Showing 138001 words to 141000 words out of 190498 words

Chapter 47 - Buzu Book 1 Complete

ce "Rakiya auren ne fa aka yi shi babu shiri, saboda magana ta nemi ta Waukko mana aka yi shi, ba wani taron kirki aka yi ba"

"Amma duk da haka, ai ya kyautu mu sani"

Baba ya taso kamar zai dake su ya ce "Kin ga ku bi hanyar da ku ka shigo mini gida ku fita".

"Dan Allah Malam Isa ka yi ha?uri, abin duk bai kai haka ba, ka bari a kaimu ko gidan nata ne, mu ga Wakinta, mu gaisa da ita, mu ba ta sa?on mahaifiyarta"

"Na yi muku iyaka da 'ya ta, ba zaku taSa ganinta ba, ba ta bu?atar ku, ku bar mini gida, kafin na yi muku Wibar albarka"

Ganin babu mutunci a lamarin Malam Isan, ya sanya suka kwashi kayan da suka zo da su, su ka fice.

Ayshercool
08081012143

40

Hargowa da bala'in da Baba ya yi wa su Adda Rakiya, ya yi masifar Sata musu rai, a zaton su duk abubuwan da suka faru a baya sun riga sun wuce, dan aure ya mutu ba ya nufin a wanzar da gaba a tsakanin yara da mahaifiyar su, ko a yanke duk wata da za su yi ala?a da ita.

Ga gajiyar tafiya da su ka sha a mota, amma Baba ya yi musu wannan mummunar tarbar.

Can gidan su Nana kuwa, ana ta neman Yusra, ba a ganta ba, hankalin Hajiya Halima ya yi mugun tashi, suka fito neman ta harabar gidan tare da Siyama.

Gurin Sayyid su ka nufo, Hajiyar take tambayarsa "Dan Allah yarinya ba ta zo ka buWe mata ?ofa ta fita ba? Wata 'yar fara haka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

"Na shiga uku, ni kuwa ina yarinyar nan ta shiga haka? Kirawo mini Nuradeeni a waya, ko sun fita tare?"

Siyama ta ce "Su fita tare su je ina, su da ba shiri suke yi ba, ina zai kai ta? Wata?ila tana cikin gidan nan wani gurin ta samu ta shige kawai"

"To tana cikin gidan nan, mu ganta mana"

"Ki yi ha?uri mu koma, mu ci gaba da duddubawa"

Nana kuwa ba ta san me ake yi ba, tana zaune a gefen Yusra, tana bin karatun Alkur'ani da ta kunna a wayarta. Ta ji daWin yadda take raira karatun yau, ba tare da ta ji kanta ya fara ciwo ba, ko ta fara jin sanyi ba. Yusra kuwa baccinta take yi da gaske.
A ?alla ta kai awanni biyu tana bacci, har Nana ta idar da karatun Al?ur'anin, ta Wora girki. Ta kammala babu jimawa ta farka daga baccin. Nana ta saka ta yi alwala, ta ba ta hijjabi ta yi alwala ta yi salla. Ta sake zuba mata abinci ta ci, sannan ta ce "Mu je na raka ki cikin gidan, zan zubawa mijina abinci shi ma na ba shi"

Ta kalli Nana ta ce "Ki na da miji?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Eh, ina da shi, shi ne a waje yake yi muku gadi"
????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ?
Yusra ta ce "Mhmm ni da na fara rashin lafiya, shekara biyu kenan, mijina ya sake ni, ya ma yi aure ba zai zauna da ni ba. Ba wanda ya san me nake ji, amma ke na ga kamar kin san me yake damuna, ke ba za ki ce ?arya nake yi ba. Mami ta ce "Ina sane na kashe aurena, na ji haushi sosai da sosai"

Nana ta ri?e hannunta ta ce "Ki yi ha?uri, na ki ?alubalen kenan, tabbas na san ciwon nan, na san babu daWi, kuma babbar jarrabawa ce a ce na kusa da mu sun kasa fahimtar mu, su din ga ganin muna sane muke yin abin da muke. Dan haka dolenmu ne, mu dage mu yi ta adduo'i da azkar domin Allah ya bamu lafiya"

Ta jinjinawa Nana kai ta ce "Na gode sosai da sosai"

Nana ta tashi suka fito daga Wakin, dama Sayyid a matse yake ya shiga Wakin, zaman Yusra a Wakin ya hana shi shiga.

"Wannan ne mijin naki?"

"Eh shi ne"

Ta ce "Sannu dattijo"

Ya Wago ya kalle ta, ya Waga mata hannu. Ta yi murmushi kawai.

Nana ta ce "Dattijo kuma?"

"Eh, ke matashi ki ke gani, ni kuma Dattijo nake gani, duk da kema ki na ganin haryanzu dai ki na wasi-wasi ne"

Nana ta ce "Haula"

Ta amsa da "Na'am uwar gijiyar ?aisar"

"Amma me yasa za ki yi mini haka? Matar ta farfaWo ta samu ta ci abinci, ta yi bacci kuma kawai sai ki zo za ki sake burkita ta"

Yusra ta yi murmushi ta ce "Tuba nake, wallahi ba da wata manufar na zo ba, gaisuwa na zo kwasa kuma na yi sai anjima"

Nana ta Wan ?ura wa Sayyid ido, amma ya ?i kallonta, ya tafi Wakin su. Ta jinjina kai a hankali ta ce "Biri ya yi kama da mutum"

Har cikin falon Nana, suka shiga tare da Kubra. Hajiya Halima na ganinsu ta mi?e ta ce "Laa a ina ki ka ganta? Tun Wazu muke bulayin neman ta a cikin gidan nan"

Nana ta ce "Subhnallah, wallahi ban sani ba, gani na yi za ta fita na hana ta, mu na tare da ita a Wakina, kuma na yi ragon azancin ban zo na sanar miki ba".

"Mami ta bani abinci, kuma na yi bacci ma"

"Ikon Allah, yau kin yi baccin kenan?"

Yusra ta ce "Eh, na yi bacci sosai mai daWi, na ga ma Sagir a baccin"

A fusace Hajiya Halima ta ce "Ba za ki daina maganar Sagir Win nan ba ko? Mutumin da ya riga ya sake ki, ba zai zama da ke ba, mene ne na zancen sa "

Siyama kuwa da ranta ya Saci ta ce "Amma baiwar Allah wannan shiga hakki ne, tun Wazu mu ke neman ta fa, kuma saboda wula?anci da rashin mutunci mijinki ya ce bai ganta ba, wannan ai gidadanci ne da rashin hankali"

"Laifina ne, ba nasa ba ki daina zaginsa dan Allah, ba na jin daWin hakan"

Hajiya Halima ta ce "Siyama ya isa haka dan Allah, amm Nana sunan ko? Mun gode sosai da sosai"

Nana ta juya za ta tafi, Yusra ta ce "?awata sai anjima"

Nana ta yi mata murmushi ta ce "Kar ki manta abubuwan da na gaya miki fa"

Ta amsa mata da "To"

*****

An Waga Shukura daga kwanciyar da take yi, an yi mata wanka, aka kawo mata abinci, amma ta ?i ci, tana zaune tamkar gawa.

"Shukura yanzu haka rayuwa za ta kasance mutum babu tawakalli kenan? Da Allah ya baki lafiyar ba za ki gode masa ba kenan?"

"Mummy"

"Naam"

"Kin ga gawar abin da na haifa?"

Hajiya Amina ta ce "Eh mana, awansa shida a nursery ya rasu, sai da na gan shi sannan Sagir ya tafi da shi ya binne."

Hawaye ya gangaro kan kumatunta, ta ce "Amma me yasa ba a bari na gan shi ba?"

"Shukura ba kya cikin hayyacinki, za a yi ta zama da gawa ne ba a binne ba? Ai ba zai yiwu ba"

Ta ce "Haka ne, amma ina baban Haidar Win yake?"

"Bai daWe da tafiya ba ki ka tashi, kuma da na san za ki farka da wuri an jira, kin gan shi. Amma na san ya Waukar miki shi a hoto ai. Na tura family group ma, amma dai na ?ara gaya musu, ban da zuwa dubiya ba kya jin daWi"

Ta ce "To Mummy na gode sosai, tun da dai kin ce mini kin ga gawar babyn shikenan, Allah ya sanya mai ceto ne. Ke ma Allah ya baki ladan Wawainiyar da ki ke ta yi da mu"

Cikin jin daWi Hajiya Amina ta ce "Amin ya Allah, ko ke fa Auta, dan Allah ki ci abincin ko na ji daWi"

"To Mummy amma saboda ki ji daWi zan ci kaWan, ba na son cin komai"

"Ba komai, hakan ma na gode sosai da sosai Autar Mummy"

Haka Shukra ta din ga ya?i da zuciyarta, da ?o?arin kawar da tunanin mafarkan da take yi.

*****
Har Gaddafi ya gota matan, da suke zaune a kan barandar ?arshen layin, sai kuma ya dawo da baya ya ce "Sannun ku"

Su ka amsa masa da "Yauwwa sannu"

Ya ce "Kamar 'yan uwan babar su Imrana"

Adda Rakiya ta ce "Laa Gaddafi kai ne?"

Sai ya gyara tsayuwarsa, su ka gaisa. Ya ce "Ya na gan ku a nan?"

Adda Rakiya ta so ta kare, amma Fati ta gaya masa abin da ya faru.

Ya girgiza kai ya ce "Ku yi ha?uri, abu ne da ya faru ya riga ya wuce, amma an ?i bari ya wuce, ake ta nanatawa, bari na nemo muku Nasiru, ya raka ku."

Bayan tafiyar sa Rakiya ta ce "Fati, wannan ba Gaddafi ba ne ba, mai cewa zai daki Mai Jidda, yau shi ne da gaishe mu"

Fati ta ce "Wallahi nima abin ya bani mamaki sosai da sosai"

Su na cikin tattaunawa, Gaddafi ya kawo musu ruwan sanyi da lemo, ya nemo Nasiru, ya tarar musu abin hawa, ya biya kuWin suka tafi.

*****
"Sayyid"

Ya Waga ido ya kalle ta.

Ta ce "Ko dattijon ne?"

"Wane dattijon?"

"No ba komai"

"Ki daina kallona, kamar ki na tuhuma ta"

Ta ce "Tuhumar ta ka nake yi ai"

Ya tsaya da cin abincin ya ce "Da me?"

"Ci abincinka, zan gaya maka"

Ya ci gaba da ci, ta sake kiran sunansa.

Ya Wago ido ya kalle ta.

Za ta yi magana, su ka ji an buWe gate Win gidan an shigo.

"Laa a buWe ka bar gate Win?"

Ya ce "Eh na manta ne"

Sallamar Nasiru ta ji, ta yin?ura ta tashi ta le?a.

Kasancewar jikinta babu hijjabi, ko Wan kwali babu a kanta, kafin ya yi magana tuni ta yi wani irin ihu, ta yi waje da gudu. Tashi ya yi da sauri, ya bi bayan ta, domin ganin abin da ya sanya ta wannan ihun haka.

Gani ya yi ta rungume Waya daga cikin matan da suka shigo tare da Nasiru. Ya koma da sauri ya rufe abincin da yake ci, ya kawar da kwanukan ya koma gefe ya tsaya.

Tare suka shigo da matan, Wayar na share hawaye ita ma. Su na shigowar ya fice daga Wakin.

Nana ta kasa magana saboda kukan da ya ci ?arfinta.
Adda Saude ta ce "Nana kukan ya isa haka"

"Adda ina mamanmu?"

"Yanzu dai ki yi ha?uri, mu gaisa mana Nana"

Ta basu gurin zama, sai dai ta kasa daina kuka, ta kawo musu ruwan roba, ta koma gefe ta zauna ta cigaba da kuka.

Anty Fati ta ce "Haba Nana, ki yi shiru mana"

"Dan Allah ina Maman take? Yanzun ma ba za ta zo ba?"

Adda Saude ta ce "Ki yi ha?uri Nana, auren nan na ki ma ba mu sani ba, waiwai mu ka ji, tare za mu taho da ita da, amma mijinta ya hana, yanzu haka ma babanki da korar mu ya yi, Gaddafi ne ya haWo mu da yaro ya rako mu, har ya biya mana kuWin mota"

Cikin kuka Nana ta ce "Na kira ta, Baban su Walida ya Wauka, bai haWa ni da ita ba"

"Ki ha?uri Nana, lamarin iyayen naki ne sai ha?uri, ita kanta babu yadda ba ta yi ba ta zo, amma ya hana har da barazanar saki. Amma ga kayan aurenki nan da ta bayar a kawo miki, mu ma da abin da Allah ya yassare mana. Yanzu zamu haWa ki da ita a waya, zan kira Lawan ya kai mata sai ku gaisa"

Nana ta ci gaba da kuka, tana jin kewar mahaifiyarta, amma gaba Waya ba ta da maraba da marainiya.

Anty Fati ta ce "Nana, mijin naki buzu ne kenan? Ke kuwa yaya aka yi ku ka haWu har danginsa su ka bari, ya aure ki, ai ba sa auren bare da wahala. Har gara matan su, idan ka na da kuWi za su baka, amma mazan dai ba sa auren wasu matan idan ba na su ba".

Ras gaban Nana ya yi wata irin mummunar faWuwa, amma ta dake ta ce "A gidan da yake gadi mu ka haWu"

Adda Sauda ta mi?o wa Nana waya, Nana ta karSa jikinta yana rawa.

"Salamu Alaikum Nana, ki na ji na?"

"Mama" ta furta cikin rauni, tana fashewa da wani irin kuka tamkar za ta shiWe.

Maijidda ma kukan ta saka ta ce "Nana ki yi ha?uri, na san ni mai laifi ce a gurinku, dan girman Allah ku yafe mini an fi ?arfina ne, na rasa yadda zan yi. Imrana ma ya daina zuwa inda nake"

"Mama dan Allah ki zo, ni ba na son na zo na saka ki a matsala ina son na ganki, dan Allah"

"Nana in sha Allah zan zo Nana, da gaske an yi miki auren ko? Kodayake daga majiya mai ?arfi na ji, Babanku bai kyauta mini ba. Ga Wan abin da na tara miki nan babu yawa, ki yi ha?uri Nana, ki ba wa Wan uwanki ha?uri dan Allah ku yafe mini. Wallahi ku na raina ban taSa mantawa da ku ba, babu yadda na iya, mijin da nake aure ba shi da fahimta, kansa kawai ya sani shi ma" Nana ta kasa magana sai wata irin sheshshe?ar kuka da take yi.

Ta sake cewa "Ki na ji na Nana, ki yi ha?uri da rayuwa, jariri ma ana haihuwar sa, mahaifiyarsa ta koma ga Allah, kuma ya rayu cikin ikon Allah, ki zama mai juriya, ki yi wa mijinki biyayya. Har yadda aka yi aka yi auren ki, an gaya mini, amma ko 'yan uwana ban gaya wa ba, kowace mace ko na ce ko wane dan Adam akwai kalar tasa jarrabawar. A raina, ban taSa jin za ki aikata, wani abu da zai tozarta ki ba. Ki yi ha?uri ki rungumi auren ki Nana, shi ne mutuncinki da suturar ki.
Yaya jikin ki kuma?"

"Da sau?i" ta faWa muryarta na fita da ?yar.

"To ki ri?e Addu'a, ki ri?e Allah. Ki ri?e auren ki da kyau, ki yi ha?uri Nana, ki yi ha?uri ku yafe mini. Dan Allah kar ki yi fushi da ni, kamar yadda Wan uwan ki ya yi, wallahi ku na raina."

"To Mama, na gode sosai, na gode" suka yi sallama, Adda Saude na ta rarrashinta da ba ta ha?uri.

Gyaran muryarsa ta ji a ?ofar Wakin, Nana ta tashi da ?yar ta nufi ?ofar Wakin.

Zuciyarsa ce ta buga da ?arfi, a razane ya ajiye ledojin hannunsa ya ce "Mene ne?"

Nana ta yi shiru tana kallon sa.

"Yi magana Husna, mene ne?"

Nana ta goge hawayenta, ta ce "Babu komai fa"

"A'a launin idonki ya canza, ba kuka ne kawai ba, akwai matsala ne"

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ka kwantar da hankalinka, zan yi maka bayani bari ba?ina su tafi"

"Zuciyata babu daWi, ki daina kuka na ro?e ki"

Cike da jarumta, ta ?a?alo murmushi ta ce "Na daina" ya jinjina kai, ya Wauki ledojin ya ba ta.

Ta koma cikin Wakin, su ma fruit ne, da fura da Nono ya kawo.

Ta hau fafutukar Wora musu girki, a hankali ta Wan ware, su ka yi ta hira, Nana ta ce "Me yasa ba a zo mini da ko Walida ba, rabona da su tun su na yara sosai"

Anty Fati ta ce "Wa zai Waukko su, ya zo ya yi ta jaraba, mussaman ya san in da aka tafi da su. Ai Maijidda ba ta yi dacen mazaje ba, daga Baban naku, har Iliyasun.

Suka yi salla, Nana ta kammala girki, ta Webarwa Sayyid nasa, su na ta yi wa Nana hira, sai dai zuciyarta cike da damuwa.

Nana ta fita ta samu Sayyid, ya mi?e tsaye yana kallon kumburarriyar fuskarta cike da damuwa.

"Sayyid ka zo za ku gaisa da 'yan uwan Mamana, su ne suka kawo mana ziyara ka zo mu je ku gaisa. Amma idan da hali ka yi musu magana dan Allah"

Ya ce "To, amma idan ina kallon fuskarki a haka, ba zan iya magana ba"

Ta yi murmushi ta ce "Ba na son rigima, mu je to"

"Ina jin kunya, wuce gaba na biyo ki"

Ta yi murmushi, ta yi gaba ya bi bayan ta.

Ya yi sallama sannan ya shigo, ya tsugunna, ya sauke takunkumin fuskar sa ya ce "Barkanku da zuwa, ya hanya?"

Jin gaisuwar ta sa suka yi banbarakwai, amma Adda Saude ta ce "Lafiya ?alau, mun same ku lafiya? Ya iyalin?"

Ya ce "Alhamdilillah mun gode Allah"

"To ma sha Allah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, bamu samu mun halarci taron biki ba, sai yanzu muka zo. Allah ya baku zaman lafiya. Sannan a yi ta ha?uri, shi aure Wan ha?uri ne, ba farkon auren ba, sai zama ya yi zama ake gane ha?urin. Ubangiji Allah ya yi muku albarka, dan Allah ka yi ha?uri da ita ka ri?e ta amana"

"In sha Allah"

Anty Fati ta ce "To ina fatan dai ba za ka yi mata kishiya ba, tun da ta ciri tuta ka aure ta, tun da dai an ce ba kwa auren wanda ba ?abilar ku ba? Dan ni 'ya ta daidai take da mata huWu, har da Woriya."

Mi?ewa ya yi yana murmushi, ya nufi hanyar fita. Nana cikin shagwaSa ta ce "Sayyid ba fa ka ba da amsa ba"

Yatsansa manuniya ya nuna mata, ya ce "Ke kaWai ce Ma vie"

"Anty Fati ki zama shaida"

Ya fice yana murmushi, Anty Fati ta ce "Ke babu ruwana, namiji na mata huWu ne, wasa nake yi kar ki saka a hakan a ranki"

Nana ta basar da maganar, dan wani irin zafi ta ji ya fara taso mata.

Adda Saude ta ce "Nana an baki 'yan abubuwa kuwa na gyara, ko kuwa haka kawai su ka ninko ki, su ka kawo ki?" Nana ta yi shiru, tare da sunkuyar da kai, wa ya tsaya bin ta kan ba ta wani abu, har gara Ummi ta kawo mata, ranar da su ka zo da su Jamila, ta rubuta mata yadda za ta yi amfani da shi, amma tun da ta jefa ledar a drower, ba ta sake bi ta kan su ba, saboda pressure gabanta ta ishe ta, ba ma ta taSa tsammanin wani abu zai shiga tsakaninsu ba.

Anty Fati ta yi wa Nana tambayoyi, a kan matsalar sanyi, Nana ta ce ita ba ta jin komai na alamar sanyi.

"To duk da ke kaWai ce a gurin mijinki, amma kar ki zauna ki mi?e ?afa Nana, kar ki ga ba shi da ?arfi, tsaf 'yan mata za su din ga kawo masa farmaki, ki na ganinsa tubarkallah da shi. Nana ki yi addu'a, ki yi gyara kuma ki yi biyayya, za ki zauna lafiya in sha Allah. Nana ki yi kissa, kar ki zauna haka sai abin da ya zo miki, ki zama mace mai tunani Allah ya baku zaman lafiya"

Suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login