Showing 84001 words to 87000 words out of 121625 words

Chapter 29 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

34

Na'ima na kwance kamar ta mutun haka ya kasa tabuka komai akanta, zuwa wannan lokacin Na'ima ta daina magana sai ido, kana ganinta kaga mai cutan depression, haka Bilal zai ta masifa bata iya ko bashi hakurin m

a sai hawaye da kuma binsa da ido, in ya daketan ma sai kukan zuci da kuma kallo da ido, qirjinta yayi ta hawa yana sauka kamar me ciwon zuciya..

Ranan wata asabar Bilal yazo gidan da Nasir, dakinta ya shiga ya sameta kwance akan sallaya as usual, yace "K

i fito ki gaisa da Nasir, and cook something quickly" dakyar ta miqe tareda gyada kai ta gyara hijab din ta sai Bilal ya tsaya kallonta, ta gefensa ta zo ta wuce ya bita da kallo har ta sauqa, Nasir na ganinta ya fara murmushi yace "Sannu Amaryanmu" ci ka

nka batace ba ta wuce kitchen ya bita da kallo, sai da takawo masa ruwa asannan Bilal yana zaune a falon shima, ciki ciki tace "Ina wuni" bata jira amsan sa ba ta koma kitchen ta fara aikin dafa musu spaghetti, data gama ta kai nan dining ko magana batayi

musu ba ta haye sama cikin sanyin jiki Bilal ya bita da kallo, sai dare Nasir ya tafi...

Amma abun mamaki..Washegari bayan Bilal ya fita sai ga Nasir a gidan, da Na'ima ta bude kofa suka hada ido sai ya fara mata murmushi, juyawa tayi adan tsorace ta koma

falon ya biyota ciki tareda cewa "Bazaki min iso ba amaryarmu" tace "Sannu da zuwa" sai ta wuce kitchen ta dawo hannunta riqe da ruwa, kafin ta ajiye akan glass table din sai ya kamo hannunta, a firgice ta kwace tayi baya sai ya miqe yana kallonta yace "I

'm here to save you Na'ima, trust me" juya kanta tayi gefe tace "Banaso" bai bar kallontan ba yace "Trust me, zan rabaki da Bilal but i need only one thing in return" sai sannan ta kallesa ta sake cewa "Ka fita Dan Allah" ganin ba fahimtarsa zatayi ba yasa

shi fara kokarin kamota sai tayi saurin daga riganta ta ciro qaramin wuqa, a firgice ta nunashi da wuqan tace "Ka fita ko in caka maka" ganin yanda hannunta ke rawa yasa Nasir yin murmushi yace "Okay" sai ya juya ya fita, yardar da wuqan tayi hawaye na kaw

owa idonta ta yi saurin saka key a kofan falon...

Dawowan Bilal ya rinqa banging kofan jin ta a kulle, cikin sauri taje ta bude masa beyi wata wata ba ya dauke ta mari yace "Banyi warning dinki akan rufemin kofa ba" tana dafe da kumatun nata tace "Kayi ha

kuri" yace "Ub*n meyasa kika kori Nasir a gidan nan dazu da yazo nemana" da mamaki Na'ima ke kallon Bilal, ransa a bace yace "Ki bani amsa before i wound you, gidan ub*nki ne nan din" ta girgiza kai tace "Ban kores..." sai ya sake dauketa da mari yace "Dam

a na lura da karban da kika masa jiya, yaushe raini yafara shiga tsakanina dake Na'ima?" Ta sunkuyar da kai batace komai ba, ransa ne ya qara baci na shirun da tayi kawai ya finciko gashinta ya jata cikin falon, jefa ta yayi nan tsakiyar falon yace "Zan sa

uke miki rainin da kikeji dashi ne Na'ima" tana kallonsa ya fara kiciniyar cire belt dinsa, sai ta kwanta kan tiles din hawaye na kawowa idonta tana jiran saukan dukan a jikinta...

Kwance Na'ima take kan gadon dakin ta fuskanta yayi jaa sosai saboda kuk

a, miqewa tayi ta nufi madubin dakin ta bude drawer, razor ta ciro tana kallon kanta a madubi, sai ta kai hannu ta tattaro gashinta da nufin yankewa, tsayawa tayi tana kallon kanta a madubin sai ta jefar da razor din ta dafa mirrorn tana kuka, sake bude dr

awern madubin tayi ta dauko takardar da Nafisa ta bata wancan ranan, by then ta riga ta haddace address din a kanta, juyawa tayi ta nufi wardrobe din ta, ta janyo akwati sannan ta fara ciro kayanta tana zubawa aciki har sannan bata daina hawaye ba, bayan t

a gama hadawa sai ta zauna tana kallon akwatin zuciyar ta na tsinkewa, jitayi an bude kofan falon sai ta miqe da sauri ta saka akwatin cikin wardrobe ta fita, dasakarewa tayi a bakin stairs ganin Nasir tsaye falon yana mata murmushi yace "Hi Na'ima" juyawa

tayi da gudu ta nufi dakinta ya biyota da gudun shima, kafin ta saka key a kofan ya banko ya shigo yana cewa "What is wrong with you Na'ima, inason in miki abunda dolon mijin ki yakasa miki shine kike guduna" jikinta na rawa tace "Dan Allah ka fita, ka ru

famin asiri dan girman Allah" yana kallonta kamar tsohon maye yace "Kin dai ga matsayina a gurin mijikin jiya ai ko?..to ko ki nutsu ko yau ma hakan ta sake faruwa" sai ya fara takowa gareta tayi baya, cikin kwantar da murya yace "Na'ima i won't hurt you,

wallahi tun ganin farko dana miki nake sonki, bazan cutar da ke ba i assure you" a wannan lokacin kan Na'ima kullewa yayi ta rasa ma ta ina zata fara kubuta daga hannun wannan azzalumin, addu'a kawai take jerowa a zuciyarta sai ta nufi toilet da gudu, da s

auri Nasir ya kamota ya dauketa, kiciniyar kwace kanta ta fara sai taga ya kwantar da ita anan kan gadon, kokuwa suka farayi Na'ima na kuka, beyi wata wata ya yaga rigar jikinta, white padded bra din ta ya bayyana, a daidai wannan lokacin Bilal ya turo kof

ar dakin ya shigo duk suka juya suna kallonsa, daskarewa Bilal yayi nan tsaye yana kallon Nasir dake kan Na'ima a gadon, saurin miqewa Nasir din yayi alamun tsoro ya bayyana a fuskarsa ya dan qarasa gurin Bilal din yace "Listen man...she wanted it" naushi

Bilal ya kai masa saida yakai qasa, ya sake binsa yana kai masa duka ta ko ina, miqewa Na'ima tayi akan gadon ta gyara riganta tana kuka da qarfi ta rasa me ma zatayi a wannan lokacin, da Nasir yaga Bilal na neman illatashi sai ya samu dakyar ya miqe ya ha

nkada Bilal din ya fita falo da gudu, bin bayansa Bilal din yayi kafin ya riskeshi ya fice through kofan gate, komawa cikin gidan Bilal yayi yana wani irin huci kaman zaki, Na'ima da zuwa sannan ta biyosu falon taga ya shigo yana huci, kafin tace komai Bil

al yasa kafa ya kwasheta ta fadi nan kan tile goshinta ya fashe, da kafa ya rinqa harbin cikinta yana huci yana cewa "F*ck you Na'ima..Damn you...kin hanani kanki zaki baiwa wani" dukanta kawai Bilal keyi kamar ba

mutum ba, tun Na'ima na gani har komai yaz

ama duhu a idanunta, sai sannan ya fincikota bai bar hucin ba yace "I'd rather kill you akan wani ya sameki" gani yayi Na'ima tayi luuuu kamar babu rai a jikinta, jijjiga ta yayi still yaga bata motsi, ai da sauri ya azata a kafada ya nufi compound din gid

an da ita, hankali a tashe yasata a mota sai asibiti, yana driving din ya dauko bottle water ya tittila mata a fuska duk da haka bata motsa ba, the same asibitin da ya kaita rannan ya sake kaita yau ma, amma likitocin emergency sukaqi karbanta akan sai Bil

al yazo da takarda, sa'a yayi Amina ta shigo part din, ganin Na'ima kwance yasata tabi bayan likitan, ba'a dau lokaci ba tadawo tasaka Bilal din daukan Na'ima ya shiga da ita, sai azahar Na'ima ta farka nan ma suka mata alluran bacci ganin yadda duk ta gal

abaita, da suka kaita dakin da zata huta, sai Bilal ya tsaya nan bakin gadon yana kallonta fuskanta da duk ya kumbura, juyawa yayi ya fita zuciyar sa na quna, sai yamma yadawo dakin, zuwa sannan Na'ima ta farka har Amina ta sake bata kaya ta saka ganin na

jikinta a yage, ita kadai ya samu a dakin dan Amina ta fita wani aiki lokacin, ta dago fuskanta tana kallonsa idonta daya yayi suntum, gefen bakinta duk ya kumbura, yanayin fuskan nata duk me imani in ya kalleta sai ya ma ta hawaye, qarasowa bakin gadon ya

yi yace "Ki fadamin dalilin da ya kai Nasir dakinki" sai ta sauqar da kanta tana hawaye batace komai, ganin bazata amsa ba yasa shi juyawa sai tayi saurin riqo rigansa tana kuka sosai tace "Dan Allah, Dan Allah ka sakeni Yaya, mutuwa zanyi in na koma gidan

ka" tsayawa kallonta yayi sai yace "Qauyen zaki koma" tayi shiru ya sake cewa "I'll give you space Na'ima, but kisani duk inda zakije you'll come back to me, And i'll be waiting, kije qauyen mugani" bai dena kallonta ba ya sake cewa "Kije na sakeki saki DA

YA" fashewa tayi da kuka me qarfi, Amina da ta shigo a lokacin tayi saurin cewa "Amma baka da imani kai dinnan, a gadon asibitin zaka mata wannan sakamakon" kusan bangajeta Bilal din yayi ya nufi kofa, tana hawayen ta qaraso gurin Na'iman tace "Ina iyayenk

i ne wai Na'ima" bata daina kukan ba tace "Dan Allah ki aramin kudi zan je gida" Amina na kallonta tace "Meyasa bazaki fadamin abunda ke faruwa bane Na'ima" sai tayi shiru bata daina kukan ba, Amina ta sake cewa "Dubu shida ne dani a account dina yanzu hak

a, zai kaiki gidan kuwa" Na'ima tayi saurin gyada kai, sai tace "Bari na ciro miki cash amma tukunna ki bari sai kin gama karban treatment dinki sai ki tafin" nan ma gyada kai kawai Na'iman tayi, fita Amina tayi taje ta ciro kudin sannan ta kawo mata, baya

n ta karba tayi godiya sai Aminan tace "I'll settle the bills, amma yanzu ki jira muga yanayin jikin naki tukunna" Na'ima ta gyada kai, fitan Aminan taji zuciyarta na zafi ta dafa hannunta a wajen tana kuka, kawai takai hannun ta cire drip din ta miqe daky

ar ta fice daga dakin, cikin sa'a bata hadu da Aminan ba ta fice daga asibitin, lokacin da fitan gari ya fara duhu amma magrib batayi ba, haka ta tari mashin tace ya kaita tashan da zata samu motan zuwa Abuja, da ta isa tashan sai ta nemi inda ake saida fa

ce mask dan daman hijabin jikin nata ta janyo har gurin hancinta, bayan ta siya ta nufi gurin motocin amma sai yaron motan yace mata kudin ta baze kai ta shiga motan ba, cikin sanyin murya tace "Ka taimakamin Dan Allah" yace "Yayata ga Daf can ta lodo kaya

n kamfani , itama Abujan ta nufa, kije ki biya dubu ukun ki zasu kaiki, ga mata can suna hawa ai" ya qarasa magana yana nuna mata Daf din ta juya tana kallon yanda mutane ke hawa bodin harda mata...

Haka ta biya kudin Daf din wani ya taimaka mata ta hau b

odin ta samu guri gefen wata mata ta zauna, a wannan lokacin Na'ima ji take ko keke akace tahau ya kaita Abujan zataje...da magriba suka kama hanya, iska kam sun shata a Express way dinnan amma haka ta jure tanajin kamar bazasu isa ba,

karfe biyun dare suk

a isa saboda gudun da motan tayi dan saurin isar da kayan da ta debo kar su baci, da sauran 2k din jikin nata ta tari taxi ta fada masa address din gidansu Nafisa, sai karfe uku taxi din ya sauketa a kofar gidansu Nafisan, ta daga kai tana kallon babban gi

dan nasu dayafi na Kano alatu, Hawaye ne taji ta kawo idonta ta nufi gate din tafara knocking a hankali, tayi knocking yafi a qirga kafin megadin ya fito cikin magagin bacci yana kallonta yace "Daga Ina?" rasa abunda zata ce tayi ganin haka ya sake tambaya

nta, tace "Gurin Nafisa nazo" sai yace "Kece wa?" tace "Sunana Na'ima", ce mata yayi ta tsaya sannan ya shige cikin gidan, bin layin tafarayi da kallo ganin ko ina gidan arziqi ne da wuta tas, can aka bude gate din Nafisa ta fito tareda Faruk, sai ta dan t

saya tace "Na'ima?" sauqe face mask din fuskanta Na'iman tayi, ai da gudu Nafisan ta taho ta rungumota ta fara kuka, sai sannan Na'ima ta fashe da kuka itama, Faruk sai kallonta yake yakasa magana, sai Nafisa ta dago tana kallon raunukan fuskan nata tace "

Muje ciki" ta kama hannunta suka shiga, a nan compound suka ga Mami da Abba sun fito suma, Mami da saurinta ta qarasa ta kamo Na'iman, ganin raunukan fuskanta yasa Mamin ta fara hawaye tace "innalillahi wa inna ilaihi rajiun" sai kawai ta rungumeta sosai a

jikinta, Abba ya dafa bayan Na'iman shima, Faruk har lokacin was in shock to see Na'ima like this..kuka Na'ima ta rinqa yi a jikin Mami, Nafisa na shafa bayanta tana kukan itama, sai can Mamin ta saketa tareda kama hannunta suka shiga cikin gidan Abba da

Faruk din suka rufa musu baya....

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 36

Shigansu falon ganin yanayinta yasa Abba cewa "Ku shiga da ita ta huta tukunna" haka Mami ta riqe hannunta suka nufi falonta na sama itada Nafisan while Abba da Fa

ruk suka bisu da kallo zuciyarsu babu dadi...

Ruwan wanka mai zafi Nafisa ta hada mata a toilet din sannan ta fito hannunta riqe da babban towel ta samesu har sannan zaune a bakin gadon Mamin na shafa fuskan Na'iman,  sai Mamin ta miqe tace "Ki shiga kiyi

wanka Na'ima Ina zuwa" bayan fitanta Nafisa ta miqa mata towel sai Na'ima ta dago kanta tana kallon Nafisan, hawaye Nafisa ta fara sai ta zauna nan bakin gadon ta riqo hannun Na'iman tace "Wallahi he'll pay for this, tun a duniya zasu ga sakamako daga shi

har uwarshi" ga mamakinta sai taga Na'iman na hawaye kuma tana murmushi , ahankali tace "Ya sakeni Nafisa, ya sakeni dai" Nafisa was shocked at that moment sai ta rungumota suka rinqa kuka hade da dan dariya tace "Alhamdulillah..Alhamdulillah"

Da Na'ima

tayi wankan tayi sallah sai Mamin ta shigo hannunta riqe da cup da kuma plate me dauke da fried egg da slices na bread, dora mata tayi anan kan gadon tace "Kici wannan sai kiyi bacci Habibti" karban plate din tayi ta sauqo daga gadon amma ta kasa ci, daky

ar suka tusata taci kadan sannan ta kwanta nan kan gadon Mamin, Nafisa ta rage Ac na dakin sannan Mami ta ja mata blanket suka fita, da farko tunani ne ya hana Na'iman bacci amma da yake ta debo gajiya sosai na mota sai baccin yazo mata babu jimawa..

Sai

bayan anyi sallan asuba Mami ta leqota taga har sannan tana bacci, bata tada ita ba ta juya ta fice daga dakin, Falon Abba ta nufa ta iddasa tareda da Nafisa, Faruk, Al'ameen amma banda Abu, fuskanta a hade ta zauna a gefen Abban tana kallon Nafisa, ganin

haka sai Nafisan tayi saurin cewa "Wallahi Mami nasha attempting fada muku abinda yake faruwa da ita amma ta hanani, daga baya ma daina fadamin matsalan nata tayi sai in ni na jata da hira" Faruk yace "To in da ta mutu fa?..sai kice da kinsani kenan" haway

e Nafisa ta fara tace "Kuyi hakuri" sai sannan Abba yace "Fada mana meya faru da ita har aka zo gandun nan"...A sannu Nafisa ta fara basu labarin tun farkon zuwanta gidan Na'ima da ta hadu da Bilal din, wani gurin in ta fado abunda ya farun sai Mami ta riq

e kai tana fadin "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" , Abba ma sauraronta yake cikin tsanaki yana gyada kai, zuwa sannan Nafisa kuka take tana maganan, Faruk sai shafa fuskansa yake zuciyarsa na tafasa, da Nafisa ta fada musu faduwanta akan glass dinnan har ta

je qauye Mami was more than shock, jikinta har rawa yake tana cewa "Wallahi sai munyi shari'a dasu, duk inda za'a je sai auren nan ya rabu, wannan ba 'yan'uwan ta bane sam" ganin yanda jikinta yake rawa yasa Abba dan riqota yace "Nima zan so hakan Fatima,

amma let's focus on sanity din Na'ima first, the girl was broken beyond pieces" kuka Mami fashe dashi tace "Kashe ta suka so yi, kashe ta suka so suyi wallahi" Al'ameen ma sai hawaye, Abba na dan shafa bayan Mamin yace "Mu gode Allah da basu yin ba" Mami t

a dago tace "Irin wannan uquban, da tayi suicide fah? kai innalillahi" rai a bace Faruk yace da Nafisa "Wai waye mijin nata ne?" sai sannan Al'ameen yace "Wani ne me zubin mahaukata haka, dan qwaya inka ganshi" Mami tace "Ni tun ranan da mukaje na kallesa

hankalina yakasa kwanciya da lafiya Na'ima ke zaune gidanta" Nafisa na share idonta tace "Ta fadamin ya saketa jiyan" Abba ya gyada tareda cewa "Good..saki nawa yayi mata?" ta amsa da "Bata fadamin ba"  Mami tace "Ai ko beyi sakin ba wallahi it's over, bal

le ma yayi" ta sake cewa "Jeki dubo ta ko ta tashi zuwa yanzu" miqewa Nafisa tayi cikin sanyin jiki ta fice daga falon sai Abba ya dauki wayansa yayi kiran doctorn sa da zai zo duba Na'iman.......

Daren ranan bayan isha, Hajiya na zaune a falo tana dann

a waya Bilal ya shigo, kallonsa ta tsayayi ganinsa adan birkice idonsa ya kada kamar wanda ya zuqi wani abu, tace "Ya dai babana, daga ina haka?" ko gaishe ta beyi ba yace "Abani abinci yunwa nakeji" sai ta kwala kira a shafa, cin abincin Bilal ya rinqa yi

babu qaqqautawa, gani haka yasa Hajiyan dake kallonsa cewa "Yau matar taka bata maka abinci bane Babana" sai ya ajiye cokalin yace "Na saketa" cikin shock Hajiya tace "Eh?" cigaba da cin abincin yayi yace "Dazu a asibiti tace in saketa, bansani ba ko ta t

afi qauyen by now" Hajiya dake cikin shock har sannan tace "Kai mahaukacin inane da kawai dan ta nemi sakin sai kayi batareda ka fadamin ba, Bilal bazaka barni in huta ba kai kullum" jefa cokalin yayi cikin plate

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login