta. Daji ne mai haWari ana tsafi iri iri a dajin, amma da na kama Kububuwar za mu tafi" ya yi maganar yana haWa wuta a gurin, ya zuba wani turare yana kewaye wutar. Ita dai Nana ta yi shiru tana kallonsa.

Sai da ya gama sannan ya yi gaba, ta bi bayansa.

Gurin wani dutse suka nufa, daidai jikin dutsen akwai wani kogo, ya ajiye fitilarsa ya watsa wani abu a bakin kogon. Ya ciro wata raga a cikin sanhonsa ya kafa a gurin. Nana tana tsaye tana kallon ikon Allah.

Ya gama ya ce "Mu je wani dajin na nuna miki wasu abubuwan"

Al'ajabi ya hana Nana magana, suna tafe yana nuna mata wasu tsirran yana gaya mata amfaninsu.

"Kin ga idan ki ka samu kashin giwa, da hauren toronta, wato namijin giwa, da kashin ungulu, ki ka haWa su da kaucin kuka, da tazargade da garin ganyen kuka, da ganyen magarya arba'in ki haWa jan miski, a haWe su guri guda. Idan aka yi haya?in su, duk wani ?aramin shaiWani sai ya gudu, ke babban ma sai ya sha wahala wallahi, kuma aljani sai dai ya ganki ya bar ki"

Nana ta dube shi ta ce "To ta yaya mutum zai samu wannan abun, duk sai mutum ya yi wannan wahalar? Najasar dabbobi ce za ta hana aljanu shafarsa? Bayan ga azkar da Alqur'ani"

Sarkin baka ya yi murmushi, yana son ?i faWin Nana ?warin gwiwar ta na burge shi ya ce "Hala ke da ?aisar yake tare da ke, ba kya azkar da karatun Alqur'ani"

Cikin damuwa ta ce "Ina yi mana, amma wasu lokutan idan ban yi ba na fi zama lafiya ma, na fara tsorata kar hakan ya sanya imanina ya yi rauni".

Ya yi murmushi ya ce "Magani fa ba ?arya ba ne ba, kin yarda bature ya baki maganin ciwon kai ki sha ki warke, wannan ba shirka ba ce ko, wannan technology ku ke wa ko?" Sai kuma ta Wan yi shiru.

Ja ya yi ya tsaya, ita ma ta tsaya, hasken wuta ta hango daga nesa, a hankali suka ?arasa daf da gurin, suka tsaya, amma su na iya hango komai.

Mutane ne tsirara sai Waurin ?yalle ja a ?ugunsu, maza da mata su na kewaye wuta kowa da Wan ?o?o a hannunsa.
Wani mutum a tsakiya yana ta karanta wasu abubuwa, gefe wata mata a kwance ba ta ko motsi da tsohon ciki a jikinta. Ta ga mutumin nan ya nufi kan matar da wata wu?a a hannunsa yana karanto wasu abubuwan.

Razana ta yi, za ta ?wala ihu sai kuma ta daina ganinsu, ta ga sun koma dajin da sarkin baka ya yi wa kububuwa tarko.

"Idan muka tsaya, ki ka ci gaba da gani,? za ki iya rasa hankalinki"

Jikin Nana na tsuma ta ce "Su suka kashe matar?"

Ya jinjina kai ya ce "Eh, jaririn cikinta za su cire, jininsa za su sha, ?an ?ungiyar asiri ne. Nan da ki ka gansu manyan mutane ne, da suka sadaukar da lahirar su domin duniya. Akwai 'yan kasuwa a cikin su, da 'yan siyasa"

Jikin Nana sai tsuma yake yi, ba ta taSa tunanin da gaske akwai ?ungiyar asiri ba, ta zata shaci faWi ne? kawai ake faWa.

"Bari mu koma ki kwanta, da asuba zan dawo na kama macijiyar nan, naga duk a tsorace ki ke . Sai dai ina son mu yi wata magana da ke".

Jiki a sanyaye ta ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login