Showing 135001 words to 138000 words out of 190498 words

Chapter 46 - Buzu Book 1 Complete

ido cike da damuwa.

Har gefin Asuba, sannan Allah ya sanya ya daina wannan rawar sanyin.

*****

An kai ruwa rana da Mama sosai da sosai, kafin ta amince ta ha?ura, amma da rantsuwa ta yi a kanz sai ta kai Gaddafi gurin 'yan sanda. Ana bata ha?uri shi kuma ya ce "Idan ba ta kai shi gurin 'yan sanda ba, ba Hudu mai ice ne ya haife ta ba" wato mahaifinta.

Duk da Baba yana cikin wannan tashin hankali, amma ya lura da sau?in da ya samu, game da ciwon da ?afarsa take yi masa tun jiya. Sai dai damuwa da tashin hankali ya sanya, bai mayar da hankali a hakan ba, ya karkata ga son kashe wutar da ta taso a gidansa.

****

Hajiya Amina na tsaye cikin matu?ar damuwa, Doctor Sharif ya ce "Hajiya ki yi ha?uri, amma a daren nan, za mu yi mata tiyata domin a ceto ta, da abin da yake cikinta.

"Kuma Doctor babu wata matsala, babanta ba ya kusa, haka ma mijinta"

"To Hajiya ai ba zamu bar ta haka a cikin ciwo ba, ki na kallo ba ta hayyacinta dole mu ceto ta da abin da za ta haifa".

Jiki a sanyaye Hajiya Amina ta karSi consent form, ta saka hannu, tana mamakin yadda suka kwanta lafiya ?alau da Shukura, har likitan da ya ganta da yamma, yana faWin za a sallame ta washegari, a ce lokaci Waya ta rikice, duk da ba a tara sani da Allah, kuma babu kusa babu nesa a gare shi.

Haka tana tsaye aka turo Shukura a kan gado, aka shiga da ita tiyata. Ta koma gefe jikinta a sanyaye tana ta adduo'i daban-daban, tana fatan Allah ya sa ba abin da Shukuran take faWa ne, zai faru ba, da take cewa tana ji a jikinta kamar mutuwa za ta yi, ba za ta rayu ba.

Shukura a hankali ta buWe idonta, tana kallon likitoci a kanta, ba ta san me suke yi mata ba, ita dai tana jin ana girgiza ta.

Anesthetic Win ya ce "Kin farka?" Ta lumshe idanunta ta buWe alamar eh.

"?aga ?afarki sama mu gani"

"Ba zan iya ba" ta faWa a hankali.

Ya ce "To yauwwa, suma ki ka yi ne, shi yasa saboda kar a rasa ki, a rasa babyn, ake yi miki tiyata ba zai yiwu mu ci gaba da barin ki da shi ba, sai mu rasa ku, kuma ba mu sani ba sarkinmu ne na gobe ko shugaban ?asa" ya yi maganar da sigar wasa.

Ta kasa dauke idanunta daga kan Doctor Sharif, da ya haWa gumi suke ta ?o?arin ciro jaririn.

****

?arfe bakwai da rabi, Nana ta dafa ruwa, ta kai masa banWaki.

Ta zo kansa ta ce "Sayyid taso ka watsa ruwa, za ka ji daWin jikinka sosai da sosai"

Ya tashi ya zauna, ya Wan jima a zaune, sannan ya yin?ura, ta bi bayansa ta raka shi ?ofar banWakin, ta mi?a masa zanin hannunta ta ce "Idan ka gama ka lulluSa sai ka fito" bai karSi zanin ba, ya kalle ta, sannan ya kalli banWakin.

A take ta gane Abin da yake nufi, amma wani irin nauyin sa take ji, saboda ba su yi sabon da za a ce ta sake ta saba da shi haka ba. Amma ganin ya ja ya tsaya, ya ?i gaba ya ?i baya, ya sanya ta wuce shi, ta shiga banWakin.

Bayan ta ya biyo, yana bin bango, saboda jirin da yake ji, Nana ta din ga sinne kai, tamkar ta gudu saboda tsananin kunyar da ta lulluSe ta.

Kafin a gama wankan, ita ma sai da ya ji?a ta jalaf da ruwan, tamkar Wan ?aramin yaron goye. Tana zuba masa ruwa a jiki yake zabura, kamar zai shiWe, sai ya rirri?e ta. Da dabara a hankali ta ci gaba da zuba ruwan a jikinsa. Ta gama ta goge masa jikinsa su ka fito.

Da ta kalle shi, sai ta ji zuciyarta ta karaya, amma ta din ga dakewa, tana mazewa.

Ta soya dankalin Hausa da suke da shi, ta dafa shayi, ta zuba masa ta ajiye masa a gabansa.

"Ko na baka a baki?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Ta yi murmushi, ta saka hannu tana ba shi.

Ya ?ura mata ido, ko ?iftawa ba ya yi, ya Wage girarsa yana ?o?arin buWe bakinsa.

Nana ta ce "Ai na san maganar ta Wauke, ba sai ka yi mini magana ba, na fahimta" ya sake kallon ta da mamaki.

Ta ce "Ka manta ka ce mini ruhinka yana rayuwa a cikin nawa? Shi yasa nake fuskantar yin?urinka ko ba ka furta ba"

Murmushi ya yi yana jinjina kai, ya haWa tafukan hannayensa biyu, ya Wago su daidai ?irjinsa, =?O? ya risunar da kansa alamar ya gode sosai.

Nana ta sauke hannun ta ce "Babu godiya tsakanina da kai, duk da ban san wace irin rayuwa ka baro a baya ba, amma kula da kai dolena ne Sayyid"

Idanunsa suka cika da hawaye, ya kamo hannayenta, ya din ga sumbata, ciki da waje. Tausayinsa ya ?ara mamaye ilahirin jikinta, cikin dakiya ita ma ta sumbaci hannunsa, ta ci gaba da bashi abinci. Sai da ya ?oshi, sannan ta saka hau kan katifar ya jingina, ta rife masa ?afafuwan sa da bargo.
Ta tashi tana gyara Wakin, horn Win mota ta ji, ya Wago ya kalli Nana. Ta ce "Ka zauna kar ka tashi" ta saka Hijjabinta ta fita waje.

Matashin saurayin nan da take gani a gidan, mai tara samari su na kallon Ball ta gani a cikin mota. Ta ?arasa inda motar take ya sauke gilashin motar ta ce "Sannu da fitowa"

Ya ce "Yauwwa sannu"

"Ka ga ba ya jin daWi ne, ba shi da lafiya, bari na buWe maka"

Ya dubi Nana ya ce "Subhnallah me ya same shi?"

"ZazzaSi ne yake damun sa"

"Allah sarki, wata?ila malaria ce, unguwar akwai sauro sosai. Kin ga wani magani da likita ya bani Waya na sha, na ji daWin sa sosai da sosai, nake yawo da shi a mota. Ki ba shi ga paracetamol ma, zai ji daWin sa. Je ki kawai zan buWe ?ofar Allah ya sauwwa?e"

Nana ta saka hannu biyu ta karSa ta ce? "Na gode sosai da sosai"

"Ahh ba damuwa" Nana ta ji dadin mutuntawar da ya yi mata, duk da za su yi sa'anni da shi, amma ya yi mata karamci saSanin 'yar uwassa da ta wula?anta mata miji"

Ya sauka ya buWe gate Win ya fita, ya dawo ya rufe.

Nana na shiga Wakin, ta tarar da shi a tsakiyar Wakin a tsaye, yana muzurai.

"Ya na ganka a tsaye kuma? Ka kwnata ka huta, ga magani ma ya bayar ya ce a baka, sai ka samu ka sha"

Ya koma kan katifar, ya kwanta, ba tare da ya tanka mata ba.


AREWABOOKS





*****
Shukura ba ta san adadin lokacin da ta shafe ba ta hayyacinta ba.

A hankali ta buWe idonta, amma sai dai dishi-dishi take gani, tana jin maganganu, amma sama-sama, ba ta gane me ake cewa. Sai sannu a hankali idanunta suka washe ta gane komai.

Mummy ta taso tana faWin "Sannu Shukura ya jikin"

A wahale ta ce "Mummy"

"Na'am Shukura"

"Ina abin da na haifa?"

"Ki kwantar da hankalinki, an kai shi nursery ne, an saka shi kwalba"

Kawai Shukura ta fashe da kuka tana faWin "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba mafarkina ne zai tabatta ba, dan Allah Mummy ni a karSo mini Wa na, a ciro shi daga kwalbar ba na so a dawo mini da jaririna ba na son wata kwalba"

Cikin damuwa Mummy ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Shukura yanka ki aka yi fa, ko awa uku ba a yi ba, sai kin yi wa kan ki illa? Mene ne dan an kai shi nursery?"

"Ni dai ba na so, ki ce su dawo mini da Wa na, wallahi zan tashi na je na karSo Wa na, idan ba za ki karSo mini Wa na ba"

"Shukura ina za ki tashi ki je, jikinki da ciwo meye haka ne?"

Iya ?arfinta take ?o?arin tashi da gaske, sai ta tashi sai dai ?afafuwanta suka ?i motsawa. Hargowar Shukura da kukanta, ya janyo hankalin ma'aikatan gurin. Suka haWu a kanta ana ba ta ha?uri, amma fafur ta ?i yin shiru. A dole aka yi mata allurai ta koma bacci.

Sosai yake tsala gudu a kan titin, yana fatan ya isa gari ya waye.

Yana yi yana kallon inda ya kwantar da jaririn a gefensa, jikinsa kaca-kaca da ?azantar haihuwa da sauran jini, ga mahaifarsa a gefe ita ma kaca-kaca da jini a jiki.

Yaron baya iya kuka, sai kaWan-kaWan, bakinsa sai rawa yake yi, saboda azabar sanyin da yake ji.

Alhaji Zailani yana yi yana kallon yaron, sai dai ?irjinsa ya yi masa nauyi, ya rasa dalilin hakan. Yana matu?ar ?aunar Shukura, haka kurum ya din ga jin kamar bai kyauta mata ba. Amma da ya tuna girman bu?atar sa, na mamaye duniyar sa da samun duk abin da ya sanya a gaba, sai ya ?ara azama da ?ara gudun giyar motar.

Daji ne sosai da sosai, ya yi parking ya Waukko jaririn, ya fita ya nausa cikin duhun du?ununun dajin.
Yana tafe ya hango wuta tana ci, ya ?arasa gurin da wutar take ci. Malam Gambo ne sanye da jajayen kaya, ya nufo shi yana faWin "Ka kusa makara fa"

"A yi mini afuwa, amma ina fatan wannan aikin zai zama daidai da sadaukarwata ta shekara".

"?warai kuwa, ba za a sake neman jini daga gare ka ba a wannan shekarar"

Ya mi?a wa Malam Gambo jaririn, ya saka hannu ya karSi yaron, ya Waga jaririn kansa a ?asa, ?afafuwansa a sama, ya danna tafin ?afar jaririn, a take ya tsanyara ihu, ihun jaririn ya cika dajin.

Malam Gambo ya haska fitila, ya Waukko wani abu a cikin wata jaka, ya saka shi a wuta, ya yi ja ya juya bayan yaron, ya zana wani hatimi a jiki, ya sanya sunan Fatuhu Magaji a cikin hatimin. Yaron ya din ga tsala ihu tamkar ana zare masa rai.

Suka haWu da shi da Malam Gambo, suka tona rami, suka binne jaririn da ransa.

Duk da ba yau Alhaji Zailani ya saba irin wannan abubuwan ba, amma na wannan karon shi kansa ya girgiza zuciyarsa.

Malam Gambo ya Wauki mahaifar, ya ce "Wannan na 'yan aike ne, su za su cinye ta, kai za ka iya tafiya, bayan kwana talatin za mu zo a cire ?warangwal Win, za a yi wani aikin da shi. Ka huta ka yi yadda ka ke so Alhajin Allah, in dai Duniya ce ka same ta yadda ka ke so".

Suka yi sallama Alhaji Zailani, ya hau motarsa ya nufi gida.

A wani irin mugun razane Nana ta tashi daga nannauyan baccin da take yi, ta tashi zaune. Tsaf abin da ta gani ya dawo mata kai fes ba ta manta komai ba.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ka duba lamarin nan, Allah ya sa shirmen mafarki ne"

Tashi ya yi zaune shi ma ya ce "Me ya faru?"

Ta yi ?o?arin Soye damuwarta ta ce "Babu komai, maganar ta dawo?"

"Eh" ya faWa a ta?aice.

"Sannu ya jikin?"

"Alhamdilillah"

"Ko na Waukko maka maganin da aka bani, ya ce yana da kyau ka jarraba sha"

Ya ce "Ba na sha" ya yi maganar yana kwanciya.

Ta dafa shi ta ce "Sayyid, duniya ba za ta yiwu mu rayu mu biyu ba kawai, dole wasu lokutan mu na bu?atar taimakon mutane, dan mu rayu cikin aminci mu ma. Na san ha??o?inka na aure da suke kai na, dan baka da cikakkiyar lafiya ba ya nufin zan ci amanar auren ka.
Na san ni Ahalinka ce, kuma wani shinge da babu wanda zai ratsa shi." Ya yi mata shiru.

Ta kwanta a gefensa, tana shafa gashin sa, ta ce "Sayyid ka yi mini magana mana"

"Ba ki san me nake ji ba ne"

"Na sani mana, ka manta ruhinmu Waya ne?" Ya yi shiru ya lumshe idanunsa yana jin daWin, yadda take wasa da gashin sa.

"Sayyid"

"Ma vie"

"Dan Allah da gaske Alhaji Zailani ya ce maka ka sake ni?"

Kamar ba zai yi magana ba ya ce "Eh, ya ce zai ba ni kuWi. Zuciyata kamar zan mutu a ranar"

Ta ce "Me ka ce masa?"

"Ba zan iya tunawa ba, kawai dai na ji numfashina zai Wauke ne, na manta meyafaru"

Ta Wan yi murmushi ta ce "Rayuwa kenan, daga ni har kai dai gamu nan kawai, Allah ya shiga al'amarinmu. Sayyid ina jin tsoron kar ka tuna waye kai, ni kuma ka manta da ni"

Ta ji shiru, bai yi magana ba. "Sayyid " ta kira sunansa, amma tuni ya yi bacci. Saurin baccinsa har mamaki yake bata.

Zuciyarta kuma ta ci gaba da hasko mata mummunan mafarkin da ta yi, da Alhaji Zailani, dan haka take ta fatan, gari ya waye, ta kira Hajiya Amina ta ji yaya ake ciki.

Sai dai ta kasa komawa bacci, ta din ga tunane-tunane daban-daban a cikin ranta.

Ba ta san adadin lokacin da ta shafe a haka ba, ta ji ya ce "Ba ki yi bacci ba haryanzu? Mafarki ba gaske ba ne ba fa"

Nana ta ce "Ba mafarki na yi ba, na kasa baccin ne"

"?arya babu kyau, kin tsorata a mafarki. Kuma kin gaji ma yau sosai, kina ta kula da ni, na gode sosai bari na yi miki tausa"

"A'a ci gaba da baccinka, daga tausar nan har a yi asuba ba zan yi bacci ba, bar ni kafin a kira salla na rage na yi baccin"

Dariya ta ji yana yi ya ce "To a bari sai bayan sallar asuba"

"A'a ba ni da lafiya" ya ?ara matsawa kusa da ita, ta ji shiru har ya sake komawa bacci.



?aisar ta gani yana Waure Sayyid a jikin wata itaciya. A razane ta nufe shi ta ce "?aisar mene ne haka? Me ya yi maka?"

"Kar ki kuskura ki zo gurin nan, ai na gaya miki tun da ya kwance ?ullin nan, sai ya WanWana shi ma"

Nana ta ce "Wai tayaya ya kwance Waurin da ka yi? Shi da ba aljani ba, kuma bai san abin da yake Soye ba, ka sauke shi dan Allah"

"Ke ki ke ganin shi mutum kamar kowa, na gaya miki kar ki kuskura ki zo gurin nan, zan yi miki illa"

Ba ta tsaya ba ta ci gaba da tunkarar sa.

HankaWe ta ya yi gefe, ya cigaba da Waure Sayyid a jikin itacen nan.

Ta yin?ura ta tashi da ?yar, ta sake nufar sa, sai dai kafin ta ?arasa, tsohon nan ya bayyana ya make ?aisar gefe.

Da sauri Nana ta ?arasa, ta hau kwnace Sayyid da yake a galabaice, ya fita daga hayyacinsa. FaWa ne ya kaure tsakanin ?aisar da tsohon.

Sayyid ya yi shiru, ya zubawa Nana ido, yana jin duk yadda take, furta abin da take gani a cikin mafarkinta a zahiri.

Ya cigaba da kallon fuskarta, ds yadda gumi ya tsatstsafo mata a goshinta, ta rirri?e shi gama tana kuka.

Ya saka yatsunsa biyu a ?yerta ya danna, a take ta yi shiru, jikinta ya saki.


Da Safe yana ta bacci, ta tashi ta yi aikace-aikacen ta.

Bayan tashin sa ya karya, ya yi wanka ya fita waje, sai dai tun da ya tashi bai yi magana ba.

Ta gama aikinta ta fito, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi tana yi masa hira, yana jin ta amma ba ya magana.

Kubra ce ta nufo inda suke zaune, tana tahowa ya sunkuyar da kai.

Nana ta tashi ta ?arasa inda take, ta ce "Sannu ina zuwa haka?"

"Fita zan yi"

"Ki je ina?"

"Fita kawai zan yi" ta bawa Nana amsa.

Nana ta mi?a mata hannu da nufin su gaisa.

Ita ma ta mi?a mata suka gaisa, sai dai a wannan karon Nana ba ta ji sanyi ba. Nana ta kalle ta daga sama zuwa ?asa, riga da wando ne na bacci a jikinta, kanta ko Wan kwali babu.

Nana ta ja ta Wakinsu, ta shimfiWa mata sallaya ta ce "Zauna" babu musu ta zuna.

Nana ta zuba mata abinci ta ce "Na ji an ce ba kya cin abinci, bismillah mu ci" babu musu ta kama cokali ta na cin abincin.
Cikin tausaywa Nana take kallonta, tana matu?ar jin tausayin mai fama da irin wannan larurar, wanda duk ba shi yake Wauke da larurar ba, ba zai gane wahalarta ba. Mussaman idan na kusa da shi, ba su fahimci kan ciwon ba.

Ta cinye tas, Nana ta Wauke kwanon ta kalli Nana ta ce "Na daWe ban ci Abinci da yawa ba"

Cikin kulawa Nana ta ce "Me yasa?"

"Ba na so kwata-kwata. Ba ma na iya bacci."

"To me ki ke ji a jikin ki?"

Ta Wan yi shiru ta ce "Kawai dai ji nake mutuwa zan yi, sai na yi ta kuka"

Nana ta tashi ta Waukko mata pillow, ta ajiye mata ta ce "Kwanta da yardar Allah za ki yi bacci" ta kwanta ta yi shiru, Nana ta kunna mata karatun Alkur'ani. Ta nutsu tana saurara, har bacci ya Wauke ta. Farin ciki ya kama Nana, ganin ta yi bacci. Ta ce "Ya Allah, kai ka ke jarraba bayinka da larura, wasu ka haska musu maganinta, wasu kuma ka Soye. Ya majiSancin lamarinmu, Allah ka yaye mana wannan larurar".


*****

Misalin ?arfe goma da rabi da safe, Baba yana ya bala'in an ba shi koko Wan kaWan babu sugar, alhalin an san ba isar sa zai yi ba.

Mama ta ce "Da ka samu wannan Win ma, Jamila ce ta bayar da kuWin gasarar, yarinyar da ka ke nufi da sharri kai da Wan ka, sai ka bari idan ka nemo, ka fara kawowa sai ka nuna isa da iko"

Sallamar da aka yi ya amsa, yana jiran ya ga suwaye, sai dai ya saroro baki buWe yana kallon masu sallamar. Su ka shigo ni?i-ni?i da kaya a hannun su.

Mama ta fito daga kitchen, ta ga suwaye, ta ce "Too ikon Allah, yau kuma da abin da muka tashi kenan?"

"Lafiya yaya aka yi?" Ya tambaye su kamar ya ga annoba.

"Malam Isa ai kwa bamu guri mu tsuguna tumu tsuguna tukuna"

"Ba wani a baku guri ku tsuguna, ba na son fitina, meya kawo ku?"

?aya daga cikin su ta ce "A'a duk ba abin zafi ba ne ba ai, labarin auren Nana mu ka ji, shi ne muka zo mu tabattar"

Baba ya ce "Eh, haka ne na aurar da Nana, tun da 'yata ce, kuma ina da hurumin aiwatar da hakan"

Saude ta ce "Haka ne, amma mahaifiyarta da mu ma, mu na da hakki a kan ta, ai yakamata a sanar da mu"

"Ba zan sanar ba, na ce ba zan sanar ba Win? Me sanar mukun zai amfanar?"

Mama ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login