Showing 36001 words to 39000 words out of 190498 words

Chapter 13 - Buzu Book 1 Complete

rai a Sace matar ta amsa da to ta fita.

Nana tana zaune tana tunani, sai ga wata matar daban ta shigo da kayan sa?i shuWaye a jikinta.

Sallamar da ta yi Nana ta amsa tana bin ta da kallo.

Cikin sakin fuska matar ta ce "Barka da yammaci ba?uwar sarki" Nana ta bi ta da kallo ba ta amsa ba.

Ta ajiye wa Nana kwanuka, ta ce "Ga abinci an saka a canza miki"

"Ina su Baba?"

Salamatu ta ce "Sun tafi, sai nan da makonni biyu za su dawo"

"Me yasa za su tafi su bar ni a nan? Ni gaskiya gida zan tafi"

"To shikkenan, amma fara cin abincin tukuna" Da ?yar Salamatu ta lallaSa Nana ta ci abinci, shi ma don tana jin yunwa ne sosai shi ya sa ta ci."

Nana ta ri?e alwalarta, a nan Wakin ta gabatar da sallar magariba, sai dai tsoro ya fara kama ta, ganin Wakin ya yi duhu babu haske kuma ita kaWai a ciki.
Ba a jin amon kiran salla, sai dai ta kintaci lokaci kawai.

Ta tura kanta tsakanin cinyoyinta, ta rintse idanunta tana ta adduo'in da suka zo bakinta.

Tana ji ana sallama, amma ta kasa Wagowa, sai da aka taSa ta sannan ta Wago a razane tana sauke numfashi.

Salamatu ce ta shigo da fitila, da kuma kayan abinci.

Ta ce "Yi ha?uri, na tsorata ki ko? Ga abinci ki ci, ga kuma fitila idan ki na bu?atar mai taya ki kwana kuma sai mu kwana tare"

Cikin damuwa Nana ta ce "Ni ba na bu?atar komai, gida nake so na tafi"

"Haba Nana, ba kya so ki samu lafiya ki rabu da abin da yake damunki ne? Magani za ayi miki, babu wanda zai cutar da ke" ta daWe tana rarrashin Nana, tana kwantar mata da hankali. Ta Wan ci abincin sannan ta kwanta, tana ta adduo'i.

Ji ta yi sanyi ya dame ta, ta dun?ule guri Waya, amma ba ta daina jin sanyin ba har cikin ?asusuwanta, ta juya domin ta gyara kwanciyarta kawai ta ganta a cikin Sahara itakaWai.
Ga dare, sai dai farin wata ya haske saharar, sai wani irin sauti da kunnuwanta ke ji, kamar na tasowar guguwa amma ba ta san daga ina sautin yake ba.
A tsaye ta ganshi a cikin saharar, a wannan karon ma fuskarsa a rufe a cikin rawani, sai dai a wannan karon dogo ne sosai fiye da kima. A hankali gurin ya ?ara haske duhun ya ?ara raguwa. Sai kuma ta ga tsayin yana raguwa har ya dawo na daidai mutane, ya saka hannu ya warware rawaninsa.
?aisar ta gani a tsaye, duk ba ta iya ?are masa kallo, amma yadda yake bayyanar mata a mafarki cikin suffar mutane shi ta gani.
Ta buWe baki za ta yi magana, ya fara rikiWewa ya zama tsoho tukuf, tun da Nana take a doron duniya ba ta taSa ganin tufa kamar wannan ba, gashin kansa yana jan ?asa fari ?wal da shi, ga wasu irin kaya masu kama da yanar gizo gizo a jikinsa saboda tsabar tsufa.
Nana ta fara ja da baya a hankali, zuciyarta na hakaito mata addu'a, amma ta kasa furtawa. Ya sake girgiza ya koma wani ba?in ra?umi mai muni, ya buWe bakinsa ya fara feso mata wuta.

Da wani irin gudu Nana ta juya, tana ihu, ma'aikatan gidan suka rirri?eta.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Baba ka yi mini addu'a, wayyo Babana, baba Imaran, Jamila dan Allah ku yi mini addu'a na kasa yi"

Cikin damuwa Salmatu da ke ri?e da Nana ta kalli mutumin da ke tsaye a kan Nana yana kallonta ta ce "Sarki ka yi wani abu a kan lamarin nan, kar fa ?wa?walwarta ta taSu"

Ya dur?uso yana haska fuskar Nana ya numfasa ya ce "Ni na san za a rina. Salamatu"

Ta amsa da "Na'am sarki"

"Idan kin ji ana zaki bari, damisa bari faWanku na manya wa yake shiga, sai wawa sai mahaukaci, to wannan rigimar ce. Wannan yarinyar da ki ke gani ban san ta ina zan fara yi miki bayani a kanta ba. Dole jikinta ya ?ara rikicewa saboda haWuwarta da buzayen nan. Da ba su riga sun tafi ba, da ?arshenta a cikin su Waya ya samu waraka Waya kuma ya mutu a haka tsakanin ita da Buzun"

"Sarki ka ?ara rufe mini kai na, ban gane me ka ke nufi ba"

Ya yi murmushi ya ce "Da ina bu?atar ki gane, ai gwari gwari zan yi miki salameme. Ya saka yatsunsa biyu a goshin Nana, take ta yi shiru bacci ya kwashe ta.

****
Sosai Imran yake nema ya hana kowa zaman lafiya a gidan, saboda rashin Nana, ya kaWa ya raya Baba ya ?i gaya masa gurin mai maganin da aka kai Nana.
?angaren Suwaiba ma abin nata gaba yake yi, sai ana zaune lafiya, sai ta yanke jiki ta faWi tana kururwar Nana na sha mata jini.
Babu shiri Mama ta ce dole ta fita nema wa Suwaiba magani, kafin Nana ta kashe ta. Baba ya ce ta bari a kai ta gurin da aka kai Nana, amma fafur ta ?i yarda.

Washegari, bayan Nana ta idar da sallar asuba, Salamatu ta zo.
A duk lokacin da ta zo gurin Nana, cikin sakin fuska da fara'a take yi wa Nana magana, hakan ya saka Nana ta Wan fara sakin jiki da ita kaWan, duk da ba magana take yi mata ba.

"Nana taso mu je ko" babu musu ta tashi ta bi Salamatu.

Suna fita daga Wakin, ta tuna mafarkin da ta yi, sai da ta ji gabanta ya faWi, ta fara karanto addu'oin da Malam Auwal yake bata. A take ya faWo mata a rai, har yanzu tana jin kewarsa sai dai a wannan karon, jikinta ne yayi matu?ar sanyi.

Salamatu na gaba tana biye da ita, sai da suka Wan yi doguwar tafiya, sannan ta fuskanci a cikin gidan da aka kawo ta neman magani suke.

Ta ga yadda ake jere masu taSin hankali, wasu a cikin mari aka ba su abincin safe, lafiyayyen kunu da ?osai. Gaba Waya suka zuro wa Nana ido. Masu Wan sauran hankalinsu, su na ta gaida Salamatu tana amsa musu cikin sakin fuska.
Masu rashin ji a cikinsu, su ?i cin abinci, su na ganinta suka kama kwanukan abincinsu. A gaba kaWan kuma Sangaren ?ananan yara ne, masu larurar ?wa?walwa, da ake i?rarin aljanu ne su ka sanya musu. Wasu Wauke ciwukan da a turance ake cewa (Down syndrome, autism, poliomyelitis) da sauran su wato masu shan inna, galhanga da sauran su.
Suka ?ara yin gaba, suka Sullo gurin da ake Sakiya, kamar yadda ta hango jiya da suka zo. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, ta rintse idanunta yau ma kibiya ake sakawa a cikin magani, sai a ciro ta a saka a cikin wuta, ta yi jawur, aka ciro ana sokawa a cikin wani mutum da cikin ya kumbura tamkar zai fashe. An tara wata tasa wani irin koren ruwa yana kwararowa daga cikin nasa mai azabar wari.
Mutumin yana zaune, tamkar ba cikinsa ake hudawa ba.

???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Salamatu ta ce "Tsoro ki ke ji har haka? Sun je Asibiti aka ce hantarsa ta lalace, sai dai ayi masa dashen wata, su kuma iyalansa ba su da hali, aka kwatanta musu nan. Lokacin da aka kawo shi, ko tafiya ba ya iya yi, yau satinsa guda a nan yana iya takawa"

Cikin damuwa, a kuma karon farko Nana ta yi mata magana kai tsaye ta ce "Ba ya jin zafi kuma? Da me zai ji? Zafin wuta ko ciwon, ko kuma huda shin da ake yi, idan ya mutu fa?"

Salamatu ta yi murmushi ta ce "Ai ba da ka muke aikin ba, kamar yadda asibiti suke da anesthesia, magunguna da alluran kashe zafi, mu ma mu na da su, irin namu na gargajiya, ba ya jin komai. Ilimi ne ya bawa likitoci damar sanin cuta da magani mu ma kuma haka"

Nana dai ba ta gamsu ba, ta ji ne amma ba ta yarda ba.

Sai yanzu take jinjina girman gidan, su shiga nan su Sulla can, ko ina Waki-Waki ne na marasa lafiya a gidan.

Wata ?aramar ?ofa su ka shiga, amma ta ga sun fito wani katafaren Waki ?ato, ba wai kayan alatun zamani ne a Wakin ba, kawai dai an tsara shi ne.
Ta kalli ?asan Wakin, an rufe shi da fatar dabbobi daban-daban, wata ta gane ta wace dabbar ce, wata kuma ba ta gane wacce ce ba.
Hatta jikin bangon Wakin, an yi masa ado da fatar dabbobi, ta damisa kawai ta iya ganewa da kura, su ma dan tana gani a tv ne wasu lokutan.
Ga kuma ?ahunhunan dabbobi su ma, an ?awata Wakin da su, sai kuma jakunkunan fata suma duk an rarrataye su a Wakin. Ga curin layoyi su ma duk an yi musu guri a Wakin.

Yana zaune a kan wata karaga, mai Wauke da ?warangwal Win kawunan zaki, bayan karagar kuma an yi mata ado da kawunan macizai.

Nana ta yi tsuru, tana tunanin anya ma a zahiri take, ko dai kawai tarkacen mafarkin da ta saba yi ne.

Tasowa yayi jikinsa sanye da kayan fatar giwa, yana faWaWa murmushinsa ya ce "Barka da zuwa ba?uwa ta mussaman, lale da ke" Nana ta yi shiru tana kallonsa, duk da ta gane shi, lokacin da aka kawota ta ganshi, amma ba a wannan Wakin ba, kuma yau ba?insa ya ragu.

Salamatu ta ce "Sarki ga ta na kawo ta, ta tashi lafiya ?alau"

Ya ce "Alhamdilillah Allah abin godiya, Nana Asma'u na san kin gane ni, amma ba ki sanni ba, ni ne Garba mai tagwayen baiwa, Sarkin bakar ?asar hausa, kuma ana yi mini take da Garba ga baka ga aska. Salamatu ba ta abin zama".

Salamatu ta zura hannu a wata 'yar ?aramar jakar fata, ta? janyo wani abu da Nana ba ta gane ko mene ne ba, shi ba kujerar tsuguno ta mata ba, shi dai ga shi nan. Tana tsaka da kallon abin ta ga yana motsi, ta ?ura ido kawai ta ga kan kunkuru ya le?o ashe kunkuru aka ba ta a matsayin abin zama.
Babu shiri ta doka tsalle ta ja gefe tana kallon kunkurun.

Sarkin baka ya bushe da dariya, ya ce "Tuba muke, mu je ki ga yadda muke gudanar da ayyukan gidan, ko kya saki jiki ayi abin da yakamata"

Wata mata ce ta faWo Wakin babu ko sallama, bafulatana doguwa mai tsayi fiye da kima. Tana shigowa Nana ta ji zuciyarta ta yi wani irin gigitaccen bugu, da sai da ta zata mutuwa za ta yi. Matar ba ta ce komai ba, ta shirya ?orran da ta shigo da su a wata ragaya.
Sarkin baka ya ce "Idan kin gama, ga sa?onki can" bafulatanar ba ta ce komai, ta buWe wata randa ta Webo wani ba?in abu ta sha, ta zo za ta wuce Nana ta fita, Nana ta sunkuyar da kanta ?asa ta fice daga Wakin.

"Asma'u kin ga matar da ta shigo ne?" Nana ta jinjina masa kai jikinta yana rawa.

"Me ki ka gani a tare da ita?"

Da ?yar Nana ta ce "Ba ta da ?afafuwa, a kan iska take tafiya" tayi maganar bakinta yana rawa.

Ya Wan yi shiru, Salamatu ta ce "Ya buWe mata ido kenan tana ganin komai"

Sarkin baka ya jinjina kai, ya ce "Taho muje" ya tashi ya yi gaba su ka bi shi a baya.

Wani guri suka nufa, sai da suka je daf da wata ?ofa, ta fara jiyo ihu mara daWin ji. Ya buWe ?ofar ya shiga, sai dai Nana ta kasa shiga.

Salamatu ta ja hannun Nana da ?arfi, su ka shiga, sai gurin ya rikiWewa Nana tamkar a film, mahaukata ne a Waki-Waki, tamkar a prison, su na ta kurma ihu sai ta ga ashe waWanda ta gani da farko ba hauka suke yi ba, wannan ne masu yin hauka na gaske. Tamkar shirin fina-finan zombie, haka suke ihu su na ziro hannayen su. Nana tsigar jikinta ta din ga tashi, tana jin tamkar ita ma ta fasa ihu saboda rawar da jikinta yake yi, da wani irin azabar ciwo da kanta yake yi.
Hatta ha?oranta da laSSanta rawa suke yi, ya yin da sautin ihu da kururwar mahaukatan, ya ci gaba da amsa kuwwa a cikin kunnuwanta, ta rintse idanunta tana sauraron bugun zuciyarta a cikin kunnuwanta dummm dummm da ?arfin gaske.

Tsawa Nana ta yi hakan ya sanya gaba Waya su ka yi shiru, su na kallonta, tamkar an yi ruwa an Wauke, a hankali ta buWe idanunta domin ta ga tsawar da ta yi ce ta sanya su yin shiru, ko kuwa?.

Sai dai ta ga tabbas ita Win ce ba wani ba.

Sarkin baka ya kalleta tare da sakin wani irin ?asaitaccen murmushi da shikaWai ya san ma'anarsa.

Wannan littafin 1k ne a telegram, ta wannan account Win 0069685771
Aisha Adam stanbic ibtc bank
Sai shaidar biya ta 08081012143
Ayshercool
08081012143


BUZU
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
YOTA 002


P13


Ya sake duban Nana ya ce "Manya gatan wasa, uban du?usa uban haWari, ai shikenan tun da haka zamu yi da kai"

Ya yi gaba yana ci gaba da murmushi, ya din ga bayar da umarnin abin da za a yi wa marasa lafiya, tare da yi wa Nana bayanin aljanun da kowanne yake Wauke da shi, da dalilin da yasa ya kama mutum.
Nana ta sha mamaki, wasu a dalilin harkar bokanci, da ta'amalli da aljanun ya sanya suka haukace, wasu kuma sun yi ?o?arin amfani da aljanun ne dan su yi kuWi, su ma suka haukata su. Wasu kuma sharuWWan da aljanun suka saka musu, suka gaza cikawa ya sanya suka haukata su.
Ya nuna mata wasu hamasha?an 'yan kasuwa ne, da masu kuWi a ka yi musu sihiri da aljanun da suka haukata su.
Babban abin da ya bawa Nana tausayi, har da wata matashiyar budurwa, da ta zubowa Nana ido, tamkar ta haWiye ta. A hankali Nana ta taka ta nufe ta. Ta zuro hannunta ta tsakanin ?ofar Wakin, tana mi?owa Nana.
Nana ta mi?a mata nata, ta din ga shafa hannun Nana sannan ta ce "Kin san tazarar da ke tsakanin ?asa da iya gejin da jirgi yake zuwa a sama? Nigeria mu na da tarin karatu, goyon bayan ?asar mu kawai muke bu?ata, mu je in da zato bai taSa zato ba. Ina da burin ina raye kafin na mutu, na kasance cikin waWanda za su ?era wa Nigeria jirgin sama nata na kanta. Dan Allah ki saka baki na je ?aro karatun nan, na warke fa ki ce ya sake ni" ta yi maganar tana kuka.

Sarkin baka ya ce "Kubra Yusuf, in sha Allah burin nan naki zai cika da zarar kin warke"

Cikin kuka ta ce "Ai na warke dan Allah ka kira Daddy a mayar da ni gida na tafi karatun nan, kar na yi missing Flight"

Cikin damuwa Nana ta ce "Dan Allah a fito da ita daga Wakin nan, kamar ta warke fa"

Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Ai ba da baki ake gane wanda ya warke ba, yanzu ana buWe ta, sai ta kusa hallaka ki a gurin nan. Ainihin ta 'yar makaranta ce, degree ne da ita a engineering, kuma ita ce overaller a department Win su. Ta fita da makin da ba a taSa samu ba a tarihin department Win su. Gwamnatin tarayya ta biya musu kuWi su je su ?aro karatu a kan fsahar ?ere-?ere su biyar, ita kaWai ce mace daga arewa. Shi ne aka yi mata asiri da wani ba?in aljani, aka ba shi jinin mutum, ta taso daga makaranta ta ba shi sadaka, shi yake ta azabtar da ita, a hakan ma zamanta a gidan nan, an rage ?arfin tasirinsa.
Cikin tausayawa Nana ta din ga kallon yadda ta koma gefe, ta zauna tana ta kuka da ?arfinta. Haka suka wuce ta.

Bayan sun baro gurin, suka tafi wani guri, shi kuma jarirai ake kawo wa sabuwar haihuwa, domin yi musu aski, kaciya da cire beli.

Idan sarkin baka ya dun?ule hannunsa, yana buWewa sai ka ga aska, ya yi siddabarunsa ya shafa kan yaro da askar, sai ka ga ya cika hannunsa da gashin yaro.
Idan ya shafa aska a wuyan jariri, sai dai ya zira hannu a bakin yaro, ya ciro wata tsoka har ya cire belin.
Haka kaciya, sai dai da gashin jariran, da belin, duk a cikin jakar zabirarsa yake zubawa.
Sannan ya kan kama hannun yaran, ya Waura musu laya, ko ya sanya musu tagulla.

Ya kalli wata mata ya ce "Ahh hajjaju an sauka ashe?"

Ta washe baki ta ce "Wallahi sarki, gobe ma suna"

Ya kalli yaron, da fatarsa duk ta yamutse ya ce "Ke ya aka yi ki ka bari mayya ta kama miki Wa? Tun yana ciki matar da ta aiko miki da kunu, ki ka sha ta kama miki Wa"

Cikin damuwa matar ta ce "Innalillahi wa innalillahi razi?una, wallahi sarki ka ga ba ya gaba yaron nan, kullum cikin kuka ba ruwan nono na rasa yacca zan yi ohh ni Sakina, amma Allah ya isa wallahi"

Daga yadda matar ta faWi Innalillahi, Nana ta ?ara tabattar da jahilci a gurin matar, yadda suke ba wa maganganun sarkin baka ammana ba tare da musu ba har mamaki yake bata. Ya faWi maganin da za a bata suka yi gaba.

Wani guri suka shiga, shi kuma masu ciwon suga ne, ya yi musu ya jiki suka amsa. Bayan sun gama gaisawa ya kalli masu kula da su, ya ce "Yauwwa, kar a kuskura a karya dokokin da na saka, da sassafe kafin su ci komai a ba su magani, a basu zuma cokali biyu da garin habbatussauda, sai su karya kumallo da ruwan dahuwar yaWiya mai Wumi, sannan su ci ganyenta. Da rana a basu faten dankalin turawa da alayyahu, a sake basu zuma da habbatussauda, sai da daddare a ba su gurji da kwaWon rama, sai a sake ba su magani. Yau maganin cikin Sawon gyaWa bibbiyu za a zuba musu a ruwa su sha. Shi ne jadawalin abincin da za a ba su yau" ma'aikatan suka amsa masa da to. Nana kuwa rasa bakin magana ta yi, sai kallon ikon Allah, tamkar likita a asibiti da marasa lafiyar sa.

Sun zagaya sosai da sosai a cikin gidan, sannan suka koma wancan Wakin da suka tarar da shi da farko.

Bayan sun shiga, ya zura hannu a cikin zabirarsa ya din ga zaro gashin jariran nan, da belin da ya din ga cire musu, yana tarawa a cikin wata tasa, sai da ya cikata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login