Showing 15001 words to 18000 words out of 190498 words

Chapter 6 - Buzu Book 1 Complete

ciwon naki ya ishe ni wallahi. Can a dangin babarki ki ka kwaso wannan jarabar, ni dangina babu irin wannan"

Ummi ta ce "Baba aka ce mahaifiyar Inna 'yar bori ce "

"In ji uban wa? ?arya ne bayar da magani kawai tayi"

Ummi ta yi murmushi, ta ce "Nana ?araso magana zamu yi"

Nana ta so wucewa Waki, ta kwanta, duk da ta yi murnar zuwan Ummi gidan, amma soki burutsun da Baba ya fara ya sanya duk ta ji komai yayi mata zafi. To idan ubanta mahaifi ya gaza da larurarta ina ga miji, da za su haWu rana tsaka su yi aure?" Ta zauna a hankali, tana jin yadda ?afafuwan nata suke yi mata zugi.

"Yaya magungunan da muka karSo a wurin mutumin nan, kin yi su kuwa?"

Nana ta jinjina kai alamar eh.

"To yaya ki ka ji, akwai sau?i?"

Da ?yar Nana ta ce "Eh akwai"

Baba ya ce "Ina fa wani sau?i, babu sau?i ko kaWan sai wurin Allah. Nan na Waukko malamin nan na almajiran gangare, yayi mata ru?iyya wai aljanun suka ?i magana, ba ki ga dukan da ta ci ba, sai da ta ba ni tausayi amma jiya i yau. Shiyasa duk na damu na aurar da ita, ko na huta. Ai ni wannan zancen da ki ka zo mini da shi, ba ?aramin daWi yayi mini ba, Allah ya tabattar da alkhairi tun da shi wancan ya?i cewa komai".

Cikin mamaki da rashin fahimta, Nana ta ce "Wane zancen ne?"

Ayshercool
08081012143
BUZU
AISHA ADAM (Ayshercool)
Arewabooks Ayshercool7724
Watpad Ayshercool7724

YOTA 002

BRIGHT PENS 3rd batch

P6

Ummi ta yi murmushi, ta tura wa Nana wata leda gabanta. Nana ta kalli ledar, daga saman ledar take iya hango sabulun wanka da man shafawa.

"Saleh ne ya aiko ni, tun ranar da ki ka je gidana, yake bibiyata shi fa son ki yake yi, auren ki zai yi" take Nana gabanta ya faWi, damuwa ta bayyana ?arara a fuskarta ta ce "Anty Ummi, Saleh kuma?"

Baba ya ce "Shi fa, ?anin mijin Ummi ba yaron kirki"

Jiki a sanyaye Nana ta ce "To Baba Auwwal Win fa, da ka ce masa ya turo?"

Sai Baba ya hau faWa ya ce "To ina na ganshi? Tun da na ce ya fito Win ya fito? Da a bawa bare ke, ba gara shi ba, tun da ya san larurar ki, idan aka yi auren ba ruwanmu da kayan Waki, ya Wauke ki ya tafi da ke can Ikkon, wurin neman kuWinsa ba, Waki Waya ya ishe ku kafin Allah ya yassare masa ku tara zuriya ba. Nana wannan iskokan duk aure ki ke bu?ata da kin yi shikenan za su daina damun ki".

Har Nana za ta yi shiru, amma ta kasa ta ce "Baba to idan iyayen malam Auwal Win suka turo fa?"

Ummi ta ce "Nana wai ?anin mijin nawa ne ba kya so ko kuwa?"

Gaddafi da yake gefe, tun da ake maganar bai ce uffan ba, ya na ta faman gyara wata radio ya ce "Ai dama ke Ummi ke ce ki ke tausayin yarinyar nan, ita ba tausayin kanta take yi ba"
Nana ta yi shiru ta rasa abin da yake yi mata daWi, ya ma za ayi Ummi ta yi mata haka, ta ce zata haWa ta da wani Saleh, mutumin da ba nutsuwa ce da shi ba, ga shaye-shaye da yake yi, askin da yake kansa kaWai ya isa ya bayyana maka, abin da yake aikatawa a Lagos Win.

Ummi ta taSa ta ta ce "Nana kin yi shiru"

"To me zan ce, Allah ya zaSa mana abin da ya fi alkhairi"

Baba ya amsa da Amin.

Nana ta mi?e ta nufi Wakinsu, zuciyarta babu daWi, addu'a take yi da fatan, Ubangiji Allah ya sa Auwal ya fito, amma Saleh kam, ba ta tunanin ko me za ayi mata, zata iya aurensa. Dan ko Suleiman da aka fasa aurensu ya fi dama dama a kan Saleh.

Ji tayi jiri yana Wibar ta, dan haka ta samu wuri ta kwanta, ta din ga yi wa Allah kirari, tana magiyar Allah ya daidaita ta da Auwwal ya fito ya turo iyayensa.
Ummi ta le?o tayi mata sallama, amma ta ganta a kwance, ta ce "Nana bacci da yammacin nan, ni dai na tafi, in sha Allah zai zo ku gaisa". Nana na jin Ummi, amma tayi banza da ita. Shikenan dan ana so ka yi aure, sai a ace ka auri mutumin banza.

Ranar dai haka ta ?arasa wunin ranar sukuku, dare ma yayi bacci ya ?aurace wa idanunta, sai wani azababben ciwon kai da ya kama ta.
A hankali ta din ga juyi a kan shimfiWarta, amma babu bacci babu alamarsa, sai wannan ciwon kan, da take jin tamkar ana sara mata kan da gatari.
A hankali kuma ta din ga jin, tamkar ana WaWWaureta da sar?a, ambaton Allah take ?o?arin yi, amma ta kasa sai a zuciyarta.
Ta saka hannun tana laluben hularta, domin ta saka a bakinta ta toshe, kar ta yi ihu cikin dare, ta hana mutane bacci.
Ji ta yi an kira sunanta a tsakar gida, duk da ba ta san muryar ba, amma ta amsa a wahale.
Jin an ci gaba da kiran sunanta, ya sanya ta yin?ura da ?yar ta tashi, kanta babu Wankwali, ta fito tsakar gida neman mai kiranta.
Kallon tsakar gidan tayi, taga duhun ya ninka na dare, ba ta iya gane komai a tsakar gidan. Ta juya don ta koma cikin Waki, amma ta rasa hanya, saboda duhu ba ta ganin komai.
Ji ta yi an ci gaba da kiran sunan ta, kawai ta hau tinkarar wurin da take jin ana kiranta.

Gaddafi yana shagonsa a ?ofar gida, ya ji an buWe gida, ya duba agogon wayarsa, ?arfe biyu saura mintuna tara na dare.
Tashi yayi ya le?o, ya ga Nana ta fito, daga ita sai zani da vest kanta ko Wan kwali babu.
Sai da ya bari ta yi nisa, sannan ya fito ya bi bayanta, a zaton sa ko wani yawon banzan take, sai dai ga mamakinsa kawai tafiya take yi.

Ganin tafiyar ta ?i ?arewa ya sanya ya ce "Ke dan ubanki ina za ki je a tsohon daren nan?" can kamar a wata duniyar, haka take jiyo muryarsa. Ba ta tsaya ba, kuma ba ta yi magana ba, ta cigaba da tafiya.

Dan?o hannunta yayi, ya din ga? jan ta har zuwa gida, sai dai ba ta yi masa musu ba, bin sa kawai take yi, dan ta kasa tantance bacci take yi, ko kuma a zahiri ne.

A tsakar gida ya hankaWa ta, ta faWi ?asa, cikin Waga murya, yake tambayarta gidan uban wa za ta a wannan daren.

Shiru tayi, ta ci gaba da laluben hanya tana ?o?arin tashi. Ya saka ?afa ya hankaWa ta ta sake bajewa a wurin. Wata 'yar ?aramar ?ara ta saki, ta sake yin?urawa za ta fita, wannan karon da azama ta yin?ura, sai dai tamkar ya samu namiji Wan uwansa ya sake janyota yayi jifa da ita.

A wannan karon, ba ta ji muryar komai, sai dai zafin buguwar da take yi.

Baba ne ya fito daga Waki, yana tambayar Gaddafi ko lafiya.

"Wannan mahaukaciyar yarinyar ce, ta buWe gida ta fita a haka, na bi bayanta na kamo ta".

Baba ya ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ni Wallahi lamarin nan na Nana ya ishe ni, kula Gaddafi za ta sake fita". Baba yayi maganar yana nuna masa Nana, da ta kwaso da gudu za ta nufi hanyar fita.
?afa Gaddafi ya saka mata, ta faWi a wurin, amma cikin ?arfin hali, ta sake tashi.
Fizgo ta ya sake yi, ya wanka mata mari har sau biyu. Amma ko gezau ba ta yi ba.

Baba ya ce "Gaddafi daina dukanta, ba fa ta hayyacinta, ba ta san me ka ke yi ba"

"Wallahi ?arya take yi, iskanci ne kawai, buWe idonki ki kalle ni" dan sai a lokacin ya lura duk abin nan idanunta a rufe suke.

"Gaddafi tofa mata abin da ya sauwwa?a, ni tsorona kar ta fita tayi wani wurin ba a sani ba"

"Ni me na iya da zan tofa mata?"

Baba ya ce "Jeka kawai, bari na zauna na ga jikinta ya saki, kar ta sake fita. Dan Allah ko da bacci zai Wauke ni, idan ka ji motsinta ta buWe gidan, ka ri?ota"

"A'a wallahi ban yi alkawari ba, bacci zan yi"

Baba ya ciro zanin mama da yake kan igiya, ya rufawa Nana da take baje a wurin kamar abin banza.

*****
Washegari da safe, Nana sai ha?ura ta yi da zuwa makaranta, saboda yadda jikinta yake yi mata ciwo, dan har targaWe ta yi a hannu. Da safe Jamila take gaya mata abin da ya faru.

Shiru Nana tayi ba ta iya cewa komai ba, ita kanta dan babu yadda za ta yi da ?addararta ne.
?ugin da cikinta yake yi na yunwa bai dameta ba, ta nemi wuri kawai ta kwanta tana goge hawaye a Soye.

*****
Fuskarta babu annuri take kallon mutumin, kamar ta fasa ihu ta ce "Wai kana nufin babu abin da ya sauya kenan?"

"?warai kuwa, komai yana nan yadda yake"

Ta sake tsuke fuska ta ce "Kuma kai babu wani abu da zaka iya yi a kai, gaskiya ba zan iya zuba ido, duk aikin da na yi tu?uru, kuma ace ba zan mori wahalata ba, ba fa zai yiwu na zama a ?ar?ashin ma?iyana ba"

Yayi murmushi ya ce "Bar ganin mu na kauce hanya, akwai abin da bamu isa mu yi wani abu a kai ba, ko kuma mu canza ba, ke za ki yi duk iya ?o?arin da za ki yi, sai mu ga ta Sangarenmu me za mu iya yi. Amma taurarinta su na da haske sosai, duk wanda ya raSe ta, za ta iya haska na su tauraron"

Guntun tsaki matar ta ja, ta ce "Ka ga duba mini wani abun, ka bar maganar nan kawai"

Can gida babu wanda ya matsa Nana ta fito ta yi aikin gida, ita ma kuma ba ta yi ba. Sai dai abin da ya Waga mata hankali, bai wuce yadda ta ji Baba su na magana da Mama da Gaddafi ba, wai akwai wani mai magani a tsanyawa, idan aljanu suka gagara, har kwantar da mutane yake yi, a tafi a bar shi, sai ya warke ya sallame shi. Babu tunanin komai ta ji Baba ya amince, za a kaita. Rasa abin yi ya sanyata fashewa da kuka.

Sallamar Jamila ce ta sanya ta goge hawayenta.

"Nana ya jikin?"

"Da sau?i" ta amsa a hankali.

"Ungo wannan naki ne" tayi maganar tana mi?a mata leda.

Ba ta karSa ba ta ce "Mene ne wannan?"

Jamila ta gyara zama ta ce "Kin tuna ranar da ki ka je kira na, a gidan maman khairat" Nana ta jinjina kai, ba tare da ta yi magana ba.

"Kin tuna matar nan da ki ka gaisar a falo"

"Na tuna"

"To ita ce ta ce a baki, atamfa ce da turaruka, kin san 'yar kasuwa ce"

"Meyasa za ta bani, ta sanni ne?"

Jamila ta ce "A'a ranar da ki ka je ne, ta ga duk kin rikice da kuka gaisa, bayan kin tafi ta tambaye ni ko ta yi miki wani abin ne; na ce mata a'a baki da lafiya ne, shi ne ki ka bata tausayi".

Ita dai Nana ta yi ?uri da ido, tana kallon Jamila. "Nana ki karSa mana, ba a mayar da hannun kyauta baya" ta saka hannu ta karSa ta ce "To na gode sosai" ba dan ta so ta karSa Win ba, ita abubuwan da suka dame ta a yanzu, sun hanata jin daWin komai na duniya yanzu. Ji take yi tamkar ta kashe kanta ta huta kawai.
Kullum cikin addu'a take, babu dare, babu rana, akan Ubangiji Allah ya bata lafiya, sai dai haryanzu Allah bai karSa mata ba. Wasu lokutan har shagala take da ro?o lahirarta, saboda yadda take fatan lafiya ido rufe, sai dai idan ta tuna ta yi ta istigfari.

*****

Ranar laraba, ta shirya ta tafi makarantar da take koyarwa, sai dai zuwanta ke da wuya, aka sanar mata da director yana son ganinta.
Ta san a rina, dan haka ta tsananta addu'a, ta nufi ofishin nasa.
Ta tarar da shi tare da wani babban mutum, zaune kirim a kan kujera. Ta gaida mutumin ba tare da ta kalle shi ba, ba kuma ta jira ya amsa ba, ta gaida director.
?an ?aramin yaron da yake zaune a jikin mutumin, ya saukko daga jikinsa, cikin gwarancin yara, ya nufo Nana yana faWin "Anti Nana" Wagowa ta yi tana murmushi, dan gaba Waya da ta shigo, hankalinta ba a jikinta yake ba, dan haka ba ta lura da yaron ba ma. Ta buWe hannayenta ta rungume shi.

Director ya ce "Kin ga wannan sha?uwar taki, da yaran nan ne, ya sanya haryanzu ban sallame ki ba daga makarantar nan. Babu wadda take iya Waukar rigimarsu kamar ki, amma ki na ta wasa da damarki. Kwata-kwata yaushe aka dawo makarantar da har za ki yi fashin kwana biyu, ba tare da kin sanar da hukumar makaranta ba?"

Cikin nutsuwarta da kamala ta ce "Dan Allah sir ka yi ha?uri, ba ni da lafiya ne, ba a son raina na yi fashi ba"

A ?ule ya ce "Wai wace irin rashin lafiya ce haka, da kullum ba ki da lafiya, idan ba zaki iya ba, ki ajiye aikin mana dole ne?"

Mutumin da yake zaune ya ce "A'a ba za ayi haka ba, ayi mata uzuri musamman duba da yaranmu suke ?aunarta. Ka ga ba zuwa makarantar nan nake yi ba, na fi shekara rabon da na zo, amma na san Anty Nana a bakin Muhsin, duk abin da yake yi, idan aka ce za a gaya mata sai ya daina. Ina nema mata afuwa dan Allah"

Director ya ce "Alhaji ba zaka gane ciwon kan da yarinyar nan take bamu ba. She's very hardworking lady, yarinya ce mai ?o?ari da juriya, amma wannan fashin nata, kullum cikin ciwo shi ne yake Sata mini rai wallahi"

Mutumin ya kalli Nana ya ce "Anty mene ne rashin lafiyar taki ne?" Nana tayi shiru ta rasa abin cewa. Bai damu ya sake tambayarta ba ya ce "Kuma ki na zuwa asibiti?" Ta jinjina kai alamar eh.
"Allah ya sarki, to Allah ya baki lafiya yanzu dai ki tashi ki je, na ro?a miki afuwa " Nana ta sake risunawa cikin girmamawa ta ce "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi"
Director ya ce "Tashi ki tafi" ta tashi jiki a sanyaye, hannunta ri?w da na Muhsin, da bakinsa ya?i rufuwa yana Wagawa babansa hannu.

Duk da ranta ba ya son faWan da ake yi mata, yanzun ma ba ta ji daWin faWan ba, amma da tuna laifinta ne, haka nan ta ha?ura, ta danne damuwarta ta shiga cikin Walibanta, tare da ?o?arin samarwa kanta nishaWi da nutsuwa tare da yaran.
Amma sai ya zamana ya?e kawai take yi, ?asan zuciyarta tamkar ta fasa ihu, ga batun kaita gidan mai magani, duk da ba a kuma zancen ba, ga kuma maganar Saleh, ga malam Auwal ya juya mata baya baki Waya.

Da ta dawo daga makaranta, ta yi sa'a, ta tarar da wata guntuwar shinkafa, an ajiye mata, sai dai ko maggi babu, ta barbaWa gishiri, ta ci ta tafi islamiyya.
Duk da ta san tayi sammako da yawa, hakan bai dame ta ba, saboda zaman gidan na su ne ba ta so, bata ?aunar duk wani abu da zai ?ara dagula mata lissafi.
Kamar yadda ta saba, ta share duk wuraren da taga zata iya sharewa, ta shiga wurin ajiye tabarmi, ta hangi Auwal a cikin ofishin malamai, yana duba wasu litattafai. ?auke kanta ta yi, kamar ba ta ganshi ba, ta shiga ta Waukko tabarmar 'yan ajinsu, ta fito.

Ba ta sanya ran zai kula ta ba, dan sati guda kenan, ko gaishe shi ta yi, sama-sama yake amsawa.

"Nana" ya kira sunanta ba tare da tayi tsammanin haka ba, ta waiwaya tare da tunanin ko ba shi ba ne ya kirata. Amma ta ga yana kallonta, tabbacin shi ne yake kiranta. Sharewa tayi, ta fice ta tafi ajinsu.

Tana tsaka da shimfiWar tabarmin ya shigo ajin, ya ce "Nana, ki na ji ina kiran ki ki ka yi share ni, Yaushe ki ka zama haka?" Ta mi?e sosai tana kallonsa, ta haWiye wani abu mai Waci da ya tsaya mata a ma?ogwaronta.

"Me yasa ba ka yi wa baba bayani ba, kuma ka hanani na yi masa; cewar kai malamina ne ba wanda yake so na da aure ba? Dama ka ce tausayina ka ke ji, ni kuma kasancewar wanda yake ruwa, ko takobi aka mi?a masa kamawa zai yi, na kawar da tunanin komai, na fara sonka ina tunanin ko yaya zan samu afuwa. Amma sai halayenka suka sha banban da abin da ka ke koya mana. Ina ma baka ce ana so na ba, na ci gaba da kallonka a matsayin malamina mai tausayina.

Jiki a sanyaye cike da borin kunya ya ce "Ki yi ha?uri Nana, na san ban kyauta miki ba, babu yadda zan yi ne, matsala aka samu, na rasa ta yadda zan yi miki bayani. Ina ta ?o?arin shawo kan matsalar ne, amma ban ce ina sonki dan na yaudareki ba, ko na yi wa mahaifinki wasa da hankali ba".

Shiru ta yi masa, ta ci gaba da gyara tabarmin, dan ba ta ma san meyakamata ta sake ce masa ba.

"Nana, ki Wan bani lokaci kaWan, ina daf da shawo kan matsalar"

"Tom" ta faWa a ta?aice, ba tare da ta ko kalle shi ba. Bai taSa zaton Nana tana fushi har haka ba.
Ya kalli yadda take ta jan tabarmin, ba tare da wani dalili ba, ya dur?usa a kusa da ita ya ce "Kalli ki ga" ta Waga kai ta kalle shi.
"Tabarmar ta shimfiWu haka, ba ita ta yi miki laifin ba, ni ne amma ki yi ha?uri"
Ta kalle shi da idanunta, masu kama da za ta yi kuka, har za ta yi magana, sai kuma ta haWiye ta fasa.
"Kin ha?ura?" Yayi maganar yana tsareta da idanunsa shi ma.
Murmushi ta yi, ba tare da ta shiryawa hakan ba.
Shi ma murmushin yayi mata ya ce "Barakallahu fik, ki ci gaba da yi mana addu'a, in sha Allah komai zai daidaita amaryata".
Sunkuyar da kai ta yi, bakinta ya kasa rufuwa saboda murmushi.

"Ya jikinki, ina fatan ki na kula da duk adduo'in da nake baki"

Ta jinjina kai ta ce "Eh, ina yi"

"Yauwwa ki ci gaba da kula, Ubangiji Allah ya baki ingantacciyar lafiya"

"Amin na gode sosai" ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login