Showing 6001 words to 9000 words out of 121625 words
/>
Bintu Musa
✍
️
Chapter 05
Washegari da safe suka kai yayan nasu Airport da motan Anty Amnah, hatta Na'ima saida taji kaman tayi kuka balle Nafisa da ta fara hawaye.
Faruk na kallonsu yayi murmushi sanna
n yace "Come on girls, nan da 3 weeks or so zaku dawo fa kuma"
Nafisa ta qarasa kusa dashi ta riqo hannunsa bata bar hawayen ba, yana murmushi ya zare hannunsa daga nata, sai ya dagawa Na'ima hannu alamun Bye itama ta daga nata hannun cikin sanyin jiki, d
a haka ya juya na nufi cikin waiting lounge na Airport din.
Na'ima ta dan daga murya tace "Allah ya kaiku lafiya Yaya" sai da ya sake juyowa yayi musu murmushi sannan ya bacewa ganinsu. Haka suka koma gurin motan su cikin sanyin jiki suka bar Airport din.
Bayan sun koma gidan Anty Amnah suka shirya kayansu tareda mata sallama suka tafi train station dan komawa Oxford saboda motan da Faruk din yaje daukansu na Anty Amnah ne.
After that memorable weekend in London, rayuwa ta cigaba yayin da suka maida han
kali kan karatunsu wanda saura few months su gama.
The weeks that follows sunyi
qoqari wajen hada wasu daga cikin thesis dinsu before the spring break, don dama auren Salma yazo within their break ne, hakan yasa lokacinsu yazamo swamped with schoolwork,
duk da basa zuwa school din akai akai don sun shigo phase na research a fagen karatun nasu, wani lokacin raba dare suke zaune nan falo kowacce tana nata aikin bisa laptop babu bacci.
Duk da ayyukansu na makarantan da suka sako gabansu hakan bai hanasu
zaman hira da cinye cinyen banza da hofi ba, dan nafisa ta koyawa Na'ima cinye cinyen itama basa zama shiru haka nan, aikace aikacen gidan nasu
kuwa daman tun farko basu raba a junansu ba, duk wacce ta samu time yi take wanda dama Na'ima ce rinjayen aikin
da dafa musu abinci most at times, kuma hakan bai taba damunta ba infact she love doing all the work tabar Nafisan ta huta because she'll ba glad to do more than that to Nafisa.
Ance kaso mai sonka, to hakan take wajen Na'ima, tanason kyautatawa Nafisan,
most at times takan shiga dakin Nafisan ta gyara ko Ina ta wanke toilet sannan ta debo kayanta na wardrobe ta goge mata su tas ta jera. Wani irin bond ne mai tsafta a tsakaninsu wanda in ba wai sani kayi ba bazaka taba cewa qawance ne mafarin haduwarsu ba.
Gashi dai ko daga yanayinsu mutum zai ga banbancin dabi'a sosai yayin da Na'ima ta zamo mara hayaniya, dan in kaga tana dogon surutu to da Nafisa ne, ga hakuri da shanye komai a ciki while Nafisa kuma mutum ce mai surutu da rashin hakuri a wasu lokutan, B
ut friendship blends them together and they became sisters from different mothers.
As lokacin tafiyansu gida yana kusantowa sai Na'ima ta zamo so uneasy ta zamo wata sanyi sanyi har Nafisan ta fara ganewa amma batayi mata magana ba saboda wasu dalilai.
Ana gobe zasu tafi, Na'ima na dakinta tayi wanka tana zaune gaban mirror tana shafe shafen ta na al'ada, bayan ta gama ta cire hulan wankanta tana kallon kitson da sukaje saloon aka mata sai ta dauko wani hair oil tafara shafawa acikin lines na kitson tan
a tunani, bayan ta gama ta maida hulan ta saka kayan baccinta ta hau gadon ta kwanta, ji tayi ta kasa baccin kuma, sai ta miqe zaune ta jawo laptop dinta dake bedside drawer shima zata dan duba ko zai dauke mata hankali, shima tana dannawa ne amma absent m
indly, daga karshe kawai ta miqe ta tafi kitchen,
bude cupboard tayi ta debo chocolates da cheese balls ta fito ta nufi dakin Nafisa, tana shiga ta sameta ta dora box dinta akan gado ta tsaya gaban wardrobe tana zaben kayan da zata koma gida dasu, Na'ima
ta qarasa ta zauna kan gadon tana cewa "Wai dama baki gama hada kayan naki ba?" Nafisa ta kama qugu tana nazarin kayan wardrobe din tace "Sai na hada sai kuma inji ba dasu nakeson tafiya ba" Na'ima ta girgiza kai tace "Allah ya shiryeki Nafee, hada kayan m
a saikinyi ruwan ido bayan tulin kayanki da kika baro can gida" sai Nafisa ta juyo tace "Hey...it's not my fault, I want nice and big collections" Na'ima tayi murmushi tace "Ruwan ido dai, bawani nice or big collections, kowanne so kike" sai Nafisa tayi mu
rmushi tace "wlh kuwa, duk wanda na dauko sai inga inason bari, kawai zan barsu Inaga" Na'ima tace "kinjiki, sai munje ki damemu da mita akan da kin dauki wasu, matsa in nema miki" sai Nafisa ta amsa da toh tareda dawowa bakin gadon ta dauki chocolate daya
zata bare. Miqewa Na'ima tayi ta tafi wajen kayan tana dubawa sukayi shiru na wasu mintuna sannan cikin kwantar da murya Nafisa tace "Na'ima in bakyason komawa babu me saki dole..you know that" juyowa na'ima tayi tace "Nafee we've talked about this over a
nd over and i said Yes, why don't you believe me?" Nafisa tace "The eyes don't lie Na'ima, I saw it in you, how you became silent these days, shin in tambayeki...why do you choose to deprive yourself happiness ne wai Na'ima?" Ta miqe ta qaraso gaban Na'ima
n tace "That pathetic, stupid person!! Should be the one hiding, not you" ta sake dafa kafadan Na'iman tace "Those vicious and wicked people should be the one's living unhappy now, not you Na'ima"
Fashewa da kuka Na'ima tayi sai Nafisa ta riqe ta suka zau
na kan gadon, itama Nafisan na hawaye.
Tayi kukan sosai da kanta tayi shiru tana goge idonta, cikin sanyin murya tace "Tsoro nake kada ayi forcing dina back to where i left, I don't know how to face what I've left Nafisa" sai Nafisa tayi saurin cewa "Abba
da Mami bazasu taba barin hakan ya faru ba kinsani"
Na'ima ta sunkuyar da kanta tace "Amma dole watarana hakan ya faru" Nafisa tace "Bance baza kije wajensu ba tunda bakida kamarsu a duniya, but forcing you back dinne ba wanda zai saki hakan, kuma kisan
i Allah yana tare dake a komai" shiru Na'ima tayi batace komai ba tana share hawayenta idonta na kallon kasan dakin.
ganin haka sai Nafisa ta cigaba "We will always be there, abubuwan da suka faru sun riga da sun faru, bance babu sauran gwagwarmaya agaban
ki ba amma what I want you to do is to Embrace life strongly as it comes, life is too short for you to be stuck up because of that stupid man, Embrace love when you find it, rayuwar nan bata jiran kowa Na'ima, it's high time you actually start living your
life to the fullest" tana gama fadin haka ta miqe ta koma wajen kayanta tafara diban na tafiyan, Na'ima na nan zaune tayi shiru tana maimaita maganganun Nafisan, encouraging words din suna shiga cikin kwakwalwanta da daddaya.
May be it's high time she st
art seeing all of it in a different direction, duk abubuwan da suka faru a baya zata ajiyesu for now idan lokacin komawanta yazo Allah zai mata jagora.
Anan dakin nafisan ta kwana sukayi ta hiransu kafin suyi bacci, Nafisa na bata labarin yanda Umar ya da
meta da kira wai zaizo daukan su a Airport in sun sauqa, Na'ima tace "Blocking dai ya fasu" sai Nafisa ta dungureta da hannu tace "kin shiga uku da rashin mantuwa" Na'ima ta kama dariya tana dan girgiza kai.
Wayewar washegari tun asuba suka tattare gida
n sukayi storing abunda sukasan zai baci kafin su dawo sannan suka kira Uber ta kaisu Airport dan jirgin safiya zasu bi.
Karfe shida da wasu 'yan mintuna jirginsu ya tashi zuwa Nigeria zuciyar Na'ima cike da wani irin yanayin da bazata iya fassarashi ba.
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 06
Tsaye Ahmad yake a parking space dake cikin compound din babban gidan nasu, Gida ne babba me cike da alatun rayuwa wanda kana gani kasan naira ta zaunu gurin mazauna cikinsa.
Yana tsayen ne jikin m
otansa da ya bude driver seat kuma bai shiga ba, wayarsa yake dannawa cikin nutsuwa yana nazarin saqon da aka turo masa.
Mai gadin gidan ne ya qaraso ganinsa tsaye nan tuntuni amma bai shiga motan ba, sai yace "Yallabai ko da abunda za ai maka?" Ahmad ya
dago kansa yana kallon maigaidin yace "A'a yakasai jeka abunka" Yakasai ya dan risina yace "Toh yallabai afito lafiya" ya juya yana komawa bakin aikinsa.
Shiga driver's seat din yayi batareda ya kulle kofar motan ba ya miqo kafarsa daya waje ya cigaba da
abunda yakeyi.
Yananan zaune for almost twenty minutes wata mota ta shigo compound din, bai dago kansa ba saida ta qaraso tayi parking dan nesa dashi sannan ya daga Ido yana nazarin motan, ganin wacce ta fito daga driver's seat yasa nan take yayi danasani
n tsayuwarsa a wajen bai fita ba, aranshi yana cewa me yasa tun dazun bai tafi ba in yaso sai yadawo inya nutsu ya duba saqon nashi.
Laila ta juyo ta kalleshi, take ta fara murmushi tana gyara gyalenta da ta saqala a kafada, a daya side din ma qawartace t
a fito suka taho tare Laila na gaba tana qarasowa garesa cikin zumudin ganinsa.
Duk wani mood din fitan yaji ya fita daga ranshi, sai ya fito daga motan ya rufeta yana maida wayansa aljihu idonsa na kallon wani gurin basu ba, qarasowan su wajen Laila tac
e "Yaya ashe kadawo?..Ina wuni" anutse Ahmad ya amsa da "Lafiya" batareda ya amsa tambayanta na farko ba, qawarta mai suna Luba ta gaisheshi ya amsa shortly, sai Laila tace "Nakira ba adadi baka dauka ba, i just want to know how you are" ta qarasa tana mur
mushi bakinta kamar gonar auduga, sai lokacin Ahmad ya dan kalleta, yace "Oh really? may be bana kusa"
Amasanshi ta qular da ita wanda har yanayin fuskanta yaso nunawa amma tayi saurin waskewa da wani murmushin tace "Kai yaya, I've been calling fa" bai b
ata amsa ba ya dago hannunsa yana duban wristwatch dinsa yace "I'm late Laila, and nayi mantuwa" ya juya tareda cewa "ki gaida su Mummy" da haka ya nufi babban part dinsa shida Adam wanda ke nan compound din gidan, yabarsu Laila nan tsaye a parking lot sun
a bin bayansa da kallo.
Laila ta cika kamar zata fashe, qawarta ta tabo kafadanta tace "Kawata waye wannan din? kinga yanda yake mana magana kuwa, ko shine Ahmad din naki?" Laila bata juyo ba balle ta bata amsa ta qurawa side din su Ahmad ido ta jijjaga
kai tayi kwafa tace "Daman naji labarin yadawo nazo na ganewa idona" Luba tace "Uhm, guy dinnan is full of himself" Laila tace "Zanyi maganinshi ne, nikuma!!...yakusa zuwa hannu wlh" Luba na kallonta tace "A yanda kike rawan kafa a gabansa dinne zakiyi mag
aninsa, girl you must be fooling yourself" sai sannan Laila ta juyo tana murmushi kadan tace "Kedai ki zuba ido ki gani" ta nufi gurin motanta tace "Mutafi" Luba tace "Ha'aa bazamu qarasa ciki mu gaisa da mutanen gidan bane?" Laila ta wani hade fuska tace
"Nagama abunda yakawoni nidai, in zaki zo mutafi to" sai Luba ta kyabe baki ta taho suka shiga motan.
Haka Laila ta tada motanta tayi reverse babu kunya megadi ya sake bude musu gate suka bar gidan batareda ta qarasa ta gaishe da iyayen Ahmad ba, wanda ma
haifishi ya kasance yayan nata mahaifin.
Bayan Ahmad ya shiga part din nasu yawuce Adam dake zaune nan falo yana kallo ya nufi stairs zaije dakinsa dake sama dan canja kayan jiikinsa saboda dagaske kuma fitan ya fice masa arai, bayan yayi changing into
qananan kaya masu kyau sannan ya dawo nan falon ya wuce qaramin dining area ya hado tea dinda Mamma, mahaifiyarsa ta aiko musu dazu.
Zama yayi akan sofan dake falon sai Adam ya juyo ya kallesa yace "Badai har kaje kadawo ba" calmly yace "Nafasa fitan" sai
Adam ya gyada kai ya maida hankali kan kallon wrestling din da yake yi, shiru sukayi while Ahmad ya ciro wayansa yana dannawa as yana sipping tea dinsa a nutse.
Bayan wasu mintuna Ahmad ya ajiye cup din shayin yana kallon Adam yace "The investors have re
ached out, they want a meeting" Adam ya sake juyowa yace "Wait....about the app?" Ahmad ya amsa da "Yes" sai Adam yace "But for real though, you really want to sell it?" Ahmad ya gyada kansa, Adam ya cigaba "Dude, you have almost 6.5 million users, this is
huge you
know" a nutse Ahmad yace "I know, but they're offering big money on this. Beside, this year nakeson launching sabon ai" Adam na kallonsa yace "It's settled then, a Ina sukayi setting meeting din?" Ya amsa da "London, but bamuyi arranging date ba
tukun" sai Adam yace "Okay, dama ka dade baka leqa branch nacan ba, this is your chance" Ahmad yayi murmushin gefen baki yace "Mundade dai" Adam yace "Dude I'm not the head, You are." ya daga kafada yace "It's part of your job too" murmushi kawai Adam yayi
yace "Anyway, I'm happy for you...for real" Ahmad yace "Thanks man" sai ya miqa hannu ya dauko ipad dinsa dake kan center table ya budeta yana qara duba emails dinda investors din suka tura masa.
Wuraren qarfe sha biyu da rabi na rana jirginsu Na'ima
ya sauqa Abuja, suka fito duk a gajiye
Bayan sun gama duk wasu formalities suka wuce bangaren arrivals, Nafisa sai juye juye take tana neman wanda yazo daukansu, can tayi tsuka tace "Yaron nan bai iso ba kenan" Na'ima tace "waye yaron, Umar?" Nafisa ta ju
yo tace "Wani Umar kuma, haka kurum yaga kamar nima ina zumudin ganinsa ne" Na'ima batasan lokacin da dariya tazo mata ba tace "Nafee babu mai iya miki sai Allah" sai Nafisa ta juya tana neman qanin nata da Mami tace zaizo daukansu tace "Sis mazan ne kamar
zuma suke saida wuta" Na'ima jijjaga kai kawai tayi batace komai ba.
Can gefe suka hango Al'ameen riqe da name sign da sunayensu rubuce ajiki, shima hangosun da yayi sai ya ajiye sign din ya nufosu yana fara'a su Na'ima suka nufeshi suma, qarasowa yayi t
areda yin side hug wa nafisa sannan ya juyo yana kallon Na'ima yace "Anty Na'ima ya zaman gajiya" tace "Alhamdulillah"
sai ya riqe wasu daga akwatin nasu suka qarasa wajen motansa Nafisa tace "Shine ko ka fada mana ka dawo sai gurin Mami muke jin labari"
yana murmushi yace "Surprise naso muku fa Mami ta batamin shiri" Suma murmushin sukayi suka shiga motan, bayan ya gama sa kayansu a booth din ya shiga motan yaja suka bar airport din suka dau hanyan gida.
Cikin 40 minutes suka isa unguwar su Nafisan, A
l'ameen yayi horn a kofar wani babban gida megadi ya taho da saurinsa ya bude musu, babban gida ne wanda kana gani kasan masu shi dasu ake murza nera a cikin qasar, suna shiga babban compound din suka hango Mami tsaye a entrance din building din ta fito ji
n qaran mota, dasauri Nafisa ta fice bayan sunyi parking tayi wajenta da gudu gudunta, sai Mami ta ware hannu tana dariya tace "Oyoyo yaranaa" Nafisa ta rungumeta tana murna, cikin nutsuwa Na'ima ta qaraso tana murmushi itama, sai Mami ta sake Nafisa ta ru
ngumota itama tace "Welcome habibti" luf Na'ima tayi a jikin Mami tana jin kaso tamanin cikin damuwan da ta taho dashi yana washewa a hankali jin embrace din Mamin, cikin raha suka qarasa cikin main falon gidan suka bar Al'ameen yana debo musu kayan nasu m
egadi yana tayasa.
KUNCIN ZUCI
📖📚
Bintu Musa
✍
️
Chapter 07
Sunga gata gurin Mami don tun kafin suyi wanka su huta ta fara sallamansu da home made juices datayi musu na musamman. Al'ameen ya shigo musu da kayan Mami tasa shi yakai musu dak
unansu.
Bayan sun huta kadan anan falon suka nufi stairs gurin dakunansu dake jere gefen na Mamin, dakin Na'ima ne daf da Falon Mami while Nafisa tana opposite din su a corridor'n.
Na'ima na shiga dakin tasamu sai tashin qamshin turare yake, ko ina neat
ta miqa hannu kan gadon ta dauko teddy bear din da Abubakar ya taba kawo mata farkon zamanta a gidan, sai ta rugume teddyn tana bin dakin da kallo kamar yau ta barshi, qarasawa tayi ta bude babban wardrobe dinta, nan ma ta ga kayanta jera cikin tsanaki sa
i qamshi suke ga sabbin kaya a gefe masu yawa an jera matasu wasu a hanger, wasu kuma a linke neatly,
tana nan tsaye gaban wardrobe din a sannu farin ciki yake samun waje cikin zuciyarta aranta tace "I missed this" lallai tayi missing pampering din da Mam
i take mata, and she made the right choice coming back.
Mami ce ta shigo hannunta riqe da sabbin towels wankakku a linke tana fadin "Kinga dazu fa nace Lantana ta jera muku su a bandakunan ku, ashe ta manta" sai Na'ima ta qarasa da fara'a zata karbesu dag
a hannun Mamin amma bata miqa mata duka ba ta dauki uku ta bata tace "Sauran na Nafisa ne" Na'ima tace "Bari nakai mata Mami" tace "A'a kiyi wankan tukunna sai ku sauqa qasa ga abinci can" Na'ima ta gyada kai tareda amsawa da "Toh" sai Mami tayi murmushi
tana kallonta tace "Welcome home daughter" itama murmushin tayi kawai batace komai ba Mami ta juya ta fita daga dakin tajiyo shiganta dakin Nafisa.
Bayan tayi wankan ta shirya cikin simple black abaya mara nauyi tayi daurin dankwali da mayafin ta fice, t
asamu Nafisa a falon har ta fito itama suna magana da Al'ameen da Abubakar wanda yadawo daga school babu jimawa.
ganinta yasa Abubakar tasowa da