Showing 3001 words to 6000 words out of 190498 words

Chapter 2 - Buzu Book 1 Complete

(YOTA)

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Arewabooks
Ayshercool7724

P2

Kiraye-kirayen sallar magariba ake yi, Baba ya shigo gida da nufin ya yi alwala ya tafi masallaci.

"Nana, Nana"

"Baba ba ta dawo ba fa" matashin yaron da bai wuce shekara goma sha biyu ba ya bashi amsa.

"Ba ta dawo daga ina ba?"

"Makarantar islamiyya"

"A yanzun da magaribar nan, ke Jamila, Sa'adatu wai kuna ina ne ina ta magana kun mayar da ni mahaukaci?"

Jamila ce ta fito tana yamutsa fuska ta ce "Baba ba ta dawo ba fa"

"To tana ina? Ina ta tafi? Ko an aiketa ne?"

Rabi ce ta fito ta ce "Wai Nanan yarinyar goye ce ne da ka ke ta wannan ha?ilon saboda ita? Idan ta gama yawon nata za ta dawo ai"

Guntun tsaki ya yi ya ce "Kai sani da aka tashe ku daga islamiyyar ba ka ganta ba?"

Sani ya ce "Ban ganta ba, kuma mu ne ?arshen tafiya, yau na makara aka sakamu kwashe butocin alwala muka gama aka kulle makarantar"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba bankaWawa ta yi, tayi wani wurin ba"

"Ko kuma yawon watsewa ta tafi ba"

"Allah ba zai nuna mini watsewa a kan 'ya'yana ba" yayi maganar yana ficewa daga gidan.

Nana kuwa tun da ta fita daga islamiyyar, babu wanda ya ganta, dan haka ta ci gaba da tafiya ba tare da ta san in da take sanya ?afafuwanta ba, ba ta iya tantance rana ce ko dare ma, sai dai tana jin yadda zafin rana yake ratsa ?afafuwanta da kuma tafin ?afarta, da take takawa babu ko takalmi. Ita dai burinta ta yi nesa da in da take, ko ta fita daga halin da take ciki, ko kuma tserewa abin da take jin tamkar ajalinta ne yake tunkarota.

Wani matsakaicin gida ta tunkara, babu sallama babu neman izinin masu gidan, kawai ta afka ciki. ?aya daga cikin jerin Wakunan ta shiga, ta cire hijjabin jikinta na islamiyya, ta cukuikuye shi, ta yi fulo da shi, ta kwanta.

Kusan mintuna goma sha biyar, da shigarta babu motsin kowa a gidan. Wani matashi ne yayi sallama, ya ji shiru, ya sake sallama ya ji shiru.

Saka kai yayi ya shiga ciki yayi tozali da Nana a kwance tana bacci. Turus yayi yana kallonta, yana tunanin ita kuma wannan daga ina.

ShaiWan ne ya shiga ?awata masa kyakkyawar ba?ar fatarta mai she?i, da kuma ilahirin jikinta.

A hankali cikin sanWa ya shiga Wakin, yana cigaba da ?are wa ?irjinta kallo.

?an dukan gefen carfet yayi, dan ya tabattar da idonta biyu ko bacci take yi.

A hankali yake ?o?arin kai hannu jikinta, kwatsam! Ya jiyo muryar matar gidan a ?ofar gida tana gaisawa da ma?wabta.

Cikin hanzari yayi baya ya dawo tsakar gida ya tsaya.

Sallama tayi tare da yara ?anana, ya amsa yana mazewa.

"Saleh, zuwa babu sanarwa haka?"

Ya Wan sosa kansa ya ce "Wallahi kuwa, ina ta sallama amma gidan shiru babu kowa"

Ta kalli gidan ta ce "Ikon Allah, kuma yarinyar ma?wabta na bari a gidan, ta jire mini na je Waukko su hafsa daga makaranta shi ne ta bar mini gidan a buWe haka?"

Saleh ya ce "Aikuwa ta yi ganganci da ta bar miki gidan babu kowa haka"

"Aikam yaushe ka shigo garin ne?"

"Shekaranjiya da daddare na ce yau bari na Sullo mu gaisa"

"Aikuwa ka kyauta" ta yi maganar tana Waga labulen Wakin.

Turus tayi, tana maimaita"Innalillahi wa innalillahi raji'un" ganin mutum a kwance.

Ya kalleta ya ce "Lafiya kuwa?"

Ba ta amsa masa ba, ta ?arasa tana ?are mata kallo, ta kai hannu ta taSa ta ta ce "Nana" sai dai shiru ba ta amsa ba.

Ta kalli ?afafuwan Nanan, futu-futu, har da jini alamar ta taka abubuwa a hanya.

"Subhnallah, kar dai da ?afa ta taho Nana, Nana tashi mana" sai dai ba ta motsa ba.

Cikin basarwa Saleh ya ce "Anty lafiya kuwa? Wace wannan Win dama da mutum a gidan nake ta sallama ba a amsa ba?" Yayi maganar yana ?are mata kallo, dan shi gaba Waya ma bai lura da raunin da yake ?afarta ba.

Anty ta ce "?anwata ce wallahi, ba ta da cikakkiyar lafiya ne, ga wayata ta lalace balle in kira gida in ce tana nan, kuma ni Wallahi ban haddace lambar kowa ba, balle na kira na gaya musu"

Suka ci gaba da jimantawa, Nana kuwa ta ci gaba da baccinta, mai kama da suma.

Baba yayi sintiri zuwa islamiyyar su Nana babu adadi, tun yana yawon neman ta har ya gaji.

Suwaiba ta ce "Wata?ila mutanenta ne su ka yi wani wurin da ita"

"Ba wasu mutanenta, ayi ta fakewa da sheWanu tana rashin mutunci, ta taSa yin irin haka ne? Allah ne kaWai ya san gidan uban wanda ta tafi"

Baba ya ce "A'a ba na tunanin za ta je wani wurin ba mu sani ba, tun da ba ta taSa yin hakan ba, amma ina Jamila ma?"

"Ta na gidan uwa Wakkinta Win nan, maman khairat, tun azahar tana can"

Baba ya ce "Kuma haryanzu goma saura na dare, ba ta gida uban me take yi a gidan mutane?"

Mama ta ce "A'a yau na ga abin tsiya, to malam ba abincin safe babu na rana, ba dole yarinya ta tafi in da za ta samu ta ci ba? Ai gara ita an san in da take, 'yar ka fa? Shi ya yi nasa wuri, ita ma gashi ta kama gabanta" Baba yayi shiru bai sake cewa komai ba.

Shirun sa ke da wuya, Jamila ta yi sallama, suka amsa baki Waya, Baba ya Waga kai zai yi magana, sai yayi shiru ganinta da babbar leda.

"Mama na dawo"

"Sannu jamila, ya ki ka barota?"

"Lafiya kalau Alhamdilillah, baba sannu da gida"

Baba ya ce 'Yauwwa Jamila, amma ina ki ka tafi haka ba kya gida?"

Jamila ta taSe baki ta ce "Baba Allah ya gani na gaji da raragefen shiga banWaki ne, ga yunwa ina ji shi yasa na tafi gidan maman khairat na wuni a can"

Baba ya ce "Ku yi ta ha?uri ku na addu'a, in sha Allah za a gyara katangar nan, kuma a gyara masan, mutanen unguwar nan ne ma, babu haWin kai da zuciyar taimako, amma yadda iftila'in nan ya afko mini, ai kamata yayi ayi gidauniyar da za a tallafa mini"

Mama ta ce "Kai wa ka ke tallafawa idan matsalarsa ta tashi?"

"Rabi wai babu damar na yi magana, sai ki nemi tozarta ni a gaban yara"

Ta girgiza kai ta ce "Ba wani tozarci gaskiya ce"

Bai bi ta kanta ba, ya kalli Jamila ya ce "Jamila, Nana fa ba ta dawo gidan nan ba, tun Wazu ake neman ta ba a ganta ba" Jamila ta tsaya da juye abincin da take yi ta ce "To ina ta tafi?"

"Wallahi ban sani ba, an rasa in da ta shiga "

Jamila ta ce "Kuma ita ba waya ba, balle a kira ta kuma dai na ga ba ta taSa yin irin haka ba"

"Wallahi kuwa. Kai Sani Waukko kwano a zuba mini abincin nan nima na saka a cikina, dan rabona da abinci tun safe, ashe akwai sauran masu zuciyar taimako a unguwar nan, irin wannan abinci haka Jamila"

Haka Baba ya karkace aka lamushe abinci da shi, har ya nemi ya manta batun Satan 'yar sa Nana.

*****
Misalin ?arfe tara na safe, Nana ce a zaune, tana kurSar kunun tsamiya, duk da babu sukari a cikinsa, amma ba ?aramin daWi yake yi mata ba, ga dankali da aka take mata kwano da shi, wanda rabonta da ta ci ta ?oshi haka har ta manta.

Ummi ta dube ta ta ce "Nana, wai garin yaya aka yi ki ka taho gidan nan a ?afa haka? Tun jiya kin ?i magana"

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban san ya aka yi ba, ni dai kawai ina islamiyya na ji duniya ta yi mini zafi, kamar zan mutu shikenan ban san meyafaru ba, na dai ji ina bacci, kawai na farka na ganni a nan"

Ummi ta ce "Ohh wannan larura taki Allah ya yaye miki Nana, an gode Allah ma da ki ka yo nan ba wani wurin ki ka yi ba, in ?ara miki dankalin ne?"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a na ?oshi Alhamdilillah"

"Nana ina kyautata zaton mutanen nan ne, suka hana miki samun mijin aure har yanzu, ga Habibu, rumi-rumi an fara magana aka fasa, ni a yanzu ma akwai wani a ?asa kuwa?" Nana ta girgiza kai alamar a'a.

"Wallahi Nana ina yi miki fatan ki yi aure, ki bar wannan gidan namu, da ba a iya amfana maka komai, idan ba uwarka ce ta yi maka ba, kin ganni nan duk da yau da daWi gobe babu, yau mu ci gobe mu yi ha?uri, ga azabar dangin miji, amma ya fiye mini wannan gidan namu, da kamar a cikin sa aka yi wahayin babu, ke kanki a yunwace ki ke, ga Baba ya damu ki yi aure, dan Allah kalli wata breziya a jikinki, dan masifa duk kin ?u??uleta, wallahi da na shiga banWaki na tarar da phant Winki, na za ta tsumma ne da yarwa zan yi, wannan wace irin rayuwar azaba ce?"

Nana ta sunkuyar da kai ta yi shiru, dan duk abin da ummi take faWa gaskiya ne, amma waye zai aureta da wannan larurar a haka? Malam Auwal na islamiyyar su, na ta nuna mata alamar soyayya amma ta yi burus, dan ta san yau da gobe sai Allah, babban fatanta ta rabu da wannan larurar, duk da tana burin yin auren, dan ita kaWai ta san masifar da take ciki.

"Kin san wani abu Nana, akwai wani mai magani da na ji ma?wabciyata su na magana rannan, zan yi mata magana ta kwatanta mini wurin, anjima mu kama hanya mu je ko Allah ya sanya a dace, daga nan na je na duba idan an gyara mini wayata sai na raka ki gida"

To kawai Nana ta iya cewa, ta cigaba da shan kununta a hankali.

*****

"Alhajin Allah"

"Na'am malam" ya amsa yana tattara nutsuwarsa a kan mutumin da yake zaune, a kan tabarma, gefensa ga carbi mai dubu, ga wani Wan farantin katako da ?asa a kai. Yayi shiru ya na nazartar ?asar da ya yi wa zane-zane a gabansa.

"Malam me ka gani ne?"

"Eh to, bu?ata zata biya Alhaji Zailani, amma gaskiya za a sha gwagwarmaya, ga magauta ko ta ina a tattare da kai, arziki zai ninku fiye da yadda ka ke zato, amma gaskiya zaka sha wahala, ?ila ma ka iya rasa ranka, kuma a gidan huWu ga wata kujerar siyasa nan ko ta mulki da zaka iya samu, sai dai gidan uku ya nuna shi ma akwai bala'i, da tarin ?alubale"

Alhaji zailani ya yakice gumin da yake tsatsafo masa daga goshinsa ya ce "Yanzu malam menene abin yi, dan ko a yanzu kasuwancina harkokin sun fara ja da baya"

Ya sake zazzana ?asa, ya Wago ya ce "Eh ga wani ?ulli nan a binne a kusurwa huWu na mararraba, a kanka, amma warware wannan ba zai yi wahala ba, yanzu mafita Waya ce da za a samu mai burujin a?rabu, ko hutu ko surdanu da zai dace da burujin ka, kuma za su taimaka maka ka kai ga ci, ba tare da ka fuskanci ?alubale ba"

Alhaji Zailani ya tattara hankalinsa, ya gyara zamansa ya ce "Malam Gambo to tayaya zan gane su, kuma a ina za a same su, ko nawa ne zan bayar a samo"

"Ba samo su za ayi ba, ka samu mace mai Waya daga cikin waWannan burujan, ka kwanta da ita, zaka samu buWi ta in da ka zata da in da baka zata ba, taurarinta za su haskaka naka da suke ?o?arin disashewa, sannan za ta Wauke wannan wahalar da zaka sha, kafin ka cimma muradinka"

Ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "In dai mata ne gasu nan kamar jamfa a jos, tayaya zan gane wadda ka ke nufi?"

Malam Gambo ya numfasa ya ce "Wadda namiji bai taSa kusanta ba ake so, kuma idan aka samo ta sai na duba ranar sa'ar burujanku. Kuma ba a fuska za a gane mai irin tauraron da nake faWa ba. A samo mai suna Nadiya, ko Wausiyya, ko badariyya"

Alhaji zailani ya ce "Ni yanzu malam ina zan samo waWannan sunayen?"

"Bincikawa za ka saka ayi, ko Asma'u ma zai yi, amma shi ma da sharaWi, idan aka samo Win sai na lissafa adadin sunanta da na mahaifiyarta na tabattar da haWuwar aikin"

"Shikenan malam, in sha Allah zan yi iya ?o?arina, zan samo in sha Allah, ga wannan ba yawa" yayi maganar yana ajiye masa kuWi a kan shimfiWarsa.

*****

Ummi ce ta kalli Nana a Wan fusace ta ce "Wai nu?u-nu?un me ki ke yi ne haka Nana?"

"Wallahi Anty ummi ba na son zuwa wurin maganin nan ne, idan ki na da ni?ab ki bani na saka, kar na je wanda suka sanni su ganni"

She?e?e ummi ta kalli Nana ta ce "Au to sai me, ba neman lafiya ki ka je ba, duk wanda ya ce ya sanki shi uban me ya kai shi? Ki wuce mu tafi dan Allah"

Jiki a sanyaye Nana ta bi Ummi, sai dai gaba Waya ranta babu daWi, sai dai ta wani Sangaren tana ?arfafar zuciyarta a kan wata?ila ta dace da maganin.

Ma?il suka je suka tarar da gidan mai maganin, tamkar ana rabon gafara, mata ne suke ta shiga suna fita.

Suka samu wuri suka zauna, wasu a shigo da su a rirri?e, wasu kuma da ?afafuwansu. Ga manyan mata masu shigar alfarma da kuma yaku bayi.

Wasu na ta tumamin iskokai, wasu na kwancez Nana dai ta raSe ta yi shiru a gefen ummi, kasancewar Ummi ba halinsu Waya da Nana ba, tuni ta saki jiki suna hira da matan wurin, wannan ta ce matsalar yara ce ta kawota, wannan ta ce matsalar miji, wasu kishiya wasu larura, wasu su ce mayu ne suka kama su, wasu kuma matsalar rashin mijin aure ne ya kaisu.

Nana ta din ga nazarin matsalolin daki-daki, ita a tunaninta matsalar rashin lafiya ce kawai za ta kai mutum wurin mai magani, wadda suke samun saSani da miji maganin me za a bata, ban da ta kai wa Allah kukanta?

Ummi da wayo da dabara, da iya daWin baki da hira, ta yi wa matan nan wayo, ta ce Nana zata shigar a gani ba ta da lafiya, kwananta uku ba ta magana, kasancewar tun da suka zo ba ta ce uffan ba.

A tsanake yake ?are masa kallo, yadda ya zauna ya tan?washe ?afafuwansa, yake ta wasa da yatsun hannunsa, ya?i Wagowa su haWa ido.

Ya mayar da idanunsa kan Habu, da yayi shiru yana jiran bayani daga bakin mutumin.

"Wannan ciwon nasa gaskiya ba zan Soye maka ba, idan na matsa ni zan shiga matsala, sai dai ku bincika wani wurin"

Cikin damuwa Habu ya ce "Yanzu babu yadda za ayi ace ko sunansa ya tuna? Ya san duk wani abu da ya shafi rayuwar yau da kullum, amma ya manta duk wani abu da ya shafe shi"

Mutumin da yake zaune a kan sallaya, "Ka san wa ka kawo mini kuwa? Anya ka san waye?"

"Na sani" Habu ya amsa cike da ?warin gwiwa, cikin gurSatacciyar hausar sa"

Mutumin yayi murmushi ya ce "Ka san dai abin da ka sani, ka bar shi a haka kawai kar ka matsa sanin abin da yake a Soye" jiki a sanyaye habu ya kalle na zaunen ya ce "Tashi mu tafi" ya yin?ura ya tashi, ya tsaya ya kalli malamin ya saki murmushi ta cikin rawaninsa suka fice.

Babu tsammani Nana su na tsaye a ?ofar shiga wurin mai magani, wasu mutane suka fito, ?afafuwansa kawai ta kalla ta ji jikinta ya saki, zuciyarta ta tsinke ta sulale za ta faWi a wurin, Ummi ta ri?e ta da sauri tana salallami.
A hankali Nana ta bi bayansa da kallo kasancewar ya riga ya wuce, zuciyarta ce ta raya mata ta bishi da gudu ta ga waye, daina ganin kowa ta yi sai itakaWai a cikin sahara, sai kuma shi wannan mutumin da ba ta ga kowaye ba, yana tafe yana jan akalar ra?umi ya yi nesa da ita, tana hango shi a can nesa sai kuma manyan sawayen ra?umin da nasa.

"Nana" ta ji muryar ummi a kunnenta, ta buWe ido ta kalle ta a hankali ta kalleta.

"Sannu Nana kin tashi" ba ta amsa ba ta Waga kai ta gansu a gidan Ummi.

"Anty yaushe muka dawo?"

Ummi ta ce "Hmm tun Wazu, ai tun kafin mu shiga wurin mai maganin, ki ka sume, ya ce manyan dakarun aljanu ne a kewaye da ke, mu na shiga ya gansu"

Cikin mamaki Nana ta ce "Ya ga su wa?"

"Aljanun mana" ta bata amsa cike da ?warin gwiwa.

"Dama mutum yana iya ganin aljani a suffarsa?"

"Ban sani ba, tambaya dawanau, yanzu ga magunguna nan da haya?i kowane zan nuna miki yadda za ki yi amfani da shi, ki ci abinci muje na raka ki gida" Nana ta jinjina mata kai kawai, amma bakinta akwai tarin tambayoyi.

Da yamma Ummi, ta taso Nana a gaba domin ta rako ta gida. Ko da suka je gidan, mamaki ne ya cika Nana, ganin an zube kayan aikin gini a ?ofar gidansu, a iya tunaninta Baba ba shi da wata hanyar da zai samu kuWaWen da za ayi musu wannan gyaran.

"Nana, haka gidan ya koma? Ummi ta yi maganar cikin mamaki.

"Eh, sai ma kin shiga, rijiya ta haWe da masai, amma na ga an kawo kayan aiki ban san a ina aka samo su ba"

Da haka suka shiga gidan da salallama, Suwaiba da take wanke-wanke ta Wago ta kalle s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????u, ta ce "Too yau kuma Allah ya yi miki dawowa daga yawon kenan?"

Ummi ce ta ce "Wane irin yawo kuma?"

But Mama ta fito daga Waki ta ce "To ina ta tafi idan ba yawon ba? Wa ta gaya wa za ta je wani wurin? Kwana biyu babanku ya hana mu sakat, saboda ba a ganta ba, ana ta cigiya a unguwa, dama na gaya masa wani wurin ta yi"

Har Ummi ta Wauki numfashi za ta yi magana, Baba ya yi sallama.

Suka amsa masa baki Waya, baki sake ya bi Nana da kallo, ya ce "Nana daga ina ki ke? Ina ki ka tafi baki gaya mini ba? Ko wurin uwartaki da ba ta san muhimmancin ki ba ki ka wanke ?afa ki ka tafi?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "Haba Baba, dan Allah ka tsaya ka ji mana, ka san halin da take ciki na rashin lafiya, shekaranjiya na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login