Showing 159001 words to 162000 words out of 190498 words

Chapter 54 - Buzu Book 1 Complete

a yi kana abokina, aminina a yi maka wannan cin kashin, kuma ka ce na karbi shugabancin nan na yi yaya da shi?"

"Wallahi za ka iya. Na fi jin tausayin ?anan 'yan kasuwa, idan aka bawa wanda bai dace ba shugabanci, za a karya masu ?aramin jari"

"?ananan 'yan kasuwar, da su suka yi wannan bita da ?ullin, da rubuta takardar lallai a sauke ka daga kan shugabancin nan, su ka ke tausayawa?"

Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Nima da ?aramin Wan kasuwa ne, kafin Allah ya kai ni matsayin da nake a yanzu. Kuma na san ba dukkannin su ne, su ka yi mini haka ba. Ni dai fatana dan Allah ka karSi tayin ri?on ?waryar shugabancin nan da aka yi maka" Alhaji Fatuhu ya Sata lokaci sosai da sosai, kafin ya shawo kan Alhaji Zailani ya amince zai karSa.

*****

Gaddafi tuni ya koma gurin neman khWinsa, saboda takaicin abubuwan suke faruwa a gidansu, ya fara damunsa.
Baba ?iri-?iri haka ya zuba ido ya yi shiru, ba ya iya cewa uffan, sai dai ya zuba ido a kan lamarin gidansa. Sai ma dai idan an dafa a zuba a ba shi ya ci. Sosai al'amuran gidan su Nana, suka fara canzawa kullum sai an Wora abinci sau uku a rana saboda hidimar da Jamila take yi da su. ?arewa ta saka ana ta yi musu gyare-gyare a cikin gidan.

Babban abin da yake damun Hajiya Sa'a da Jamila, shi ne yadda take ta ?o?arin janyo ta, cikin Waya mummunar Wabi'ar da suke aikatawa ta lesbian.
Sai dai Jamila ta kafe da kai da fata, ta?i amincewa da hakan.
Sai da Hajiya Sa'a ta yi mamaki, saboda a ?ulumboton da ta yi wa Jamila, babu yadda za a yi ta iya kaucewa duk wata bu?ata da ta zo mata da ita, amma ta kasa galaba a kan Jamila.
Duk wani shashashanci da suke yi tana kallo, amma sam ba ta ji abin ya kama hankalinta ba, balle ta yi sha'awar aikatawa.

Ta fito harabar gidan tana shirin tafiya, sai ga Mus'ab Wa Waya tilo ga Hajiya Sa'a. Yana ganin Jamila ya tsaya. Duk da ba shiga harkarsa take yi ba, amma ta yi ?o?arin tare shi daga shiga cikin gidan, ya yi mummunan gani.

"Ina wuni?"

"Lafiya ?alau Jamila. Ya ki ke?"

"Lafiya ?alau Alhamdilillah. Amm Yaya Mus'ab ko za ka ajiye ni a hanya ne, ba na jin daWi"

Ya yi murmushi ya ce "Me zai hana? Bari na kai wa Mummy sa?on nan"

Da sauri ta ce "A'a ai bacci take yi, ta ce kuma kar a tashe ta"

"Ok to mu je na ajiye ki" ta yi gaba ya bi ta a baya.

*****

Nana kuwa ita ma a wannan karon, basar da Sayyid ta yi, ta ?i kula shi sam. Shi ma ya maze ya share ta.

Baccinta ya yi nisa sosai ta ganta a daji ita kaWai ?wal. Ta Waga kanta ta ga wani ?aton tsuntsu yana shawagi a saman kanta.
Ba ta tsorata ba, ta Wan ja numfashi ta ce "?aisar laifin me na yi maka, ka zaSi ka hukunta ni ta wannan hanyar? Me ya sa za ka zama dalilin zubewar cikina?"

Tsuntsunan nan saukko ?asa, ya yi girgiza ?aisar ya bayyana. Ya zauna yana fuskantar ta ya ce "Komai ma kin yi mini, babu abin da ba ki yi mini ba, abin da ya dace nake yi"

"Ba ka tsoron Allah ?aisar, ba ka tsoron Allah ya kama ka da hakkina, abubuwan da ka ke aikata mini na cutarwa.
Kai ka yi mini, wannan tsohon ya yi mana, mijin nawa ma na fara daina gane kansa. Ya fara ?o?arin cutar da ni"

Ya Wan kalli saman bishiya sannan ya ce "Babu abin da ban gaya miki? ba ai. Amm kin tuna abin da na nuna miki, Alhaji Zailani yana yi wa abokinsa? Da gaske ya faru a zahiri. Kuma tsafi gaskiyar mai shi, domin kuwa al'anura sun fara juya wa Alhaji Zailani baya. Nan zuwa wani Wan lokaci zai rasa komai nasa. Lafiyar sa da dukiyarsa."

Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Dan Allah idan ka na dama ka yi wani abu a kai mana. Ka tona abin da aka yi masan"

Ya girgiza kai ya ce "Ba ma shiga abin da babu ruwanmu, ko warware wani abu da aka yi wa wani, muddin ba yarjejeniya aka yi damu, aka bamu damar yin hakan ba. Zan iya taimakonsa ne kawai bisa amincewar ki, da kuma umarnin ki. Zan gaya miki inda abin yake ya saka a je a tone, ko kuma ki je ki tone. Idan ba haka ba nan da kwanaki uku rak za a tono ?warangwal Win yaron nan, a kuma yin wani tsafin da ita."

Har Nana ta motsa baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa, dan tana amincewa a taimaki Alhaji Fatuhu ba ta san me zai biyo bayan hakan ba, ka iya tabbatar da bu?atar ?aisar a kanta.

AREWABOOKS

Kasancewar ba ta salla, ya sanya har gari ya waye tana bacci.

Bayan ta yi wanka ta rasa abin yi, ta Webo kayan wankin ta, ta shiga banWaki ta wanke. Nasa dama Habu ne yake zuwa ya Wauka.

Ta gama, ta saka hijjabinta, ta Waukko bokitin, ta fito daga Wakin. Yana kan kujera a daf da gate Win, yana aikin dafa shayi, gefensa ga radio tana yi.

Ba ta kula shi ba, ta zagaya baya, ta yi shanyar kayan nata. Ta fito ta ja ta yi turus tana kallon ikon Allah.

Siyama ce a tsaye, da Wan ?aramin flask a hannunta. Nana ba ta san me take ce masa ba, ta ga ya sauke rawanin fuskarsa ya saka hannu ya karSi flask Win, ya yi magana.

Kawai ta shiga Waki, a ?ofar banWakin, ta jefar da bokitin jin wani irin matsanancin Waci yana taso mata.

Ta cire hijjabinta kawai ta tsaya ta ri?e ?ugunta, ta tsaya tana jiran ya shigo, amma bai shigo ba, zuciyarta ta din ga raya mata, yana can su na hira da Siyama.
Kawai ta buWe ?ofa ta shiga banWaki, sai dai ta rasa uban abin da ya kai ta banWakin ma. Ta gama tsayuwarta ta fito daga banWakin.

Tana fitowa ta gan shi a tsaye, da flask Win a hannunsa, ya nufo ta zai yi magana, ta riga ta Sarar da flask Win. Farfesun kifi da dankalin ya tarwatse a ?asa.

Ya kalli gurin ya kalli yadda take huci, zuciya ta yin?uro shi, sai dai ya ga ?aisar a bayan Nana, ya zubo masa ido.

Ya haWiye wani abu, mai Waci. Ya kalli Nana ya ga yadda idonta ya rufe, ta fara ?o?arin wuce shi ta fita. Ya ri?e ta yana ci gaba da kallon ?aisar.

Ya kwantar da Nana a kan katifa, idanunta a rufe sai hawaye da yake fita, ta gefen idonta.

Ya dur?usa ya gyara gurin ta Sarar da abincin.

Ya sake kallon yadda ?aisar ya jingina da bango, ya tsaya a kan Nana.

"Tun da ka yi abin da ka yi, ya kamata ka bani guri" Ya yi maganar yana kallon inda ?aisar yake.

"Gurin ka na zo ne? Idan ba gurin ka na zo ba, sai ka ?yale ni"

"Ka zubar mini da ciki, kuma saboda rashin kunya, ka zo haWa fitina a tsakaninmu"

?aisar ya yi murmushi ya ce "Ina mamakin yadda Aljani yake shiga al'amuran bil adama har haka. Kai ka fara lalata cikin, ni kuma na zubar da shi."

Sayyid ya shafi fuskarsa ya ce "Waye Aljanin a tsakanin ni da kai?"

?aisar ya ce "Ba da kai nake ba. Ka san da wanda nake"

Buzu ya Wan yi shiru sannan ya ce "Ka gaya mini, wane ne ni? Daga ina nake? Kuma suwaye iyayena? Me ya kawo ni ?asar nan?"

"Ba ni za ka yi wa wannan tambayar ba, zuwa yanzu na san ka bambance tsakanin ni da shi"

"Haka ne, na banbance, yanzu ka tafi ka bani guri, ka bar ni da matata"

"Ba zan tafi ba"

Buzu ya dur?usa ya kwance rawanin kansa, ya cire rigar jikinsa, ya Wago Nana da take cikin yanayin gushewar hankali.
Ya fara cire kayan jikinta, tamkar an aiko wa ?aisar sa?on mutuwa ya murtuke fuska.
Bai tsinke da lamarin ba, sai da Sayyid ya rungume Nana yana sumbatar bakinta.

Jikin Nana ya din ga rawa, tana fatan ta saka baki a maganganun su, amma ta kasa, tana ganin duk abin da yake faruwa, amma tamkar an Waure ta, ta kasa motsa ko da ?aramin yatsanta.

Da ?yar ta fizgo numfashi ta tashi a zabure, ta ce "Sayyid" ya taso da sauri daga inda yake zaune ya nufo ta.

Ya kasa magana, ita ma kuma ta kasa cewa komai, sai rarraba ido da take yi, ta yi zaton mafarki ne, amma ta ji Wakin yana ?arnin kifi, ga kuma flask Win da ya shigo da shi.

Da ?yar ta ce "Ina wanda ku ke magana da shi?"

Ya kalli Wakin ya ce "A ina?"

Ta kalli daidai gurin da ?aisar ya tsaya, ta ce "Wanda ya tsaya a nan, wani dogo"

"Ban yi magana da kowa ba" ya yi maganar yana girgiza mata kai.

Ta yi ajiyar zuciya ta ja ta zauna, tana jin kanta yana ciwo.

****

"Suwaiba" Alhaji Fatuhu ya kira sunanta.

Ta kalle shi ta ce "Ya dai?"

"Ba na jin daWin jikina ne, kuma wani abu ne yake damuna"

"Me ke nan?"

"?ara ta za a kai kotu"

Ta waro ido ta ce "Kotu kuma? Me ka yi?"

"Kayan nan da suka yi Satan dabo, ranar Litinin zamu shiga kotu da 'yan kasuwa. Kujerata ma an sauke ni. Amma bai dame ni ba, kayan mutane nake tunani"

Ta kwaSe baki ta kaWa kai ta ce "Ai Alhaji Fatuhu duk Wan da ya hana uwassa bacci, shi ma ba zai yi ba. Babu irin wahalar da bamu sha tare ba, amma abin Duniya na samuwa, ka auro yarinya ?arama saboda ka ?untata mini, ka ci duniyarka da tsinke. Ai ga shi kai ma Allah ya kama ka" Ya yi zuru da ido yana kallonta.

Ta gama maganganunta ta bar masa Wakin.

Tana zuwa bedroom Win ta, ta rufe ?ofa, hawayen da ta ma?ale ta ba su damar gangarowa.

Ta hau nanata "Innalillahi wa innalillahi raji'un"

Ta Wauki wayarta ta kira Yayanta.

Yana Wagawa ya ji muryarta wani iri, ya ce "Lafiya kuwa?"

"Yaya Baban su Raudah wai za a kai kotu, 'yan kasuwa su na zargin ya cinye musu kuWi, dan Allah ka yi wani abu a kai dan Allah"

"To ikon Allah, amma ba sai ki bari sai da Safe ba, kya kira ni. Amma ku kuma kin tabattar bai ci kuWin ba?"

Suwaiba ta ce "Yaya kai ma ka san shi da gudun Duniya, da abin mutane wallahi zan iya rantsuwa bai ci kuWin kowa ba"

"Ki bari zan kira ki da Safe" ta ajiye wayar jiki a sanyaye cikin damuwa.

Kasancewar a sashen Fadila yake, ta fahimci damuwa a tattare da shi, sai dai fafur ya ?i gaya mata, ya lallaSa ta ta yi bacci.

*****

Da daddare Nana ta kasa karanta Alqur'ani, amma wannan karon ta samu ta saka a wayarta, ta daWe tana saurara tana jin nutsuwa na ratsa ta.
Kasancewar jini ya Wauke, ya sanya ta yi sallar Isha'i, ta kwanta karatun Alqur'ani yana tashi ?asa-?asa a wayarta.
Tana kallon Sayyid, ya shirya ya kwanta a ?asa, gurin da yake kwanciya da. Gaba Waya sai ta ji ta damu. Ta daWe idonta biyu, tana jira ta ga ko zai ta so, amma bai tashi daga gurin ba.
Ta tashi a hankali ta nufe shi, har ta ?arasa kusa da shi, ta kwanta.

Ba ta ce masa uffan ba, ta caza masa hankali har ya biye mata.
Bayan wani Wan lokaci ya numfasa ya ce "Kin daina fushin?"

"Ba kai ka saka na yi fushin ba? Amma ka yi ha?uri"

"Me na yi miki?"

"Me yasa za ka yi wannan yarinyar magana, har ta baka abu ka shigo mini da shi Waki?"

"Ki na gurin kin san meyafaru?"

Ta tashi daga jikinsa, ta ce "Ni ba na son jin meyafaru kawai babu ruwanta da kai, kar ka sake kula ta. Dan wallahi za ka iya nema ta ka rasa. Idan ka na son ta maye gurbina ba wani abu, ni zan iya tafiya ta na baku guri".

"Ki daina faWar abin da ba za ki iya aikatawa ba"

"To ka ci gaba, zan baka mamaki kuwa" ta yi maganar tana tashi zaune, da nufin ta bar masa gurin."

Amma ya ri?e ta gam, yana yi mata numfashi a wuya. A gurin suka kwana tare. Sai Asuba bayan ta yi wanka ta yi salla, ta koma kan katifa.

Tana tsaka da bacci, ta ji yana tattaSa ta, ta buWe idonta ta kalle shi tana yanutsa fuska, saboda bacci ne a kan ta sosai.
Wayarta ya ajiye mata a daidai kunnenta.
Wa?ar Ali jita ce take tashi, ta Aminiya. Shiru ta yi tana sauraren baitukan tana kallon kyakyawar fuskarsa da ya tsare ta da manyan idanunsa yana kallonta yana murmushi.
Ita ma murmushin ta sakar masa, ta yin?ura ta tashi zaune, ita sam ba ta san da wa?ar ma a wayar ba, kasancewar ba gwanar jin wa?a ba ce, amma har cikin zuciyarta take jin baitukan, tamkar shi ne yake rairai
mata.
Gaba Waya suka manta, da batun saSanin da ya shiga tsakaninsu.

(BAYAN MAKONNI BIYU)

Gaba Waya Fadila ta rasa abin da yake yi mata daWi, hankalinta ya ?i kwanciya, tun da aka fara zaman kotu ta ji halin da ake ciki ta rasa abun da yake yi mata daWi, yanayin yadda shari'ar ke gudana, za ka san da gayya ake yi, kawai shi ake son ya tozarta.
Dan tashin farko Al?ali cewa ya yi a tsare shi, sai an ajiye wasu miliyoyi da kadarori, za a sake shi.
Wasu tuhume-tuhumen ma, bai san da su ba, sai ranar da aka fara zaman kotun, sannan ya san da su. Har wasu ma?udan kuWin, da ake zarginsa da sama da faWi da su, a lokacin da yake shugabanci.
Haka aka sayar da wasu daga kadarorinsa, aka bayar sannan aka ba da belinsa.
Kotu ta yi umarnin a yi gwanjon kadarorinsa a sallami mutane kuWinsu.

*****
Alhaji Zailani, tare da Malam Gambo suka koma gurin da suka binne, jaririn nan, su ka tono ?warangwal Win sa, duk ya zagwanye. Suka saka a akwati, suka tafi da shi.
?akin da Malam Gambo yake tsaface-tsafacensa su ka je. Ya Waukko ?warangwal Win jaririn, aka babbaka wata irin wuta, aka Wauki ?warangwal Win jaririn nan, ya rubuce jikin da sunan Alhaji Fatuhu, ya zana wasu hatimai, ya nannaWe su a jikin ?warangwal Win aka saka a cikin wutar nan.
Malam Gambo ya din ga zuba wani magani a cikin wutar, ya kawo wasu irin layoyi da ya zana hatimai daban-daban, ya din ga jefawa a cikin wutar. Alhaji Zailani kuma yana kiran sunan Alhaji Fatuhu.
Sai da ?warangwal Win nan ya yi ba?i ?irin, zaren da aka naWe ?warangwal Win, ya kama jikin sosai. Ya kuma naWe shi da wani zaren, sannan ya naWe da likkafani, su ka je suka samu wata tsohuwar rijiya, suka jefa a ciki.

Alhaji Zailani ya koma gida, kulle kansa a cikin Waki, ya din ga SaSSaka wata irin mahaukaciyar dariya, tamkar zai haukace.

Ya ce "Alhaji Fatuhu ka gama yawo, yanzu sai na ga wanda za ka hura wa hanci, wai ka ga mai kuWi kuma mai tsoron Allah, mu zuba mu gani. Wannan burin nawa ya cika, saura kuma waccan yarinyar"

Alhaji Fatuhu kuwa, sun dawo daga kotu, Yayan Hajiya Suwaiba, lauyan da ya tsaya masa, yana ta yi masa nasiha a kan ya karSi ?addara.

Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi Barrister, na karSi ?addarata. Na kuma gode wa Allah. Abu Waya nake tunani iyalina na saba musu da rayuwar jin daWi da kwanciyar hankali. Ina jin tausayinsu fiye da abin da ya same ni"

Cikin tausaywa Barrister ya ce "Na sani Alhaji, tabbas kai mutum ne mai kyautatawa iyali. To yanzu ne ranar da za su nuna maka halacci su ma, a yi ha?uri"

Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, mun gode Allah"

Ji ya yi tamkar ana ?o?arin fizgo ?wa?walwarsa. Ya yi wata irin zabura, ya ri?e kansa gam. Barrister ya ce "Alhaji lafiya dai?"

Ya girgiza kai ya ce "Zafi nake ji" kafin ya kuma wata maganar, ya yanke jiki ya faWi a gurin.

Nana tamkar tana kallon talabijin, haka ta ga komai a cikin mudin da ?aisar yake nuna mata.

Yana gefe yana rubutunsa, ita kuma ta zuba uban tagumi tana kallon mudubin.

"Shigen irin wannan sihirin aka yi wa mijinki, shi ne wannan wutar da yake cewa tana ci a jikinsa. Sai dai shi nasa ya sha bambanda wannan ta wasu fannukan"

Nana ta zabura ta kalle shi ta mi?e tsaye ta ce "?aisar ka yi mini bayani, waye ya yi masa asirin? Kuma daga ina yake? Suwaye iyayensa?"

Ya Wago ya kalle ta ya ce "Kin manta sharaWin ne?"

Ta yin?ura za ta yi magana, ta yi ido huWu da Sayyid, yana kusa da ita, ya zuba mata ido.

Ta yi ajiyar zuciya.

"Waye ?aisar?" Ya jefo mata tambayar babu zato babu tsammani.

Ayshercool
08081012143.

45

Ganin abun ba na ?are ba ne, ya sanya Nana yin?urawa da ?yar, jikinta babu ?wari, ga sanyi tana ji.

Ta Wauki hularta, ta zubo ruwa a kwano, ta zo ta ajiye a gefensa, ta zauna da niyyar karanta abin da ya sauwwa?a a Al?ur'ani, ta busa a ruwan ta shafa masa. Amma ta ji komai ya Wauke daga kanta, ta kaWa ta raya amma ta kasa tuna komai.

Ta janyo wayarta, ta fara laluben folder karatun Alkur'ani, amma wayar ta fara haske tana Waukewa tamkar ta ci screen, abin fa ba taSa yi ba sai yau.

Ta ajiye wayar jikinta yana rawa, ta rasa abin yi, ga shi yana kwance sai tsuma yake yi. Tashi ta yi ta nufi wardrobe, ta buWe watso kayanta ?asa. Jakar gurin sarkin baka, ce ta faWo daga cikin kayan. Nana ta dur?usa ta Wauka, ta nufi gurin da yake kwance. Ta Wora masa a ?irjinsa. Kamar ta Wora masa wuta, haka ya zabura, ya juya a hankali ya gyara kwanciyar sa, ya daina wannan tsumar ya hau bacci.

Ta saka hannu ta Wauki jakar, tana ?are mata kallo. Sam ba ta ga wani abu na musamman a tattare da jakar ba. Ta ajiye ta, ta kwanta a gefe tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo.

Bayan wani Wan lokaci ya yi juyi a hankali, ya kalli agogon Wakin, ya kalle ta ya yin?ura ya tashi, ya yi alawala ya yi sallar la'asar. Ya zauna a kan sallayar ya yi shiru, fuskarsa na bayyanar da damuwa.

Nana ta tashi daga gurin da take. Ta ja ta zauna sosai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login