Showing 75001 words to 78000 words out of 190498 words

Chapter 26 - Buzu Book 1 Complete

ce "Ki yi ha?uri Hajiya, kin san komai rabo ne, kuma Allah ya fi mu sanin abin da ya dace da mu. Ko kin bar duniya in dai Wan Adam zai rama halacci ire-irena da yaran da ki ka ri?e, za su yi miki addu'a. Kar ki manta ba ke kaWai ba ce uwar mumunai Allah ya ?ara mata yarda, ba ta samu haihuwa ba amma uwa ce ga dukkanin muminai, a rashin samun haihuwar nan, ke ba ki san me Allah ya tanadar miki ba, wanda bai bawa waWanda suka haihu ba" kai tsaye kalaman Nana suka din ga shiga zuciyar Hajiya Amina, da sai da hawaye ya cika mata ido. Ta ji daWin kalaman Nana, na ?warin gwiwa, ta yi mamakin yadda Nana ta iya tsara maganganu cikin hikima.

"Na gode sosai Nana, kin ?ara sawa na ji nutsuwa, Allah ya ba ki zuriya ta gari. Ka da Allah ya jarrabe ki da ?addarar rashin haihuwa. Duk ta tawakallinka, akwai gaSar d???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a mutane mussaman 'yan uwanka mata sun saka ka ji tamkar ba ka da amfani."

"Amin na gode sosai Hajiya. Amma ta ki jarrabawar ki ka sani, da wata jarrabawar gara rashin haihuwa sau dubun dubu" haka su ka din ga hira da Hajiya Amina, har lokacin tafiyar ta ya yi.

Tana shirin tafiya, Shukura ta dawo, Haidar yana kallonta, amma bai damu ya je gurinta ba, ya rirri?e Nana yana cewa zai bi ta ta tafi da shi ba. Da ?yar ta lallaSa shi, ta fita.

Habu na ganinta ya taso zai buWe mata gate, ya ce "Malama har kin taso?"

Nana ta ce "Eh malam Habu, shekaranjiya na zo zan fita, duk ba kwa nan"

"Eh wallahi mai gidan nan ne ya aike mu"

Ta ce "Allah sarki, yauwwa dan Allah ina wannan Wan uwan naku?"

Habu ya ce "Wanne daga ciki?"

"Wannan Win nan"

"Ya sunan shi?"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ban san sunansa ba, Waya Wan uwan naku dai Sule ya ce mini ba shi da cikakkiyar lafiya, kurman nan" Habu ya kwashe da dariya ya ce "Kayya ba kurma ba ne ba yana magana"

Ta ce"To ai shi kullum baya magana, fuska a rufe kamar amarya. Shi ya buWe mini ?ofar ranar na fita"

"Allah sarki, yana gane komai, kawai da larura ce a ?wa?walwarsa, ba kuma wai hauka yake yi tuburan ba, wasu lokutan ma sai ya shafe sati bai ce uffan ba, yana kwance ma ba lafiya"

Cikin tausayawa Nana ta ce "Allah ya sauwwa?e, na tafi sai da safe"

"To sauka lafiya, Allah ya tsare" ta amsa da Amin ta tafi.

?oye wayarta ta yi, saboda ta san tsaf Baba zai ?wace wayar nan, mussaman yanzu da yake neman kuWi ido rufe.

Bayan Nana ta koma gida, Jamila take tambayarta ashe sun haWu da Hajiya Sa'a a gidan rasuwa, amma ta ce ba ta santa ba.

Nana ta ce "Ina cikin jimami da alhinin mutuwar yaron ne, shiyasa na kasa gane ta"

Jamila ta ce "Allah sarki, ashe yaron ma sunanki ya yi ta kira kafin ya rasu"

Nana ta kalli Jamila daga sama zuwa ?asa ta ce "Wannan karon ma ni na kashe shi ko?" Ta yi magana tana tsare Jamila da ido.

Jamila ta ce "A'a ni ban ce ba, kawai labari fa take bayarwa"

Nana ta gyaWa kai cikin gargaWi ta ce "Jamila ina son hawainiyar matar nan ta kiyayi rama ta, idan ta ci gaba da ?o?arin cin iyaka ta, za ta faWo cikin wutar da za ta ?ona ta da ita da amfanin gonarta, wannan sa?ona ne a gare ta." Saroro Jamila ta yi cikin tsoro, jin yadda Nana take magana kamar an sha?e ta.
Kamar kuma wadda ta razana a cikin bacci, jikin Nana ya Wan yi girgiza sannan ta ce "Jamila yau wainar fulawa nake sha'awa, zan sai fulawa ki sai mana manja, mu soya mana" da yake sun saba yin haka.
Jamila kawai ta jinjina mata cikin tsoro.

Da daddare Jamila ta samu Nana tana shirin kwanciya bacci ta ce
"Nana wai Hajiya Sa'an wani abun ta yi miki ne, ki ke cewa na yi mata kashedi?"

Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wace ce Hajiya Sa'a?"

"Wadda ku ka haWu a gidan rasuwa"

Nana ta ce "A'a wani abin ta ce na yi mata?"

"A'a to ai ke ce ki ke cewa na ce ta kiyaye ki, kuma babbar mace kamar wannan shi yasa na tambaye ki"

Nana ta waro ido ta ce "Ni babu abin da ta yi mini, ni fa ko magana ban yi mata ba, me ta yi mini zan ce ta kiyaye ni?" Sai a lokacin Jamila ta fahimci kamar Nana ba ta san ta yi maganar ba sai ta ?yale ta.

Ranar da aka bawa Nana albashi, kamar ta taka rawa, ganin ta mallaki dubu ashirin ta ta, ta kanta. Ga dubu ashirin da Alhaji Zailani ya ce a bata, baban Haidar kuma ya ce a bata dubu goma, sai da ta tashi da dubu hamsin. Iya salarynta ta yi murna da shi, wanda aka ce Alhaji Zailani ya bata kuwa, ji ta yi tana ?yan?yamin su.

Da murna ta nufo gida, tana tunanin wace bajintar yakamata ta yi a gida, yadda kowa zai amfana.
Amma tana zuwa Baba ya turke ta da bala'i "Wai Asma'u ba za ki ?u?uta a samu komai a hannunki ba? ?anin uban yaron nan ya kira ni a waya, yana idan ba zan dawo da kuWin ba, hukuma ce za ta raba mu, ba ki da asara ko a jikin ki ko?"

Nana ta saka hannu a aljihun rigarta, kasancewar kuWin dubu goma goma ne, ta ciro uku ta bawa Baba ta ce "Baba wannan ne kawai a hannuna, nima yau aka biya ni albashi".

"Yauwwa ko ke fa, ba zan taSa su ba kiran su zan yi su zo su karSi abin su, duk da koma me aka yi mini ke ce sila, da kin ha?ura kin kwantar da hankalinki shikenan, amma mugun halinki ya sanya ki ke ta yi wa yaron nan wula?anci, yanzu kalli halin da ki ka jefa mu" Nana ta daina mamakin ?arfin hali da son kai irin na Baba, sai dai ta yi shiru ya gama surutansa ta tashi ta tafi.

Abu kamar wasa, ?aramar magana ta juye zuwa ga babba, domin kuwa Saleh cewa ya yi ba zai karSi dubu talatin ba, dan ko kwatan abin da ya kashe ba a ba shi ba. Dan haka ya kai Baba police station.

Haka aka turo jami'an tsaro, suka tisa ?eyar Baba zuwa gurin 'yan sanda. Sai Gaddafi aka nemo, ya bi bayan su.

Gaddafi ya kalli Saleh, ya ce "Yanzu kai Saleh saboda rashin ta ido, ka rasa wanda za ka kawo gurin 'yan sanda sai mahaifina, saboda rashin kara, ko dan zaman amanar da muka yi a ikko, ga yayanka na auren ?anwata."

Saleh ya ce "Ka ga malam, a batun kuWi babu wata kara, yarinyar nan ba ?aunata take yi ba, har tana neman hallaka ni, ban aure ta ba zan bar muku kuWina ne?"

Duk yadda a ka yi da Saleh a yi sulhu, amma ya ?i yarda, sai da aka yi yarjejeniya, cewar nan da kwanaki uku za su kawo kuWinsa gaba Waya a ba shi".

Ranar yau na Waya daga cikin ranakun da Nana, ba za ta iya mantawa da su ba, domin bayan dawowarta gida, Baba ya din ga yi mata bala'i tamkar zai tsine mata, har da cewar ya yi dana sanin haihuwar su da Wan uwanta, ya yi dana sanin haWuwa da mahaifiyar su har ya aureta ta haife su".

Gaddafi ya ce "Dan Allah Baba ka yi ha?uri ka yi shiru haka mana, sai Waga murya ka ke yi duk ma?wabta su na jin ka, kuma ka na ta cewa ta nemo kuWi a biya, ka san dai ba wata sana'a take yi ba, idan kuma ba hanyar banza ka ke son ta shiga ba"

Cikin takaici Baba ya ce "Ka bar ni Gaddafi, ban taSa haifar Wan da yake neman ya yi ajalina ba kamar Nana, da me zan ji ne? Ba ta tausayina ko kaWan duk wata hanya da zan bi na aurar da ita, ta nutsu nima na nutsu ta ?i, a dalilinta a ka kai ni station a ke nema a rufe ni. Lokacin da aka haife ki babu farin cikin da ban yi ba, na so ki, amma kina neman ki kashe ni. To wallahi idan kuWin nan ba su samu ba a ka rufe ni, sai kin bar gidan nan, kuma kwana ki bakwai na baki ki fito da wani mijin, ko ki koma gurin uwarki ki bar mini gida"

Ayshercool
08081012143
23


Cikin maWaukakin sauti Nana take kuka "Baba ka kashe ni ka huta, idan ma ba ka kashe ni ba, ni zan kashe kaina wai ya ake so na yi ne?" Gane nufin Nana da Gaddafi ya yi, ya sanya cikin tsananin zafin nama ya rigata isa gaban rijiyar, ya rufe ta, tana ?arsowa ta yi karo da Gaddafi ta faWi ?asa.

Ya kalli Baba ya ce "Yakamata ka din ga ha?uri, ka din ga tausasa lafuzanka, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya idan ta kashe kanta, kai fa abin zai dama fiye da kowa. Kuma maganar kuWin nan, ka bar komai a hannuna ko ba duka ba za a samo wasu, ka daina cewa ta fita ta nemo kuWi a biya. Ka daina biye shawarar da ake baka ta banza, mai baka shawarar ba za ta bari ka yi wa yaranta haka ba"

Ya dur?usa ya Waga Nana, kawai ya ji tausayinta ya kama shi. Matsaloli sun yi wa rayuwar ta yawa.
Duk da uban nauyin da ta yi, tamkar ta haWiyi dutse, haka ya Waga ta ya kai ta Wakin su, ya kwantar da ita.

Har ya yin?ura zai tashi, Nana ta dan?o rigarsa, ya kalle ta, idanunta a rufe, sai ruwan hawaye da yake zuba ta gefen idonta.

"Nan gaba kan tsohon nan zan cilla a rijiya, ya iya bakinsa"

Gaddafi ya ce "Wane tsohon? Baban ki ke nufi?"

Kawai ta tashi zaune, ba tare da ta buWe idonta ba ta ri?e hannayensa. Ji ya yi kamar an jona masa shocking, jikinsa tamkar za fizge naman jikinsa, ga shi ya kasa motsi, ya kuma kasa magana.

Ta yi murmushi ta ce "Ina fatan yanzu ka gane mai baka sa?on? Ina ?yale ku ne saboda ku ne abu ma fi soyuwa ga uwar gijiyata."

A hankali ta saki Gaddafi ta silale a gurin. Tamkar korarrare Gaddafi ya fita cikin tashin hankali, babu wanda ya tsaya yi wa magana ya fice. Tun da Gaddafi yake bai taSa shiga bala'i irin wannan ba. Har a lokacin da ya fita, da ?yar yake iya sarrafa jikinsa tamkar zai fita hayyacinsa.

Washegari da safe tamkar babu abin da ya faru, Nana ta shirya ta gaida Baba za ta fita amma ya yi mata banza, jikinta babu ?wari ta tafi gidan Alhaji Zailani.
Inda Allah ya taimake ta, tun da wannan abin ya faru, bai ?ara yin?urin far mata ba.

A hankali take bubbuga gate Win, duk da ba ta da tabbacin ma, ana iya jin bugun nata. A yadda take jin duniyar ta yi mata zafi, ji take tamkar ta nemi guri ta kwanta a nan ?ofar gidan.

Aka buWe gate Win, tana Waga kai suka yi ido huWu. Dumm! Gabanta ya yi mummunar faWuwa, babu shiri ta sunkuyar da kanta, ita ba ta shiga ba, ita kuma ba ta koma ba.
Kawai ya mayar da ?ofar zai rufe, babu shiri ta tura ta shiga, ta kalle shi tana son ta yi magana, amma ya yi mata wani irin kwarjini da babu wani Wan Adam da ya taSa yi mata. ?o?arin gane kamaninsa take yi, amma babu dama rawaninsa ya rufe ko ina na fuskarsa sai idanunsa kawai.

Ta kama hanya ta nufi cikin gidan, sai da ta je tsakiyar harabar gidan, sai ga wasu irin murguza-murguzan karnuka da ba 'yan Nigeria ba, idan ta zo haushin su kawai take ji, ba ta taSa ganin su ba, da daddare ake sakin su, da safe kuma a mayar da su keji, da guda Waya ne a ka ?aro biyu. Yau kuma Sule bai samu ya mayar da su ba.

A gigice ta kurma wani irin gigitaccen ihu, ta watsar da takalmanta ta zura da gudu, aikuwa suka rufa mata baya su na wani irin haushi mai ban tsoro. Yana tsaye yana kallonsu, kafin ta ?araso gurin da yake har ta fara fita daga hayyacinta.
Cukuikuye shi ta yi tana ihu, ta daina ganin komai, sai su biyu a cikin sahara, sai kuma jin sautin haushin karnukan.

?aisar ne ya bayyana, ya yi wata irin girgiza, ya zama wani irin narkeken kare shi ma, haushi Waya ya yi sai da gurin ya yi amsa kuwwa a take karnukan suka gudu, kamar barewar da ta ji kukan zaki.

Ya girgiza jikinsa ya koma yadda yake, ya mi?a masa hannu ya ce "Ko da wasa, idan ka sake yin?urin razana ta, ko wani abu na cutarwa a gare ta, zan shafe tarihinka a duniya".

Nana ta buWe idanunta da kyar, ta kalli yadda buzun nan, ya rikiWe ya koma tsohon nan mai kama da ?aisar. Sai dai ko motsi ta kasa.

Wata irin dariya tsohon ya din ga SaSSakawa, gurin ya din ga amsa kuwwa.
"Kai Wan samari, ka sake nazarin kalaman da ka faWa, bayan tsawon shekaru mun sake haWuwa, mun kuma haWu a gaSar da ta dace ?aisar" ya yi maganar yana ci gaba da dariya.

A hankali ya Wago Nana daga jikinsa da ta riga ta suma, ya kalli harabar gidan duk wannan kururwar da ta yi, babu wanda ya fito.

Ya sanya yatsunsa biyu, manuniya da na kusa da shi ya daki goshin Nana sau uku.

A hankali ta motsa ta Waga kanta, a falon cikin gidan ta ganta. Hajiya Amina ta ce "Ohh sannu Nana, haka ki ke tsoron kare? Laifin masu gadi ne da ba su mayar da su sun rufe ba, sannu ba ki ji ciwo ba ko?"

Nana ta jinjina kai hawaye na zubowa daga idanunta. Alhaji Zailani ya fito falo, sai baza ?amshi yake cikin dakkakiyar shadda.
Ya tsaya a falon ya kalli inda Nana take ya ce "Lafiya kuma take kuka?"

"Wallahi karnuka aka bari ba a kulle ba, suka biyo ta shi ne har da kakunta, yanzu suka shigo tare da Yusuf"

Ya girgiza kai ya ce "Laifin masu gadi ne ai, bari na fita sai na dawo"

Nana ta ?ura masa ido, tana son tuna wani abu a kansa, amma ta kasa, ta ci gaba da kallonsa har ya fice.

Da ?yar ta iya jan ?afafunta, ta tafi Wakin Haidar. Ta shiga banWaki domin wanke fuskarta, ta tsaya ta zuba wa fuskarta ido a jikin mudubi.
Ta yi shiru tana tuna tun daga tashinta, zuwa yadda ta zo gidan nan, daga lokacin da karnukan nan suka biyota, tunaninta ya hargitse gaba Waya, ta kasa bambance mene ne ya faru a zahiri, menene ya faru ba a zahiri ba, kuma Hajiya Amina ta ce mata, tare suka shigo da Yusuf to ta yaya?
?angaren kanta Waya ya sara, da sai da ta dafe kan nata. "Wai ko ni ma dai ba mutum ba ce ba? Ko kuma dai ?aisar ya fara nasarar raba ni da hankalina ne?" Ta furta a hankali cikin tsoro da sheshshe?ar kuka.

Jin ana bubbuga ?ofar banWakin, ya sanya ta sauri ta wanke fuskarta ta fito. Haidar ta gani a tsaye yana mutsutsuka idanunsa. Ta kama shi ta wanke masa baki, ta yi masa wanka.


*****
Alhaji Zailani ne a zaune a cikin motarsa, gefensa kuma doctor Sharif ne a ciki a zaune.

"Sharif"

"Na'am Alhaji" ya yi maganar cikin girmamawa.

"A wannan karon ma, taimakon da ka saba nake so ka yi mini"

Doctor Sharif ya ce "Babu abin da zaka nema, na kasa yi maka shi, ka faWi ko mene ne"

"Yaushe ne EDD Win Shukura?"

Ya Wan yi shiru ya ce, scanic biyu dai ta yi a yanzu, amma duk a cikin watan jibi ne, suka nuna za ta haihu"

"To ka saurare ni da kyau, na san dole a asibitinku za ta haihu, idan ta sauka ina bu?atar jaririn"

Doctor Sharif ya kalle shi da sauri, ya ce "Ban fahimta ba"

"Sharif da hausa nake magana, idan Shukura ta haihu, ina bu?atar jaririn duk yadda za a yi, a yi kawai ina bu?atar jaririn. Ka tuna idan ka kuskura kalma Waya ta fita daga maganar da muka yi da kai, to zan iya zame kaina na barka, kuma ba ka da shaida, idan kuma ka yi shiru komai ya tafi dai-dai, zan baka abin da zatonka da tunaninka bai taSa zata ba" Jiki na tsuma Sharif ya ce "In Allah ya yarda babu wanda zai ji, ba zan taSa buWe sirrinka ba"

Alhaji Zailani ya ciro envelope ya bawa Doctor Sharif ya sallame shi.

*****

Nana kuwa tana tunkarar gida, gabanta na tsananta faWuwa, tabbas da tana da wani gurin zuwan, babu abin da zai sanya ta je gidan ta kwana, saboda fargabar abin da za ta tarar a gidan.

A can ?asan ma?oshinta take sallama, Mama ta kalleta ta yi mata banza, haka ma Suwaiba.
Ba ta sake magana ba, ta shiga Waki ta jima a Waki sosai, sannan ta fito tsakar gida ta fara Wan kaye-kaye, saboda yadda zama Wakin ya ishe ta, tunani da damuwa, duk suka addabi Zuciyarta.
Tana jin sallamar Baba, gabanta ya faWi, ta mi?e tsaye hannunta ri?e da tsintsiya, dan ta san dole sai ya yi mata wani abin da ranta zai Saci. Sai dai ga mamakinta sai ya washe mata baki.
"Yarinyar kirki irin albarka, kamar dai yadda na yi tsammani, ke Win ce dai maganin hawayena. A dalilinki Allah zai fitar da mu daga wannan ba?in talaucin da wahalar da muke ciki. Idan zan iya tunawa shekarar da aka haife ki an yi ruwan sama marka-marka, an samu amfanin gona mai kyau da yawa"
Nana ta yi fakare da kai tana kallon Baba, duk wannan hawa da saukar da yake yi ba ta gane ina ya dosa ba.

"Zo ki zauna mu yi magana Asma'u ma'ulle, maganin kukana dama na daWe ina mafarki gani a harami, ashe ke ce za ki yi silar komai" da kansa ya jawo tabarma ya shimfiWa, ya karSe tsintsiyar hannunta ya jefar, ya yi mata umarnin ta zauna.

Ta nemi guri ta zauna, ya kalle ta fuskarsa cike da farin ciki ya ce "An gama biyan wancan matsiyacin kuWinsa"
Kai kawai Nana ta jinjina,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login