Showing 63001 words to 66000 words out of 121625 words
dai da suka saba Hajiya na cewa "Kinji nayi rantsuwa Larai, wallahi ko zanyi yawo babu
kaya sai na raba Bilal da yarinyar nan, kuma indai Ina numfashi bazai aureta ba, ke indai ina numfashi Bilal baze auri wadda yake so har ransa ba, bazan raini dana na tsawon lokaci dayawa a rayuwa wata banza can ta rabani dashi sama ta ka ba, inaaaaa" Lar
ai tace "Gaskiyarki kawataaa kuma kedai mu zuba Ido akan wannan din, aikinsa sosai yake ci kinsani tunda Bilal yana daukan wayanki akai akai yanzu, da sannu komai ze zo qarshe" Na'ima ta kawo ruwan kafin ta ajiye Hajiya ta
harareta tace "Ke fita muna magan
a" tace "Toh" sai kuma ta gaishe da Larai dake bin ta da kallo ta juya ta fice, Larai tace "Kefa kawataa ga maganin matsalarki a gida kina gani amma idanunki sun rufe" Hajiya ta kyabe fuska tace "Mene?" Larai tace "Yarinyar nan mana da kike riqo, kiwon ki
ce sai abunda kika ce tayi zatayi, kuma kince Bilal din ba wani kulata yake ba ai ke hakan yazo miki a daidai" Hajiya ta sake cewa "Bangane ba kawata, fitomin a mutum" dan matsowa Larai tayi tace "Kinsan fa malamin nan yace yaron nan yana dawowa gida ayi g
aggawan yi masa aure sai mu bar masa sauran aikin ze ji da komai, da kike ikirarin zaki yiwa Bilal din aure toh wa kike nufin aura masa da toh?" sai Hajiya tayi shiru tana tunani, ganin haka yasa Larai cigaba da magana tace "Na daya ba son yarinyar yake ba
, na biyu kince daga kauye kawunan ta suka baku ita a gantale, na uku ke kika riqe yarinyar sai yanda kikaso zata tafiyar da Bilal, na hudu batada rawan kai da magana..toh me kikeso bayan nan" Hajiya tace "Allah ko..yanzu tayaya zan bullowa lamarin toh?" L
arai tace "Matso in miki dalla dalla"......
Ranar da Na'ima zata fara zuwa lecture tun asuba ta fara aikace aikacen gidan tana dokin zuwa school din, ita kadai tana aikin tana murmushi, bayan tayi wanka ta dauko gogaggun kayanta da hijabi dogo data ajiy
e wanda zata fara zuwa aji dasu, data shirya din ma a gaggauce taci abincin anan kitchen sannan ta nufi falon su Alhajin dan tayi musu sallama, bata samu Alhajin ba sai Hajiya dake zaune tana kallo, tsugunnawa tayi nan qasan carpet ta gaishe da Hajiyan, am
sawa tayi tana bin ta da kallo wanda yasa Na'iman duk ta taqura, sai tace "Makarantar zakije ne?" Na'ima tace "Eh" tace "Toh Allah ya bada sa'a Na'ima, Allah yasa kufara a sa'a" dan daskarewa Na'ima tayi jin yau Hajiyan nayi mata addua akan abunda ya shafi
rayuwanta sai kuma ta amsa tareda miqewa ta nufi fita daga falon Hajiya na bin bayanta da kallo...
Rataye da class bag dinta taje hall din da zasuyi morning lecture din, bayan ta samu guri dan baya haka malamin ya shigo, nan ya fara bada darasin Na'ima t
a maida dukkan hankalinta tana sauraro kuma tana joting key words a qaramin takardanta, sai da suka kwashe 2 hours kafin malamin ya fita, Na'ima ta dan yi miqa tana hamma na gajiya, yan class dinne suka fara fita da daddaya Na'ima ta dan kwantar da kanta a
kan desk ta rufe idanunta kamar me bacci, ji tayi a jikinta kamar ana kallonta sai ta bude idanun nata ahankali, Ido hudu tayi da wata budurwa yar baqa haka dake opposite dinta tana kallonta at the same time chocolate ne a hannunta takai baki tana gutsura
bata daina kallon Na'iman ba, dan gyara zama tayi ta miqe zauna tana kallonta, ganin Na'iman na kallonta kyam yasa ta dan daburce tafara murmushi sai kuma ta miqowa Na'iman chocolate din hannun nata alamun ta karba, murmushi ne yazowa Na'iman bata shirya b
a ganin wai miqo mata chocolate take kamar wata yarinya qarama....
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 28
Sake miqo mata chocolate din budurwar tayi sai Na'ima ta jijjiga kai har lokacin murmushin be bar fuskanta ba tana mamakin wannan b
aiwar Allah, kawai daga ganinta sai miqo mata chocolate, sai tace "A'a nagode"
budurwar ta sake cewa "Allah kisha, yanada dadi sosai" daga hannu kadan Na'ima tayi alamun "A'a" , kafin yarinyar ta amsa mata wata kawarta ta shigo cikin Hall din, dago hannu w
acce ta shigo din tayi tace "Nafee" sai wadda aka kira da Nafee din ta miqe ta fara tattare kayayyakin ta data baza akan desk dinta su wayanta, ear pod, car key, chocolate har da cheesy, kuma duk wajen ciro chocolate dinne ta fito dasu duka, bayan ta gama
saka kayan cikin wata qamar side bag dinta me kyau sai ta juyo ta kalli Na'ima tana murmushi tace "Sai anjima" Na'ima ta gyada kai tana bin ta da kallo ganin sai faman gyara wani ficicin gyale dake kafadanta takeyi, fita daga hall din Nafee'n tayi tare da
kawarta da ta kiratan, Na'ima bata dade ba itama ta tashi ta maida littafinta jaka ta fice dan dama shi kadaine lecture'n da za suyi ranan saboda farkon semester ne lokacin, abubuwa da dama basu miqe ba, sai da tayi tafiya me nisa sosai cikin makarantar ka
fin ta samu bus stop , nan bakin main gate aka sauqeta ta sake neman abun hawa, har qofar gida aka sauqeta ta sallami me mashin din ta shige gida, tunda ta nufi entrance din gidan take jiyo kamar muryan Hajiya na tashi daga cikin falo, ji tayi kamar karta
shiga gidan saboda yanda hankalinta ya tashi a take amma ta daure ta qarasa, bude kofan da zatayi tayi Ido hudu da Bilal daya doso kofan da nufin fita, fuskansa a hade cikin bacin rai yace "Get out of my way you B*tch" kafin Na'ima tayi azaman matsawa kawa
i ya qaraso ya hankadata da karfi saida ta bugu da jikin gini ta fadi nan qasa, dafa kanta tayi tadanyi qara, shi kuwa dama kansa tsaye wajen ya nufa ko kallonta bai sakeyi ba, Hajiya da ke ihun kiran sunansa ce ta biyo bayansa, sai ta tsugunna tana kamo h
annun Na'iman tace "Sannu Na'ima, tashi...tashi kinji" miqewa Na'iman tayi da taimakon Hajiya idonta yana kawo hawaye dan har lokacin mamaki ne da firgicin abunda ya farun shimfide a fuskanta, ita kuma me ta masa?..
Hajiya tace "Yi hakuri zai dawo ya same
ni ne" Na'ima ta jijjaga kai batace komai ba dan har wani sarawa kan nata taji yanayi, Hajiyan ta sake cewa "Sannu, kin dawo?" nan ma Na'ima ta gyada kai, sai ta sake cewa "Kije ga abinci can a kitchen na ajiye miki" wani sabon mamaki ne ya kama Na'ima
n dan tunda take Hajiya bata taba yin abinci ta ajiye mata na musamman ba saidai inta je school din tadawo ta girka, haka ta wuce dakinta tabar Hajiyan nan tsaye tana leqa compound din cikin tararradi...
Da Na'ima taje daukan abincin a kitchen sai taga
anyi girkin har da wanda yakamata tayi anjima dan shafa batanan sai yamma zata dawo, da mamaki ta zauna nan kitchen din taci..da dare tana dakinta shafa ta shigo ta isar mata da saqon kiranta da hajiyan keyi, samun Hajiyan tayi zaune falo sai ta juyo tace
"Na'ima sannu, ga magani nan nasan kanki ze yi ciwo na buguwan da kikayi dazu" to fah, abubuwan da Hajiyan ke yi sun ma fara daina bawa Na'ima mamaki sai kawai ta karba tayi godiya ta koma dakinta tana ta kallon maganin cikin al'ajabi...
Washegari sai qar
fe goma ta tafi makaranta shima sai da Hajiyan ta rakata da addu'o'i dataje yi mata sallama, as usual yau ma a seat din bayan ta zauna, kafin malamin ya shigo Nafisa ta shigo hall din, qarasowa tayi gurin Na'ima ta zauna a gefenta tana murmushi tace "Good
morning" cikin sanyin murya Na'ima ta amsa da "Morning yakike" Nafisa tace "Lafiya Alhamdulillah..Sunana Nafisa kefa?" ta amsa da "Na'ima" sai Nafee ta gyada kai tace "Nice name, ke 'yar garinnan ce?" Na'ima ta gyada kai tana mamakin extroverted attitude d
in yarinyar.
Sunanan zaune malamin da ze musu darasin ya shigo, kusan Rabin lecture din Nafisa tayi shi ne cikin danna waya, lokaci lokaci zata dago kanta koda malamin yana kallonta duk Na'ima na ganinta, da aka gama sai Nafisan
tace mata ta tashi su fita
, da farko qi tayi sai da Nafisan ta sake requesting sannan suka fita taren, anan cikin faculty sukayi sallah, bayan sun idar Na'ima ta miqe tana salaqa jakanta bisa kafada tace zata tafi, Nafisa tace "Muje muci abinci mana sai mutafi tare" Na'ima ta jijji
ga kai tace "A'a zan tafi yanzu Nafisa, sai anjima" sallama sukayi ta wuce gida..
Ranan wata asabar Na'ima taje gyaran falon su Hajiyan tasamu bata nan, tana cikin goge gogen Hajiya ta fito ta zauna tare da cemata sannu, can kuma sai tace "Na'ima in kin
gama kizo mana, inason magana dake" ta amsa da toh, sai da ta gama komai bayan taje ta ajiye kayan aikin nata sannan ta dawo, nan qasan carpet ta zauna cikin sanyin murya tace "Nagama Hajiya" gyara zama Hajiyan tayi tace "Ya makarantan toh, dafatan kina m
aida hankali" ta gyada kai tareda amsawa da "In sha Allah" cikin kwantar da murya Hajiyan ta sake cewa "ki maida hankali sosai kiyi karatu Na'ima dan muma munason kiyi karatun nan, kinga gatan da zakiyiwa kanki a yanzu shine karatun, da kuma aure Na'ima, b
a abunda nake miki fata irin kema kiyi auren nan ki kama dakin ki asirinki a rufe" Na'ima ta gyada kai, sai ta cigaba "Na'ima a riqon da na miki nasan babu cuta cikinsa, sannan ke amanace a hannuna, duk abunda zansowa yar cikina shi zan so miki" sunkuyar d
a kai Na'ima tayi tanajin wari iri a zuciyarta , Hajiya tace " Allah ya baki baiwar nutsuwa, hankali da kuma haquri Na'ima, kicigaba da tafiya a haka watarana zakici moriyan halayenkin nan masu kyau, inason halinki sosai wanda har hakan yasa nakeson hada z
uriya dake wallahi, ga dan'uwanki Bilal nan Na'ima, inason ki amince mu hadaku aure ko Allah zai sa ya nutsu sanadinki" zuciyar Na'ima saida ta buga da karfi a wannan lokacin, ta kasa ma dagowa ta kalli Hajiyan, suka zaunan shiru babu wanda yace wani abu s
ai qarar Ac dake aiki kawai akeji a falon, Hajiya ta sake kwantar da murya tace "Bilal dan'uwanki ne na jini Na'ima, kaf duniya bakida kamarmu a yanzu, kuma riqon da muka miki Allah ya gani shi kadai zai bamu ladan, ko auren Bilal kikayi baki biyamu ba" Na
'ima ta gyada kai har lokacin ta kasa magana saboda wani gumi daya fara yanko mata a goshi, Hajiya tace "ba lallai sai na baki lokacin yin tunani ba, magana ce da take buqatar Eh ko A'a" a wannan lokacin Na'ima tasani bawai amincewanta Hajiyan ke nema ba,
A'a...umarni ne kai tsaye Hajiyan ke bata ta auri Bilal din, kuma tasani rashin amincewanta daidai yake da katse duk wani walwala na rayuwanta daya kunno kai a yanzu, rashin amincewanta daidai yake da katse makarantar ta, daidai yake da har komawanta qauye
, toh inta koma qauyen menene makomarta a yanzu, talla ko auren lawan da har yau bata sake jin labarinsa ba?, jin shiru yasa Hajiya ta sake cewa "Ina sauraronki Na'ima" dago kai tayi cikin sanyin murya tace "Toh" ai atake fuskan Hajiya ya yalwanta da murmu
shi tace "Kin amince Na'ima?" ta gyada kai idonta na kallon carpet, Hajiya tace "Masha Allah, Allah ya miki albarka Na'ima, kema Allah ya baki masu miki biyayya, tashi kije abunki"
Miqewa tayi tanajin wani jiri na dibanta a haka har ta kai ga dakinta, za
ma tayi a gado tanajin zuciyarta na damqewa guri daya, hawaye ne suka fara taruwa a idonta sai ta kai hannu tana shafa kanta inda Bilal din ya bugata da ginin rancan hawayen na zubowa kan kumatun ta, har dare zuciyarta be rintsa ba dan data yi sallan isha
ma nan kan darduman ta kwanta...
Cikin wannan halin Na'ima takai kusan qarfe daya saura idonta biyu tana saqa da warwara, horn din motar Bilal tajiyo sai da zuciyarta ya tsinke dan a tunaninta da bata ganinsa kwana biyu agidan baya garin ne, tananan kwanc
en tajiyo tashin muryan Hajiya da Alhaji a falo, sai dai yau kuma
masifa take jiyowa Alhajin nayi a falon Hajiya na tausarsa, qara juyawa Na'ima tayi ta ja hijab dinta ta rufe har qafarta tareda addu'an bacci yazo mata koda kadan ne....
A washegarin Sunda
y ma haka ta wuni cikin wannan kuncin na tararradin maganar da Hajiyan ta mata, har zuwa ranar Monday bata warware ba, da taje school ma kasancewan tayi latti sai ya zamto cikin sauri tayi excusing kanta ta shiga hall din har bata lura da Nafisa data dan
dago mata hannu akan ta zo gurinta ba, da aka gama darasin ma cikin sauri ta tattare kayanta ta fice daga hall din...
Hajiya ce kwance kan gadon dake dakin Alhaji while shi yana bandaki, bayan ya fito ya kwanta nan kan gadon yaga still bata kashe side l
amp dinta ba idanunta bude tayi matallafi da hannunta alamun tayi nisa cikin tunani, juyowa Alhaji yayi yace "Menene ya hanaki bacci Ladi, kinada damuwa ne?" Shiru tayi har se da ya sake maimaita mata tambayan sannan ta dan miqe zaune tana gyara zamanta ji
kin fuskan gadon, cikin kwantar da murya tace "Alhaji wata magana nakeson muyi" yace "Inajinki" tace "ina neman alfarman ka hada auran Na'ima da Bilal" shiru Alhaji yayi sai kuma ya miqe zaune shima yace "Kema tunanin da yazo kanki kenan" ganin kamar zance
n nata zai samu guri a garesa yasa ta juyowa gaba daya tana fuskantarsa tace "Me ka gani Alhaji" ya sauqe numfashi sannan yace "Wallahi na dade Ina saqa abunnan a zuciyana, amma kinsan dan yau, ba'a garaje a lamarinsa, na yaba da hankalin yarinyar sosai am
ma kuma kinga shi Bilal watacan yagani yanaso kuma itama Na'iman bamusan zuciyarta ba kar mu mata dole" Hajiya tayi saurin cewa "Duk wannan ba matsala bane Alhaji, kuma Na'iman da bakinta ta fadamin tanason Bilal din" Alhaji yadan ware Ido yace "Da kanta k
uma?" tace "Zan maka qarya ne Alhaji, ai gaka ga itan sai ka kirata gobe ka tambayeta" yace "A'a bawai ban yarda bane, yarinyar nan 'yarki ce ai, kinfi kowa saninta, zan dai kirata in tambayeta dan fita hakkinta ne" farin ciki ne ya lullube Hajiya ganin ha
qarta na neman cimma ruwa tace "Allah ya kaimu goben"......
Washegari da safe bayan Alhaji yagama breakfast yana zaune tareda Hajiyan ya kira Na'ima, shima sai da ya fara yabon halayenta sannan ya dora da maganar da sukayin da Hajiya har da cewa cikin i
kon Allah da wannan kyawawan halayen nata zata iya chanja Bilal , tunda Na'ima taji hanyar da zancensa ya dauko tasha ruwan jikinta, sai da yakai qarshe yace "Inason jin abunda yake ranki Na'ima karki ji nauyi na, Uba nake a gurinki, wannan batu ne na rayu
war ki, ke zakiyi rayuwan auren dan haka kina da 'yancin fadin Eh ko A'a" sai a lokacin Na'ima ta dago kanta ta kalli Hajiya dake kallonta kyam cikin Ido itama tana jiran amsarta, duqar da kanta ta sake yi sai ta gyada kai alamun "Eh" tanajin qunci na daba
ibayeta, tayaya zasu ce zasu aura mata dansu wanda tana gani suma yana neman gagararsu, Albarka Alhajin shima ya rinqa saka mata yace ta tashi ta tafi, cikin sanyin jiki ta miqe ta nufi fita daga falon suka dan bita da kallo, saida ta fita Hajiya na murmus
hi tace "Ma Sha Allah kaga abunda nake fada maka ko" Alhaji ya gyada kai shima yana murmushin, tace "Yanzu dai kasamu lokaci kaje qauyen nan ko ka kira su ka sanar musu, yarinya ta amince me zamu jira kuma, Bilal dai munsan ta yanda zamu bullo masa shi" Al
haji yace "Gaskiya ayyuka sun min yawa kwana biyun nan zan kira Ayuban yazo muyi magana" tace "Duk daya ai, gaskiya banason abunnan ya dauki lokaci Alhaji, ka biya masa sadakin ayi auren inyaso ko daga bayama ayi lefen" Alhaji yadan hada rai yace "Meye kik
e cewa haka ne Ladi, 'yar tawa za'ayiwa aure babu lefe" tace "Toh ai naga ze dauki
lokaci ne" yace "A'a ko zai dauki lokacin dai sai anyi mata lefe, ki yi lissafi sai in tura kudin, in kuma hakan ze cinye miki lokaci ga Sufi nan babu abunda bai iya ba" tay
i saurin cewa "Za'ayin ma Alhaji wane Sufi kuma, kamanta nima Na'ima 'yata ce, in sha Allah komai za'ayi" da haka Alhajin ya miqe ta rakashi nan bakin falon sukayi sallama ya wuce gurin aiki driver na jiransa a waje, wayanta ta dauka tayi kira, ana dauka t
ace "Kawata abun dai yanata tafiya as planned, nagode da wannan shawara taki" ta dayan bangaren larai tace "Na fada miki ba wani wahala zakisha ba ai, yanzu na gama magana da dan haure ma, yace indai akayi auren nan to Bilal din ze zauna anan Kano, kawai d
ai ba lallai yaso yarinyar bane saboda har yanzu abun tsinannniyar can din be sake shi ba" Hajiya tace "Ita wannan ya dama, tunda ze dawo gabana Ina kallonsa ai an gama komai kuma, batun son yarinya kuma ai dama baso nake ya so ta ba tun farko" Larai tayi
dariya sai Hajiyan ta sake cewa "Har yanzu yananan be koma ba kamar an masa dauri aqafa" Larai tace "Bazai kuma koman ba".....
Da taje makaranta ranan tana shiga class dinda zasuyi lecture din Nafisa ta dago mata hannu tareda kiran sunanta tana murmushi
, qarasawa tayi ta zauna kusa da ita suka gaisa fuskan Na'iman babu yabo babu fallasa, Har aka gama darasin batasan me akeyi ba tayi nisa a tunani, da suka tashi ma sallama tayi