Showing 33001 words to 36000 words out of 190498 words

Chapter 12 - Buzu Book 1 Complete

je aka taho da Yaya Atine daga gidanta, a taxi Win malam Shehu, gari yana fara haske suka tafi. Jiya ne Suwaiba ta din ga ihu cikin dare wai Nana tana sha mata jini, shi ne suka tafi da sassafe"

"Kuma shi ne ba a gaya mini ba, ina ne garin mai maganin, kar aje a kai ta gurin bokaye"

"Wallahi ban sani ba"

Imran ya ce "Ke Suwaiba, ya aka yi Nanan ta sha miki jini, ita ba mayya ba, kar ki ja a Sata mata suna, ni ba na son ?ananan maganganu ki bar ta ta ji da halin da take ciki mana"

A fusace Mama ta Waga labule ta fito ta ce "Ban gane ba, za ta yi mata ?arya ne? ko dan kai ba a gidan ka kwana ba, ba ka san a halin da ta kwana ba"

"Eh Alhamdilillah, na ji daWin hakan ma, ai da gani ku ke yi Nana tana sane, duk abubuwan da yake faruwa da ita, tana sane ita ta yi wa kanta ?arya take yi. Yanzu idan ma ?arya take idan ma gaske ne, ai kwa gani, kuma wallahi na ji wata magana a unguwa ta cin zarafin Nana, ko yi mata ?age wallahi sai na saka an Waure mutum igiya ta yi saura"

Jamila ta ce "Mama dan Allah rabu da shi, kar ya yi miki rashin kunya"

***
Nana kuwa rarraba ido kawai take yi a hanya, tana ta ?o?arin tuna wasu abubuwa a ?wa?walwarta, amma abu ya gagara. Abin da take iya tunawa, kawai hango Suwaiba tana zubar da jini, amma ta kasa tuna takamaiman yadda aka yi ta ga jini a jikin Suwaiba.

Gaba Waya ta nemi kuzarinta ta rasa, jikinta yayi sanyi ?alau, ko ?wa?w?waran motsi, sai ta yi da gaske take iya yin sa.

Sannu a hankali, ?wa?walwarta ta fara fassara mata maganganun da ta jiyo Baba yake yi. Wai ana idar da sallar asuba, ya kira Saleh a waya ya ce masa wai idan akwai kuWi a hannunsa, ya turo wani abu za a nema mata magani. Wani irin takaici ya kama Nana, sam Baba ba ya gudun abin kunya da duk wani abu da zai zubar musu da kima.

"Atine, ai yakamata tun yanzu yaron nan, ya fara ?o?artawa shi ma, tun da dai aurenta zai yi, duk wata hidima da za a yi mata, ya saka hannu a yi da shi"

Babu kunya Yaya Atine ta ce "Gaskiya ne, ai kamata yayi ace ya Wauke maka wasu nauye-nauyen".

Baba ya ce "Sosai fa, kuma kin ga hakan zai ?ara tabattar masa da gaske zan ba shi aurenta. Ai mu na dawowa daga gurin maganin nan kawai iyayensa su zo a wuce gurin"

Nana ta rintse idanunta, tana fatan bacci ya Wauke ta, ba ta tunanin akwai wani wanda zai aureta ta yi mutunci a idonsa, da irin wannan halin na Baba, na son jinginawa wani Wawainiyar da shi yakamata ace ya yi abarsa.

Sun sha doguwar tafiya sosai, kafin su isa wani sur?u?in ?auye, sai da suka yi nisa sosai da sosai, suka daina ganin gidaje. shige da ficen ababen hawa ne, ya sanya suka tabattar da akwai mutane a gurin, domin kuwa hatta kwalta babu a gurin, sai uwar zangarniya.

Yanayin sur?u?in gurin, sai parking Win motar suka yi a bakin hanya, suka saukko domin takawa su ?arasa, sai dai ?afar Nana ta ?i takuwa sai ma lan?washewa da ta yi, kamar mai shan inna.

Sun daWe a gurin, Nana ta kasa taka ?afafuwanta, sai da ?yar ta Wan saki, ta takawa a hankali.

Tun da suka doshi hanyar da aka nuna musu, aka ce a nan gidan mai maganin yake, Nana take ganin garke garke na Ra?uma su na fitowa daga hanyar, jajaye da farare. Yaya Atine ce ta ri?e ta suke tafe a hankali, saboda da ?yar take taka ?afafuwanta.
Nana ta ce "Yaya Atine dama akwai ba?in ra?umi?"

Yaya Atine ta ce "A ina?"

"Ga su nan su na ta wucewa, ba ki gansu ba?"

Yaya Atine ta ja ta tsaya ta ce "Kai Gaddafi, ku na ganin ra?uma ko kuma nima abin nata ne zai shafe ni, nice ba na ganinsu?"

Baba ya ce "Ra?uma kuma a ina?"

"Yo ai ji na yi tana zancen ba?in ra?umi, ni kuma ko kofato ban gani ba balle ra?umi. Kai zo ka ri?e 'yar ka, kar na gano abin da ba shikenan ba"

Nana na jin haka, ta zame hannunta daga na Yaya Atine ta ci gaba da takawa a hankali.
Daga nesa suka hango gidan, mutane na ta shiga su na fita.

Ja da baya Nana tayi da sauri tana kare fuskarta.

Baba ya ce "Me kuma ya faru?"

Cikin damuwa Nana ta ce "Baba wai ba ka gani, ba?in ra?umin nan ne yake feso mini wuta fa"
Cikin takaici Gaddafi ya ce "Dan Allah Baba ku daina biyewa yarinyar nan, ku zo mu ?arasa."
Su na tunkarar gidan, amma ra?uman na ?ara yawa, Nana ta fahimci ita kaWai take ganinsu, su ba sa ganinsu.

A haka har suka ?arasa ?ofar gidan, Ko da su ka shiga gidan, jikin Nana ya hau rawa, sai dai hakan bai hanata gode wa Allah da halin da ga tsinci kanta. Saboda yadda ta ga wasu a cikin mari su na hauka tuburan, ban da masu ciwon galhanga, shan inna da sauransu.
?aki Waki ne a gidan, ma'aikatan gidan, duk su na sanye da jajayen kaya, kamar ma'aikatan jinya a asibiti.
Hankalin Nana yayi mugun tashi, da ta ga ana yi wa wasu daga cikin marasa lafiya sakiya. A saka kibiya a cikin magani, sannan a sakata a cikin wuta, sai ta yi ja sannan a soka a gurin da yake da larura.

Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, hankalinta yayi mummunan tashi.

Su na ?o?arin shiga ?ofar da za ta sada su, da ainihin gurin da mai maganin yake ganin marasa lafiya, idon Nana ya sauka a cikin na Waya daga buzaye ukun da suke ?o?arin fitowa daga cikin gurin.

Ji ta yi tamkar an watsa mata wuta a cikin idanunta zuwa jikinta, ?ara ta saki ta dafe kanta ta faWi a gurin. Taku uku ya yi, ya ja ya tsaya ya waiwaya ya kalli gurin da Nana ta faWi. Habu ya kama hannunsa suka yi waje.
Ma'aikatan gurin, su ka zo su ka Waga Nana, su ka shiga da ita gurin mai magani, su Baba su na biye da su.
Mai maganin ya fito sanye da rigar fatar damisa, sai warki a ?ugunsa idanunsa Jawur tamkar garwashi, ba?i ?irin da shi.

Da sauri ya ?arasa kan Nana, tamkar likitan da aka kawowa mara lafiyan da yake bu?atar agajin gaggawa. Ya sunkuya a kanta yana kallonta sai kuma ya Wago a gigice ya ce "Baushe, maza bi buzayen nan ka dawo da su, wata?ila ga makarin na sa ciwon a nan, maza hanzarta kar su tafi"
Su Baba dai su ka tsaya sororo su na bin sa da kallo.

Nana kuwa tari ta hau yi, tamka ?irjinta zai buWe, ganinta ta yi a cikin ?ura, ko tafin hannunta ba ta iya gani saboda yadda ?urar ta turnu?e gurin. Bayan wani lokaci ?urar ta lafa, ta Waga kanta ta na kallon gurin, ita kaWai ?wal a cikin sahara.
Waige-waige ta hau yi, sai dai babu tsammani ta ga mutum a tsaye a bayanta, sanye da ba?in rawani da shigar fararen kaya na buzaye, hannunsa ri?e da akalar ra?uminsa.
Sai dai duk ?o?arin Nana a kan ta gane kamaninsa, abu ya gagara fuskarsa a rufe take da rawani.

Mi?a mata hannunsa yayi, mai Wauke da dogwayen yatsu. Duk da a tsorace take, ta fara takawa a hankali, har ta ?arasa gurin da yake, ta mi?a masa nata hannun.
Yana kama hannunta, ta ji an zuba mata ruwa mai matu?ar sanyi a jikinta. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke, tare da buWe idonta.

Su Baba ta gani a zaune tsuuruu, kamar mara gaskiya a hannun hukuma.

"Sannu Nana Asma'u" mai maganin ya yi maganar cikin sakin fuska.

Nana ta tashi zaune, ta koma jikin Baba, tana jin yadda haryanzu jikinta yake a sanyaye.

Mai maganin ya zura mata ido, sannan ya sake murmushi ya ce "Manya gatan wasa, wa ya isa ja da ku, idan ba wawa ba? Tuba nake uban du?usa" dubawa Nana take ta ga da wa yake.

Ya ci gaba da cewa "Asma'u, ki na ganin wani mutum a mafarki, ku na magana ko?" Nana ta yi shiru ba ta ce komai ba.

"Za ki iya tuna me da me yake ce miki?" Still ta yi shiru ba ta yi magana ba.

Ya sake murmusawa ya ce "Malam, gidanmu wanzamai ne, na kuma yi ?arfa-?arfa a kan farauta, duk da mahaifiyata sun gaji farauta . Na daWe ina hatsabibanci, har na zo na fara bayar da magani, na daWe ban ga abin mamaki ba kamar yau. Aljanin da yake Wawainiya da yarinyarka hadiminta ne, tun zamanin kakaninka ai 'yan bori ne. Kuma tun daga kansu ba a kuma samun haihuwar mai irin tauraronta ba, sai da aka haifeta dan haka dole ya yi mata hidima, ita kuma ta?i yadda shiyasa yake ta azabtar da ita. Duk ba wannan ba yanzun nan aka tafi da wani buzu, shi dama na gaya musu ba ni da maganin larurarsa, sai dai a shigowar ku, na ga wani abin mamaki da na daWe ban gani ba, ina kyautata zaton wata?ila maganin nasa ciwon na da ala?a da nata.
Kodayake ba a kan wannan gaSar muke ba. Yanzu ita Nana Asma'u za ku bar ta a nan, sai bayan kwana goma sha huWu zaku dawo, aljaninta sai dai ayi sulhu da shi idan aka takura shi, ba ita ba ni kaina zai iya halaka ni."

Kallonsa Nana tayi, gaba Waya maganganun mutumin nan ko gaske ne, mushiriki ne shi ma, jira take ta ji me su Baba za su ce, ko me za ayi ba za ta yarda a bar ta a gurin nan ba.

Baba ya ce "Mu tafi mu bar ta har mako biyu kuma, itakaWai?"

Gaddafi ya ce "Ba magani ake mema ba? Ma samu mu huta kwana biyu mu ma, da wannan tamSelen da take yi ai gara a batta Win, Allah ya kaimu makwanni biyun"

Yanayin Baba ya nuna ba haka ya so ba.

Nana ta buWe baki za ta yi magana, ta ji kamar an saka dutse a ma?ogwaronta, tayi tayi amma magana ta gagara.

Ta dage iya ?arfinta ta mi?e tsaye, amma jiri ya kwashe ta, tana ji tana gani, masu jajayen kayan nan, suka zo suka Wauke ta, tana fizge-fizge tana komai aka kaita wani Waki aka kulle.

Littafin BUZU 1k ne a telegram.
0069685771
Aisha Adam
Stanbic ibtc
Sai shaidar biya
https://wa.me/2348081012143


Ayshercool
08081012143

BUZU
AISHA ADAM AYSHERCOOL

YOTA/002


(Bright pens 3rd batch)

P12

Imaran tun yana jiran dawowar su Baba da daWin rai, har ransa ya gama Saci, zuciyar sa ta din ga tafasa.

Mama kuwa tuni ta din ga kiran 'yan uwanta tana gaya musu, abin da ya faru da Suwaiba. Suwaiba kuwa ko a jikinta, sabgoginta kawai take yi. ?arshe ma da yamma, ta sha wanka za ta fita zance, ta ga turaren nan a kan kayan Nana, ta Wauki abin ta ta ?ara fesawa ta fice.

Bayan sallar magariba, Imran yana zaune a waje, sai ga taxi har ?ofar gidansu, su Baba sun dawo.

Bai motsa daga gurin da yake ba, sai da ya ga duk sun fito daga motar, amma babu Nana.

Su na shiga gida, ya tashi ya bi bayansu.

"Wai ina Nanan take? Ya ku ka dawo babu ita?" Daga Baba har Gaddafi babu wanda ya kula shi.

Ransa ya fara Saci ya ce "Baba ka yi magana, ina ku kai mini Nana?"

"Tana gidan Atine" ya bashi amsa a gajiye, saboda sun kwaso gajiya.

"To me yasa za a kaita gidan Yaya Atine? Me yasa ba ku dawo da ita gidan nan ba?" Ganin Baba ba zai ba shi cikakken lokacinsa ba, balle ya yi masa bayani, kawai ya fice ya nufi gidan Yaya Atine.

Yaya Atine, ta mimmi?e tana cin tuwon dare, saboda wahalar da suka sha.
Kamar an jefo Imran ta ji sallamarsa.

Ta amsa masa, ba tare da ya ko gaisheta ba ya ce "Ina Nana?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Nanan?"

"Baba ya ce mini tana gidan nan?"

"Kuma saboda rashin Wa'a, ko gaishe ni ba za ka yi ba, ka zo kana tambayata wata Nana, to mun sayar da ita"

Ya ce "Yi ha?uri, a ruWe nake ne"

Yaya Atine ta ce "Ba wani ha?uri da zan yi, gidan uban wa ka tafi tsawon shekarun nan?"

Duk da ya fara ?uluwa ya maze ya ce "Kudu na tafi neman kuWi, tana ina?"

"Kai ban sani ba, ni ba ta gidan nan, ka koma ka tambayi uban naka"

Imran ya kalle ta ya ce "Kamar yaya? Shi fa ya ce mini tana nan"

"A'a tana gidan mai magani, sai nan da mako biyu za aje a taho da ita"

Ashar Imaran ya yi ya ce "Wane irin magani ne, sai an kai mutum a baro shi, to ai ko asibiti ana barin Wan jinya, balle wani shashasha da bai shiga aji ba, aje a ajiye masa yarinya shi ba muharamminta ba".

"To ai ubanka za ka je ka yi wa ba ni ba. Kuma ba fin mu hankali da tunani ka yi ba, gurin akwai ma'aikata mata da suke kula da mata marasa lafiya " Imran ji ya yi kamar ya kifa wa yaya Atine mari, wannan ai ganganci ne da rashin hankali.

Takalmansa ya shura, ya fita daga gidan zuciyarsa kamar ya fashe saboda takaici.

Gida ya koma cikin takaici, sai dai ya tarar Baba baya nan.

Labarin mutuwar malam Auwal ya karaWe ciki da wajen unguwar su Nana, saboda an san shi sosai, saboda ya kan ja salla a masallatai daban-daban.
Ga koyarwar da yake yi a islamiyya, kowa yayi masa shaidar mutumin kirki ne shi. 'yan unguwa suka yi alwashin tsayawa tsayin daka, gurin bibiyar jam'i an tsaro da tabattar da an kama waWanda suka aikata masa haka.

Cike da jimami Nasir ?anin su Nana yake ta nanata mutuwar malam Auwal, ya ce "Allah sarki Nana, ko ya za ta ji idan aka ce mata malam Auwal ya mutu an kashe shi?" Duk da Baba yana cike da takaicin wasa da hankali da malam Auwal ya yi masa, na ?in fitowa ya auri Nana, amma hankalinsa ya tashi bayan dawowarsu daga kai Nana gurin mai magani ya samu labarin mutuwar.
Yana tsaka da jimamin mutuwar, ana tattaunawa a masallaci bayan sallar isha'i, Nasiru ya zo ya kira Baba ya ce ana nemansa a gida.

Ko da ya je gida, ya tarar an daddane Suwaiba, tana ta kurma ihun Nana na sha mata jini.

Cikin kuka mama ta ce "Ka gani ko? Kalli halin da Suwaiba take ciki, wallahi an cuce ni ban yafe ba, kuma wallahi ko ka Wauki mataki ko ni na Wauka. Dan ba?in bala'i a gaban saurayi ta faWi tana wannan kururwar fa"

Cike da damuwa ya ce "Wai Rabi ya ki ke so na yi, ki na gani domin neme wa Nana magani, a can gurin mai magani na baro ta, kuma na ce a tafi da Suwaiban ki ka ?i yarda"

"Ni wallahi ka san yadda za ka yi, dan ba zan yarda a kashe mini 'ya ba"

Imaran ne yayi sallama, yana watso takalmansa da suka tsinke ya ce "Yauwwa Baba na je gidan Yaya Atine, ta ce Nana ba ta gurinta wai a gidan mai magani aka baro ta. Baba ko fa asibiti ana bar wa mutum Wan jinya, ya za ayi a kaita gurin da babu idon wani nata da sunan neman magani? Ina ne gurin da aka kaita gaskiya zuwa zan yi na Waukkota"

Baba bai yi magana ba, Suwaiba ta ci gaba da kakari "Baba ku taimake ni, Nana za ta kashe ni, jinina take lasa tana sha, dan zatin Allah ku hanata jikina zafi yake yi mini"

Imran ya ce "Wace Nanan? Nanan da bata gidan nan?"

Mama ta ce "Amma dai a yanayin da take ba za ta yi wa Nana ?arya ba"

Imran ya ce "To Nana dai ba mayya ba ce, abin da ku ke zunWenta ne Allah ya jarrabe ku. Ni dai dan Allah Baba ka gaya mini in da ku ka kai Nana, ni fa hankalina ba zai kwanta ba ina nan tana wata uwa duniya da ban sani ba"

A fusace Baba ya ce "Ban sani ba, ba zaka iya rayuwa tana wani guri ba, da ka tafi gantalinka shekara nawa tana nan ka na can gantalinka?"

Cike da ?warin gwiwa Imran ya ce "Amma ai na san tana gida a gabanka, ni gaskiya ban ji na gamsu da wannan tsarin ba"

Ga dai Nana ba ta gida, amma yadda suka ga rana haka suka ga dare, Suwaiba na ihun Nana na sha mata jini.

****

A hankali Nana ta ja jikinta ta zauna, duhu kawai take gani ba ta iya gane komai, ko tafin hannunta ba ta gani. Ta shafa bayanta ta ji alamun bango, ta ja jikinta ta jingina da bangon tana sauke ajiyar zuciya.
Cikin damuwa ta haWa kanta da gwiwa, zuciyarta sam babu daWi yau kuma nan Allah ya kawo ta.

Jin ?arar buWe ?ofa, ya sanyata Wago kanta. Wasu mata ne biyu sanye da uniform su ka shigo Wakin. Suka bubbuWe tagogi sai ga haske ya ratso Wakin. Duk da yanayin hasken ya nuna rana na daf da faWuwa.

?aya daga cikin matan ta ce "Ta ce taso" babu musu Nana ta tashi, ta bi su suka fita, sai ta ga kamar ba gidan da aka kawota ba.

"Za ki yi salla ne?" ?aya daga cikin matan ta tambayeta.

Da sauri ta jinjina kai alamar eh.

Aka janyo mata ruwa a rijiya, aka nuna mata banWaki. Ta yi alwala ta fito aka mayar da ita Wakin nan ta yi salla. Su na tsaye su na jiranta kamar wata fursina, wata matar ce daban, ta shigo ta kawo wa Nana abinci da ruwa pure water.

Nana ta kalli Abincin gasashsen nama ne, amma ta kawar da kai.

"Ki ci abinci mana" matar ta yi magana cikin kulawa.

"Na ?oshi" ta faWa a ta?aice. Babu yadda ba su yi da ita ba, amma ta ?i ci.

Har sai da ran Waya ya Saci, ta fice ta tafi gurin mai maganin.

"Sarkin baka, yarinyar nan fa ta?i cik abinci"

"Ahh haba dai? Ta tashi kenan?"

"Eh tun Wazu har ta yi salla ma"

"Na fa gaya muku yarinyar nan ku lallaSa mini ita, ba na bu?atar a takura mata, ko Sata mata rai. A nemo Salamatu ta tura 'yar aike cikin gari, a samo mata wani abincin"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login