Showing 75001 words to 78000 words out of 121625 words

Chapter 26 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

48

iyayen nasa suka karbe shi da hannu bibbiyu, rungumesa Hajiya tayi tana kuka tana fadin bazai koma China ba, saida ya zo kwanciya da dare Alhaji

yace ya tafi gidansa gurin matarsa, qememe Hajiya tace sai danta ya kwana gu

rinta tukunna, haka Alhajin ya hakura dan shima har ransa yayi missing dan gudaliyan nasu.....

Wayewar washegari Na'ima nada wani test me zafi a school, cikin saurinta ta gama kintsa gidan sannan ta shirya cikin wani maroon abayanta ta tafi makaranta, w

aya tayi da Nafisan ta biyo nan bakin hanya ta dauke ta suka wuce tare, basu fito ba sai karfe goma, shima suna fitowa Na'ima tace da Nafisan zataje gida ta yi bacci kanta na ciwo na karatun da tayi jiyan, tare suka sake barin makarantan Nafisa takaita har

qofar gida sukayi sallama ta ja motanta ta bar layin, sai lokacin Na'ima ta samu nutsuwan gaisawa da megadin sannan ta shige ciki, baquwar motan data gani a parking space sai da yasa zuciyarta harbawa tuna Bilal, dan stiff tayi a tsaye nan compound din ba

ta shiga gidan ba tana kallon motan, can ta ja kafafunta cikin sanyi ta nufi entrance din gidan, a hankali ta tura kofan falon dake bude ta shiga, qarasawarta cikin falon yayi daidai da fitowan sa daga kitchen hannunsa riqe da cup yana sipping tea, tsayawa

kallon kallo sukayi jikin Na'ima na dan rawa, it's been three years.... Amma Na'ima bata daina jin tsoron wannan bawan Allah'n ba, bata daina kyarma aduk sanda ta gansa ba..

Muryanta na dan rawa tace "Sannu da dawowa" yana kallonta shima cikin nutsuwa ya

ce "Yauwa, ina kika ajiye sugar, i've been looking for it since" mamaki ne ya lullube Na'ima najin yana mata magana cikin nutsuwa yau din, sai tayi saurin nufan kitchen din zata dauko masa kanta a qasa tana gyara zaman gyalen abayan jikinta, bin ta da kall

o Bilal yayi har ta shige......

KUNCIN ZUCI

πŸ“–πŸ“š

Bintu Musa

✍

️



Chapter 32

Bayan Na'ima ta shiga kitchen din sai da tadan tsaya ta sauke numfashi sannan ta nufi cupboard dinda take ajiye sugar'n, daukowa tayi sai ta fara tunanin yanda z

ata qara komawa wajen Bilal dake tsaye can falon, can dai cikin sanyin jiki ta bar kitchen din ta nufeshi yananan har sannan a tsaye yana kallonta, kanta a qasa ta miqa masa ya karba ahankali yace "Thanks" sai ta nufi stairs da dan saurinta ya bi bayanta d

a kallo..... bata sake fitowa daga dakin ba har sai bayan azahar taji ya kwala mata kira a falo, cikin sauri ta yafa gyale ta fita, samunsa tayi nan bakin stairs yana tsaye ranshi a dan bace yace "Aren't you making me lunch?" sai tayi saurin girgiza kai ta

ce "Kayi hakuri yanzu zanyi", sauqa tayi ta wuceshi tana dan saurin nufan kitchen din, cikin sauri take aikin tana duban bakin kitchen din aikuwa sai gashi ya shigo ya tsaya nan bakin kofan kitchen din hannuwansa harde a qirjinsa yace "Daga ina kike dazu?"

tsayar da aikin tayi cikin sanyin murya tace "Makaranta naje" sai lokacin Bilal ya tuna da tana makaranta ashe, sai ya juya zai bar kitchen din ya sake cewa "In kin gama ki kaimin can dakina" ta amsa da "Toh" sannan ta cigaba da aikin..a tray ta hada abin

cin ta nufi dakinsa tanajin zuciyarta

na dan bugawa, shiganta ta gansa nan tsaye bakin wardrobe sanye da only boxer, cikin sauri ta juya kanta da kadan abincin ya zube saboda yanda zuciyarta ta buga ganinshi hakan, Bilal dake duban kayansa ko a jikinsa ya

nuna mata bedside drawer yace "Ajiye acan" cikin sauri ta kai ta ajiye kanta a qasa ta nufi fita daga dakin yana kallonta, bata sake jin motsinsa ba sai bayan magrib taji fitan motanshi wanda bai dawo gidan ba sai tsakiyar dare bayan tayi bacci...

Washega

ri ma tayi mamakin amsa gaisuwan ta da yayi lokacin da ta kawo masa breakfast nan inda yake zaune a falo yana kallon Ball, da ta shirya zataje makaranta ma gyada mata kai yayi bayan tayi masa sallama ya bita da kallo ganin yanda baqin abayan ya sake fito d

a haskenta, shi sai lokacin ya lura da yanda halittan idanunta suke ma...

Zaune Na'ima take tareda da Nafisa a wani rest bench hannunsu riqe da burger'n da Nafisa ta taho musu dashi suna ci, ganin Na'ima na kaiwa baki a hankali kamar ta fada tunani yasa N

afisan cewa "What is wrong with you Na'ima?, you seem lost tunda kikazo school dinnan yau" shiru Na'ima tayi sai kuma ta sauqe numfashi, ahankali tace "He's back Nafisa and bansan da me ya dawo ba" ajiye burger'n Nafisa tayi tana ware Ido tace "What?...yau

she ya dawo, No wait..did he beat you?" Na'ima ta girgiza kai tace "A'a" Nafisa tace "Then.. me ya miki?" ta amsa da "He just keep staring at me" da sauri Nafisa ta juyo da kafadan Na'iman tana kallonta cikin ido tace "Shi kadai ya dawo babu karuwar tasa?"

Na'ima ta gyada kai, Nafisa ta cigaba "Toh wallahi ki kula, Bilal HIV zai saka miki" saida zuciyar Na'ima ya buga na wasu 'yan daqiqu ta kasa magana, Nafisa tace "Ya gama bin kan karuwan Lagos din shine zai dawo kanki yanzu, we have to do something" haway

e ya ciko a idon Na'ima tace "Nafisa ya zanyi?" tace "Duk yanda zakiyi karki yarda dashi, duk inda za'aje kuwa" tunani Na'ima ta fara yi ta yanda ma Bilal din ze ce zaizo gurinta bayan yace "In matan duniyar nan zasu qare he won't give a f*ck about her"...

sunanan zaune Nafisa tayi ta bata qarfin gwiwa akan ko me Bilal din ze ma ta be kai cutan da zai qaqaba mata ba, har suka gama school activities dinsu na ranan hankalin Na'ima bai dawo jikinta ba, a hanyarsu ta komawa gida ma haka ta jinginar da kanta jiki

n window tana tunani Nafisa na sake bata qarfin gwiwa akan yanda zatayi facing dawowan Bilal din.

Bayan Nafisan tayi parking anan qofar gidan sai ta juya ta kamo hannun Na'iman tace "Bobo let's talk" kallonta Na'ima tayi batace komai ba sai ta cigaba da m

agana cikin kwantar da murya tace "It's high time you leave this God forsaken marriage before you loose your sanity, Bilal zeyi ruining dinki ne Na'ima, zan iya rantsuwa ba ke bace a gabansa saboda inda ya damu da rayuwanki bazeyi shekarun nan batare da ya

san yanda kike ba, and i sense that kallon nan da kikace yake miki kawai neman hanyarsa zeyi dake ya cuceki" hawaye Na'ima ta fara ta kasa magana, Nafisa tace "ki fadawa Alhaji bakyaso, nasan he'll listen" gyada kai Na'ima tayi tace "Toh" ganin bata iya ma

gana yasa Nafisan yi mata sallama itama tana jin zuciyarta wani iri, da haka suka rabu rai babu dadi..

A wannan ranan ma bai wuni a gidan ba sai dare ya dawo, Haka suka cigaba da rayuwa na tsahon two weeks Bilal baida aikin yi sai kallonta inta fito zata

giftashi, gashi dai ko wane dare da kalan macen da yake kebewa a club amma yarasa meyasa ya kasa dauke idonsa daga kan Na'ima, ranan wata talata ta gama hada masa breakfast tana jerawa anan dining ya sauqo qasan, nan gefenta ya tsaya tadan yi baya, sai yac

e "Me kika dafe me qamshi haka" kasa magana tayi ganin ya matso daf da ita yana kallon idonta, matso da fuskansa yayi daf da nata har tana jiyo numfashinsa

zuciyarta na bugawa cikin tsoro saboda maganganun Nafisa dake echoing a cikin kanta, kissing dinta y

a so yi sai ta juya kanta kadan, again be daddara ba ya sake miqo fuskansa, batasan lokacin da ta dan dafa hannunta a qirjinsa ba alamun ya dakata, ji yayi ransa ya baci sai ya fara kiciniyar riqota duk da haka taqi juyo da kanta, Mari ya kai mata me qarfi

sai da tayi baya, ya sake biyota ya hankadata ta bugu da dining table din abincin ya zube, cikin diri yace "Damn you Na'ima" ya qarasa maganan tareda shafa fuskansa cikin frustration, dafa kuncin ta tayi aranta tana fadin "There we go again" plate din gur

in ya dauka ya sake bugawa a qasa yace "Me kika dauki kanki da har zan kawo kaina wajenki kiyi rejecting dina, ke kin isa?" Na'ima na hawaye har sannan dafe da kumatun ta batace komai ba sai ya juya cikin bacin rai ya koma dakinsa...

Daren ranan bayan Na'

ima ta samu bacci ya dauketa dakyar taji anja blanket dinda take kwancen, da sauri ta bude idonta jin mutum a gefenta, qoqarin miqewa tafara yi Bilal ya sa hannu ya danne ta sai ta fara kuka bata daina kiciniyan kwace kanta ba, yaga rigan jikinta yayi bear

skin dinta ya bayyana tayi saurin kai hannu ta kare jikin nata bata daina kuka ba tace "Dan Allah kayi hakuri" Bilal bai saurareta ba ya kai fuskansa wuyanta yana wani irin numfashi, sai da ya raba ta da duk kayan jikinta ta karfi kafin yaji kansa yayi wa

ni irin bugawa wanda yasa cikin sauri ya dagata yana dafe kansa, ganin haka yasa ta miqewa ta lalubo bedsheet din zuwa jikinta kafin ta nufi hanyan fita ya finciko gashinta tayi qara me karfi, dawo da ita gadon yayi bata daina ihun ba wanda yake jinsa kama

r ze tsaga masa kwakwalwa, nan ya hau dukan bakinta bata daina ihun ba, ranan Na'ima taga other side of Bilal da bata taba gani ba, monstrous side dinsa ya bayyana mata nan kan gadon yana dukanta kamar ba mace ba, ji yayi ya tsaneta kamar ya kasheta a wann

an lokacin, sai da Na'ima ta galabaita sannan ya fice daga dakin cikin fushi, hannu takai hancinta tana tare jinin dayake fita har sannan hannunta damqe da bedsheet din tana kuka me tsuma zuciya...Har asuba idonta biyu ta kasa tashi daga kan gadon, zuwa sa

nnan babu hawayen ma sai kukan zuci da takeyi, da asuban taji fitan motansa daga gidan, wunin ranan komai ji tayi baya mata dadi, kuka kam tashashi kamar ranta ze fita tana jin ta tsani har iyayen Bilal din...

Bilal bai dawo gidan ba sai tsakiyan daren

ranan, da aka wayi gari washegari Na'ima tayi masa breakfast ta ajiye nan dining be fito ba, ta nemi face mask tasaka bayan ta gama shirin zuwa makaranta, a falon ta samesa zaune, cikin sanyin murya ta fada masa zataje makaranta ya bita da wani mugun kallo

da ya kada 'ya'yan hanjinta, calmly yace "Bazakije ba" kanta a qasa ta juya ta nufi upstairs tanajin wasu hawayen na zuwa mata...daga wannan lokacin zamansu yakoma bala'in dare kuma, wataran a buge zai dawo gidan ya biyota dakinta neman abunda yake so amm

a abu ya gagara, jin haushin rashin idda gaci yake sashi dukanta sosai, wani qunci zuciyar Na'ima ta shiga a wannan lokacin, zaman gidan ma yazamo a firgice takeyinsa, saida tayi sati harda dori bataje makaranta ba tun tana boyewa Nafisa har ta fito fili t

a fada mata Bilal ne ya hanata zuwa school din, a ranar da ta fada matan sai ga Nafisa a gidan da yammaci, ganin yanayin Na'iman da ciwukan fuskanta yasa Nafisan fashewa da kuka ta rungumota suka fara kukan tare nan tsaye falon, sai da suka tsaya da kukan

Nafisa tace "Na'ima mu tafi police station yanzu" da sauri Na'ima ta girgiza kai tareda cewa "A'a Nafisa" cikin bacin rai Nafisa tace "Baki kalli yanda kika koma bane Na'ima, kinaso sai ya kasheki kenan" Na'ima na hawaye tace "Zanje gun Alhajin, amma banda

police station Nafisa"..ranar Nafisa ce ta

tsaftace mata gidan har girki tayi sannan ta fita ta siyo maganin da zata shafa mata a ciwukan fuskanta da jikinta, tana hawaye tana shafa mata suka zauna shiru can tace "Na'ima you're slowly dying, this man is k

illing you slowly" Na'ima na hawaye batace komai ba Nafisa tace "Ki bini mu koma Abuja, let's run away Na'ima, mutafi gidanmu na can" Na'ima tace "They are my family Nafisa, i can't leave" cikin bacin rai Nafisa tace "F*ck that Na'ima, and they stand aside

watching you like this" Na'ima ta sake cewa "Zanje gurin Alhajin gobe, ai be san yana dukana ba" tsayawa kallonta Nafisan tayi sai ta miqe takai mayukan kan mirror..sai dare Nafisa ta bar gidan kuma tayi sa'a har sannan Bilal din be dawo ba...

A daren ra

nar Bilal yadawo gidan tare da Stella data biyoshi Jin shiru bai koma ba, Na'ima na dakinta ta jiyo muryansu sun shiga dakin Bilal din..Ba qaramin nutsuwa Na'ima ta samu ba ranan jin Stella a gidan, bata taba jin dadi da hamdala ba irin zuwan da Stella tay

i a ranan, bayan ta idar da salla cikin daren ranan har addua tayi akan zaman Stella yayi tsaho a gidan kodan ta samu sararawa kan uquban da Bilal ke gana mata....

Washegarin ranar bayan ta yi musu breakfast ta koma dakinta sai ta jiyo tashin muryansu a

lamun suna sa'insa, bude kofan dakin Stella tayi ta fito Bilal ya riqo hannunta sai ta fincike ranta a bace tace "Don't touch me" anan kofar dakinsa suka tsaya ta sake cewa "Have you touched her?" Bilal yace "Meye hakan kike cewa ne Baby" ta daga masa hann

u tace "Just answer me Bilal, did you sleep with her?" Jinkirin da taji yayi gurin amsawan ne yasata juyawa ta nufi dakin Na'ima tana fadin "Where is this B*tch" ta banko kofar lokacin da Na'iman ke gaban madubi tana gyara gashinta, Stella batayi wata wata

ba ta finciko gashin nata sannan ta dauketa da mari, Bilal ne ya biyo Stella dakin tareda riqota duk da haka taqi sake gashin Na'ima tana qunduma mata zagi, dakyar ya rabasu Stella na cewa "Ka barni in koya mata hankali tasan ta shiga gonata" sai ta sake

yin kan Na'ima, da sauri Na'ima ta nufi toilet Bilal ya sake riqo stella'n, beyi wata wata ba ya dauke ta da mari tayi baya tana ware idanu cikin mamaki, ransa a bace ya nunata da yatsa yace "No One, i mean No One..gets to beat Na'ima except Me" Stella na

kallonsa cikin shock tace "Bilal ni ka mara akanta" yana kallonta cikin ido yace "Get out", fuu ta juya ta fice daga dakin, Na'ima na nan tsaye bakin toilet ya juya ya kalleta bai ce komai ba shima ya fice daga dakin.....

Da daren ranan ta gama abinci Bil

al ya sauqo daga upstairs yace mata "In kin gama ki kai mana abincin can dakina" gyada kai tayi ta amsa da "Toh" bayan ta gama hada abincin akan tray sai ta hada da plates na tangaran as usual har da glass cups da take hadawa akai saboda bottle water'n da

takeh kai masa..nufan dakin nasa tayi sai da ta gama hawa stairs din Stella ta fito daga dakin hannunta janye da akwatinta suka kusa cin karo, dan baya Na'ima tayi sai stellan ta matso daf da ita tana kallonta fuskarnan kamar hadari, hannu ta kai ta banke

tray din daga hannun Na'iman kwanukan suka rinqa tumbling anan stairs har suka kai qasa, juyawa Na'ima tayi tana kallon yanda duk tangaran din suka tarwatse, duk sun fashe sunyi daddaya, kafin ta juyo ta kalli Stella'n sai taji ta hankadata da qarfi, tun d

aga matakalan farkon Na'ima ta fado har kan fasassun glasses dinnan a sume, jinine ya fara bin jikinta nan kwance... Bilal dama tun jin qaran farko yayi saurin kashe shower dinda yake wanka a toilet, da saurin sa ya fito sanye da towel, daskarewa yayi a a

bakin stairs din ganin abunda ke gabansa ga Stella nan tsaye itama tayi stiff tana kallon Na'iman dake kwance cikin jini...

KUNCIN ZUCI

πŸ“–πŸ“š

Bintu Musa

✍

️



Chapter 33

Cikin kidimewa Bilal yayi nufin sauqa stairs din sai ya dakata ya j

uya zuwa dakinsa da sauri ya dauko takalmi saboda glasses dinda suka fashe nan gurin, a rikice ya qarasa gurin Na'iman ya dagota, ganin kamar bata numfashi ne yasa ya dago kansa yana kallon Stella da tayi mutuwar tsaye har sannan, tsawa ya buga mata "Dalla

aa ki daukomin Car key" da saurinta taje ta dauko, cicciban Na'iman yayi ya nufi waje da ita, sai da ya kwantar da ita a back seat sannan ya koma cikin gidan da gudunsa ya dauko jallabiya, figanΒ  motan yayi bai jira shigan Stella ba ya nufi near by asibiti

da Na'ima dake sume har sannan..

Dakyar asibitin suka karbeta ganin injuries din jikinta sannan sukayi emergency da ita, Bilal na tsaye ya kasa zama, addu'an sa daya a lokacin shine Na'ima tayi rai dan be san da wani baki zeyi explaining kanshi gurin mah

aifinsa ba..Sai da Na'ima ta dauki two hours me kyau kafin ta farfado, kuka ta rinqa yi nan kwance kan gadon, bayan an ciccire mata glasses din da suka shiga cikin fatarta aka wanke ciwukan tareda saka mata bandage, Allura suka mata sannan suka fito da ita

daga dakin ture a gado tana bacci, qarasawa gurinsu Bilal din yayi suka tafi dakin da akayi referring dinta tare wanda ya kasance single room, har asuba Na'ima bata farka ba nurse din da ke kula da ita tana ta zuwa akai akai, Bilal na nan zaune kan kujera

a dakin jefi jefi yana kallonta, kiran Stella ne ya rinqa shigowa wayansa babu qaqqautawa yana rejecting, dan ransa ya baci da abunda tayin sosai, Ganin har safiya Na'ima bata farka ba yasashi tafiya gida canjo jallabiyan jikinsa dan ta baci sosai da jini

, bayan tafiyansa bada dadewa ba Na'ima ta farka, da farko bin dakin ta fara yi da kallo sai can kuma abun da ya farun suka fara dawo mata kwakwalwa, rufe idonta tayi tanajin hawaye na sauqo mata tana jin wani irin zafi acikin zuciyarta da jikinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login