Showing 93001 words to 96000 words out of 190498 words

Chapter 32 - Buzu Book 1 Complete

?aramin gini ne.
Sule ya buWe Wakin ya ce su shiga. ?aki ne babba falle Waya, sai banWaki sai ?amshin sabon fenti da kuma turaren wuta yake tashi.
Sabuwar katifa ce gal babba a Wakin, ga labulaye da wardrobe mai guda biyu da mudubi ?arami, ga kuma carfet a tsakiyar Wakin.

Yaya Atine ta ce "Yanzu a sati Wayan ku ka yi wannan shirin?"

Sule ya ce "Eh, wani mu muka yi, wani kuma Hajiyar da muke yi wa aiki ce, ita ta sai labulaye da abin shimfiWar nan, da kayan Wakin ma, abubuwa kaWan mu ka ?arasa"

"Lallai tana da kirki sosai, bayan kayan da ta je ta kai mata gida. Amma Ummi babanku ya tafasa makaronin asara ko cokali fa bai saya wa Nanan ba"

Ummi ta tsuke fuska ta ce "Babu kitchen kenan? A ina za mu ajiye mata kayan kitchen Win"

Sule ya ce "Ai abu ne na maleji, sai dai a ajie mata a nan Win, tun da yana da girma sosai"

Anty Saude ta ce "Bawan Allah kuma cikin gidan da mutane?"

Ya jinjina kai ya ce "Eh akwai, sai dai ba ma zauna bane ba"

Ya Atine ta shiga banWaki, ta kunna famfo ta ga ruwa na zuwa, ga shi har da wearing Win nepa da sola na gidan a Wakin.

"To yanzu ina angon, mu fa ko sau Waya ba mu gan shi ba"

Sule ya ce "Yana nan tafe, sai an jima za a rako shi, idan kuma za ku jira ne to shikenan"

Yaya Atine ta waro ido ta ce "A ina Win? Wannan unguwar duk kangwaye, ku wuce mu tafi ke Nana Allah ya baku zaman lafiya"

Ummi ta ri?e hannun Nana ta ce "Nana kin dai ji abin da Baba ya gaya miki, ki yi ha?uri da abin da ?addara ta zaSa miki, ki yi zaman ki, ke kin san wannan gidan namu, ba gurin da idan ka bar shi zaka so koma masa bane. Ki zama mai tuna wace ce ke, kuma daga ina ki ke, sharrin da ake yi miki kawai a gidan ya ishe ki. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a Wayyiba. Na karSi kuWin sadakin ki a hannunsa, da kyar ya bayar da dubu hamsin, wai sauran da su aka yi hidimar biki. Ina son Wan sayo miki kayan kwallita, da underwears idan kin amince, idan ba ki amince ba na baki kuWin ki"

A hankali Nana ta ce "Duk yadda ki ka yi na amince"

"To shikenan, ga wata dubu ashirin ki ri?e a hannunki, a irin kuWin gudunmawar bikin ki ce, ko za ki yi amfani da su, a sha amarci lafiya" Nana tana ji suka tafi suka bar ta ita kaWai ?wal.

Shiru garin, ko ?wa??waran motsin wani abin ba ta ji, ta Waga kai tana kallon Wakin.

A zuciyarta ta din ga addu'a, tana ro?on Allah ya shiga lamarinta. Yawan gane-gane da Nana take yi, ya sanya zuciyar Nana fara ?e?ashewa. Ta bayan Wakin take jin hayaniya, ana surutai da dake-dake ana hira, tamkar a irin gidan yawan nan.

Kiran sallar magariba ta ji, ta tashi tsam, ta shiga banWakin ta Wauro alwala, ta dawo Wakin ta yi sallar magariba.

Bayan ta idar duhun magariba ya ?ara yi, sai dai Wakin akwai hasken fitilar solar.
A hankali kuma tsoro ya fara shigar Nana, ta daina jin hayaniyar da take jiyowa, ko ina ya yi tsit.
Daga bisani kuma ta din ga jin bugun zuciyarta yana ?aruwa, sai kuma hasken fitilar Wakin ya Wauke baki Waya. Ta kifa kanta a kan ?afarta, jikinta ya fara tsuma.
A hankali ta Wago kanta, ta ganta a cikin sahara a zaune, sai sautin iska da yake kaWa yashin saharar. A wannan karon ma yana tsaye, hannunsa ri?e da akalar ra?uminsa. Tashin sautin kaWe-kaWe ta din ga ji, ba tare da ta ga daga inda kiWan yake tashi ba, ga wata zazza?ar murya da take ta rangaWa guWa, muryar na amsa kuwwa a dajin. Ya taka a hankali ya je gabanta, ya mi?a mata hannu. Ta Wago a hankali ta kalle shi, ta Waga hannunta za ta mi?a masa. Ta ji an yi sallama firgigit ta buWe idonta tana kallon mai yin sallamar.

Ayshercool
08081012143

Page 28

Da Sule suka yi ido huWu, ya shigo wasu buzayen suka biyo bayansa, hannunsu ri?e da kaya.

Ya kalli Nana ya ce "Afuwan mun tsorata ki ko? Ki yi ha?uri ba mu zo da wuri ba, mun tsaya mun yi salla isha'i ne.
Ita dai Nana ba ta ce komai ba, aka din ga jere cartons na ruwa a Wakin.

Ita dai ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ?asa.

A hankali ta din ga jin tamkar numfashinta zai Wauke, wani irin bugu zuciyarta take yi, sanyi yana ratsa ta.

Ta Wago kanta domin sha?ar wadatacciyar iska, kar numfashinta ya Wauke.

Fararen kaya ne a jikinsa, irin na buzaye, ya yi rawani da shuWin yadi, ga wata Wamara da ya yi da wani shuWin yadin, gefen ?ugunsa kuma soke da takobi a cikin kubenta, wuyansa yana sanye da wani abu, na fata wanda ya Wara laya girma, kuma bai kai girman jaka ba. Yatsunsa sanhe da zobunan azurfa, ga kuma ?arfen tagulla a tsintsiyar hannunsa, ya dafe gefen cikinsa, shigar ta buzaye ce, kuma ta wata fuskar kamar ta larabawa.

Yana gaba Habu yana bayansa, shi ma ya sha kwalliya cikin shigar buzayen. Wani irin daddaWan ?amshin turare,
ya karaWe ilahirin Wakin, Nana ba ta taSa jin turare mai tsananin ?amshi kamar wannan ba.
Sai kuma sauran buzayen a?alla su biyar, duk sun sha kwalliya.
Dadduma suka shimfiWa masa ya zauna. Gaba Waya suka zauna a gefe, suka yi shiru. Habu ya ce "Mu yi addu'a" aka fara Addu'a.

Nana ba ta san a tsakaninsu waye mijin nata ba, sai dai tana ?o?arin satar kallonsa, duk da kamar kullum kamar yadda ta saba ganinsa, fuskarsa a rufe take da rawani.

Ba ta san me aka karanta a addu'ar ba, saboda ta lula tunani, sai muryar Habu da ta ji ya kama sunanta.

"Nana"

Ta ce "Na'am"

"Da farko dai ina mai ba ki ha?uri a kan abin da ya faru, kin san komai Allah ne yake ?'addarawa. Jikina ya yi matu?ar sanyi da abin da ya faru. Na gane dalilin wannan auren ne ya sanya muka baro gida. Ki yi ha?uri bawa ba ya tsallake ?addararsa. Ina yi muku fatan alkhairi da fatan Allah ya baku zaman lafiya. Na san abubuwan da mu ka ba ki na aure, be kai abin da ake kashe muku na aure ba, amma ki yi ha?uri a hankali za mu duba a yi miki, kin san masu ?aramin ?arfi ne mu. Dama Wan kuWin gadin tarawa muke yi, za mu tura gida wannan abu ya bijiro, kuma kuWin hannunmu duk ya ?are. Dan Allah ki yi ha?uri da abin da Allah ya ?addara miki."

Nana dai ba ta ce komai ba, ya sake nuna mata kayan da suka zo da su ya ce "Ga sayayya nan, abin wanka ne da kayan wanke baki, da Wan abin da ba a rasa ba na kayan tsafta. Yanzu mu na sauri mu koma, ba wanda zai kula da ?ofa dole mu koma da wuri, amma zamu dawo da yardar Allah" su ka ?ara yi musu fatan alkhairi.
Shi kuwa tun da ya zauna, ?wa?w?waran motsi ma bai yi ba, balle ya tofa wani abu ba.

Sai da Nana ta ga sun mi?e baki Waya shi yana zaune, sannan ta fara zazzaro ido.

Gaba Waya sai suka juya yare, su na yi masa magana, har suka gama maganar, shi dai bai ce uffan ba.

?aya bayan Waya suka fice, hakan ya ?ara tabattar mata da shi ne mijin nata. A take ta tuna Sule ya taSa gaya mata ba shi da cikakkiyar lafiyar ?wa?walwa. 'kenan mahaukaci Baba ya aura mini?' ta tambayi kanta.
?o?arin tuna wasu abubuwan take yi a kansa, amma abu ya gagara, ta ji gaba Waya kanta ya toshe.

Ta yin?ura ta tashi, ta tafi banWaki domin ta yi alwala ta yi sallar isha'i.
Sai dai bayan ta yi alwala da ?yar ta baro banWakin, saboda duk taku sai ta ji tamkar zuciyarta za ta fashe.
?afafuwan ta su ka gaza Waukar ta, a dole ta zauna ta kalli gabas, ta tayar da salla. A zaunen ma jiri take yi, da haka ta yi salla.

Shi dai bai kula ta ba, bai kuma tashi daga gurin da yake a zaune ba, kamar gunkin budda.

Ta idar da s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????allar, ta koma jikin bango ta matse jikinta, ta rasa abin da yake yi mata daWi, ji take kamar ta kurma ihu, ga sanyin nan da take ji ?aruwa yake yi, tsigar jikinta sai tashi take yi.

"Allah ka dube ni, dan Allah ?aisar kar mu yi haka da kai, ni hauka shi hauka ta ya ya za a yi wannan zaman" ta furta hakan a hankali.
Sun shafe dogon lokaci, kamar babu halitta mai motsi da ta wanzu a gurin, Nana tana ta tufka da warwara a zuciyarta, kawai ta ga ya tashi tsaye. Zuciyarta ta ?ara tsinkewa da tsoro da razani, tare da hakaito mata miyagun abubuwa, yanzu idan ya yankata a gurin nan ya gudu fa? Mussaman wannan takobin da take gani.
A hankali yake tafiya, ya tafi gefen wardrobe Win Wakin, da aka kafe abin rataye kaya. Ya cire takobin ya rataye ta. Ba tare da ya waiwayo ba, ya fara kwance rawaninsa. Kasancewar ya juya mata baya, ya sanya ta zuba masa ido ko ?iftawa ba ta yi. Ya kwance rawanin gaba Waya, ya ninke Nana ta zuba wa sarautar Allah ido, ganin kansa Wauke da gashi ba?i wuluk, ya tufke shi tamkar an yi wa kan bahauhishiya saloon.
Ya saka hannu ya zare rigar jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta, tana kallon gefe, kamar mara gaskiya.

A hankali ta ?ara Wagowa, ta ganshi da dogon wando, da shirt, ya ninke rigar da rawaninsa, ya buWe wardrobe Win ya saka kayan a ciki.

Ba ta san ya aka yi ba, kawai sai gani ta yi sun haWa ido. A take ta tuno ganin da ta yi masa, har ta suma a Wakin su.

Da wata irin azama ta tashi, duk da bugun zuciyar da take ji da kuma jiri, ta ja da baya ta tsaya cikin tsoro da razani.

Ya ci gaba da kallonta, ba tare da ko ?ifta ido ba.
Kawai Nana ta fashe da kuka, ba tare da sanin dalilin da ya sanya ta kukan ba.

Gani ta yi Wakin yana juya mata, ya kawar da kansa daga kallonta, ya fice daga Wakin. Fitarsa ke da wuya ta silale a gurin ta faWi.

A hankali ta fara juyi tana tari, a cikin kunnuwanta take jin bugun zuciyarta, ta ja jikinta ta tashi da ?yar. Ta karkaWe hannunta saboda ?ura, ?aisar ta gano sanye ba?ar riga tana jan ?asa, yana shirya litattafan sa, yana goge su.

Da ?yar tarin ya Wan lafa mata ta ce "?aisar"

"Ya aka yi?" Ya amsa ba tare da ya kalle ta ba.

"Tsoro nake ji, ji nake yi kamar zan mutu. Ba ka ji yadda zuciyata take bugawa ba"

"Ina jin yadda take bugawa mana, ai mutuwar ma za ki yi idan ba ki yi wasa ba, tun da ke dai kin ?ware a taurin kai. Wannan mutumin ?ila shi zai yi ajalin ki. Ki kan ji bugun zuciya da sanyi ne, idan ina guri to me yasa ba na gurin daga ke sai shi ki ke jin bugun zuciyar?" Ya jefo mata tambayar.

Nana ta Wan yi shiru, sai kuma ta ware ido, amma ta kasa magana. Ya ce "Eh, ai na gaya miki ba ki da tabbacin abin da ki ka aura, mutum ne ko kuma jinsinmu" yana gama maganar ya yi gaba. A rikice Nana ta bi shi tana faWin "Dan Allah ka tsaya ka saurare ni, yanzu ya zan yi dan Allah?"

Ya waiwayo ya kalle ta ya ce "Au tambayata ma ki ke yi ya ya za ki yi? Shirka fa ki ke ?o?arin ko kin manta?"

Nana cikin kuka ta ce "Ba haka nake nufi ba, amma wallahi tsoro nake ji idan na ci gaba da rayuwa da shi, zan iya mutuwa"

?aisar ya ce "Ai da da na gaya miki ba ki yadda ba" ya juya zai tafi, ta ri?o rigarsa"

"Zan watsa ki ta waje, idan ki ka kuma bi na"
Za ta yi magana ya ce "Sai kuma ki yi" kawai ya Sacewa ganinta.

Kawai ta koma gefe ta tsaya tare da fashewa da kuka.

Yana zaune a gefen Wakin nasu, ya na shan hantsi, sai ga Sule ya zo da kwandon kayan abinci.

"Ango har ka tashi? Ya mari?e Win ?"

Ya nuna masa Wakin, alamar tana ciki. Gaba gaWi Sule ya nufi Wakin da kwandon Abincin cikin hanzari Buzu ya mi?e ya tsaya a ?ofar Wakin.
Sule ya ce "Au yi ha?uri, bari na zauna daga nan" ya nemi guri ya zauna a gefensa.

Nana kuma ta buWe idonta, ta ganta kwance a kan katifar, jikinta babu naWin lafayar da aka kawo ta da shi, sai riga da skirt Win ta na ciki, kanta ko Wan kwali babu. A razane ta dubi jikinta tana tambayar kanta, ko ya yi mata wani abin ne?. Ta kalli gefen katifar ta ga lafayar a ninke a ajiye. Da azama ta yin?ura ta faWa banWaki, amma ba ta ga alamar an yi mata wani abu ba.
Ta yi tsarki, ta yi alwala tana ta istigfari ta yi sallar asuba, cike da jin kunyar Ubangiji, yadda lokaci ya ja gari ya yi haske ba ta yi salla ba.

Bayan ta idar tana jiyo Sule yana ta zuba da yaren su, shi dai ba ta ji maganar sa ba. Ta yi mamakin abin da ya sanya Sule kasa yin zuciya ya ci gaba da surutu ba tare da ana kula shi ba.

Babu tsammani ya shigo Wakin, ba tare da ko sallama ba. Aikuwa ta zabura ta ja da baya tana kallonsa.
Kai tsaye ya nufo ta, ya ajiye mata kwandon Abincin a gabanta. Ya nemi guri ya zauna ya zuba mata ido, da kwandon kayan abincin a tsakiyar su.

Nana ta sunkuyar da kanta, sanyi na ratsa ta.

"Zan ci abinci" ta ji muryarsa kamar daga sama, Waga kai ta yi ta kalle shi, ji ta yi kamar ta ce masa to ya ci mana, sai kuma ta tuna ashe fa wai yanzu mijinta ne. Mamaki ne ma ya kamata, dan har a lokacin tana mamakin idan ba kurma ba ne ba.

Ta janyo kwandon ta sassuke abincin, ta fara ?o?arin zuba masa, kawai ta ga ya tashi ya fita. Sai ga shi ya dawo da abin da suke hura wutar dafa shayi, har da butar shayin ma, da alama abin da suke yi a wajen tun Wazu kenan, shan shayin.

Ya buWe cikin kayansa, ya Waukko turaren wuta, ya zuba a kan sauran garwashin. Take Wakin ya karaWe da ?amshi mai daWin gaske. Ya samu guri ya zauna, ya karSi abincin, ya koma gefe ya sauke takunkumin rawaninsa ya hau ci.

Nana kuwa kasa cin abincin ta yi, ta yi tsuru sai satar kallonsa da take yi, ya gama ci ya Wauki kwanukan da ya ci, ya fita waje ya wanke ya dawo ya ajiye mata. Ya tsiyayi sauran shayinsa na butar, ya shanye abin sa.

Ya kewaye ta, ya Wauki pillow ya koma can gefe ya ajiye ya kwanta. An shafe tsawon lokaci, na zaune ba tare da sanin abin yi ba. Jin yunwa ta uzzura mata ya sanya ta Wan zuba abincin ta fara ci. Tun tana cakala har ta saki jiki, ta ci gaba da zurawa kawai suka yi ido huWu, tana ta loma. Sai kuma ta yi sak, ta ci gaba da ci ta kasa kamar wadda ta aikata rashin gaskiya, kuma ya ?i daina kallonta. ?arshe sai ha?ura ta yi da cin abincin, kallon da yake yi mata duk ya sanya ta damu.

*****
Gidan su Nana tun a ranar kowa ya watse, dan baba faWa ya yi ta yi, yana cewa duk wanda ya kwana sai dai ya nemi abin da zai ci, shi ba shi da abin da zai sake bayarwa a bawa mutane.

Suwaiba ta ?arewa Wakin su kallo ta ce "Ohhh abin tsiya, ko tsinke ba ta bari ba, duk ta kwashe komai balle mu gada."

Mama ta ce "Au ke har wata tsiyar ki ke saka ran gada a gurinta? Me za ki gada banda gayyar masifa, ai gara da tarkata komai ta tafi, ma sake mu mi?e ?afa mu huta mu ma"

Jamila da ta shirya tsaf za ta fita ta ce "Aikuwa dai"

"To kafin hankali ya dawo kan ku, Ubangiji Allah ya kawo muku mazaje na gari 'yan uban uban su, wanda kowa sai ya koka a tashi kan munafukan unguwa da na family"

Suwaiba har da tsalle ta ce Amin Mamanmu maganin kukanmu.

Jamila ta yi murmushi ta ce "Ni dai sai anjiman ku"

Mama ta ce "To a sauka lafiya"

*****

A tsanake take kallon yadda mai gidan nata, yake Wan yamutsa fuska bayan ya kammala cin abinci.

A hankali ta ce "Daddy"

"Na'am baby"

"Ya dai? Jikin ne ko garin? Na ganka so silent"

Ya Wan yi mi?a ya ce "Pressure ce ta Wan yi mini yawa wallahi, ina shirin tafka asara ne, kwana biyun da ban je kasuwa ba, har an yi mini Sarna wallahi. Ga kaya sun iso Nigeria na gama clearance amma coustom sun ?i sakar mini kayan"

"Subhnallah, in sha Allah ba za ka yi asarar ko naira biyar ba. Allah zai warware komai, bari mu du?ufa da addu'a in sha Allah ba wani abu"

Ya yi murmushi ya ce "Sweetheart, Allah ya amsa mana, Wan duba mini paracetamol idan ki na da shi, kaina yana ciwo, ina so na je asibiti ma a duba ni ko bp na ne ya hau"

Cikin damuwa ta ce "In sha Allah ba shi ba ne ba ya hau, dan Allah ka kwantar da hankalinka, mu na bu?ar lafiyarka just recently fa kai ne ka ke yi mini nasiha a kan yadda da ?addara"

Ya girgiza kai ya ce "A'a ba ma damuwar na saka a raina ba, kawai jikina ne babu daWi"

Ta tashi ta ce "Bari na Waukko maka" ta nufi bedroom Win ta.

*****

Alhaji Zailani ne zaune a gaban malam Gambo, sai gumi yake yi kamar ya yi wa sarki ?arya.

"Na rasa gane abin da ya faru gaba Waya, ni dai na san mun yi da kai za mu yi magana da wanda ta aura Win, na ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login