Showing 60001 words to 63000 words out of 121625 words
sai anyi serving dinsa, Nasir ne yayi saurin cewa "Zuba 'yammata, ko in tayaki" sai sannan Bilal ya dago kansa ya
ce "Nasir stop" sai ya kalli Na'ima yace "Ke fitaa" gyada kai tayi cikin sauri ta miqe ta fice daga dakin Nasir na kallonta...
Daga wannan incident din kuma Bilal be sake attempting taba Na'ima ba a gidan, sai ya koma yawonsa da yake hanasa zaman gidan,
tun horn din motansa na damun Na'ima cikin dare har hakan yabi jikinta ma, gashi zuwa wannan lokacin ba wai iya shawuwa da buguwa Bilal yake ba har 'yan pills dinnan yafara tabawa wanda Na'ima tanaji kuma tana ganin komai dake faruwa dakuma irin yanda han
kalinsu Alhaji ya tashi ganin irin rayuwar da Bilal ya sake maida kansa ciki, ko ace ya cigaba, don Allah ne kadai yasan me yayi a Luxembourg kuma...
Damuwan hakan se tayi yawa a Alhaji gashi dai yana gani in ya biyewa Hajiya to haka zasu zuba ido Bilal
din ya sake lalacewa da sunan wai a bishi a hankali, sai ya samu Hajiya Babba da zancen akan suyi shawaran hanyar da zai bullowa yaron nashi, maganar farko daman cewa tayi ayiwa Bilal aure sannan Alhajin ya samo masa aiki me traffic dayawa in the sense tha
t aikin yazamo me cinye lokaci wanda zai hana Bilal din yawan yawon club din ma, shiru Alhaji yayi yana tunani sai kuma ya gyada kai cikin amincewa dan shima yayi tunanin hakan amma komai da shawaran yafi, A lokacin da ya samu Hajiya da wannan maganan har
a fuskan ta saida ta nuna batason auren Bilal din don a nata tunanin kullum fargaba take kada yayi aure mace ta janye mata danta, more especially in ya auri wadda yakeso sosai, amma ta bada amanna da batun aikin sosai, sai sukayi shawara akan akwai wani co
mpany na atampopi na Alhajin a Lagos, though ba nashi bane shi kadai akwai partners akai amma kuma shine jagora, yace zai tura Bilal din can tunda akwai abokinsa acan kuma ayanzu shine leader a wajen in yaso tunda Kano itace gurin da Bilal din ya tara abok
an sharholiyarsa, Lagos din zai zamo masa sabon guri ga kuma aiki da zai ci lokacin sa sosai...
Da wannan shawarar suka lallashi dan nasu kuma bai yi musu ba ya tattara ya koma Lagos da aiki....
Bayan shekara biyu da watanni...
Zuwa sannan Na'ima ta
gama secondary dinta ta zama budurwa me cike da kyawun siffa da haiba, wani kyau Allah ya bata da Inka kalle ta saika sake yi mata wani kallon, wasu irin idanu ne da ita masu jan hankalin duk wanda ze kalleta, ga suman gashi da kullum ke qara fitowa akant
a har zuwa gaban goshinta, kuma har zuwa wannan lokacin Na'iman nan ce me shiru mara hayaniya, zataje makaranta ta dawo tayi ayyukanta wanda zuwa lokacin ta saba sosai har tasan me zatayi ma kafin a fada mata, har zuwa lokacin
bata taba kawo kawa gida ba,
rayuwanta takeyi sama sama da kawaye, inda yanzu tana jiran admission dinta ne ya fito wanda tayi applying BUK kano...Har zuwa lokacin Bilal be dawo gida ba wanda hakan kuma se ya fara damun iyayen suka fara dana sanin turasa Lagos din, Amma dai ba'a watan
ni Hajiya bataje dubosa ba kuma yaqi dawowan, rayuwansa ya bude sabuwa acan yake zuba badalarsa babu idon iyayensa, Hajiya duk tafi kowa shiga damuwan rashin dawowarsa gida, babu shiri ta fara banka maganin kiranye akan Bilal din, shiga da fita suka rinqa
yi itada kawarta Larai akan duk yanda za'ayi Bilal din ya dawo gida itadai ta hakura da aikin ma yadawo ta rinqa ganinsa a gabanta hakanan..
Tsafi gaskiyar meshi, Rana tsaka Bilal ya waiwayi gida kuma bai tashi dawowa ba saida tsaraba babba..Hajiya daman
ta shiryawa zuwansa dan an tabbatar mata yananan kan hanya kwana kusa...
Ranar da ya dawo kuwa kwatsam su Na'ima suka ji shigorwa motarsa gidan a lokacin tana kitchen tana dafa abinci, bayan wasu lokuta shafa ta shigo cikin kitchen cikin sanyin jiki tace
"Na'ima je ki kai wa Bilal ruwa yana falo, bari mu dora masa wani abu cikin sauri"
Gyada kai Na'ima tayi ta debi drinks daga fridge ta fice zuwa kai masa, zaune ta samesa Hajiya na tsaye kansa bata zauna ba, duk wani annurin fuskanta ya dauke ganin irin r
akiyar da Bilal din ya samu, wata mace ce gefensa nan kan kujera, bleaching duk ya cinyeta da kitson attachment wanda yakai har mazaunanta tareda dogin nails da eye lashes, irin mata masu kama da ashawon Lagos dinnan dai masu BBL wanda in sun zauna mazauna
nsu sai yaci rabin kujera...toh ita Bilal ya kawo gida kuma kyam take kallon Hajiya dan Hausa ma ba isarta yayi ba, qarasowan Na'ima wajen itama saida ta tsaya kallon wannan mace dake manne gefen Bilal kamar ta shige jikinsa, ajiye ruwan tayi cikin sanyin
jiki ta dago sukayi Ido hudu da STELLA, cikin sauri Na'ima ta sauqe idonta tanajin idon stellan ya mata kaifi dayawa......
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 27
Cikin sanyin jiki Na'ima ta nufi hanyan kitchen bayan ta ajiye ruwan, a
ranta tana ayyana yau kuma wace irin drama za'ayi a gidan dan itama kanta Na'iman a dan zaman da tayi a gidan na 'yan shekaru tasan Hajiya ba mace bace me son a rabi danta ko da wasa, shiganta kitchen din shafa ta juyo tace "Kin kai musu ruwan" Na'ima ta g
yada kai, shafan ta sauqe numfashi cikin jimami ta sake cewa "Allah ya kyauta dai" Na'ima batace komai ba suka hau aikin abincin tare babu wanda ya sake cewa komai cikinsu dan kowannensu da abunda yake saqawa arai..
Hajiya na tsaye nan kansu Bilal sai kal
lonsu take with confusion, dakyar ta zauna cikin sanyin jiki nan kan kujerar dake facing dinsu ganin Bilal yaqi kallon idonta, daukan juice daya yayi ya tsiyaya a cup ya miqawa Stella dake dan murmushi a Hajiyan, yace "Ina wuni Hajiya" fuska a dinke Hajiya
n ta amsa da "Wannan fa? wacece Bilal?" sai Stella ta duqar da kanta kadan alamun ladabi tace "Inah woni Ma.." ko kallon inda take Hajiyan batayi ta sake tambayan Bilal da "Babana a ina kasamo wannan?" Bilal yace "Hajiya tana gaishe ki fa" tace "Ba matsala
ta bane wannan, a
ina kuka hadu har ta rakoka gida" Bilal yace "Girlfriend dina ce, mun kwana biyu tare da ita and mun fara maganar aure ne shiyasa muka yanke shawaran ta fara zuwa ku ganta tukunna" Hajiya ji tayi a lokacin kamar ta kai mangari a dan nata
tukunna, tace "Toh ita mahaukaciyar ina ce dan kun fara maganan aure sai ta biyo ka gida" Bilal yayi saurin cewa "Tana dan jin Hausa fa hajiya, mamarta 'yar nasarawa ce" Hajiya ta juya ta kalli Stella dake kallonta kyam cikin Ido, ta bude baki zatayi maga
na sai ga megadi ya shigo kinkime da akwatuna, sanin kayan bana Bilal ne kadai ba yasa Hajiyan miqewa tace "Muje sama muyi magana, da kai kadai kuma" ya juya yace da Stella "Baby I'm coming" Stella ta gyada kai tareda cewa "Ina jiranka fa" gyada kai shima
yayi duk Hajiya na kallonsu cikin mamaki, danne zuciyarta tayi ta nufi stairs Bilal din yabi bayanta suka bar Stella nan zaune tana bin bayan Hajiyan da wani mugun kallo, dauko juice din tayi ta sake tsiyayawa a cup ta cigaba da kurba tana bin falon da kal
lo....
Isarsu saman ko zama basuyi ba Hajiyan ta juyo tace "Sakayyar da zaka mana kenan Bilal, wai me yasa bakason kaga hankalina ya kwanta ne a koda yaushe" Bilal ya matso yace "Wallahi inasonta Hajiya, Stella tanada kirki sosai sai kin zauna da ita za
ki gani" Hajiya ta ware ido tace "Au har zama zamuyi da ita kenan, tukunna ma da ka kawo kayanta cikin gidan kana nufin anan zata zaune kenan, a wane gidan bahaushe ka taba ganin anyi haka, Bilal meyasa kullum burinka kasamun ciwon kai ne" ya kwantar da mu
rya tareda cewa "Na fada mata hakan tun acan, toh batada kowa a Kano ne shiyasa na kawota nan din ai Hajiya" jijjaga kai Hajiya ta fara sai ga stellan ta shigo falon cikin kashe murya tace "Baby i need to pee" cikin masifa Hajiya tace "Yau naga jaraba, duk
dakunan qasan bazakiyi fitsarin acan ba sai nan, ki fitaaa nace" sai Stella ta kalli Bilal tace "Bilal what is this? You promised me they're going to like me" Bilal ya nufeta hankali tashe zeyi magana Hajiya ta mulmulo zagi ta hada da "Dan uwarki ki bar
gidan nan, dan iskanci har gida zaki biyomin da saboda gidan ku babu tarbiya" Bilal yace "Haba Hajiya, meya hakan kikeyi kuma" kawai Stella ta juya ta nufi fita daga falon Bilal yabi bayanta da sauri, daskarewa Hajiyan tayi nan tsaye sai can ta nemi guri t
a zauna batasan me ma zata fara tunani ba..
Na'ima ta fito daga kitchen zataje dakinta taga stellan ta fito cikin sauri zata nufi kofa tana cewa "I can't stay here" Bilal dake biye da ita a baya be ma kula da Na'iman ba yace "Baby wait..." Tsayawa kallons
u Na'ima tayi har suka fice daga falon Bilal be daina cewa wait din ba, sauqe numfashi tayi sum sum ta wuce dakinta cikin sanyin jiki, saida ta koma daki ta danyi uzurirrikan ta sannan ta fita backyard din gidan debo kayanta da ta wanke dake nan kan igiya,
muryoyunsu ta rinqa jiyowa a nan parking space na gidan, Bilal ya kwala kira a megadi yace masa yaje ya debo kayan da yakai cikin gidan, shima cikin sauri ya wuce ciki yin abunda aka saka sa, bayan Na'ima ta koma daki tana zaune kan gadonta tana linke kay
an nata tajiyo tashin motarsu Bilal din sun fice daga gidan...
Da suka gama yin abincin sai shafa ta miqa mata na hajiyan tace ki kai mata sama ba lallai yau ta sauqo ba, Na'ima ta gyada ta nufi can din riqe da tray din, shiganta falon ta samu Hajiya na w
aya hankali tashe, muryarta har rawa yake tana cewa "Wallahi banga ta zama ba Larai, anyi ba ai ba ne wannan, na kirenye'n yaci sa amma kuma na menene harda dawowa gida da kilaki, nashiga uku ni Ladi" sai tayi shiru tana sauraron Larai daga daya bangaren,
kasa qarasawa Na'ima tayi tana sauraron wannan abun al'ajabin, Hajiya da idonta ya fara kawo ruwa ta cigaba da magana cikin
tashin hankali tace "Komawa gurin dan hauren zamuyi Larai, dan wallahi a yanayin yanda naga ya bita ba qalau yake ba, ni dama baha
ushiya ce shine zan samu sauqin bullowa al'amarin, amma irin arnan nan tsorona kada ta kaimun da gurin 'yan shan jini" ta sake cewa "Toh shikenan sai kin fito goben, ki fito da wuri dan Allah nima Alhajin bayanan" da haka ta ajiye wayan tana dafa goshi, da
n gyaran murya Na'ima tayi tareda sallama Hajiyan ta juyo cikin sauri tana kallonta, Na'ima tace "Ga abincin Hajiya" tace "Ajiyeshi nan ni tsk" haka Na'ima ta ajiye abincin tanajin wani iri ta juya ta fice, zama tayi akan gadonta tana tariyo maganganun haj
iyan cikin mamaki...
Washegari ko breakfast Hajiya batayi ba ta sauqo nan falon cikin shirinta harda face mask, Na'ima dake sharan falon ta dago kai tana kallonta, fadawa Na'iman tayi "In shafa ta fito kice mata akwai kayan wanki na dana hada ta wanke" Na
'ima ta amsa da "Toh" tabi bayan Hajiyan da kallo ganin ta fice da sassafen kuwa...
Bayan Na'ima ta gama aikace aikacenta taci abinci sai takoma dakinta ta kwanta dan ta dan ta huta, madadin tayi bacci sai ta hau tunani kuma, rayuwarta tafara tariyowa tir
yan tiryan daga sanda akace yau mahaifiyarta ta mutu zuwa lokacin da mahaifinta ya bita shima, hawaye taji yana kawowa idonta takai hannu ta share still bata daina tunanin ba, tananan kwance tajiyo qarar bude gate aka shigo falon, muryan Sufi taji yana gai
sawa da shafa sai ta miqe tasaka hijaba tafita, bayan sun gaisa ne sufi yace mata ta shirya sannan ta debo takardunta ze kaita makaranta tayi screening....
Stella ce kwance akan gadon cikin dakin hotel din da suka kama nan cikin garin Kano, saida ta tab
batar Bilal ya shige wanka sannan ya kuma rufo qofan sannan ta dauko wayanta ta fice balcony na dakin nasu tayi kira, daga daya bangaren qanwarta me suna chiamaka ta dauka suka gaisa cikin yaren pidgin sannan Stella ta fara bata labarin zuwanta gidansu Bil
al din, duk ta cikin yare suke maganan dayake hausan bawani kwarewa sukayi acikinta ba se ya zamto sunfi yin yaren Igbo da pidgin in suna tare, chiamaka'n ce tace "Toh datace ki fitan ke kuma se kika fitan kenan?" Stella tace "Ai gashinan muna tare dashi a
nan hotel tunda na baro gidan, kuma na rantse sai naga dama zata sake ganinsa ma" chiamaka tace "Ai daga hotel din ku taho Lagos abunku, ita tasan wahalan da kikasha akan dan nata ne gurin rabashi da mata da har zata miki rashin mutunci, har yau fa bamu ga
ma biyan cikon kudin me maganin ba Stella" gyada kai stella'n tayi tace "Zata san ni ta zaga, itada Bilal se gani a nesa yanzu kuma, dama ta barni a gidan at least zata rinqa kallonsa ma akai akai" chaimaka tace "Yanzu kin shafa masa wancan din?" Ta amsa d
a "Eh" sai chiamaka ta sake cewa "Toh yaya zakiyi da wanda akace kisa cikin katifarsa" Stella tace "Tunda ba zama zamuyi ba zan bar wannan din kawai" , da haka sukayi sallama ta dawo dakin daidai Bilal din ya fito daga bandaki daure da towel, ta qarasa ta
rungumesa tayi masa kiss a kumatu tace "Baby im so tired of this place, we have to go back to Lagos" Bilal ya gyada kai tareda cewa "It's okay, but you have to meet my parents again when we come back next time" ta gyada kai tana qara riqesa aranta tana fa
din "There won't be a next time"........
Weeks Later.....
Zuwa wannan lokacin Na'ima ta samu admission dinta na makaranta har sun fara cuku cukun fara registration wanda duk Sufi ne ya shige kan komai yanda Alhaji ya umarcesa, dan zuwa sannan Alhaji ya
dawo gari, duk wanda ya kalli Hajiya a wannan lokacin yasan tana cikin damuwa saboda yanda duk
tabi tasawa kanta damuwan rashin dawowan Bilal har sannan tun wannan fitan da yayi daga gidan tareda Stella, har wata yar rama Hajiyan tayi sai tunani kuma, day
awan lokuta in Na'ima taje gurinta zata sameta tayi nisa cikin tunani kuma, gashi har lokacin malamin nasu yayi buge bugensa ya bata assurance na cewan Bilal din zai dawo gidan da qafarsa ta kwantar da hankalinta saboda akwai abunda yake cin danta kuma za'
a karya sa da sannu... Ranan suna zaune da Alhaji suna magana tace "Yanzu Fisabilillah rashin dawowan yaron nan gida baya damunka?" Alhajin yace "Ladi kinason dagawa kanki hankali, yaron nan fa aikinsa ya koma ya cigaba da yi, mun samu ya nutsu yana aikin
yanzu sai kice ba haka ba" idon Hajiya ya kawo hawaye tace "Amma aiki ne shine baze waiwayi gida ba, kana gani wayata ma be cika dauka ba, sannan Alhaji da mace fa yadawomin gidan nan, Mace faaa, kuma arniya" Alhaji ya kwantar da murya yace "Da ya kawo mac
en sai ki tsaya ki sauraresa ai, ke fa kikace mubisa ta lallami, ai bawai an haramta aurensa da yarinyar bane, sai ki tsaya ki fahimci yaya alaqan yake, sannan wace irin yarinya ce" masifa tafara tana cewa "A'a wallahi, banda kirista Alhaji, zai dawo gidan
nan ya sameni ya gama zaman Lagos din kenan, kuma gaskiya ka dawomin da dana cikin garin kano da aiki hakanan, aure kuma 'yar uwarsa bahaushiya zamu aura masa bawani zance wannan fitinanniyar yarinyar, wallahi baze yiwu ba" Alhaji ya tsaya kallonta na wan
i lokaci sannan ya sauqe numfashi yace "I'll talk to him then" tace "Ahtoh, ba ita tayimin naqudar dana ba wallahi bata isa baa" Alhaji yace "Duk me ya kawo wannan maganar Kuma?" Tace "Nidai fada nake, baze yiwu ba wallahi, yarinya me tarbiya zan aura masa
in sha Allah" Alhaji ya gyada kai sannan ya miqe sai kuma tace "kunyi finalizing takardun can dinne " ya gyada kai batareda yace komai ba, ganin alamun ransa ya baci ne yasa bata tambayesa abunda ke cin ranta ba, dan satikan da suka wuce Alhajin ya fara
kammala duk wasu dukiyansa zeyi finalizing Will din sa a ajiye (yawancin masu tarin dukiya sukan rubuta will dinsu tareda shaidun lauya ko lauyoyi sannan a ajiye koda me dukiyan zai riga iyalinsa mutuwa, a lokacin ne za'a ciro takardun a kuma karanto kason
kowa da me dukiyan yayi niyyan badawa) toh hakan ce ta faru ta fannin Alhaji, kuma duk yanda Hajiya tabi na sanin ko kadan daga cikin mind dinsa yaqi bata daman haka...
Lamuran makarantar Na'ima ya kankamaa sosai tasamu admission nan Bayero University
har sun fara registration, wanda duk Sufi dinne ya shige mata gaba takeyin komai, a lokacin da time table dinsu ya fito ta sanar da Alhaji yayi mata addua sosai yace duk wani abun kudi da ya kama na school din ta rinqa magana da Sufi ze bata, godiya ta mas
a sosai tanajin dadi hakan har ranta, Hajiya ko bi takanta ma batayi ba da taje mata da batun makarantan, itama tana ta kanta, sai yawon bala'i da suka sako kai itada kawarta Larai, yau sune nan gobe sune can, sunyi chanjin malamai sunkai uku adan tsakanin
nan abu yaci tura har lokacin Bilal muqut kakeji ba labarinsa Stella ta kammale abunta..
Ranan Na'ima ta je falon Hajiya kai wa larai ruwan sha, tasamu suna zancen nan