Showing 93001 words to 96000 words out of 121625 words

Chapter 32 - KUNCIN ZUCI Complete

30 Aug 2026

13

Auta, ina nan dake zai zo har gidan nan kinji, badai koroki sukayi ba, zasu san sunyi

hakan dukansu har Amnah'n" Laila na kuka tace "Narantse ko bazan aureshi ba wannan sh*giyar bazata aureshi ba Mummy" cikin lallami Mummy tace "Balle ma zaki aureshi auta, duk abunda kikeso sai kin samu matuqar ina raye kinji" Laila ta gyada kai tareda kwan

ciya nan kan kujeran Mummy na shafa bayanta tunani iri iri nazuwa mata kanta, inaa ai dukiyar Ahmad 'yarta ce kawai zata moresu....

Ana gobe Ahmad zai tafi Italy din yazo gidan Anty Amnah da dare, Na'ima na daki jabeer ya shigo ya fada mata zuwan sa, Ja

far dake gefen ta suna kallo a laptop ya tashi da gudunsa ya fita, kasa fita tayi kuma bata cigaba da kallon ba, can taji shigowan message dinsa awayanta dake gefenta, murmushi tayi bayan ta karanta content din, ta ajiye wayan

batayi reply ba, can sai ga N

afisa ta shigo tana murmushi tace "Kinsa Yaya na yana ta raba idanu, na neman ta inda zaki fito" Na'ima na murmushi cikin sanyin murya tace "Ni ba gurina yazo ba" zama a bakin gadon Nafisan tayi tace "Kiji tsoron Allah Bobo, yaushe muke sanin lokacin tafiy

an Yaya Ahmad har ya mana sallama" dan girgiza kai Na'ima tayi tace "Ku yazo yiwa sallama bani ba" dariya kawai Nafisan tayi sannan tace "Yanzu yake fada mana ashe Italy zai tafi gobe, da kamar zan fada masa zamu bisa amma nasan halinki shiyasa nakeson jin

ta bakinki" aikuwa nan take Na'ima tace "kije abunki, nidai bandani" Nafisa ta hade gira tace "Haba Na'ima, Rome fa ake magana, it'll be like a vacation" Na'ima ta sake girgiza kai, cikin masifa Nafisa tace "Mufa beach resort zai kama mana, yana can yana

aikinsa mu na hutawan mu, mun gama makaranta kuma me ya saura in ba yawon bude Ido ba" shiru Na'ima tayi at first sannan tace "Hakan bazai zamo burden ba, kinyi maganan dashi?" ta amsa da "Waa? burden ta ina, ai in qasa goma kikace muje Yaya zai kaimu, tas

o muje ni zan fada masa" da haka ta kama hannun Na'iman suka fice, ganin yana tare da Anty Amnah yasa Na'iman jin kunya saboda kallon da yake ma ta ko a jikinsa, sai da suka zauna tace "Ina wuni" yana kallonta yace "Lafiya Na'eemah" Anty Amnah ta cigaba da

maganan da suke yi din tace "Son ai ka dade ma this time, ko ayyuka ne sukayi yawa a branch din ku na nan din?" Ahmad yadan shafa kansa a nutse yace "Eh momma, but in na dawo zan koma Lagos in sha Allah" Nafisa tace "Yaya ka tafi damu Rome din" Anty Amnah

ta girgiza kai tana murmushi tace "Nafisa sarkin yawo" tana dariya tace "Graduation trip ne Anty" Ahmad ya gyara zama tareda dauko wayansa yace "It's settled then" dan daga hannu Nafisa tayi tana murna tace "Thank you Yaya, amma dan Allah muje da Lauren,

wallahi in ba haka ba zatace naci amanan ta" daga Anty Amnahn har Ahmad din dariya sukayi wanda yasa Na'iman kallon Ahmad dan bata taba ganin dariyarsa haka ba, yana danna wayar tasa ya dago kai suka hada ido tayi saurin dauke kai tana murmushi, sai ya tur

a mata wani text din kamar haka.

"I know this will be the best working trip i've ever had"

Bayan ta karanta ta dago kanta taga yana kallonta fuskansa dauke da murmushi me kashe mata zuciya...

KUNCIN ZUCI

📖📚

Bintu Musa







Chapter 39

A

daren Na'ima suka fara shirin tafiya Rome tareda Ahmad, tana zaune bakin gado Nafisa sai jeka dawo take a dakin tana hada musu kayansu, sai da tayi arranging creams and oils dinsu sannan ta kalli Na'ima tace "Bobo please dubamin weather forecast dinsu, in

da dan sanyi sai in hada mana da light jackets" dauko waya Na'ima tayi ta fara dubawa sai taga wani message din Ahmad ne ya shigo wayan nata, murmushi tayi ta koma baya ta jingina da gadon suka fara chatting sama sama dashi, wanda mostly short and casual m

essages ne akan tafiyan nasu amma Na'ima jinsu take har ranta, sai da Nafisa ta fara jera kayan ta juyo tana kallonta tareda riqe qugu tace "Sannu Na'ima" da sauri tace "Eh?" Nafisa tace "The forecast?" sai sannan ta tuna, tana murmushi ta sake dubawa ta f

ada mata, kiranta video call yayi da kamar bazata dauka ba da farko, sai can ta dauka

fuskanshi ya bayyana yana kwance akan three seater na falonsa, kallonta ya tsaya yi sai ta juya kai dan har ga Allah abunda yasa batason video call dashi kenan, direct ta

ke kallon idanunsa da suke mata kaifi dayawa, ganin taqi juyowa yasashi yin murmushi a nutse yace "Rowan fuskanki zakimin Babe" ta girgiza kai tana murmushi, dan juyowa tayi taqi kallonsa a ido, ganin kunya ya cikata yasashi kwantar da murya, ahankali yace

"Inason kunyan nan naki Na'eemah" batace komai ba sai murmushin da yaqi barin fuskanta, wani farin muzurun mage ta gani ya hau kan fuskan Ahmad din sai ya fara lasan wayan, dariya ta fara ganin Ahmad na qoqarin tureshi daga kan fuskansa, shima dan dariyan

yafara yace "Babe, meet Simba" ta dan daga hannu cikin sanyin murya tace "Hi Simba" kamar magen yaji me tace sai yayi meow, nan ma dan dariya sukayi Ahmad yace "Ya gane kin kirashi fa" ta sake cewa "Nice to meet you Simba" kirane ya shigo wayan Ahmad din

yayi excusing kanshi a gurin ta sai ta gyada kai sukayi sallama, sai sannan ta dago kai taga har Nafisa ta gama hada musu kayan tsaf tana saka musu accessories dinsu acikin qaramin jaka....

Washegari sai karfe goma na safe suka fara shirin tafiyan, Na'ima

ta shirya cikin wani classy black abaya da ya haska farin fatarta sosai, nan bakin mirror ta tsaya tareda yin light makeup na lip gloss and powder a fuskanta, Nafisa ma abayan ta saka amma nata milk color, Kiran Mami ne ya shigo wayan Nafisan sai tace ta

saka a handsfree, bayan sun gaisa ta tambayesu ko sun shirya tafiyan, dan sun kirata har Abba sun sanar musu da tafiyan tun jiyan, bayan sun amsa mata sai tace "Ku kula sosai fa, banason shiririta" suka amsa da toh sannan tace "Allah ya kaiku lafiya, Allah

yayi albarka" da haka sukayi sallama suna amsa addu'an nata...Ahmad ne ya zo daukansu shida drivern sa, Antyn Amnah na gida lokacin dan ranan bata je asibitin bama wai batajin dadin jikinta su twins kuma suna school, har bakin motan ta rakasu sukayi salla

ma tayi hugging dinsu, sai da suka biya aka dauki Lauren sannan suka wuce airport din, acan suka tadda Lamin a tsaye yana jiransu a waiting lounge, handshake sukayi da Ahmad, Lamin na cewa "Hey man" Ahmad ya gyada kai kawai, sai Lamin din ya kalli Na'ima y

ana murmushi yace "Our sleeping beauty princess" Ahmad ya kalli Na'iman yace "Karki kulashi" sai tayi murmushi tace "Ina kwana" dan dariya Lamin yayi sannan ya amsa tareda kallon Nafisa da Lauren, gaisawa sukayi Nafisa na magana cikin nutsuwa wanda se da N

a'iman tadan kalleta dan mamaki, basu dade ba akayi kiran jirgin su, a first class suka zauna amma seats dinsu Na'iman daban da nasu Ahmad shida Lamin, within 3 hours din suka isa Rome, Na'ima nata kallon city din through window...kamar yanda Nafisan ta fa

da din ne kuwa, a wani tsadadden Beach resort Ahmad ya kama musu babban daki me hade da falo har da balcony da ke facing beach me ban sha'awa, sai da ya tabbatar sun shiga dakin nasu sannan ya juya zai koma nashi masauqin, shigan su dakin Nafisa ta wullar

da jakanta tayi tsalle tareda kifewa kan gadon tace "Wow...this is life" Lauren sai videon dakin takeyi itama bakinta yaqi rufuwa tace "This is beautiful", tafiya wajen balcony Na'ima tayi ta dafa rail din tana kallon cikin resort din cikin ban sha'awa, da

n kallon qasa tayi sai ta ware Ido tana murmushi da dan mamakin ganin Ahmad dake kallonta, yana tafiya da baya da baya tareda dago mata hannu alamun bye bye, daga masa nata hannun tayi tana fadada murmushinta har hakoranta na bayyana, sai sannan ya juya ya

cigaba da tafiya tareda da sa hannuwansa a aljihu sai ta tsaya kallon bayansa bata ko kifta ido tanajin zuciyarta na amsawa da abunda takeji akansa....

Har dare basu fita daga dakin ba sun baje anan falon sai ciye ciye suke suna hira, washegari ma da suk

ayi waya da Ahmad da safe sai yace musu

yana da aikin da zeyi suyi hakuri baza su gansa ba, Nafisa tace "Yaya ai dama aiki kazo yi, mu kuma hutu" yana murmushi yace "Ku huta Nafisa" tayi dariya Na'ima na girgiza kai tana murmushi, haka suka wuni a beach ra

nan Lauren na ta musu video a bakin sea na beach din, babu yanda Nafisa batayi ba dan Na'iman ta shiga ruwan amma taqi, haka tana ganinsu suka rinqa video acikin sea din, har abincin da zasuci a restaurant din sai Lauren tayi video'n sa, wanda hakan ba qar

amin ba wa Na'ima mamaki yake ba tana ganin qoqarin content creators, har dare babu labarin Ahmad sai dai waya da sukeyi, washegari ma haka suka wuni gurin shopping wanda Ahmad dinne ya aiko musu card dinsa, hannunsu cike da shopping bags suka koma masauqi

nsu, A kwana na ukun ne da dare ya kira Na'ima bayan ta fito daga wanka ahankali tace "Aiki ne ya maka yawa?" daga daya bangaren Ahmad yadan sosa girarsa da yatsa yana kallon laptop din da yake aiki da ita a gabansa, sai ya sauke numfashi yace  "I'm almost

done in sha Allah" ta gyada kai bata ce komai ba, sai ya sake cewa "I'm trying to finish everything soon, so we could have time together Babe" sai sannan tace "Allah ya taimaka" da haka sukayi shiru, can Ahmad yace "Can i video call you?" da sauri ta kall

i towel din da ke daure a jikinta tace "No..um..um" yana murmushi shima a hankali yace "Are you wearing your night dress?" tace "No..it's, uh.." sai ta daure kawai tace "Nayi wanka ne" shiru yayi yanajin wani sauyi a yanayin sa, kawai sai ya kashe wayan, d

ago wayan tayi daga kunnenta jin shiru sai taga kiran ne ya katse ashe, kawai sai ta ajiye wayan ta nufi jakan kayansu zata yi shirin bacci dan har sannan su Nafisa basu dawo daga restaurant din cikin resort din ba....

Basu sake waya ba sai washegari da d

are ya kirata, da ta dauka yace "I'm outside, can you come out?" ta gyada kai tareda cewa "Okay" sai da ta sake shiri ta dan fesa turare sama sama sannan ta fice, a lobby ta gansa tsaye sanye cikin black three quarter da T-shirt me dogon hannu, hannunsa da

ya cikin aljihu dayan kuma yana danna wayarsa, dago kai yayi suka kalli juna sai ya dan yi murmushi, sai da ta qaraso gabansa sannan yace "How i missed you Babe" cikin kunya ta juya kanta tana murmushi, sai yace "Should i order us food?" ta girgiza kai tac

e "Na qoshi" ya gyada kai, ta sake cewa "kaifa? bakajin yunwan" yace "i'm okay" da haka suka fita wajen resort din suka nufi can bakin ruwan beach din suna tafiya a hankali, Ahmad ne yafara magana tareda kallonta, yace "Can i ask you something Na'eemah?" t

a kallesa itama tace "Yes" yace "Shekaru nawa kikayi da ex husband dinki?" sai ta kauda kai tana kallon sea din tace "About four years" ya gyada kai sannan ya sake cewa "What about kids? kin taba haihuwa dashi?" dan stiff Na'ima tayi na tuna Bilal bai taba

saninta ba ma balle ta haihun, sai tayi kasa da kanta tana girgiza kai alamun "A'a", ganin kamar mood dinta ya fara chanjawa yasa Ahmad barin maganan, yace "Do you like Rome?" ta juya ta kalli resort din tace "I love it, the place is beautiful" yace "Zamu

dawo mu kadai watarana, tunda kinaso" tayi murmushi tana kallonsa sai ya miqo mata hannunsa yace "Here, mutafi kar sanyin ruwan nan yasaki mura" ta gyada kai tareda kama hannun nasa suka bar bakin ruwan tareda komawa cikin resort din zuciyarsu cike da ann

ushuwan kasancewa tare da junansu...

Sai da suka qara wasu kwanaki biyar suna hutawansu a Rome kafin wani tafiyan Ahmad din zuwa Venice ya taso masa, zuwa sannan duk wani ancient gurare sai da su kaje, siye siye dai kam sunyi shi da card din Ahmad har s

un gaji, ana gobe zasu tafi shima tareda dasu Ahmad da Lamin din suka fita, wani finest restaurant in town din suka je cin abinci suka sha hira cikin raha,  washegari da zasu koma Ahmad sukazo kaisu airport dan shida

Lamin din zasu wuce Venice sai wani sat

in zasu koma London, A airport din Na'ima sai kallon Nafisa take tana danne murmushi ganin yanda take sunkuyar da kai suna magana da Lamin, Ahmad dake gefenta sai ya kamo hannunta ya rada mata "They'll make a good couple, Lamin is a good guy" bakin Na'ima

kamar ze yanke dan murmushi tana kallonsu, gani tayi Lamin ya dan sunkuyo yana fadawa Nafisan wani abu sai ta fara dan dariya tana rufe bakinta da hannu, Lauren ce ta qaraso gurinsu hannunta riqe da cocktails ta miqawa Nafisan sannan ta kawowa Na'ima ta ka

rba tace "Thank you Lau" sai ta gyada kai sannan ta kalli Ahmad tana murmushi tace "Thank you so much for this trip, it's surely unforgettable" ya dan girgiza kai yace "No thanks", sai da ta koma gurinsu Nafisan sannan Na'ima ta kallesa zatayi masa godiya

sai taga ya saka yatsansa a baki alamun tayi shiru,  da aka kira jirginsu suka yi sallama zasu tafi,  sai ta juyo tana kallonsa yana tsaye shida Lamin din sai ya daga ma ta hannu yana murmushi yakai hannunsa kunne alamun "Sai munyi waya" ta gyada kai cikin

sanyin jiki ta juya suka tafi....

Bayan sun koma London nan gidan Anty Amnah suka fara tsumayin lokacin graduation din nasu wanda ji suke kamar lokacin bazai zo ba, dan suma suna son komawa gida hakanan, Ahmad ma bai cika satin ba ya dawo a kwana na bi

yar, ranan da ya iso gidan Amnah'n ya fara zuwa yasamu daga ita sai Na'ima dan ko twins ma sun fita tareda Abban su, da suka gaisa anan falon sai ya miqe akan zai tafi, da tayi masa tayin abinci ma yace ya qoshi, sai da ya qarasa gaban motan sa sannan yayi

texting Na'ima, tana zaune falon tagani, da farko kunyan magana da Anty Amnahn tayi sai can ta daure ahankali tace "Anty zanje yana kirana" Anty Amnah na murmushin tace "Je ki abunki daughter" ta miqe tana gyara veil din jikinta ta fita, bin ta da kallo A

nty Amnah'n tayi har sannan tana murmushi, dan lamarin nasu na burgeta, tana matuqar son alaqan tasu takai da gaci...

Da ta samesa a wajen suka gaisa sai yace "Babe ki rakani restaurant inci abinci" sai ta dan ware Ido tace "Yanzu fa aka gama maka tayin a

bincin" ya gyada kafada yace "I want to have time with you" da haka ya bude mata front seat ta shiga sannan ya shiga ya tada motan suka tafi, tun kafin su qarasa restaurant din ya nemi wajen parking dan cikin gari ne tsundum jama'a sai bustling suke kowa n

a harkan gabansa, a kafa suka taka zasu qarasa, sai da suka je daf da restaurant din kiran Mamma ya shigo wayan Ahmad din, bayan ya ciro wayan daga aljihu sai yace da Na'ima "Sorry i have to take this" ta gyada kai, yana cikin wayan ta masa alama da hannu

akan zata shiga cikin gurin kafin ya gama, sai ya gyada ma ta kai ta juya ta shige restaurant din, yana nan tsaye yana waya sai wani ya zo ya wuce ta gabansa zai shige restaurant din, dan binsa da kallo Ahmad yayi sannan ya cigaba da amsa maganar da Mamma'

n ke masa, ba'a fi minti biyu ba Na'ima ta fito a rikice daga cikin restaurant din Bilal ya biyo bayanta yana kamo gyalenta yace "Ki tsaya ko in ji miki ciwo wallahi" Ahmad bai qarasa Jin ma abunda ake fada a wayan ba ya taho da hanzari ya tura Bilal din b

aya da karfi yana cewa "Back off Man, who are you?" da sauri Na'ima ta miqe bata ma san ina take nufa ba, sai Bilal ya ture hannun Ahmad din daga qirjinsa da bacin rai shima yace "Kai zan tambaya, who da f"ck are you?" Ahmad was taking aback with suprise d

a kalman Bilal din, gashi turawan da ke wucewa suna kallonsu sai ya juya yaga Na'ima na tafiya da sauri sauri tana gyara gyalenta, hankali a dan tashe ya bi bayanta, shima Bilal ganin hankalin mutane yadawo kansu harda mutanen dake cikin restaurant din ne

yasa bai bi bayansu ba ya tsaya...da sauri Ahmad ya iddata tana tafiyan, ya kai hannunsa zai riqe nata ta kwace hannunta da

qarfi tace "Don't touch me Bilal" sannan ta juyo taga Ahmad, ganin hawaye a idonta yasa hankalinsa tashi, ya kwantar da murya yace "

Babe don't cry here, muje mota" sai sannan ta fara bin mutanen dake zirya a wajen da kallo, ahankali ya sake cewa "Not here Na'eemah" sai ta gyada kai tafara goge hawayenta suka juya, idon Ahmad ne ya fada cikin na Bilal dake tsaye a bakin restaurant din h

ar sannan yana kallonsu fuskar nan kamar hadari, Ahmad na kallon cikin idonsa ya miqa hannusa ya damqe hannun Na'ima da take kallon Bilal din itama, sai ya juya ya tafi cikin bacin rai, tana riqe da hannun Ahmad suka qarasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login